ƊAURIN ZUCI

Chapter 2

by @maryamstar248

***
***

Chapter 2
Daga faɗin haka sai ya soma disashewa daga madubin yana komawa ainahin kalar shi.

Da wani irin sauri mutumin ya tashi ya shiga furta wasu kalmomi baƙar fuskar shi zagaye da nishaɗi....
Alhaji Abdullah MAKAFA kenan, azzalumin mutum wanda ya maida cuta da zalunci abin yin shi, indai a fannin muginta ne za'a same shi a layin farko.
   Riƙaƙƙeb ɗan siyasa ne wanda ake damawa da shi ta fanin mulki, sannan kuma shahararen ɗan kasuwa wanda sunan shi ke yawo a cikin jerin manyan ƴan kasuwa, sai de kuma kasuwancin naci haramtacen kasuwanci ne, domin kuwa babban dila ne ta hanyar dafarar miyagun ƙwayoyi da kuma safarar yara zuwa sauran ƙasashe suna karuwanci.

A fanin siyasa shine na hanun daman president Murtala Usman, shi ke bada shawarar a fanoni da dama a zahiri, a baɗini kuma shi ke gudanar da mulkin gaba ɗaya domin president Murtala da taimakon MAKAFA ya samu hawa karagar mulki.
   (Yawancin abin da ke faruwa kenan a ƙasarmu, wanda ke mulki daban wanda ke karagar mulki daban Allah ka dube mu ka bamu ba dan aiyuka ko halayenmu ba ka ba i adalan shuwagabanni na ƙwarai masu tsoronka waɗanda zasu sauke nauyin haƙƙinmu da ke rataye a wuyansu amin😭🤲).

Ba a iya nan MAKAFA ya tsaya ba, a fannin tsafi da bokanci ma ba'abar shi a baya ba, domin kuwa gawurtar shi takai matakin da har ungiyar asiri ya kafa wadda yake jagoranta ta ƙarƙashin ƙasa da taimakon wasu baƙaƙen aljannu daya mallaka.

A taƙaice dai sunann MAKAFA shine sunan da yake yawo ako ina a faɗin ƙasar nan.
    Ku biyo ni sannu a hankali zamu warware muku zaren labarin.

Cike da nutsuwa kamar bashi ya gama ɓaɓɓakar dariya ba ya soma saukowa daga kan matattakalar, zuwa parlon ƙasa wanda ke cike da kayan alatu na more rayuwa, kan shi tsaye yayi hanyar dinning room yana saita fara'ar fuskar shi.
   Wata fara tas ɗin macece ce me tsananin kyawu wacce sam bata yi zubi da bahaushiya ba zaune akan kujerar dinning ɗin, yayinda aka cike kan table ɗin da launin abincika iri daban-daban.
    Sanye ta ke cikin shiga ta alfarma, dogon wuyanta ya sha sarƙar ɗanyan gold, matar ta kai ajin ƙarshe ta fanin kyawun halitta.
   A kan fuskarta kuwa wani yanayi ne me wuyar fassara.

Tun sanda ta soma jiyo ƙaƙƙarfan takunsa, can ƙasan zuciyarta ya soma rawar mazari, yayinda zufa ta soma yayafo mata a kan goshi, bata nuna yanayin tsoro, fargaba gami da tashin hankalin da take tsintar kanta a du sanda ta yi tozali da shi ba, ta ɓoye hakan ne saboda ƙara tabbatar masa da ta yarda da shi ɗari bisa ɗari kamar yanda ya ke fatan samu daga gareta.

Hajiya Rimsha Zayd kenan balarabiyar mace gaba da baya,  kuma mata ga Abdallah MAFAKA wacce ya aura shekaru huɗu kenan, ba wai ya aureta kawai don zallar soyayya ko sha'awa ba, ya aureta ne don cikar muradansa domin kuwa ƙungiya da aljanun shi sun tabbatar da ita ce mahaɗin dukanin nasarorinsa taurarinta masu haske ne ƙwarai da gaske muddin ya mallaketa zai samu cikar burukansa babu shamaki.

     Sai da ta danne yanayinta sannan ta ƙaƙali sassanyan murmushi ba tare da ta kalle shi ba ta gaisar da shi.

Sai da ya ƙura mata ido na ƴan sakanin sannan yaja numfashi ya sauke bai tankata ba yaci gaba da aika lafiyayyen girkin da aka jere.

Bata sake motsi ba tun daga zaman shi wajen, kanta na ƙasa tana yaƙi da zafafan hawayen da ke shirin ɓalle mata.

Sosai ya cika narkeken tumbin shi sannan ya tashi bayan ya goge hannun shi da tissue ya miƙe tsaye yana shafa tunbinsa daya ƙara girma kamar na me cikin wata tara.

Zagayawa yayi tare da ɗaga kantareren hanun shi ya ɗago ta tsaye, aiko sai yayi wani rusheshe a gabanta kaya guda, ita kuma ta fito ƴar tsut, duda itama ba daga baya ba wajen tsayi da cikar halitta.

    Jan hannunta ya soma yi yana tafiya da ita baice komi ba  kai tsaye ya haura sama da ita ya nufi ƙofar wani ɗaki.


Du yanda ta so ta haɗiye kukanta kasawa ta yi, sai da ta sake shi tare da ƙoƙarin soma turjewa tana magiya cikin harshen larabci.

Da iya ƙarfinsa ya jefata cikin ɗakin tare da saka lock ya rufe ya nufeta gadan-gadan yana soma rage tufafin jikin shi.

Sosai ta daku a hanunta amma tsabar kaɗuwa da abin da ta fahimci yana shirin aikata mata ya saka ta soma kaluben wajen ɓuya tana kuka cike da firgice, rintse idonta ta yi daga kallon baƙaƙen inuwar da ke tattare da shi suna firgitata, a zahiri ba siffar shi take gani ba, siffar halitta mummuna me firgitarwa ta ke gani, yana sake doso ta tana sake ruɗewa tana neman mafaka, hausa turanci da larabci ta dinga haɗawa tana yin du addu'ar  da tazo bakinta.

   Yayinda wannan yanayin da take shiga ya sake hasala Makafa ya damƙi kafaɗarta a cikin hannunya ya ɗagota yana jijjigata gami da yi mata tsawa.
   Ita kuwa Rimsha gaba ɗaya ta sake tsorata domin ba hannu taji ya riƙe ta ba, wani abu ne me tauri kamar itaciya kuma me cike da ƙarfi, yatsunsa kuma ta jisu tamkar   kaifin wuƙa me dafi, hakan ya saka ta sake rikicewa musamman daya daka mata tsawa.

Da ace Makafa yasan abin ban tsoron da Rimshake gani tattare da shi da ya dinga sassauta mata a wasu lamurran musamman a yayin kusanta....

*****
Yawo take da idon ta tana ƙarewa ɗan ƙaramin ɗakin wanda ko arziƙin ƙyaure bai samu ba, bama wannan ne damywarta ba yanda taga ƙanunun ƙwari na yanyame jan kwan nepar daya haske ɗakin, wanda hasken ya yi mata wani iri a ido, a karo na babu adadi ta kai hanunta tana sosa wajen da yagi bororon lafcecen cizon sauro, kamar zata fashe da kuka ta kalli inda yake a zaune.

Gaba ɗaya hankalinshi na kanta ita ya ke kallo tun tsayin lokacin da suka kasance  tare a ɗakin, wannan launin me firgitarwa na nan daram a idanuwansa masu kaifi a gareta, da sauri ta ɗauke daga kallon shi gabanta na dokawa fiye da kima.

Itafa tun usul kalar ja bata burgeta, ba kasafai take amfanin da abu me launin ja ba, ba zata mance wata rana da wani ɗan shaye-shaye da ya sha yayi tatul ya firgitata da jajayen idanuwansa daga ranar bata sake gigin kallon mazan waje ba direct bare har su haɗa ido, launin idanuwan shi na ɗaya daga cikin abin da....✍🏻

Dan Allah kuyi haƙuri yau page ɗin ɗan kaɗan ina cikin damuwa amma in sha Allah zuwa safe zan baku another page.


Dan Allah ina barar addu'ar kuyi mahaifina da Allah yayi mashi rasuwa yau watanni takwai kenan Allah ya jiƙanshi ya gafarta mashi tare da sauran al'umar musulmi baki ɗaya Allahumma amin.

@all 
MARYAM STAR.