MEERAH

015

by @oumfatima33

*MEERAH*

      *015*


    "Muje office muyi magana." Doctor ta faɗa wa Nawaz sannan ta fice. Ajiyar zuciya ya sauke shima yabi bayanta. A ofishinta ya same ta zaune saman kujera. Wuri ta nuna masa ya zauna sannan ta fuskance sa tace.

    "Kenan dai ba ƙanwarka bace kamar yanda ka sanar dani?." Ta yi masa tambayar tana tsare sa da ido. Ajiyar zuciya Nawaz ya sauke sannan yace.

    "Ƙwarai kuwa ba ƙanwata bace, na haɗu da ita inda wasu ɓata gari ke ƙoƙarin cutar da ita ne. Lokacin dana kawo ta kuma aka tambaye ni kawai sai nace kanwa ta ce don a bata kulawar data dace." Ya mata bayani cikin natsuwa. Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace.

    "Ka yi abinda ya dace kam, kana da zuciya mai kyau gaskiya. Kuma gashi ka yi sa'a ƴar manyan mutane ka taimaka wa." Doctor tayi maganar tana murmushi. Murmushin kawai shima ya yi sannan ya ƙara mata godiya da sallama ya miƙe ya fice, ɗakin da aka kwantar da Meerah ya koma don ɗaukar kayan breakfast ɗin da ya taho mata da shi, wan da bai samu damar bata  shi ba saboda ƴan gidansu daya tarar sun zo.

    Gadon da ta kwanta ya bi da kallo, yana jin wani abu mai kama da kewa yana kama shi. Wani ɗan abu ya hango a saman filon da ta kwanta a kai, a hankali ya shiga takawa zuwa gaban gadon. Hannu ya saka ya ɗauki abin ya shiga duba wa yana son ganin ko miye.

   Ƙaramin ribbom ne irin na ɗaure gashi ya gani, cikin aljihunsa ya saka shi sannan ya ɗauki basket ɗin kayan breakfast ɗin ya fice a ɗakin. Kai tsaye gida ya koma don mayar da kayan breakfast ɗin kafin ya wuce studio, saboda yana son su tattauna da JB a kan maganar kudin da aka biya su na waƙar birthday da suka je suka gabatar.

   Da sallama ya shiga gidan nasu dake a tsaftace komai yana muhallin da ya dace, Daga cikin ɗaki Umma ta amsa masa tana cewa.

    "A'a Yayansu har ka dawo da wuri haka? Yaya mai jikin?." Ta jera masa tambayoyin gaba ɗaya, ƙarasa wa ya yi cikin madai-daicin Plan nata da yake a gyare tsaf yana tashin ƙamshin turaren tsinke da aka kunna.

   Zama ya yi a saman kujera yana sauke ajiyar zuciya sannan ya ɗora da bawa Umma amsa yace.

    "Eh Umma na dawo, mai jiki kuma Alhamdulillah taji sauƙi." 

   "Masha Allah, Allah ya bata lafiya." Umma ta kuma faɗa, basket ɗin da ya ajiye tabi da kallo ganin ba'a taɓa komai ba tace.

   "Yaya kuma ka dawo da abincin?." Numfashi ya furzar sannan ya bata amsa da cewa.

   "Lokacin da naje na samu Iyayenta sun zo tafiya da ita ne." Ajiyar zuciya Umma ta sauke tace.

   "To ai shike nan, Allah ya kiyaye gaba. Sai ka samu ka karya kai ɗin tunda baka ci komai ba ka fita dama." Tana kammala faɗa ta ƙwala kiran Raihana ƙanwarsa wacce ke bi masa, wannan shekarar ta kammala secondary tana zaune a gida ne kafin a sama mata makarantar da zata ci gaba.

   Ba'a jima ba matashiyar budurwa mai matuƙar kama da Nawaz ɗin ta shigo da sallama.

   "Yaya har ka dawo ne?." Ta tambaya lokacin da take zama kujerar dake kusa da shi. 

   "Eh na dawo, baki wuce wurin koyon ɗinkin bane?." Ya bata amsa haɗi da mayar mata da tambaya.

   "Yanzu nake shirya wa Yaya." Ta bashi amsa sannan ta mayar da kallonta ga Umma tace.

   "Gani Umma."

      "Kizo ki haɗa wa Yayanku abin kari." Umma ta faɗa tana miƙe wa ta nufi uwar ɗakinta don ɗaukar wayarta da aka kira. Raihana ta kalli Nawaz tace.

    "Yaya a haɗa maka wannan ɗin ko." Amsa ya bata da.

   "Eh." Kawai ya zaro wayarsa ya amsa kiran JB dake shigo masa. Raihana kuwa tsuguna wa ta yi ta shiga fito da kayan dake cikin basket ɗin, tea flaks ne sai ƙananun kofuna guda biyu. Sai madara pik ƴar leda guda biyu da Milo shima na leda. Sai ƙaton bread a ciki. Sai kuma ƙaramin Food flask da aka zuba jalof ɗin macaroni wanda suka yi a gidan na karyawa.

   Shayin ta fara haɗa masa ta miƙa masa ya karɓa, a hankali ya furta.

   "Thank you Sisi." Murmushi Raihana ta yi masa tana jin ƙaunar ɗan'uwanta sosai a cikin ranta, don shi ma yana matuƙar son su da kaunarsu. Yana kuma bakin ƙoƙarin sa wurin ganin ya inganta rayuwarsu baki ɗaya. Ledar bread ɗin ta buɗe ta ajiye masa a gabansa tana cewa.

   "Na saka maka Macaronin ne Yaya?." 

   "No, wannan ma ya isa, Abba ya fita ne?." Ya bata amsa haɗi da tambayarta Abbansu. Amsa ta bashi da cewa.

   "Eh bai jima da fita ba ka shigo."

      "Okay." Kawai yace, ya mayar da hankali ga abincinsa. Sai da ya kammala karyawa sannan ya miƙe don wuce wa, dubu ɗaya (1k) ya ciro ya bawa Raihana kuɗin adai-daita sahu don zuwa wurin da take koyon ɗinki. Shine ya sama mata wurin ta fara zuwa kafin a samu a sama mata makaranta taci gaba, don a halin yanzu shima karatun yake yi. Kuma babu damar ɗaukar nauyin su su biyun.

   Amma duk da haka bai barta haka ba, koda ya fahimci tana da ra'ayin ɗinkin don tana hawa tsohon keken Umma da ta kasance tsohuwar tela a da, sai dai a yanzu bata iya ɗinkin saboda girma da kuma rashin lafiyar ƙafafu da take fama. Shine Raihana take hawa tana jagwal-gwala  ɗinkin yara a kai.

   Da yaga hakan sai ya sama mata wata makarantar koyon ɗinki da aka buɗe ta fara zuwa, saboda ko babu komai shima ɗinkin idan ta koya zata taimaki kanta har ta taimaki wani nata, tunda sana'a ce mai kyau. Idan result dinta ya fito aka samu dama sai taci gaba da karatun.

   Sallama ya yi wa Umma wacce ta fito daga uwar ɗakinta bayan ta kammala wayar da aka kira ta.

   "Zan wuce Studio Umma." Nawaz ya faɗa yana duba agogon wayarsa.

   "To shike nan Allah ya tsare." Ta bashi amsa sannan ta juya kan Raihana ta miƙa mata kuɗin data fito da su tace.

   "Idan an taso ki biya ki yi mana cefane." Karɓa Raihana ta yi tana cewa.

   "To Umma, na wuce nima."

       "Allah ya tsare." Ta bata amsa sannan suka fice tare da Nawaz....


××××××××××××

   *Meerah*

       Kai tsaye gida muka wuce kamar yanda na buƙa ta, don da farko Dady cewa ya yi ko zamu wuce asibitin da muke ganin Doctor a ƙara duba ni. Shagwaɓa na saka masa a kan na warke ni dai a mayar da ni wurin Momyna.

   Bayan mun isa gida Inspector Alim ya musu sallama yace zai koma idan na samu natsuwa zai buƙaci gani na domin ya yi min tambayoyi a kan abinda ya faru. Yace shima Nawaz ɗin zasu gayyace sa don amsa tambayoyin. Alkairi mai yawa Abby ya masa yace babu matsala, idan na samu natsuwa zai iya zuwa ya ganni. Da wannan ya koma wurin aikinsa, mu kuma muka shige ciki.

    Duk yanda nake jin jikina babu ƙwari ina haɗa ido da Momy na saki hannun Dady na ƙarasa da ɗan guduna na, ita ma tana gani na ta miƙe tsaye ta buɗe min hannu, ina zuwa na shige jikinta na fashe da kuka. Ita ma hawayene suka cika mata ido, da ƙyar ta shanye su ta rungume ni tana cewa.

   "Ina kika shiga ne Auta? Ina fatan dai babu abinda ya same ki? Yaya jikin naki? Kin ji sauƙi dai ko?." Ta jero min duka tambayoyin tana ɗago ni daga jikinta ta shiga dudduba jikina." Wasu irin hawaye ne suka ƙara sauko min, ina jin tsananin ƙaunar Mahaifiyata tana ƙara ratsa ni.

   Gaba ɗaya mutanen dake Palon babu wanda bai ji tausayin Momy ba, da ƙara jin-jinawa girman soyayyar Mahaifiya ga ɗanta.

   (Allah Sarki Uwa mai daɗi duk wan da ya rasa Mahaifiya a rayuwa ya rasa babban bangon jingina, Uwa ita ce mutum ta farko da take shiga tsananin damuwa idan wani abu ya samu ɗanta. Zata iya jure komai, zata iya sadaukar da komai domin ta bawa ɗanta kariya. Allah ka saka wa Iyayenmu da alkairi, ka biya musu dukkanin buƙataunsu na alkairi, ka yi musu sakamako da gidan aljanna. Allah ka bamu ikon yi musu biyayya, da kyautata musu, amin.)

    "Na samu sauƙi Momy." Na bata amsa ina ƙara shigewa jikinta tamkar zan koma ciki, zaunar dani ta yi saman kujera tana cewa.

   "Zauna ki huta, kafin a haɗa maki ruwa ki yi wanka." Zama na yi a hankali, sannan na shiga gaishe da su Mamy Safiya tare da Mom ɗin Zeezee da suke yi min yaya jiki. Zeezee kuwa inda nake zaune ta ƙaraso ta rungume ni, hawaye na zubo mata. Cikin kuka tace.

    "Sannu Bestie, yaya jikin naki? Allah ya sa dai babu abinda ya same ki?." Rungumeta na yi nima ina mata murmushi nace.

    "Ke babu komai fa, na riga na warke." 

    "Na gode Allah." Ta faɗa murmushi da ajiyar zuciya suna ƙwace mata lokaci ɗaya, kowa dake wurin sai da ya murmusa saboda irin yanda tayi maganar tana sauke ajiyar zuciya. Yamutsa fuska na yi ina rintse ido saboda kartawar yunwa da cikina ya yi.

   "Ki shiga ciki ki kwanta ki huta." Ya Ajmal ya faɗa idanunsa a kaina, kafin ya mayar kan Bintu da ta fito daga Kitchen yace.

   "Ki sama mata abinda zata iya ci."

   "To Ranka ya daɗe." Bintu ta faɗa tana juyawa ta koma Kitchen ɗin da ta fito.

   "Bari na haɗa mata tea ta fara sha kafin bintu ta kammala yi mata ɗanwaken fulawa, tunda tana son sa." Momy ta faɗa sannan ta mayar da kallonta ga Zeezee tace.

   "Daughter raka ta sama ina zuwa."

   "Okay Momy." Zeezee ta faɗa tana miƙe wa, kama ni ta yi na miƙe muka shiga haura sama a hankali. 


  *Ajmal....*

  Tun ɗazu idanunsa suna a kanta ne yana kallon ta ƙasa ƙasa, ta yanda ba wanda zai iya gane hakan. Duk wani motsinta a kan idanunsa take yinsa, don shi bai gamsu da cewa ta samu kulawar da ta kama ta ba a wan can asibitin. So yake ta huta sosai sannan ya kaita permanent Hospital ɗinsu a kara duba ta da kyau. Don ya ji tsoro sosai yanda ya ganta jiya a CCTV pottage ɗin da aka nuna musu.

   A kan idanunsa ta rintse ido sannan ta yamutsa fuska shi yasa yace taje ta huta, ya kuma buƙaci a sama mata abinda zata ci. Don ya lura bata yi breakfast ba, tunda a gabansu wan can guy ɗin yazo da breakfast ɗin kuma bata ci ba. Ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da ta ɓace wa ganinsa baki ɗaya.

    Sallama ya yi wa su Momy sannan ya wuce part ɗinsu don ya samu ya rama baccin da bai samu yi a daren jiya ba, saboda tashin hankali da fargabar da suke ciki. Yanzu da aka ganta Alhamdulillah sun samu natsuwa, duk da dai shi a ɓangarensa baya jin cewa zai samu natsuwar baki ɗaya har sai ya ga an kamo waɗan can yaran da suka yi gangancin taɓa ta. 

   Bayansa Sultan ya bi yana cewa.

   "Jira ni mu wuce Man." Jiran nasa ya yi har ya ƙaraso inda yake suka ci gaba da taka wa tare suna tattauna maganar abinda ya faru ɗin....


 *Nawaz....*

     Sai da ya tare wa Raihana aɗai-ɗaita sahu ta hau ta wuce sannan ya ci gaba da takawa a ƙafa zuwa Studio ɗin nasu, kasancewar bashi da nisa sosai don a cikin unguwar tasu yake. Kamar ko yaushe ya samu JB a gaban computer yana ta aikin editing ɗin waƙoƙin da aka ɗora a satin, tare da fitar da sababbin kiɗa masu daɗi.

   Hannu ya bashi suka gaisa kafin ya janyo kujera ya zauna yana lumshe ido haɗi da sauke ajiyar zuciya, haka kawai tunaninta ya tsaya masa a rai ya kasa barinsa. Musamman ma murmushin da ta yi masa lokacin da zata fita wanda ya tsaya masa a zuciya tamkar rubutu a kan dutse. 'ko yaya jikin nata yake? Ko taci abinci yanzu?.' tambayar da tazo masa rai kenan, sai dai bashi da mai bashi amsa.

   "Nawaz tunanin me kake yi  wai? Ko dai wani abu ya faru a asibitin ne?." Muryar JB ta dawo da shi daga tunanin da ya tafi, numfashi ya ja ya sauke ajiyar zuciya sannan ya bashi labarin abinda ya faru a asibitin. Ya ƙare maganar da cewa.

    "JB ashe ƴar gidan Hon. Abbas Mamman Gwangwazo ce yarinyar nan."

   "Kai haba dai?." JB ya tambaya bayan ya daka ta da abinda yake yi.

   "Ƙwarai kuwa, don tare suka zo asibitin shi da Yayansa Alhaji Bashir Mamman Gwangwazo mai B. M. G. MOTORS, tare da Yayunta guda biyu." Nawaz ya bashi tabbaci.

    "Haba biri ya yi kama da mutum, ai da ganin yarinyar nan dama ka san ba ƴar ƙananan mutane ba ce." JB ya faɗa yana jin-jina abin.

   "Ƙwarai kuwa, don har da securities suka je asibitin, don hani ni shiga suka yi da farko sai da na kira Nurse ɗin nan ta fito ta shiga da ni." Nawaz ya faɗa kamammiyar fuskar Jamal na hasko wa a cikin idanunsa. Musamman kallon da ya masa sau ɗaya ya ɗauke kai.

   "To ya ake ciki yanzu? Na san dai kana cikin alkairi dumu-dumu, don ba zasu maka ƙaramar kyauta ba." Cewar JB yana gyara zama. Ajiyar zuciya ya sauke yace.

   "Ka bar wannan maganar JB ni don Allah na taimake ta, ba don neman wani sakamako ba. Yayanta dai ya amshi lamba ta bisa umarnin Mahaifinsu, na san kuma dole za'a nemi ni a kan binciken mutanen da su ka yi ƙoƙarin ɗauke ta." Nawaz ya faɗa.

   JB zai yi magana yace.

      "Kaga mu bar wannan maganar yanzu dai mu tattauna abinda ya kawo ni, makaranta zan wuce ina da lectures 11:00 am."

   "Okay to ina jinka, menene ya kawo ka ɗin?." JB ya tambaya yana mayar da hankalinsa ga Nawaz. Shima zaman ya gyara ya fuskance sa yace.........

   Oum Fatima
     ***