DA JININSA NAKE RAYUWA
by @legendspen
Ba iya Ashraf ba har da Husna jin maganar ta yi kamar shigar ƙaya, wai taje gidan Ashraf, ina wannan ma ba zai yu ba, wannan matar ta shi mai kama da sakwara wallahi ba zata saɓo ba chab.
Kallon Mimi Ashraf ya yi, yana so ya yi magana amma bakinsa ya yi masa nauyi, Mimi ta sake cewa. “Kaji ni, ko ba kaji ba?”
“Mimi naji, amma ba zata iya zama anan ba?”
“Eyh ba zata iya ba, na ce taje gidanka ko? Ko tsoro kake ita uwar taka ta gidan ba zata zauna da ita ba? To ka ce mata umarnina ne idan kuma taƙi wallahi zata ga mummunan hukuncin da har kai sai ya shafa.”
“Kin burgeni Bilki, ai Asharaf baya buƙatar lallaɓawa, irin wannan umarnin zaki ba shi.”
Dade ta faɗa tana yi wa Mimi jinjina, sannan ta koma ga Ashraf ta ce.
“Idan ni ban isa da kai ba, ai na isa da ubanka shi kuma ya isa da kai, sai mu gani.”
“Mimi ni dai da ba gidansa ba, kin san dai wannan matar tasa wallahi, kuma ba mutunci take muku ba bare kuma ni, shi kan sa kina ganin yanda yake cin zalina bare kuma an haɗa da wannan matar tasa mai kama da sakwarar legas.” Wani ƙululun takaici ne ya tsayawa Ashraf a maƙogwaro, wai Jamila take cewa mai kama da sakwarar legas, ba gwanda Jamila ba a kan ta shi yanzu ai kallon da yake wa Husna gwanda kowa a kan ta, yarinya ko secondry ta gagara gamawa.
“Babu ruwanki da matarsa ai gidan yayanki ne, kar ki tanka ta duk abin da za ta yi miki.”
Dade ta faɗa, Mimi kuma ta ce.
“Idan kin mutunta ita ma zata mutunta ki, ki tashi ki ɗauko kayan da kika haɗa ku tafi.”
“Ni dai Mimi a'a dan Allah, wallahi ni tsoronsa nake ji, ba iya matarsa ba ce abar tsoro.”
“Ki tashi kije ki ɗauko jakar ki, shi ya isa ya ce zai dake ki ne, me kika yi masa.”
Tashi Husna ta yi, bata son jan zance da Mimi amma suna fita zata lallaɓa shi ya kai ta ko gidan su Hajjo ne cikin gari, wallahi ba zata iya zuwa gidansa ba. Sai bayan ta tashi ya ce.
“Mimi ki faɗa mata ta girmama mata ta, kar ta yi mata rashin kunyar da ta saba.”
Kamar jira Mimi take ta hau sababi.
“Ita matar taka girmama mutane take? Ko ganin mu take yi da mutunci? Idan kakai mata ita a hulaƙance dole ta ɗauke ta hulaƙane, idan a mutunce ka kai ta dole ta mutunta.”
Miƙewa Dade ta yi tana faɗin.
“Bilkisu Allah Ya ƙaddara saduwa, ni kam na yi nan.”
Tana faɗin haka ta fice ba tare da ta jira amsawar wani ba, ta tafi taje ta dira bala'i da ‘ya'yan Hajiya Babba.
Yana zaune kamar mutun-mutumi Husna ta fito tana han jakar da ƙyar, Mimi ta ce.
“Ku tashi ku tafi, nima da wuri zan kwanta sabida na tashi da wuri, Allah Ya tsare.”
Miƙewa ya yi, ciki ciki ya ce.
“Allah Ya kaiku lafiya.”
“Amin.” Ta amsa, Husna ma ta ce.
“Mimi Allah ya tsare.”
“Amin Husna, kar naji kar na gani.”
“In sha Allah.”
Husna ta faɗa, Mimi ta sake cewa.
“Ai ka kama mata kayan ko? Ashraf wai yaushe zaka fara tausayi ne a rayuwarka? Kai mace in dai ba matarka ba babu wadda kake tausayi kenan?”
Kallon ‘yar jakar ya yi, gaba ɗaya wannan nawa take da har sai an ɗaukar mata, hannu ya sa ya ɗauka ya rasa me ya sa Mimi take son haɗa shi da wannan yarinyar.
Husna ta so ta roƙeshi ya kai ta gidan Hajjo, amma suna fita girman kai ya hau kanta sai kawai ta yi shiru har suka isa wajen da ya ajiye motarsa, baya take ƙoƙarin buɗewa ya daka mata tsawa, ba dan taso ba ta buɗe gaban ta zauna. Haka suka fara tafiya Husna na kallon titi dan ita ko iska ɗaya bata so ta shaƙa tare da shi, wallahi mantawa take da shi, amma kwana biyu sai neman takurawa rayuwarta yake, a cikin zuciya ta ce.
“Aikin banza.” Tare da jan tsakin da bata san a fili ta yi ba, kallonta ya yi ya ɗauke ba ta isa ya kula ta ba, a haka suka ƙarasa gidan nasa babu wanda yake ce da wani uffan, Jamila ta window ɗin falon ta hangi mace a gaban motar mijinta, ba shiri ta ƙwalalo duka idanunta waje tana son ganin wace mai tsautsayin ce wannan, sai dai ganin Husna na fitowa taja wani dogon tsaki, a fili ta furta.
“Allah ka kashe yarinyar nan, na tsane ta wallahi, bana son ta ko kaɗan. Yanzu uban me tazo yi min gida kuma, har da shiga gaban motarsa wajen da ni ka ɗai yakamata na shiga.”
A can waje kuwa Husna ba ta yi ganganci cewa ya ɗaukar mata jaka ba, daman a can ma ba ita ta buƙata ba Mimi ce ta sa shi, nan kuwa babu Mimi dole ta kama kanta har Allah ya raba su.
Yana gaba tana binsa a baya suka shiga cikin falon, Jamila na zaune ta haɗe rai kamar wadda aka sanarwa saƙon mutuwa, mamaki ba tashi kashe ta ba sai da taga hannun Husna riƙe da jaka wadda ko ba ta tambaya ta san kayane a ciki.
“Honey, wannan abun fa?”
Ta faɗa tana nuna Husna, wadda wani takaici ya maƙure mata wuya, wai ita ake cewa wannan abun, cikin su waye ya yi kama da wani abu ma idan ba ita ba, gatanan kamar doya.
Ɗan haɗe rai ya yi, sannan ya ce.
“Bangane abu ba, yarinyar ce baki gani ba ko me?”
“Na ganta Honey, amma me take anan?”
“Mimi ce za ta je ganin likita, shine zata zauna anan kafin ta dawo.”
“What impossible, wallahi ba zata zauna ba.”
Jamila ta faɗa tare da shigewa cikin ɗaki, bayanta yabi daman ya san dole ya yi fama da ita, Husna kam yana shiga ta taɓe baki ita dai bata ga abin damuwa a kan Ashraf ba, ita daga mijin har matar babu na zaɓa a ciki kowa bakin hali, to su ci kan su ita dai babu wanda ya isa ta kula shi cikinsu wallahi.
Jamila na shiga ɗaki ta zauna a kan gado ta fara zubar da hawaye, me ya sa yarinyar nan take son fitinarta ne, wallahi ko ganin yarinyar nan bata son yi a rayuwarrta bata son alaƙar ta da mijinta kuma tasan wannan aikin Mimi ne ita ce ta turo ta sabida kawai a raba musu zaman lafiya su.
“Jamsy, me ya sa haka ne? Me kike yi anan?”
Banza ta yi da shi, dan wallahi tun kafin dare ma ya yi masa yazo ya sa 'yar mutane a gaba ya mayar musu da ita, dan ba zata zauna mata a gida ba, yarinyar da bata da kunya bata da mutunci.
Zama ya yi kusa da ita ya kama hannayenta duka ta yi saurin ƙwacewa da dukkan ƙarfinta.
“Karka ma fara, ni ba abin da zan ji, tun dare bai yi maka ba ka ɗauki yarinyar nan ka mayar musu da ita, dan ba zata zauna a gidan nan ba.”
“Jamsy ki tsaya mana ki saurare ni, Mimi ce fa ta bani na taho da ita, kawai sai na koma da ita na ce me?”
Ya faɗa rai a ɓace, gaba ɗaya ya fara gajiya da yawan surutun nan.
“Ka ce ba zata zauna ma a gida ba, suma sun san yarinyar nan ba kunya ba ne da ita, ni bana son tana raɓar mu wallahi.”
“Jamila, kin san abin da kike cewa? Mimi zan mayarwa da ita, kwana nawa ne za ta yi? Gaba ɗaya ba zata yi one week a gidan ba fa.”
“To ai itama Mimi ɗin ba dan Allah ta baka ita ba, ya zaayi ma ace zankaɗeɗiyar yarinta kamar wannan ba zata iya zama a gida ita kaɗai ba, to ta kuma gidan ubanta mana.”
“Enough Jamila, ya isa haka Mimi kike faɗawa wannan maganar? To na gama yanke hukunci zata zauna anan gidan, har Mimi ta dawo idan kinga dama ki zauna idan kinga dama ki yi duk abin da zaki yi, ko ni na faɗa miki son zaman nata nake yi ne?”
Tashi Jamila ta yi ta fita daga ɗakin ta shiga ɗakin da ke kusa da shi, tana shiga tasa key ta kulle ƙofar, ita dai Husna na tsaye a falo tana jiran a fito a bata ɗakin da zata zauna. Sai da ya ɗauki wajen minti goma sannan ya fito, wani kallon banza ya watsawa Husna sannan ya ce.
“Tsayuwar me kike anan?”
Turo baki ta yi gaba, sannan ta ce.
“Ina ne ɗakina?”
Jin maganar ya yi banbarakwai wai ɗakinta, hannu ya ɗaga ya nuna mata ɗakin da ke gefenta sannan ya ce.
“Ki yi using wannan ɗakin.”
Yana faɗin haka ya wuce, bata ce mai komai ba ta tura ƙofar ɗakin ta shiga, ɗakin a gyare yake tsaf ajiye jakarta ta yi a ƙasa ta kwanta a kan gadon, Allah Ya so ma ta yi salla a gida, kawai ta kwanta ta yi addu'a, sai bayan ta yi addu'ar ta kece da dariya, a fili ta ce.
“Yau su sakwarar legas babu bacci.”
Sai kuma ta ƙara tuntsirewa dariya, ita wallahi mamaki ma Jamila ke bata, wannan mijin nata waye zai iya da shi, ita dai da Allah Ya ɗaurawa ta yi ta fama, haka Husna ta yi bacci tana mamakin Jamila da haukanta.
Ashraf kam bazan ya yi da Jamila ya ƙyaleta zuwa safiya ya je ya rarrashe ta, shi bama gwani ba ne wajen rarrashi, shi fa har yanzu akwai abubuwa da yawa da ba zai iya yi wa mace ba, su wannan rarrashin da lallaɓawa gani yake bazai taɓa iyawa ba, ga abokansa nan su wani karyar da murya ga matansu shi bai ga abin da zai kai shi wannan zubar da girman ba.
Cikin dare wajen ƙarfe ɗaya ya tashi ya nufo ɗakinta, ya san lagonta kullum tana son jinsa a kusa da ita shi ya sa ya bari sai wannan lokacin. A ɓangaren Jamila kam tun tana saka ran shi yazo ya rarrasheta har ta ji shiru, ita dai ba zata zauna tare da wannan yarinyar ba, ko da a ce ƙanwarsa ce Uwa ɗaya Uba ɗaya ba zama za ta yi da ita a gida ɗaya ba, bare wannan kuma da ba wata kyakyawar alaƙa ce a tsakaninsu ba.
Jin shirun nasa ya yi yawa ya sa ta kwanta, amma gaba ɗaya ba haka ta so ba, sai dai kafin ta kwanta ta cire key ɗin da ta a jikin ƙofar, hakan ya sa da ya tashi cikin dare yana murɗa ƙofar ta buɗe ya shiga.
Bacci take yi kamar wata mara damuwa, amma cikin zuciyarta ranta a ɓace yake, ƙare mata kallo ya yi sosai, Jamila fara ce tas wanke hannu ka taɓa, tana da jiki amma ba irin lukutayen matan nan ba, sai da ba za ace mata siririya ba, akwai tsayi akwai ƙiba za ta yi ɗaya da rabin Husna a tsaye, shi kuma ta zarar sa da ita kaɗan ce, dan ma yana da kwarijini ya sa idan ya tsaya kusa da ita ake ganin shi sama da ita.
Kwantawa ya yi a kan gadon a hankali ya jawo ta jikinsa ya rugumeta, cikin barci ta fara shaƙar ƙamshin turarensa, a hankali ta buɗe idonsa ta kalleshi ya sakar mata murmushi tare da kai mata kiss a saman goshinta, a hankali ya fara magana cikin sanyi murya.
“Jamsy, ban ji daɗin abin da kika yi min ba, wannan fa umarnin Mimi ne fa, kina so na yi mata gardama ne? Idan na yi mata gardama wacce riba zan samu a rayuwa?”
“Amma Honey yarinyar bata da kunya kasani fa, zamanta anan zata takura mana.”
“Babu abin da zata yi mana, kuma na sa Mimi taja mata kunne sosai, ba za ta yi miki rashin kunya ba kin ji.”
“Honey kaman kana son zaman yarinyar a nan ko?”
Kallonta ya yi, bai taɓa tunanin wannan maganar daga bakinta ba, shi mene haɗinsa da son zaman yarinyar a nan? Bata san yanda yaƙi jinin yarinyar ba, yarinya bata da kunya ba mutunci tana abu kamar goyon gauro, uwa uba kuma ta ajiye karatu ta ce ba zata yi ba kuma an barta, idan akwai abin da yafi tsaya masa a rai shine rashin karatunta.
“Tunanin me kake?”
Jamila ta faɗa tana shafa sajensa, ya yi murmushi ya ce.
“Babu komai, kawai ina mamakin wannan tambayar taki ce.”
“Sorry My Love.”
Ya gyaɗa mata kai kawai, shi kuma ya sake rungumeta tare da kai mata kiss, ni kuma na yi gaba😂😂😂.
Washe gari Husna ba ita ta tashi ba sai wajen ƙarfe shida, wani dogon tsaki taja ta saba a gidan Mimi kiran sallah ne ke tashinsu, amma anan sai ta ji shiru da alama masu gidan ma basu ta shi ba, dariya ta kece da ita bayan ta tuna fuskar Jamila a jiya, ta ci wasu ƙananan kaya irin waɗanda ake yi wa miji kwalliayar dare da su, sai gashi ta shige ɗaki. A fili ta ce.
“Ƙila ma ko abincin dare ba ta ci ba.”
Ta sake tuntsirewa da dariya, sai da ta yi mai isarta sannan ta tashi ta shiga toilet ganin akwai toilet a cikin ɗakin, bayan ta yi sallah ta koma kan gado ta kwanta, bata koma bacci ba sabida gaba ɗaya bata saba da baccin safe ba, sabida a munjibir tun tashin safe ba a komawa, yanzu ne ma ta lalace amma da ko hutu suka dawo gida duk inda huɗu da rabi na dare take Husna ta miƙe.
Motsi motsi ta fara ji a falon, hakan ya sa ta miƙe ta shiga toilet ta yi wanka, bayan ta fito ta shirya cikin doguwar rigar ta wanu material wanda Yaya Abdul ya ɗinka mata kwanaki, yadika ya siyo ya bada a ɗinka mata a sabon gari wajen set goma sha biyu, kuma kowanne da ƙaramin veil ɗinsa.
Veil ɗin ta ɗaura a matsayin ɗan kwalli, bayan ta yi simple light make-up sabida zamanta a gidan Mimi kullum bata da aiki sai kwalliya, yanda take ganin Yaya Leemah na shiga da fita cikin kwalliya ko babu inda zata, ya burge Husna shi ya sa itama ta fara tun tana gajiya har ya zama jikinta sabida naci irin nata, ta yi kyau daidai abunta, ta kusa minti goma a jikin mudubi tana ƙarewa kanta kallo, ashe gaba ɗaya zaman da suke a munjibir cutar su ake, duk an disashar musu da kyansu, yanzu gashi take zama a nan take sa kayan da tasu kullum ganin kyanta take yi, gaskiyya wanda ya aure ta ya more, sai kuma ta yi shiru sakamakon tunawa da zancen da Abba ya yi mata, gashi ita bata son sake ƙaunar wani namijin a rayuwarta. A fili ta furta.
“Allah ka sanyaya zuciyar Abbana, Allah ka nesanta zuciyata da ƙara ƙaunar wani namijin, Allah idan Uncle Dee yana da rabon shiga addinika, ka rabautar da shi ka sake haɗa fuskokin mu da alheri, Amin.”
Ta shafa addu’arta ta fito, a lokacin da ta fito Jamila ce ka ɗai a falon tana ƙoƙarin shirya abinci a dinning, Husna ta tsaya daga gefe tana kallonta, tana ƙoƙarin shiga kitchen Husna ta ce.
“Ina kwana?”
Wani kallo Jamila ta yi wa Husna, sannan ta ce.
“Lafiya.”
A daƙile, Husna ta taɓe baki a fili ta ce.
“Gidanki na zo, ki yi abin da kika so.”
Sarai Jamila ta ji abin da Husna ta ce, taso ta koma ta kwashe ta da mari sai kuma ta tuna yanzu Mijinta zai fito, kuma ita ba girmanta bane ma mu sayar yawo da wannan yarinyar. Kofi daban da plate daban ta ware wanda zata bawa Husna ta dinga amfani da shi, dan ba zata iya sharing kayan amfanin da Husna ba, wace ma Husna.
Lokacin da ta fito daga kitchen ɗin shima lokacin ya fito daga ɗakinsa, Husna dai na tsaye a tsakar falo tana kallonsu, sai da ya ƙaraso cikin falon ta ce.
“Ina kwana?”
Ba tare da ya kalleta ba ya ce.
“Lafiya ƙalau.”
Husna ta taɓe baki a ranta ta ce. ‘Dan uban izzah.’ Ganin ya nufi Dinning Jamila ma ta nufi dinning ɗin ya sa Husna ma nufar dinning ɗin, wani kallo Jamila take wa Husna lokacin da take ƙoƙarin zama.
“Malama dakata, ba zaki zauna min a dinning ba, sannan waɗannan plate da cup ɗin su zaki dinga amfani da su har ki bar gidan nan, idan ma kin so zaki iya tafiya da su dan babu amfanin da zan sake yi da su.”
Jamila ta faɗa tana nunawa Husna faranti da kofin roba, wani irin kallon banza Husna ta yi wa Jamila, kallon mai cike da tambayar kin san abin da kike yi?
“Dake fa nake magana.”
Legendspen-Sayyid
***