MATAR GIDA PAGE 62
MATAR GIDA BOOK 2
SHUUKRAN/022
YOTA ASSOCAITION
P62
Karfe goma dai dai na dare Anty Aisha ce tare da Unaisa sai Mama zaune cikin ɗakin Mama,Anty Aisha da Mama sun yi jigum suna kallon Unaisa,da ƙyar Anty Aisha ta samu Unaisa ta yi shiru amma ta ƙasa cewa komai sai ajiyar zuciya da take saukewa a kai a kai,tambaya Anty Aisha ta jefo wa Unaisa a karo na babu adadi, ta ce ''me ya faru kin baro gidanki?" kasancewar yanzu an kawo nepa yasa Mama da Anty Aisha zubawa Unaisa ido suna kallon yadda ta yi ƙiba ga wani haske da ta ƙara,numfasawa Anty Aisha ta yi kafin ta ce ''sakin ki ya yi?" sai a sannan Unaisa ta ɗago ta kalle Anty Aisha da ƙyar ta iya furta ''a'a'' Anty Aisha ta ce ''to me ya faru tun ɗazu nake tambayar ki kin ki cewa komai me kike so na ce? aiy dole na yi tunanin sakin ki ya yi'' ta kare magana tana huci Mama da tun ɗazu take kallon Unaisa ta ce ''Aisha ina ganin mu barta ta huta in Allah ya kaimu gobe sai ta faɗa mana ko ma menene'' Anty Aisha da ranta ya fara ɓaci ta ce ''me zai sa mu jira har sai gobe Mama magana za ta yi,ta faɗa mana laifin me ta masa ya ƙurata gida,in ma ba laifi ta yi masa ba to ta buɗe baki ta yi magana ta faɗa mana dalilinta na zuwa gida,shigowa fa ta yi tana kuka kamar wacce aka yiwa mutuwa'' ''Aisha na ce a bar duk wata magana sai gobe ki duba yanayin da take ciki'' Mama ta faɗa tana mayar dubanta ga Anty Aisha jiki babu kwari Unaisa ta ɗago tare da mayar da dubanta ga Anty Aisha ganin yadda hankalin Anty Aisha ya tashi yasa Unaisa tattaro sauran gwaiwa ta kai hannu ta goge hawaye kafin ta gyara zama cikin muryarta da bai fita sosai saboda kuka ta ce ''korata ya yi saboda na siya mota'' cike da mamaki Anty Aisha da Mama suka mayar da duban su ga Unaisa wai ta siya mota ko dai basu ji da kyau bane Mama ta ce ''me ki ka ce?" ta yi magana tana kallon Unaisa da son jin tabbacin abinda Unaisa ta faɗa ita ko Anty Aisha tsabar mamaki ƙasa magana ta yi sai kallon Unaisa take kamar yau ta fara ganinta idon Unaisa ƙasa ta ce ''eh Mama mota na siya shine ya korani gida'' cike da mamaki Mama ta gyara zama gaba ɗaya kanta ya kulle wai ta siya ina ta samu kuɗi ''ban fahimta ba Unaisa ki ka ce kin siya mota,ko dai mijinki ya siya maki mota?" Unaisa ta na goge hawaye ta ce ''ni na siya'' Anty Aisha da haushi ya gama cikata ta tashi tayu kan Unaisa kamar zata daketa ta ce ''uban wa ya siya maki mota? ina ki ka samu mota?" Mama ta ɗagawa Anty Aisha hannu ta ce ''dakata Aisha zata yi bayani kar ki taɓa ta'' sosai Mama ta mayar da hankalinta ga Unaisa ta ce ''ki amsa tambayar da yayarki ta yi maki ina ki ka samo mota?" tsoro ya gama kama Unaisa ganin yadda lokaci guda hankalin Mama ya fara tashi kawai ta yanke hukunci faɗa masu komai,ɗakin ya dauki shiru na kusan mintina biyar Anty Aisha da Mama suna kallon Unaisa suna jiran jin abinda zata ce wani dogon numfashi Unaisa ta ja kafin ta gyara zama ta fara magana kamar haka ''shekaru biyu da suka wuce ƙawata Fadeelah da muke zuwa islamiyya tare ta sa na shiga kungiyar matan gida wanda ita ma yayarta Zainab ta sata cikin kungiyar,gaba ɗaya islamiyya babu wacce zata haɗa kanta da Fadeelah wayar hannuta ta fi tamu tsada suturar da take sa tafi tamu kyau da tsada,wanda hakan ya sa takr burgi ni naji nima ina son rayuwa irin nata,da fari na yi tunanin kuɗin sana'ar awarar mahaifiyarta take amfani da su wajen siyan abubuwa da take siya,sai daga baya na fahimci samari ke bata kuɗi,lokacin Audu yaron liman ke nema na,da na fahimci samari ke bawa Fadeelah ƙudi na riƙa tambaye Audu kudi kusan kullum,da fari duk abinda na tambaye sa yana bani a lakacin harna canza waya na siya sabbin takalma uku da hijabai biyu,daga baya ya fara canza ko na kira sai ya ga dama yake amsa kirana karshe dai ya rabu dani,wata ranar juma'a a ranar muna hutun islamiyya,na je gidan su Fadeelah na faɗa mata Audu ya rabo da ni ina tunanin ya gaji da yawan raƙon kuɗi da nake masa ne,a ranar na buɗe mata gaskiyar dalilin da yasa nake ƙawance da ita nan ta riƙa min dariya kafin ta faɗa min cewar ba kowanne namiji ake tambaya ƙudi ba, na gode Allah Audu bai nime komai daga wajena ba kawai ya rabu dani wasu mazan sai su nime lalata mace dan kawai ta ci masu kuɗi nan dai ta faɗa min gaskiya cewar akwai wata kungiya da take ciki wannan kungiyar aka haɗata da samari dake bata kuɗi da fari na yi tunanin ko wani abun suke marar kyau na ce mata a'a bazan shiga ba na hakura,da ta ga na tsorata sai ta faɗa min babu abinda ke haɗa su da samarin soyayya kawai suke amma a kungiyar ake haɗa su da samarin duk abinda nake so saurayin zai yi min,jin haka yasa na amince na ce mata na yarda zan shiga a ranar ta kaini gidan Hajiya Bilƙisu,ita ta yiwa Hajiya Bilƙisu bayani,Hajiya Bilƙisu ta ce babu damuwa za'a haɗa ni da saurayin da zai riƙa bani kuɗi a lokacin bata faɗa min dokokin kungiya ba kawai ta ce za a hada ni da saurayi sauran ƙa'idoji da dokokin ƙungiya sai bayan na yi aure za su hau kaina a lakacin ban yi wani tunanin ba na amince bayan sati biyu da faruwar haka Fadeelah ta faɗa min Hajiya Bilƙisu ta gayyaci mu taron kungiya da za a yi a unguwar barnawa gidan yayar Fadeelah Zainab,a wannan unguwar Muhsin abokin mijina ke zama tare da matarsa,a wannan ranar Ɗalha ya fara ganina,abinda ban sani ba shine Hajiya Bilkisu ta bada cigiyar matashi mai kuɗi ko mai rufin asiri a kungiyar shine Zainab ta ce da akwai wani mutumin dake yawan zuwa gidan abokinsa a unguwar su dake suna mutunci ita da matar Muhsin cikin dabara ta tambaye matar Muhsin sunan Ɗalha ita kuma ta faɗa mata a nan ne Hajiya Bilƙisu tasa aka yi aiki akan Ɗalha,ko wacce ranar Lahadi Ɗalha yake uni gidan Muhsin,ranar asabar ake taro gidan ƴan ƙungiya amma saboda ni aka mayar da taron gidan Zainab ranar Lahadi,ban san dalili ba aka yi ta tura ni gidan Muhsin da sunan saƙo har Allah yasa Ɗalha ya ganni tun daga wannan ranar muka fara soyayya,matar Muhsin ta so tona mana asiri inda ta fadawa mijinta cewar tana tunanin ina kungiyar matan gida shi kuma ya fadawa Ɗalha,bayan Ɗalha ya tambaye ni ko ina kungiyar na ce masa a'a kanwar Zainab ƙawata ce,Ɗalha ya yarda da abinda na faɗa masa tun da muka fara soyayya da Ɗalha duk abinda na nema ina samu daga wajensa,bayan bikin mu aka yi taro a gidana nan ne Hajiya Bilƙisu ta faɗa min dokoki ƙa'idojin kungiya'' shiru Unaisa ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta shiga faɗawa Mama da Anty Aisha dokokin kungiya kamar yadda Hajiya Bilƙisu ta faɗa mata ranar da aka yi taro gidan
Wani irin dariya Anty Aisha ta shiga ɓaɓaƙa ita ko Mama mutuwar zaune ta yi labarin da Unaisa ta basu yana mata yawo a kai kamar flim,duk waɗannan abubuwan da suka faru tana ina? yaushe aka yi hakan?tsawon shekaru biyu Unaisa na cikin wata kungiya ita bata sani ba kungiyar ma ta matan gidan da basu zaman aure,muryar Anty Aisha ne ya katse wa Mama tunani in da Anty Aisha ta ce ''kenan ranar bikinki dan ke suka zo?" a ranar na tambaye ki ki ka ce min ba ki san wanda ya gayyato su ba'' Anty Aisha ta ƙare magana tare da rintsa idanu ta ce ''bayan mun kai ki ɗakin ki a Kano babu yadda ban yi dake ki faɗa min alakar ki da matan gida ba ki ka ƙi faɗa min,bayan barin mu Kano kin kulle ni kin kulle Mama duka saboda matan gida'' wani irin murmushi da ya fi kuka ciwo Anty Aisha ta yi kafin ta ce ''saboda su kin rabu da dangin yanzu kuma za ki rasa mijinki wai tsaya tukuna ina ki ka samu mota kin faɗa mana komai amma ba ki faɗa mana yadda aka yi ki ka siya mota ba,hala albashi Hajiyar take biyanku?" Unaisa ta yi shiru bata ce komai ba Mama dake gefe ta daka mata tsawa ta ce ''ba ki ji abinda ƴar uwarki ta faɗa ba ina ki ka samu mota!!" lokaci guda jikin Unaisa ya dauki rawa cikin rawar murya ta ce ''lefena na siyar wa Hajiya Bilƙisu ita ta yi min hanyar mot... ba ta kai ga ida zancen ba Mama ta buge mata baki cike da mamaki da tsantsan ɓacin rai Mama ta ce ''me ki ka ce? hauka ki ke? ƙlau ki ke kuwa?" Mama ta ƙare magana cike da tsantsan ɓacin rai tun sanda Unaisa ta ce ta siyar da lefe Anty Aisha ta miƙe tsaye zumbur lefen kusan miliyan biyar ta saida saboda mota Anty Aisha ta daura hannu a ka ta shiga furta kalmar ''innalillahi wa inna ilaihi raji'un'' saida ta maimaita kalmar kusan sau huɗu wani tunani ya faɗo mata hakan yasa ta mayar da dubanta ga Unaisa ta ce ''me kuma ki ka bata bayan lefe?" gaba ɗaya Unaisa ta gama tsorata har sannan jikinta na rawa ta ce ''kayan kitchen'' Mama bata san sanda ta saki wani irin salati ba ta ce ''shikenan Unaisa kin kashe ni wallahi kin kashe ni har kayan kitchen?" Anty Aisha ta shiga jijjiga kai tana salati can ta nime waje ta zauna tare da mayar dubanta ga Mama da ta gama cika da mamakin Unaisa, shiru Anty Aisha ta yi na wasu ƴan sakanni kafin ta ce ''laifin ki ne Mama ke ce silar komai'' cike da ɓacin rai Mama ta mayar da dubanta ga Anty Aisha ta ce ''ki kiyaye ni Aisha kin dai ji na faɗa maki,ban son raini duk sanda yarinya ta yi rashin hankali sai ki ce laifi na ne zan saɓa maki fa kin ji na faɗa maki'' Aty Aisha ta yi murmushi kawai can ta kira sunan Unaisa ta ce ''Unaisa'' ta faɗa tana kallon Unaisa da kyau,Unaisa da ta gama tsorata ta amsa kiran cikin sanyin murya ta ce ''na'am'' Anty Aisha ta daura da ''wa ya tuka motar? ko kin iya tuƙi ne?" sai da Unaisa ta haɗe wani yawu tana gyara zama da ƙyar ta ce ''ni ce'' ta faɗa a tsorace tana kallon Mama da Anty Aisha cike da mamaki Mama ta ce ''ke kuma?yaushe ki ka iya mota?" ita dai Anty Aisha tsabar mamaki ƙasa magana ta yi kawai ta yi tagumi tana kallon Unaisa,labari Unaisa ta dauka yadda aka yi ta iya mota da yadda take zuwa makarantar koyan mota duk sanda ta fita da niyyar zuwa islamiyya ta faɗa masu,wani sabon salati Mama ta sake tana tafa hannaye Anty Aisha ta yi murmushi da ya fi kuka ciwo can ta yunƙura ta miƙe tsaye tana kallon Mama ta ce ''koma me ta yi ki ce silah'' Mama ta yi shiru tana kallon Anty Aisha,buɗe baki Anty Aisha ta yi da niyya magana Mama ta ce ''fita bani son jin komai..fita ki bani waje'' Anty Aisha ta ja ƙafa ta fita daga ɗakin ba tare da sake cewa komai ba,bayan fitar Anty Aisha Mama ta mayar da dubanta ga Unaisa ta ce ''tashi ki fita'' ta yi magana fuskarta babu alamar wasa da ido Mama ta bi Unaisa tana daf da fita daga ɗakin Mama ta ce ''kin ci abinci?" a hankali Unaisa ta waigo kafin ya ce ''bana jin yunwa'' Mama ta yi shiru bata ce komai ba, bayan fitar Unaisa Mama ta yi jigum tana tunani kan abinda Anty Aisha ta faɗa ta iya yiwuwa gaskiya Aisha ta faɗa,daga haka Mama ta fara tunanin abubuwa da suka faru shekarun baya
SHUUKRAN