Gidan Aurena By Oum sharifat

Gidan Aurena Chapter 1 By Oum sharifat

by @oumsharifat

*GIDAN AURE NA*
*EP1*
*By Oum Sharifat ce*
   

بسم الله الرحمن الرحيم

Soyayya ta itace mabuɗin ƙaddara ta, dabara ta da kuma yawo na sune suka zamo mabuɗin shafukan baƙin ciki na.
Shin laifi ne idan na ɗauki ragamar rayuwa ta na damkawa mijina? Laifi ne idan na ɗauka cewa miji na shine ƙarshen sirrina fa kuma fata na?

Yau wata rana ce wacce ta zama tamkar ranar tunawa da zuwa na duniya ranar idin ƙaramar sallah.

Unguwar Daɓai wata unguwa ci a cikin garin Kano Gwale local government.

 unguwa ce wacce ta haɗa mutane daban daban, masu ƙaramin ƙarfi da masu rufin asiri kamar mu.
Allah ya rufa mana asiri munfi ƙarfin buƙatun mu, muna cikin farin ciki da kwanciyar hankali idan aka cire ƙalubalen rayuwa na yau da gobe.


Wannan shekarar tazo min da laulayin ciki wanda take matuƙar bani wahala wannan yasa na kasa aikin sallah, inajin maƙota suna ta karaf karaf ana ta soye soye nidai Ina kwance na kasa motsawa, ƙamshin da nake juyowa na suyan nama shima ƙara hargitsamin ciki na yakeyi sai amai da nake ta aikin, yi tin ina yin sa da ƙarfi na har nazo na kasa. 

Babu komai a ciki sai ruwan da nake sha saboda na samu sauƙin aman 

Yara na uku Abdullahi shine babba shekarar sa tara sai Abdulhakim mai shekara shida
sai Juhaina ƴar shekara huɗu.

shekara ta goma da aure bansan mai ake cewa baƙin cikin ɗa namiji ba, idan aka cire na yau da gobe wanda kowacce mace ta saba dashi amma nidai banida tsayayyen ɓacin rai.

Madaidaicin gida muke ciki falo ne da bedroom guda biyu a ciki sai kitchen da store sai toilet sai kuma ƙaramin ɗaki mai ɗauke da toilet a tsakar gida.

Alamar shigowa da machine naji na tashi da ƙyar ina gyara ɗaurin zani na na fito tsakar gidan Ina washe baki.

Sannu da zuwa nayi wa sanyin idaniya ta ina murmushi, shima murmushin ya sakar mun ya shige falo na bishi a baya .

Hanyar kitchen nayi naji ya kira suna na, a hankali na juyo har yanzu akwai murmushi a fuska ta da kuma alamun shagwaɓa.
kusa dashi ya nuna min babu alamun wasa a fuskar sa, nima banyi wata magana ba na dawo na zauna.

Kallo na yayi na wasu ƴan mintina kafin ya buɗe baki yana gyara zama yace" Hindatu" a hankali na ɗago kaina na kalle shi, bazan iya tina ranar da ya kirani da suna na ba wannnab ya ƙara tabbatar min magnar tana da muhimmnci sosai .
"na'am" nace ina sake bashi dukka nutsuwa ta.

Kinsan Ina sonki ko? Murmushi na saki na ɗaga masa kaina nace nasani Habiby soyayya ta dakai shiryayyiyar kyakkyawar ƙaddara ce da Ubangiji ya haɗamu da ita .
"Yawwa! yace yana saka hannu a cikin aljihun sa ya ciro wani kati ya riƙe shi a hannun sa yace " kiyi haƙuri Hindatu ba zanyi wannan don ƙuntata rayuwar ki ba, ban kuma daina sonki ba, inason sanar dake nan da kwana uku za'a ɗaura min aure .

Suman wucin gadi nayi na rasa a duniya nake ko a lahira, Khamis!! a'a ƙarya kunnuwa na suka jiyo min, akwai alƙawari mai ƙarfi tsakani na dashi, akwai rubutaccen alƙawari wanda ya rubuta da kansa yayi signing akan kishiya.

Ban dawo daidai ba na jiyo muryar sa cikin wata magar da ta tabbatar dani a taɓaɓɓiya.

Yarinyar da zan aura marainiya ce batasan daɗin rayuwa ba, nayi mata akawai I will make her like a Queen, kiyi haƙuri inaso ta ɗanɗani daɗin dake cikin rayuwa , masu ruƙon ta basuda halin da zasuyu mata kayan ɗaki, ina roƙon ki da ki barwa kanwar ki wannan ɗakin ki koma ƙaramin ɗakin waje keda yara kafin na samu na siya miki wani gidan nan da ƙarshen shekara .
zan ware ki ke kaɗai daga ke sai yayan ki ya ƙarasa maganar yana laluben idanuwa na da mayaudarin murmushin sa.

Ganin naƙi bari idon sa ya shiga cikin nawa ya sauke ajiyar zuciya ya cigaba da cewa.
 "Sannan kinga ɗakin bazai ɗauki furniture ba ki ɗauki katifa kawai dama kinga wannan kayan nine na siya miki to duk ki bar mata su nayi miki alƙawarin sabon gida da sababbin kayan ɗaki wanda suka fi wannan.

Ji nayi zuciya ta tana wani irin zullo kamar zatayo waje, idanuwa na suka ƙanƙance ga zafin ciki ga zafin kishi ga zafin cin zarafin da nake ganin anyi min.

A hasale na buɗe bakina nace au kai yanzu har kasan alƙawari kamis? ka iya manta Alkawarin da yake tsakanin mu na shekara goma sha biyu sai wannan zaka cika? badai kaiba wlh azzalumi ne kai Khamis bakada imani.

 ban kƙarasa faɗar abinda yake baki na ba naji saukar marin da ya haddasawa fitsarin dake marata zubowa wanda yayi daidai da juyawar da ɗan ciki na yayi a wahalce.

 Kamar kububuwa haka kamis ya tashi ya fice daga falon sai ƙarar sautin tashin machine naji.
Na daɗe a wajan ina saƙa abubuwan da koda kasheni za'ayi bansan me nake tinani ba, nidai nasan Ina tantamar kasancewar hankali a jiki na.

Na daɗe a zaune a wajan kafin na iya tashi na gyara jiki na, ko wajan ban gyara ba na ciro akwati na na shiga loda kayana a ciki ina hawaye, sai da na cika akwati taf sannan na janyo ta na fito na kulle gidan na wucr bakin titi.

Napep na tare na kama hanyar gidan mu zuciya ta tana suya, har ƙofar gida ya sauke ni ban jira wani canji ba na tura kaina ciki .

 zuwa yanxu zuciya ta ta ƙeƴashe hawaye na sun bushe, da sallama a kasan maƙoshi na na shiga gidan maƙogarona yana mun suya wata irin ƙishirwa nake ji, ina shiga na wuce wajan randar dake tsakar gidan mu na buɗe na debo ruwan na kai kofin baki na.

 ban kai ga fara shan ruwan ba muryar mahaifiya ta ta daki dodon kunne na " badai yaji kikayo na ko? Ajiye kofin ruwan nayi sababbin hawaye suka zubomin haɗi da sangarta ganin gata na na juyo na fuskanci mahaifiya ta na buɗe baki nace "mama"kafin na ƙarasa faɗa ta ɗaga min hannu tace "kar ki fara wlh ba'a gidan nan ba, ni zaki tonawa asir yaji? Abinda ban taɓayi ba ba zan fara gani akan ki ba.

 nima haƙuri nake da baban ki, ya zama dole ki koma kiyi haƙuri da mijin ki ko mai yake miki kuwa.

ai tinda kika haihu zance ya ƙare haka zakiyi haƙuri dashi, babu gidan auren da babu matsala amma haka ake haƙuri a cigaba da zama.

Sake buɗe baki nayi zanyi magana zuwa yanxu kuka nake sosai abubuwa sun fara fin ƙarfin kaina ta sake dakatar tani tace "wlh sai kin koma ba zaki zauna ba bakida waje anan gidan can shine gatanki bakida wani gata daya wuce gidan mijin ki, haka zaki koma ki zauna dashi, an faɗa muku auren daɗi ake sha? ai dama ibada ce ita kuma aljanna ba'a samun ta da sauƙi.

Koda hakan yna nufin rasa rayuwa ta? nace ina kallon mama da matsanancin mamaki.
 Murmushi mama tayi kmar na fadi wani abn dadi tace " koda hakan yana nufin mutuwar ki ni a waje na abin daɗi ne kin mutu a gidan aure kinga aljanna zaki tafi ba wata kokonto, maza tashi ki koma ɗakin ki kafin babanki ya dawo raina da naki ya ɓaci nima lallaba nawa auren nakeyi.


Jiki a sanyaye ina kallon mama abubuwa suna dawowa cikin kwanya ta naja akwati na na fara tafiya ina waiwaye gidan da aka haifeni aka raine ni nayi rayuwar farin ciki har aka aurar dani saidai yanzu igiyar aure tasa sun sallamani sun yafe ni sun barwa wani ni koda zai kashe ni burin su in zauna.

Tinani nake tayi ina jefa ƙafafuwa na duk inda na samu. Menene abin tonon asiri a yaji? Meyasa iyayen mu bazasu saurari matsalar mu ba? Mu mata wai bayin waye? Bayin Allah ko bayin maza ?




Aliya


Sauri sauri nakeyi da farin bokiti shaƙe da kayan miya a hannu na, inayi ina canza hannu saboda nauyi na tsallako titi, saura ƙiris wata mota da ta shararo da gudu ya bige ni, ƙamewa nayi a wajan ina jiran ikon Allah, shutt naji ya wuce na sauke ajiyar zuciya na ƙarasa tsallakawa .

Rumfar Hajiya Mariya mai abinci na shiga na ajiye markaɗen dana ɗakko na kunna wuta na ɗora ƙatuwar tukunya na zuba mai na soya shi sannan ya zuba markaɗen dana ɗakko na kofa gefe na kama yankan albasa.

Yanayin garin akwai zafi ga rumfar langa langa ga wuta itacen sai mutuwa yakeyi ina gyarawa ido na yayi ja fuska ta ta kumbura sai hawaye dake zubowa daga ido na.

Ni kaɗai na gama aikin abincin ranar ban gama ba dai yamma liƙis.

Take away guda biyu hajiya ta dakko daya ya zuba min shinkafa da miya daya ta zuba min dambu sannan ta bani dari biyar nayi mata sallama na kama hanyar gida.
Tafiyar akwai dan nisa saidai ko tinanin hawa mota banayi saboda yanayin wahalhalun dake kaina da kafata na dinga tafiya Ina sakawa da warwarewa daf da magarib na iso gida.

A shagon dake jikin gidan mu na tsaya na siya pure water na naira dari da omon wanki na dari

Sannan na shiga gidan, tin daga soron gidan mu na jiyo kukan Hanifa zuciya ta ta buga da ƙarfi jiki na yayi sanyi na ƙarasa shiga .

Sulaiman yaron yaya na shine ya saka Hanifa a gaba yana duka wai tace Sulaiman ba yaya Sulaiman ba, mama na da sauran ƙanne na suna gefe suna dariya suna cewa batada kunya..


Ina shiga ciki na ja hannun Hanifa muka wuce ɗakin dake matsayin namu nida yarana guda biyu.

Muna zama naji an banko labulen ɗakin da sauri na dago kaina mama ce ranta a ɓace tace " wato Aliya ke bakida tarbiyyar zaman aure shine kike son lalata ƴarki itama kada tasan mutuncin na gaba da ita ko? ke yanzu ko kunya bakiji ba kamar Sulaiman don yayi wa Hanifa hukunci kika janyo ƴarki ke ga wacce tasan darajar haihuwa, kinsan kinason ta kika kasa zaman gidan ubanta kuma kika ƙi baro wa uban su yaran sa? To wlh ki shiga taiyayin ki na rantse da Allah idan kika kaini ƙarshe zan haɗa kan yaran nan dan uban su in maida su inda suke da wajan kwana, idan yaga dama uban su ya saka kansu a gabas ya yanka ni banida asara atoh

ƙara shigewa jiki na hanifa tayi tana sauke ajiyar zuciya, kaina a ƙasa nace dan Allah mama kiyi haƙuri , wani dogon tsaki mama taja tace na banza ne ai, kina da ladabin bada haƙuri kika kasa zaman aure? ai cikakkiyar mace itace wacce take zaune gida mijin ta da daɗi ko ba daɗi ba wacce take yawon gidan mai abinci tana karafkiya da maza ba.
Maza sun fito nema kema kin tafi nema wlh kinyi asara Aliya.
Ai duk matar data wuce zaman gida wlh saidai ta ƙare da raɓe raɓe.

Hawayen da nake shanyewa masu zafi suka zubo min. "karafkiya da maza" na shiga maimaita maganar a zuciya ta, wani ƙululun baƙin ciki da takaici ya tokare min maƙoshi, na shiga sauke ajiyar zuciya akai akai ina maƙale da Hanifa wacce ta fara bacci a jiki na.