JUYIN LAMARI

Page 07

by @ummufadeela01

JUYIN LAMARI

 By  

Ummu Fadeela

Book One
Page 07

Haka na wuni a wannan ranar jikina babu kuzari. Sauran lectures da suka biyo baya babu abin da na fahimta a cikinsu har muka dawo gida.

Tsabar damuwa mantawa nayi da cewa mun yi fada da Mufidah da safe, ko da driver dinsu yazo ban bata lokaci ba wajen shiga motar.

"Haba ki saki jiki mana Dubulle, duk kin tsangwami kan ki kamar wacce tayi cikin shege me haka plsss?"

"Mufidah ba dole in tsangwami kaina ba. Ke bakiji abunda su Sumy da su Ruqayya ke fada ba, wai har nono na ya taɓa fa suka ce. gaskiya an gama dani wallahi, ba a taba ci mini mutunci irin na yau ba."

"God! Dubulle ki bar zancen nan ya wuce haka mana, naga fa baki bar yan matan nan haka ba, sai da kika tabbatar kowacce kin mayar mata martani har suka koma baki hakuri tsabar masifar ki. To me ya rage kuma."

"Allah ko Mufidah da ace ban mayar musu amsa ba ina jin sumewa zan yi tsabar bakin ciki. Thank God na mayar musu dai-dai su."

"Amma har yanzu takaici nake ji. Shi ina hankalinsa yake har ya bugeni. ko dai mahaukaci ne?"

Halima ta kare maganar tana kallon idanun Mufidah with seriousness.

Mufidah tayi dariya tace.

"Ke za'a tambaya ina hankalinki yake ai.
Sannan ba mahaukaci bane, shi ne sabon lecturer din da ya maye gurbin Dr. Bashir, so get ready madam don kune a tare. And I noticed that he is very strict."

Halima ta zaro idanu da dafe kirji tace.

"Wanda ya maye gurbin Prof Bashir?"

"Yes of course "

Mufidah ta amsa dai-dai isowarsu gida tana bude kofar motar.

Har na shiga bangarenmu zuciyata bata daina tsinkewar da na rasa dalilinta ba.

'Hakan na nufin shi ne zai ci gaba da Supervision na project namu?'

Bani da mai bani amsa, hakan yasa na ci gaba da harkokina don bani son karawa Ummata damuwa a kan wacce take ciki.

Washegari misalin karfe tara na safe ina zaune da Ummah tana yi mini kalaba a dogon gashi na, kasancewar lectures din yamma gareni.

"Wannan gashi naki Dubulle, duk ranar da fushinsa ya waiwayeki ba zai yi miki da kyau ba. Kina mace, amma ki rufa wata biyu ko fiye babu Kitso?" Cewar Ummah.

"Allah Ummah da zan samu ayi mini aski sai nafi kowa farin ciki, gashin nan takurani yake."

"Shi ke nan idan aka yi miki askin sai ki kwashi gashin ki ba mijin da zaki aura ya makala a kansa." Umma ta bani amsa da dan fada.

Dariya nayi sosai nace.

"Kai Ummah, namiji kuma da gashin mata."

Tace "eh mana ba macen ma tayi askin Maza ba."

Wannan karon tare muka yi dariya. Sai kuma mukayi shiru jiyo hayaniyar jiniya a main compound.

"Yau kuma me ya faru a gidan Baraya, Baffa Attajiri ya yo mana sammako irin wannan"

Halima ta fada tana dan sakin dariya kadan. Umma ta dungure kanta da fadin.

"Gidanku Dubulle, kanin mahaifin naki ne ya zama abokin wasanki?"

"Ummata gaskiya na fada fa, idan kaji karar jiniyar nan ta masifa da sassafe a gidan nan, tabbas wani abun ya faru a ahalin Baraya za'ayi zaman gaggawa. Wayyo har na hango fuskar Innani."

Halima ta karisa da sakin wani dariyar da bugun cinyarta.

"Asshha! Ba kuma lallai ya zama hakan ba, watakila ya shigo su gaisa da Karami (Usman) ne, naji Malam yana fadin jiya ya shigo daga Kaduna gabanin magariba."

"Hmmm, Umma idan Baffa Karami yazo ai shike zuwa ya gaida Baffa Attajiri tunda shine karami. Dole wani abun ne ya faru."

Umma tayi shiru, jikinta yayi sanyi, ta saki kitson da take yiwa Dubulle. Cikin sanyin jiki tace.

"Allah dai ya sanya taron gaggawan ba a kan ki bane Dubulle, a yan kwanakin nan zuciyata bata iya jure radadi tun bayan mutuwar Ikleema ta. Naga kema kin daina dauko mini magana."

Halima ta dafe kirji da zaro idanu.

"A kaina kuma Umma, ni me nayi da za'ayi taro a kaina?"

"Ban sani ba Dubulle, amma kin san magana bata yi musu kadan. Musamman a kan sabgar data shafi bangaren nan".

Umma bata gama rufe bakinta ba, wayarta ta dauki tsuwwa.

Ganin Baba ke kiranta kuma bai dade da fita ba, ta dauka da hanzari gami da yin sallama.

"Mairiga ki same ni bangaren Innani keda Halima yanzun nan"

"Lafiya dai ko Malam" Umma ta tambaya.

Ba tare da ya bata amsa ba yace, "Ku hanzarta nima gani nan karasowa." Baba ya fada da umarni.

Umma tayi jimm sai kuma ta shafa kaina tace, "Dauko mini hijabi na saman taga, kema ki dauko taki mayafin muje.

Kasancewar naji maganganun Baba sai ban nemi karin bayani ba.

A karon farko tun da ake zaman gaggawa a bangaren Innani naji jikina ya mutu. Naji kamar kada inje, wannan karsashi da rashin barin ko ta kwana da nake dashi naji kamar yana guduwa ya barni.

"Ummata" Halima ta fada a karo na biyu. Umma tayi firgigit ta mike tunani da damuwa kwance a fuskarta.

"Ga mayafin"

Ta sa hannu ta karba, sai ta hada da hannun Halima ta rike duka biyu.

"Dubulle me kika aikata yau kuma."

"Wallahi Allah Umma ba komai, kina gani ai yau ko kofa ma ban leka ba."

Na bata amsa cikin sanyin murya tamkar ba Dubulle mai hali dubun da babu na zabe ba.

"To duk tsanani, a duk inda kike ki riki gaskiyarki ko a gaban waye ne. Ki guji karya itama koda barazana za 'amiki."

Halima ta gyada kai da fadin.
"Insha Allah Umma"

Lokacin da suka isa falon Innani karkataf jama'ar gidan sun hallara a falon. Manya da matasa, kamar ana karbar makoki.

Idanun Halima ya fara sauka a kan fuskar Ya Abdul. Kamar ko yaushe Idan dai yana waje shi take fara kallo.

Da sauri ta kawar da idanunta taja ta rufe, ganin yadda fuskar Abdul ta cika taf da bacin rai har wani hayaki hayaki take hangowa yana fita daga cikin idanunsa.

Jin gaisuwar da Umma ta hada jam'u tana yiwa yan falon ne ya dawar da Halima hayyacinta, itama ta fara mikawa kannen Ubanta dake zaune a falon gaisuwa.

"Shi Gadanga yafi karfin zuwa ne?"

Innani ta jefawa Umma tambayar.

Umma ta risisnar da kai tace, "Ayi masa gafara Innani yana hanya yanzu haka. Watakila bai samu abun hawa da wuri ba.

"Tafiyarka ga talaka ke nan, yar abun hawa ko wannan keke da jama'a ke lallabawa da ita Gadanga ya kasa siya, to ai shi ke nan"

Karaf a kunnen Baba da isowarsa ke nan yana kokarin shigowa falon. Ya rumtse idanu ya bude, ya juya ya kalli Compound da parking space na kowanne bangare dake cikin makeken gidan. Motoci ne na kannensa da matansu da kuma yayansu tsala tsala birjik iya kallon mutum, ba zai ce ga adadinsu ba sai daukar idanu suke yi.

Wasu ma a wajan sun fi shekara ba a hau su ba, suna lullube da tamfol.

Gadanga ya hadiye wani yawu da kyar, yayi saurin a'uziya yana korin shaidanin da ya fara kawata masa kyan motocin.

Jarumta ya dora a fuskarsa ya shiga falon da sallama.

Yana gama daidaita zamansa bisa kujera Innani ta mike tana dubansa da kankance idanu tace.

"Gadanga lallai yarka Halima ta zo mana da abunda bamu san shi ba a cikin zuriyar mu. Ta shigo mana da sabon al'amarin da dole mu dakile shi, gudun kada yan baya su fantsama a cikinsa."

Innani ta dan ja numfashi ta dora da fadin.

"Tabbas Halima tana son zubarwa da gidan nan mutunci. Amma ka sani, ba zan taba lamuntan wannan ba, domin duk abunda ya taba gidan nan, mutuncin yayana ne ba kai ba. Da rayuwata kuma ba zan amince da zubewar mutuncin da kimar ahalina ba".

Ta karishe tana mikawa Ramlah hannu da fadin. "bani nan".

Ramlah da tayi wuki-wuki da idanu ta dukar da kanta kasa.
Innani tace, "jama'a wai ba Ramlah nake yiwa magana ba, kika yi kibi-kibi da idanu kamar na kibibiya?"

Ramlah ta dago wayarta ta mikawa Innani.

"Bani zaki bawa ba ai. Jonawa a tv zaki Yi kowa ma ya ganewa idanunsa kawai, wadanda suka gani kuma sukara gani"

Ramlah ta mike tana jin yadda idanu ke binta ta nufi tangamemen tvn Innani.

Halima ta rufe idanunta ruf, gudun da zuciyarta take ya karu. Baba kuwa kuri yayiwa tvn Innani da Ramlah ke ta kokarin hadawa. Umma kuwa kanta na duke a kasa ta kasa dagowa.

A ranta tana tambayar kanta me yasa kullum Halima?

"Domin ita din ta musamman ce"

Wata zuciyar ta bata amsa.

Gabadaya jama'ar dake falon suka bi tvn da kallo baki bude lokacin da ya kawo wuta, hoton Halima ya bayyana tana kwance a kirjin wani a cikin makaranta.

Basu gama dawowa daidai ba wani hoton ya bayyana, Halima ce dai still kwance a jikinsa ya dora hannunsa kan breast dinta yana shafawa, suna kallon juna dukkansu suna murmushi. Wannan karon Baba mikewa yayi tsaye ba tare da ya san yayi hakan ba.

Wani hoton da ya bayyana ya kuma sanya Baba komawa ya zauna dabas ya dafe kansa yana ambatar "Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un" Suna rike da juna bakin mutumin kan nata yana bata kiss cikin shauki.

Wani kara Umma tayi tace, "Sam! Wannan ba yata bace. Dubulle ba zata taba aikata wannan mummunar aikin ba."

Attajiri yayi gyaran murya yana kallon Ramlah calmly yace, "Ramlatu kashe wannan abun".

Da sauri ta kashe jikinta yana rawa ganin yadda ya tsare ta da idanu.

"A ina aka samo wadannan hotunan?" Ya kuma jefo mata tambayar.

"Wata kawata ce da suke department daya da Dubulle a BUK ta turo mini".

Attajiri ya mayar da kallonsa kan Dubulle ya mata kallon sakan biyar kafin yace, "Halima me yake faruwa a nan?"

Ta dago kanta a hankali cikin rawar muryar da bai kasance dabi'arta ba tace. "ban sani ba Baffa, nima ban gane ba."

Attajiri cikin tsananin fusata yace, "Me kike nufi da baki sani ba, shin wannan ba Halima bace jikin hoton da muka gani?"

Halima tayi shiru don gabadaya kwakwalwarta toshewa tayi.

"Itace Baffa, amma ba haka al'amarin yake...."

Tsawan da Mamy ta dakawa Mufida ne ya sa tayi shiru daga bayanin da ta dauko. Tunda ai komai a gabansu ya faru.

Wani dogon kabbara Innani ta saki da fadin, "yo dama mene ne abin mamaki a wajan Dubulle yar gidan Mairiga da Gadanga.

Baffa Karami ya tari numfashin Innani da fadin.

"Ba shakka Halima ta kawo jiki, tunda har ta san yadda ake kwanciya a kirjin maza nan da dan lokaci zata iya kawo mana jika a gidan nan. Don haka kafin tabbatuwar hakan dole ayiwa tufkar hanci."

Baba ya rumtse idanu da karfi. Umma ko dama, tunda Mufida ta tabbatar da cewa Halima ce, Umma tayi suman zaune, ta fara kokawa da numfashinta Amma babu wanda ya lura.

Baffa Alaji ya ce, "Innani a dai tsananta bincike, wannan zamani da muke ciki na hade haden kwamfuta."

Innani tayo kan sa da masifa. "Mukhtar ko dai idanunka basu gani da kyau ne. Ko kuma bakaji abinda Mufida ta fada bane cewa lallai Halima ce a hoton. A gabansu komai ya faru".

Abban su Abdul ne wannan karon ya karbi maganar yace.

"Kafin ta janyo mana abun kunyar da zai bibiyemu har abada, inaga kawai ayi mata aure."

Ya dubi Halima yace, "daga yau zuwa sati mai zuwa Halima ki fitar da miji ko kuma mu baki duk wanda ya yi mana. Sannan zancen Boko an soke shi, baza ki kuma fita daga gidan nan da sunan zuwa makaranta ba".

"Tabbas zancenka haka yake. Nayi Naam da matsayarka Ummaru." Cewar Innani.

"Ban amince ba, baza'ayiwa Halima auren dole ba"

Gabadaya jama'ar dake falon suka juyo suna kallon Umma da tayi maganar da kyar idanunta suna kakkafewa. Ta ci gaba da fadin.

"Dubulle zata cigaba da zuwa Boko babu kuma wanda ya isa ya yi mata auren dole. Baza ku mayar mini da yayana hajar bazawa a baja kolin duniya ba."

Babu wanda Mairiga bata shayar mamaki ba a wajan, al'amarin ya zo musu sabo. Duk wulakancin da za ayi musu Mairiga bata taba daga idanunta tace komai ba. Lallai yau tura ta kai bango.

Baffa Karami ya mike a fusace kasancewar duk yafi su zafin zuciya yana nuna Umma da yatsa yace.

"Mairiga baki isa mu yanke hukunci a kan yayanmu ki tanka ba. Muke da iko da duk abinda kika haifa a cikin gidan nan ba ke ba"

Umma ta dago kai da kyar tayi murmushin da ya fi kuka ciwo tace. "Karami ke nan, lokacin da marigayiya Ikleema ta nuna idan bata auri Tahir ba bazata iya rayuwa ba. Me yasa baku nuna karfin ikon naku ba a kanta, ku samar mata farin ciki. Don haka bazan amince bakin ciki ya kuma salwantar mini da yata a karo na biyu ba."

Karami ya fusata ya mayar da kallonsa kan Baba cikin fushi tamkar dansa ba wansa ba yace.

"Gadanga ni kaninka Usmanu na bawa Alhaji Sambo mijin marigayiya Ikleema auren yarka Halima ta maye gurbin Ikleema."