MISHAL

Page 1

by @ayshagaladima22

MISHAL



By BLACK QUEEN đŸ€đŸż
***



Book 1 
         page 1 

Matashiyar budurwa ce kwance akan wani lallausan gado na zamani.

Gado ne irin na masu kud’i, yana da fad’i da girma , da a’kalla mutane uku zuwa hud’u zasu iya hawansa.

An shinfid’a masa bedsheet cream colour me adon ribbon da tiny flowers green colour . 

Matashiyar tana can ‘karshen gado, ta d’an d’aga ’kafafuwanta sama , tayi crossing d’in su  cikin salo na nishad’i da rashin damuwa . 

Pillow d’in da ta kwanta ya kusa rufewa sabida brownie colourful gashinta da ta baza akai . 
Gashin yana da tsaho sosai daga kwancen da take , ga santsi da yake faman yi alamar yana shan gyara a ko wana lokaci. 

Hannunta d’aya tana ri’ke da wani English novel , yadda tayi focusing hankalinta sosai alamar tana jin dad’in abunda take karantawar. 

‘Daya hannunta ta ri’ke sweet , kamar wata yarinyar , time to time tana tsotsan sa cikin bakinta . 

Tana sanye da blue Pjamas mai d’auke da ‘kananan teddy bear designs white colour. 
    Kayan suna da santsi sabida yadda suka yi luf luf a jikinta. 

A shekaru ba zata fi 19 to 20 ba .

Tana da tsaho dai dai na shekarunta , tana da perfect slim body, tana da ‘kirji ba cancan manya ba, sai kuma bum bum da Allah ya bata duk da a kwance take gana iyan ganin shape d’in jikinta , wannan tafi Coca Cola shape dan shape kam akwai shi irin wacce duk budurwa zata so ta samu kalar shape din. 

Cikin d’akin nata tsaf yake babu wani tarkace , amma kana ganinsa kasan d’akin mace ne , from the decoration 
zuwa daddad’an ’kamshin Bakhoor da yake tashi. 

Paint  d’akin, zuwa white teddy bear da yake can gefen carpet , duka na Girly ne , ga sanyi Ac da ya had’e da ‘kamshin turaran yana bada wani vide me dad’in gaske . 

Tayi nisa a duniyar karatun da take , aka turo ‘kofar d’akin da d’an ’karfi . 

A hankali ta d’ago kanta , hakan yasa beautiful face d’inta fitowa ga baki d’aya. 

Tana da tsananun kyawu mai matu’kar saka shau’ki akan fuskar duk wanda ya kalleta .

Bawai irin natural beauty ba , wannan kyawunta nata har da wani baiwar kyau a tattare dashi. 

Idanuwanta kuwa 
. Sune farkon abun da zai fara d’aukar hankalin duk wanda ya kalleta . 

Tana da Amber eyes ( irin wad’anda suke kama da zuma mai haske , wani lokacin kuma suna d’aukar yanayin golden eyes ). 

Shape d’insu kuwa , unturned almond ne , wanda yake shigen yanayi da irin na mage .

Tana da kyawun ido sosai da sosai , gashin girarta a cike yake , amma ba mai yawa ba , yana da kyau sabida yadda ya kusa had’ewa da d’an uwansa, sai dai da alama tana gyara wajan sosai da sosai . 

Gashin idanuwanta dogaye ne , ba’ka’ke masu ‘kara wa idanuwan armashi a duk lokacin da ta ‘kifta su . 

Hancinta dogo ne me kyau da ya dace da kyawun fuskarta sosai . 

A gefen hafu akwai ‘karamun nose ring , silver colour me kyau da, ya zauna d’as akan hancinta .

Lips d’inta ’kanana ne , rosy pink , masu d’aukar ido. 

Skin d’inta kuwa
.. Golden light brown ne mai she’ki da santsi babu d’igon pimples ko d’aya a fuskarta , ga skin d’inta sai faman glowing yake 

A hankali ta sake ‘kifta idanuwanta tana kallan ‘kofar d’akin. 

Budurwa ce tsaye a wajan , ta nad’e hannayenta biyu akan ‘jikinta, tana kallan wacce take kan gado cike da mamaki. 

Kamar wacce taga wani abu da ya bata shock , ko magana ta kasa, itama kuma wacce take cikin d’akin kallanta tayi babu alamar mamaki a face d’inta . 

Daga ‘karshe , wacce take ‘kofar ta sauke ajiyar zuciya , kafin ta waiga , sannan ta shigo cikin d’akin tana rufe ‘kofa da sauri. 

Itama kyakkyawa ce , amma bata kai ta kan gado kyau ba . 

Skin d’in su kusan iri d’aya ne , kuma akwai d’an kamanceceniya a fuskar su , musamman a gira da kuma shape d’in bakın su . 

A shekaru za ta kai 25 years , ba doguwa bace sosai, kuma ba gajera bace , amma jikinta ya fi cika sosai akan na wacce take kan gadon. 

Tana sanye da red lace mai kyau, tayi d’aurin V shape da d’an kwalinta, wanda ya fito mata da kwantaccen gashin kanta waje kad’an . 

Ta kalli yarinyar kan gadon cikin mamaki ta furta “ MISHAL
.. me kike yi a kwance haka baki shirya ba ? Na d’auka zanzo na sameki a shirye , amma kina nan kina karatun novel ?.” 

Ba cikin zafi tayi maganar ba , amma akwai mamaki a ciki.

Yarinyar kan gadon ta juyar da idanuwanta cikin wani salo mai kyau , kamar tana wasa dasu , ta d’an turo bakinta gaba.

Cikin soft baby like voice cike da shagwa’ba ta furta “ Aunty Shukra
 kalli yadda kika bugomun ‘kofa, yanzu ai sai kisa kai na ya soma ciwo .”

Ta ‘karasa maganar tana ‘kara rolling idanuwanta cikin shagwa’ba .

Aunty Shukura ta jinjina kai a hankali , tana kallanta kamar wacce ta gaji da halinta . 

“ Dole kice zan saka miki ciwan kai , kowa ya shirya , ana jiranki a ‘kasa , ke kina zaune sai kace ‘yar gwal, kina karatun novel kamar baki san da zaman mu ba.” Ta d’an ‘karasa maganar  d’aga murya kad’an , kafin ta cigaba da magana. 

“ Lokacin da na barki , already kin fito daga wanka fa , amma yanzu kin wani saka Pjamas , kin koma kan gado , What nonsense is this ?” 

Ajje littafin Mishal  tayi a gefenta, sannan ta bud’e both  hannuwanta , cikin rashin damuwa ta furta 

“ Aunty shukura
 kin san bana san hayaniya. Don Allah ku tafi kawai , ni bance muku ku zauna zaman jira na ba , I don’t want stress, ba dole sai dani ba . 

Naga gathering d’in nan ba dole bane , so am not in the mood . 

Da nayi niyar zuwa but na canza mind d’ina yanzu , so feel free to go please.” Ta ‘Karasa tana d’an sauke ajiyar zuciya , sannan tayi murmushin da ya saka dimples d’inta lotsa wa, fararan idanuwanta kuma sukai haske sabida yadda tayi  narai narai dasu . 


A hankali ta kuma furta “ Please 
. Let me be .” 

Aunty Shukura ta d’an yi shiru , tana kallanta da wani irin yanayi, kafin ta girgiza mata kai .

“ Ki ci gaba amma idan Mamy ta tanbaye ni , zan fad’a mata gaskiya . Me kunnen ‘kashi kawai .”

Bata jira MISHAL ta bata amsa ba ta juya ta fita daga cikin d’akin. 

Tafiyanta sai yasa d’akin ya sake komawa yadda yake , babu single hayaniya .

Mishal  ta sauke wani ajiyar zuciya mai nauyi. 

Ta koma ta kwanta kamar d’azu, amma yanzu waya ta d’auka ba littafi ba , tana scrolling a hankali cikin IG. 

After some minutes



Sai akai knocking ‘kofar , sau d’aya kuma babu ‘kara ko sauti sosai , idan baka lura ba sai kayi tunanin ko ba ‘kwan’kwasa ‘kofar akai ba .

Kallan ‘kofar Mishal tayi sabida taji knocking d’in , ranta har ya soma ‘bacı , ta wani turo lips d’inta kad’an kamar wata Baby , ta nufi ‘kofar tana magana . 

“ Aunty Shukra
.. please nace miki I’m not going any
.” Sai numfashinta ya tsaya cak, sabida yadda ta san dare a bakin ‘kofar bayan ta bud’e door d’in. 

Lips d’inta na ‘kasa har ya soma rawa shi kad’ai. 

At the same time kuma ‘kamshi me dad’i yana dukar hancinta . 

Har wani ‘kasa ‘kasa take da idanuwa tanasan rufe su amma kuma kamar tsoran rufewar take. 

Cikin ‘karfin hali tayi ajiyar zuciya mai ‘karfi , tana bud’e idanuwanta sosai , cikin sha’kewar murya ta furta “ UNCLE 
.. MOH .” Kamar me tsoran ambatan sunan . 

Yana tsaye a bakın ‘kofar , hannayensa duka biyu a cikin aljihu. 

Kyakkyawane sosai , irin sosai d’in nan , Tubarkallah Masha Allah , dan har yaso yafi Amalili kyau ma , kuma fari ne shi sosai kamar balarabe . 

Yana da hasken fata mai kyau, idanuwansa masu kyau ne sosai black colour , sai dai kamar wanda ya saka kwalli sabida yadda zagayen idansa yake kamar wanda ya saka kwalli. 

Yana da dogayan eye lashes, ga jagiyarsa da take a cike sosai, black colour kuma mai cikowa .

Idanuwansa ßuna da matu’kar kaifin da duk wanda ya kalle su sai ya saukar da nashi idanuwan sabida kaifin su. 

Yana da dogon hanci, Ya Allah, ga bakinsa me kyau , dai dai peach colour ..

Yana da sumar kai kamar curly hair sai dai an gyara ta sosai, an d’anyi aski daga gefe gefen kan kad’an , da kuma bayan kan, sai ragowar gashin da aka tufke shi daga ‘keya .

Daga wajan fuskarsa kuma siririn gashi guda d’aya ya le’ko. 

In ana neman saurayi da ya cika 1 in a million toh wannan ya fisa ma , gashi dogo, yana da faffad’an ‘kirji, da kana kallan jikinsa zaka gane yana d’aga ’karfe sabida hannunsa da yake a murd’e , gashi alamar jini a jika.

Yana sanye da black shirt d’in riga da hannayenta suka fito da damtsen hannunsa , da kuma farin hannunsa da babu komai a jiki sai wani d’an siririn abu, ba’ki. 

Wandan jikinsa ma ba’ki ne , amma ba jeans bane , sai takalmin ‘kafarsa shima da yake ba’ki , amma kana iya ganin ‘yan yatsun ‘kafafuwansa farare .

‘Kamshin da yake tashi a jikinsa me dad’i sai ka rasa wana irin turare ne haka mai dadi sosai , har ji zakai hankalinka yana kwanciya da zaran ka sha’kesa . 

Itama Mishal sai faman bud’e hancinta take , sabida yadda take bala’in san ‘kamshin turaran da har yanzu bata san sunansa ba . 

Sau d’aya kawai ya kalleta , tayi saurin dawowa cikin nutsuwarta , har tana ja baya sabida yadda taji zuciyarta ta buga da ‘karfi sosai. 

Cikin sauri ta sunkuyar da kanta ‘kasa sabida yadda taji idanuwansa masu kaifi, wanda ko kyauta aka ce ta d’ago ta kallesu ba zata iya ba .

A hankali taji saukar muryarsa cikin dodan kunnanta , duk da ba da ‘karfi yayi maganar ba  , amma taji iko da sautin amon da yake ciki. 

“ 10 minutes 
.” Sai ya d’an tsagaita, kafin ya ‘kara fad’in “ 10 minutes kawai na baki
” 
Sai kuma ya d’ago ya sake bata wani irin kallo “ Ki same ni a ‘kasa 
” sannan ya juya ya bar wajan.

Mishal batasan ma ya tafi ba sabida tsoran da ya shiga zuciyarta .

Amma tunawa da kallar 10 minutes da tayi , gabanta ya sake fad’uwa sosai .

Ta d’ago kanta da sauri , ganin bayanan , ta sauke a jiyar zuciya amma har time d’in gabanta bai dena fad’uwa ba .

Cikin sauri ta janyo ‘kofar ta rufe tana jingina a jikin ‘kofar, kafin ta dafe zuciyarta , a hankali tana shafa ta , cikin sauke wani nannauyan ajiyar zuciya , kafin ta d’an ‘bata fuskarta tana turo bakinta , ita kad’ai sai guna guni take .

Tasan idan ta ‘kara bada wani time d’in, sai ta gane kuranta , tayi saurin nufar wardrobe d’inta , saura kad’an tayi tuntu’be sabida  sauri . 

Bata tsaya ‘bata lokaci ba , ta janyo rigar da ta gani a farko farkon kayanta , tana so ta ‘kara gasa rigar da turare amma tasan abunda zai tunkaro ta .

Sai kawai ta ajje tunanin gasa kayan, ta koma gaban mirror d’inta da yake cike sosai da kayan shafe shafe da maya mayai. 

Ta shafa duk abunda take bu’kata , ‘kamshin turaruka da humra da tayi amfani dasu ya cika ko ina na d’akin.

Ba tayi make up ba , ta dai saka lip balm da kuma kwalli a idanuwanta , sai nose ring da ta canza zuwa golden. 

Fuskarta sai faman glowing take sosai, da alama skin care product  d’inta ba ‘karamun amsa ta yayi ba. 

Haka ta zauna taje uban gashin kanta, shima ko rabi ba tayi ba tayi packing d’insa sabida ta kasa tajewa ga baki d’aya .

Rigar da ta d’auko fitted gown ne me launin deep wine , bata da over ado a jikinta sai pattern d’inta da ya fito sosai da sosai . 

Kayan sosai suka fito da shape d’in jikinta , ‘karamun ‘kugunta ya fito kamar wacce bata cin abinci , sai kuma hips d’inta manya da suka fito cikin kayan.

Kayan sunyi mata kyau sosai , ta d’auko heels , silver colour , sannan tayi d’aurin d’an kwalinta mai kyau, daga baya baya gashin kanta yana d’an le’kowa duk da ba duka ba .

Ta kalli kanta from head to toe , kafin ta yi murmushi kad’an tana ‘kara feshe jikinta da mayafinta da turare me dad’i. 

Bata d’auki purse ba , wayanta kawai ta d’auka , har ta saka hannu a handle d’in ‘kofa zata bud’e, sai tayi sauri ta koma gaban mirror tana kallansa, lokaci d’aya kuma ta soma kalle kalle , kamar tana san ganin wani abu. 

Daga bayan kunnanta taji ance mata “ Kinyi kyau 
.” 

Cikin murmushi Mishal ta juyo tana kallan matar da tayi magana .

Baka ce sosai , tana sanye da diga da kuma shirt da ya rufe ‘kafafuwanta ga baki d’aya , sai gashin kanta da yake a cike shima kuma a waje , da wasu sar’ko’ki guda uku , d’aya daga cikin su akwai me cross a jiki . 

“ JOY
” Mishal ta fad’a tana ‘ko’karin matsota , amma sai Joy ta nuna mata lokaci, tana kashe mata ido d’aya , kafin ta ‘bace daga d’akin ga baki d’aya. 

Hakan yasa hankalin Mishal ya dawo jikinta sabida Uncel Moh da ya fad’a mata a rai, tayi saurin nufar stairs , sabida gudun abunda zai iya faruwa idan lokacin da ya fad’a suka cika 







âž»
Clock it đŸ€đŸżđŸ€đŸżđŸ€đŸżâ€Šâ€Š..

***