Page 2
MISHAL
By BLACK QUEEN đ€đż
***
Book 1
page 2
A hankali takun takalmanta ya soma sauka akan marmaran stairs , kudâi sosai yayi a wajan âkawata sa .
Daga Ćamansa akwai babban chandelier da take dâaukar haske sosai .
Idan ka kalli Mishal yadda take tafiya hankali , sai kayi tunanin babu abunda yake damunta, sai dai âkasan zuciyarta cike take fal da tsoran Uncle Moh , dan ta riga ta san lokacin da ya bata ya wuce .
Tun daga fitowarta har zuwa sakkowarta Joy na binta a baya amma bata bari Mishal dâin tasan tana wajan ba .
Sai da ta kusa âkarasa sakkowa âkasa ta riâke handrail da dâan âkarfi tana sakin ajiyar zuciya , har lokacin zuciyarta bata dena dukan uku ukun da take ba .
Tana sakkowa âkamshin turaran wuta da dâamshin turaran su suka cika hancinta ga baki dâaya.
Falon yayi kyau sosai , interiors da akai anfani dasu Ćuna da matuâkar kyau . Sannan akwai 3 different set dâin kujeru a falon .
A dai dai side dâin da zuciyarta ta bata yana zaune , nan dâin ta kalla , kuma yana zaune a wajan kamar yadda tayi hasashe .
Yana zaune akan 2 sitter , ya dâan jinginar da kansa da bayan kujera , idanuwansa a rufe suke , hannunsa dâaya akan cinya , dâaya hannun kuma daga gefen kujerar da yake .
Yadda yayi zaman very comfortable alamar yana jin dadâin yanayin da yake .
Rasa abunyi Mishal tayi , wani zuciyar na raya mata tayi magana , wani kuma yana raya mata ta tsaya har ya budâe idansa , a wani side dâin kuma tana tuna kashedin da yayi mata .
Cikin sanyin murya ta furta â Assalamu AlaikumâŠâ yadda tayi maganar kamar me shagwaâba , sai dai da alama haka muryarta yake , sabida kusan ko wana magana idan za tayi haka turn dâin muryanta yake .
Bai amsa mata ba , bai kuma budâe idanuwansa ba , sai 1 finger dâinsa da yake dâan motsawa da hannun daman sa.
Kasa haâkuri Mishal tayi ta kuma fadâin â Assalamu Alaikum⊠Uncle Moh , na shirya ..â
Sai a time dâin ya budâe idanuwansa , duka kallan seconds uku yayi maga ya dâauke kansa , kafin ya nunata da finger from head to toe, fuskarsa babu wani walwala ya furta â âYar iska kika zama da zaki fita da wannan kayan ko kuma ni kike so ki mayar dâan iska?â.
Cikin shock Mishal ta kallesa , ganin baya kallanta , tukunna ta kalli kayan da suke jikinta , ita shaf ta manta bayasan kaya irin haka .
â Kayi hakuri Uncle Moh but I think âŠâ
Bata ma âkarasa ba ya mata wani kallan up and down da yasa ba shiri ta hadâiye maganar da za tayi.
â Ki wuce kije ki canza kayan jikin ki , sannan ki cire abun karuwan da kika saka a fuskar ki , kika âbata mun lokaci kuma sai na âballa miki wuya a wajan nan , tunda ba ajje ni kikai ba , get lost my friend âŠ.â
Juyawa Mishal tayi zata bar wajan , ya daka mata tsawa, sai da ta dâan dafe kanta sabida yadda taji tsawarsa har tsakiyar kanta .
â Canât you answer me ?â Are you mad ? Ko ni saâan kine?â.
â Wallahi you have big anger issue Uncle Moh , duk âkanâkantar abu sai ka mayar dashi babba âŠâ ta raya cikin zuciyarta .
A fili kuma ta furta â Uncle Moh kayan zanje na canza , am sorry if i offended you in any way..â Ta
âkarasa maganar wasu siraran hawaye na sakko mata akan kuncinta .
Zata kuma juyawa ya kuma dakatar da ita , muryarsa yanzu ta dâan fi zafi sosai â Dukan ki nayi zaki mun kuka ? Very manifulated girl , dallah wuce ki bani waje , kafin na âballaki my friend .â
Sai da ta hadâiye wani abu me dâaci a zuciyarta , sannan ta goge hawayen fuskarta â Uncle Moh kayi hakuri , ni bansan lokacin da kuka yazo mun ba .â Tana âkarasa maganar tabar wajan , bata bari ya sake magana ba , sabida haushinsa da take ji yanzu zata iya fadâa masa magana mara dadi.
Tana barin wajan yaja wani siririn tsaki kafin ya furta â Manifulated girl âŠâ sannan ya bar falon shima .
Ita kuma tana shiga dâaki, ta turo âkofar da dâan âkarfi , tana tsugunnawa a bakin âkofar , hannayenta biyu akan fuskarta tana âkananan shash sheâkar kuka .
Tana cikin kukan ne taji muryar Joy a kusa da ita har tana dafa kafadâunta .
â Mimi badai wannan dâan âkaramun abun bane zai sa ki âbata hawayenta har ki zauna a âkasa kina shash sheâka, kamar baki saba da halinsa ba .â
Kallanta Mishal tayi tana goge wani hawayen da taji yana san sakkowa . â Joy ko na saba da wulaâkancin amma kinsan wannan cin mutuncin da yayi ba kowa akai wa bazai ji dadâi , har sai yaushe zai manta da abunda ya faru , ko lefi na ne a wancan lokacin da zai dâauki karan tsana ya dâora mun?.
Yanzu ina ruwansa dani , ina zaune ya wani zo cikin isa yace na fito , na fito yana faffadâa mun maganganu, idan nace bazani ba yazo ya âkona gawata mana idan ya ga namu sai ya dena tsanar da yake mun .
Shi komai baya wucewa a wajansa ?.â
Cikin girgiza kai Joy ta furta â Mun wuce wannan wajan Mimi , kar mu taso da abunda ya wuce , kiyi hakuri da halinsa , kema kinsan da ba haka yake ba ko? Dole yayi abunda yake yanzu , na tabbata ko kece a cikin condition dâin da yake , zakiyi haka koma fiye da haka âŠ
Ki tashi ki canza wannan kayan kema kinsan sarai bayasan irin wadâan nan siturun, karki zauna ki âkara janyo wani abun tunda shi âkaramun abu yake mayarwa babba .â
â Wallahi JoyâŠ.â
Joy bata bari ta âkarasa maganarta ba ma ta taya ta miâkewa tsaye â Kinsan nima zuciyata a kusa kusa take , banasan musu , kawai ki shirya ki koma , kema kına sane kike janyo magana a wajansa .
Tunda kinsan halinsa sai kisan maganin zama dashi ba sai kin zauna kina biye masa ba .â Daga na tabar dâakin , bawai ta hanyar budâe âkofa ba, âbacewa tayi ga baki dâaya a dâakin.
Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke , kafin ta wuce toilet , sai da ta wanke face dâinta sosai da soap , sannan ta fito daga toilet tana yarfe hannuwanta a hankali .
Kai tsaye wardrobe ta nufa , tana bubbudâe su , a gefe dâaya na zuciyarta kuma tana tunanin kayan da zata saka .
Daga âkarshe âbangaran abayas dâinta ta budâe , ta dâauko wata Red dâin abaya, gefen hannunta da design dâin rose black , haka gefen mayafinta .
Turare kawai ta saka musu shima kadâan sannan ta saka , ko lipstick bata saka ba , ta canza takalminta zuwa baâki mara tsini wato flat , tayi rolling mayafin abayar sannan ta fito daga dâakin.
Yanzun ma a hankali take tafiya har ta sakko âkasa .
Sake kallan inda ya zauna dâazu tayi , ganin bayanan ta taâbe bakinta kadâan sannan tabi hanyar da tasan zata samesa .
_____ Lokacin da ta fito babban compound dâin gidan , a hankali ta soma rarraba idanuwanta , tana tunanin ta inda zata hangosa âŠ
Duk da cewa dare ne , amma farfajiyar wajan akwai haske sosai kamar rana sabida fitilu da aka saka sosai .
Masu aiki , da sauran mutanan da suke kula da wani wajen kowa harkar gabansa yake , dai idan sun zo wucewa zasu dâan rusunar da kai âkasa su gaisheta kafin Ću wuce .
Motar da ta hanga daga can side dâin palm tree , ta nufa dan haka kawai zuciyarta take bata yana cikin motar .
Motar cadillac escalade ce baâka wuluk , tasha wanki , sabida yadda ko âkura baâa gani a jikinta .
Motar tayi kyau sosai , shiyasa Mishal ta dinga satar kallanta dan sosai tayi mata , ba âkarya motar ta hadâu ..
â Allah ka nuna mun nima tawa irin wannan Ameen ..â ta raya cikin zuciyarta .
Kafin tayi knocking a dai dai saitin window motar.
Cikin âyan sekonni motar ta soma budâewa , âkamshin turaran cikin motar yana sake busowa waje .
Cikin sallama ta shiga motar .
Yana zaune a wajan driving seat , ya jinginar da kansa akan kujerar da yake kai , fuskarsa da wani baâkin glass da ya âkara fito da dogon hancinsa .
Gashi daman fari kuma, sai haskensa ya âkara fito da duhun glass dâin.
Sai da ta kulle âkofar , tukunna ta dâan kallesa ganin bai amsa sallamar nata ba .
Batasan lokacin da ta dâan turo baki kadâan ba , tana fadâin â Uncle Moh..â
Sai a time dâin ya motsa daga jinginen da yake , amma har zuwa lokacin bai amsa mata ba .
âAssalamu AlaikumâŠâ ta kuma yin sallamar .
Yanzu ma bai amsa ba , sai kawai ta juyar da kanta itama gefe , ta dâan jiginar da kanta a jikin kujera tana rufe idanuwa kamar me bacci sabida kwata kwata batasan ma , su âkara hadâa ido balantana har wani abu ya sake hadâasu .
Kusan mintuna uku, kafin ya amsa sallamar a hankali . Sarai Mishal taji sallamar tasa amma ko motsawa itama ba tayi ba , ta sake lafewa a jikin kujera kamar me bacci , ga sanyin Ac shima da yake sake ratsa mata jiki.
Sai da taji ya kunnawar motar , sannan ta dâan muskuta kadâan , yadda za tayi balancing zamanta sosai .
A haka motar ta fice daga gate dâin farko , na biyu da na uku bayan tazara masu yawa da suke tsakanin su, ko wana gate kuma akwai masu kulawa dasu sosai.
Cikin âkanâkanin lokaci motarsu ta fice daga Maitama zuwa Asokoro.
Har lokacin kuma babu wanda yayi magana a cikin su , sai sautin karatun Al- Qurâani da yake fitowa âkasa âkasa .
Duka tafiyar da sukayi bata fi na 15 minutes ba , amma Mishal ji tayi kamar sunyi hour dâaya dan duk ga baki dâaya ta gundura a cikin motar.
A haka har suka âkaraso wani Area so quite babu hayaniya kwata kwata .
A dai dai saitin wani âkatan building , aka budâe musu gate , Securities da kowa da yake wajan, suka dâan russuna kawunan su lokacin da motar take shiga ciki .
Gidan yana da girma sosai da sosai, daga gate zuwa cikin gidan shima tafiyar mintuna uku ne zuwa biyar , ya danganta da speed dâin motarka .
Nan dâin ma akwai maâaikata kowa kana gani harkar gabansa yake.
Parking lot guda biyu ne a wajan , manya ko wacce kuma da motoci a wajan , a âkalla guda biyar ko fiye da haka .
Bai shiga cikin su ba , yayi parking motar daga wani side da yake hannun hagunsa.
Yanayin parking Mishal tayi saurin dâaukar wayarta zata fita daga cikin motar , sai taji saukar muryarsa .
â Are you okay ? Me yasa baki da nutsuwa ne ? Komai ba zakiyi shi kamar mace ba? Namiji ne ke?â
Da mamaki Mishal ta juyo ta kallesa , batasan lokacin da tayi masa wani irritated kallo ba , ji tayi wani haushi da baâkin cikin shiga motarsa yana kamata ,
Ko baâa fadâa mata ba , itama tasan banzan kallo yayi mata ta cikin glass dâin da yake fuskarsa.
Idan ka kalli idanuwanta kuma akwai taruwar âkalla da take âkoâkarin mayarwa , sai kawai tayi rolling idanuwanta kadâan , tana taune lips dâin âkasan bakinta , cikin jin zafi ta furta
â Kayi hakuri Uncle MohâŠâ
â You didnât answer my questionâŠâ ya fadâa cikin kausashin murya .
Sake rolling idanuwanta Mishal tayi , a sanyaye ta furta â Iâm fineâŠâ
âDan karkatowa yayi side dâinta , da finger dâinsa dâaya ya nunata , sannan ya nuna kansa â You donât look fine , it seems idanuwanki sun soma budâe wa , makarantar da kike zuwa ne ya mayar dake haka ko mutanan banza kika hadâu dasu at your young age now ?â.
â Wai me yasa baka nufata da alkairi sai sharri ? Duk wani mugun abu idan yazo bakinsa sai ka dinga hadâani dashi?.
Ko me zanyi sai ka kushe ko kuma ka fadâi aibu akansa , please lets me be âŠ.â Ta âkarasa maganar a zuciye zata juya , shi kuma ya fusgo hannunta , har sai da tayi âkara sabida hannuwanta da taji a murdâe .
Ido cikin ido take kallansa sabida a lokacin shima ya cire glass dâin idanuwansa , ita kuma hawaye yana sakko mata a fuska .
âKara matse mata hannu yayi yanzu saida taji hannuwanta kamar zasu âballe dan ko motsasu bata iya yi .
â Ke har kin isa ina magana ki mayar mun da magana? Yaushe aka haife ki, Yaushe kika girma? Nace yaushe kika girma ?.â Yayi maganar cikin tsawa .
Kuka Mishal ta fashe dashi, tana rintse idanuwanta sabida zafi da hannunta yake mata .
Cikin rawar lips ta furta â Dan Allah ⊠Dan Allah ka sakar mun hannuna zaka âballamunâŠâ
Kallan hannun yayi sabida kalar damâkar da yayi mata , sai ya saki hannun, ita kuma bata jira ya kuma magana ba ta fice daga cikin motar , duk taku dâaya da take , tana ja masa Allah ya isa hannunta da ya matse mata .
_______________
ISTANBUL
Bosphorus StraitđȘ
âž»
To be continued⊠đ„
***