MISHAL

Page 3 / page 4

by @ayshagaladima22

MISHAL



By BLACK QUEEN đŸ€đŸż
***



Book 1 
         page 3 / page 4

_______________
ISTANBUL
  BOSPHORUS STRAIT

Bosphoru Strait na d’aya daga cikin manyan mashahuran ruwa da yake cikin birnin Istanbul.

Waje ne mai kyau da kuma nishad’i. 

Manyan jiragen ruwa na alfarma ( Yacht đŸ›„ïž) suna yawan wucewa a hankali a tsakiyar ruwan, yayinda wasu ke tsayawa domin sha’katawa, hakan yasa wajan yake da matu’kar armashi na ban mamaki . 

A wasu ‘bangarori na ruwan akwai jerin jiragen ruwa da basa tafiya . 

A wani gefen kuma manyan gidaje ne na alfarma da aka gina a bakın ruwan. 

Gida je masu tsada da ke nuna girman arziki ga duk wanda ya mallaki gida a irin wajan . 

Idan aka cigaba da tafiya kuwa , daga farkon Bosphorus har kusan tafiyar awa guda , mutum zai lura da sauyin yanayin wurin. 

Daga cunkoson jirage da motsin mutane , zuwa waje mafi nutsuwa , inda manya manyan gidaje ne a wajan na musamman da yake zagaye da ruwan , gidaje ne da ake kira da Private yali , mallakin manyan mutane da attajirai masu dukiya fiye da tunanin me tunani. 

Daga ‘karshe ‘karshen ginin akwai gida d’aya fita daban sosai , bawai sabida girmansa ba , sabida yanayin yadda aka tsarawa yasha banban da sauran. 

Gidan kata fare ne da aka gina kai tsaye a bakın ruwan Bosphorus .

Ginin yana da launin farı mai had’e da cream a jikin bango da.
Yana d’auke da manyan tagogi masu tsayi daga ‘masa har sama , glass d’in su me kyau kamar mirror sabida yadda take nuna reflection d’in ruwan Bosphorus da yadda ruwan yake motsawa a hankali lokaci zuwa lokaci.

A tsakiyar gidan akwai balcony mai fad’i sosai , anyi shi da ‘karfe me kyau da kuma glass , shima kuma yana kallan saitin ruwa , ga wani sanyi da yake kad’awa a wajan . 

Daga gaban gidan kuwa akwai private dock , wuri na musamman da aka tanada domin saukar Yacht . 

A gefensa akwai wani babban yacht da ya fita sosai da sauran. 

Daga harabar gidan kuwa , yanayinsa gwanin ban sha’awa . 

Green garden, palm trees da kuma fountain da yake tsakiya , ruwansa yana tashi sama sannan ya sauko ‘kasa . 

Hanyar shiga cikin gidan shinfid’e yake da tiles , ga fitilu manya da suke haskawa musamman idan dare yayi . 

Idan mutum ya kalli gidan sosai sai yayi tunanin babu security , sabida babu mutum d’aya da yake cikin harabar gidan. 

Abunda mutane basu sani ba kuwa hidan akwai ‘boyayyun cameras , ‘boyayyan securities da kuma manya manyan automatic door , wanda tun daga farkon taka ginin gıdan, na’ura zata sanar dashigowar ka . 
  
Cikin main entrance d’in gidan , babba ne me kyau shima , bayan babban chandelier da aka saka a saman ceiling , har da wasu ‘kananan fitilu suma da suke bada kalar nasu hasken . 

Bangon wajan ma cream ne sai ‘kasansa da yake d’auke da shinfid’ed’d’en marble tiles mai santsi , har mutum zai iya ganin reflection d’insa idan ya kalli ‘kasan , akwai kuma ‘kofa da take kallan mutum wanda shi zai sa daka da asalin babban falon gidan . 

_____ Cikin falon yana da matu’kar girma , da interiors masu kyau , na asalin masu kudi . 
   Sai dai babu hayaniya ko tarkace a cikinsa , an ‘kawata sa irin yadda duk wanda ya kallesa sai ya sake kallan sa .

Sofa din falon ash and cream ne masu kyau , daga tsakiyar su akwai babban table na glass . 

Daga gefe d’aya a falon kuma kawai floor to ceiling glass windows , suna nuna kai tsaye ruwan Bosphorus da yake motsawa a waje . 

Hasken wajan yana shigowa cikin falon  , yana had’uwa da hasken cikin gida , yana bada kalar nashi vibe d’in cikin d’aukar hankali . 

Akwai mini office setup a cikin falon , ga ‘kamshi da sanyi da yake d’auka . 


Akan d’aya daga cikin Sofas d’in akwai wani matashin saurayi da yake zaune, a shekaru ba zai wuce 27 ba .

Fari ne shi sosai kamar balarabe , tana sanye da simple but expensive outfit . 

Shirt d’in jikinsa dark grey ne , wandan ma haka amma rigar tafi haske da kad’an , kayan kuma sunyi masa kyau sosai , gashin kansa kuma ba’ki ne irin curly d’in nan amma bashi da tsaho sosai .
Kyakkyawa ne Masha Allah san kowa ‘kin wanda ya rasa . 

A gabansa akwai laptop , da yake faman operating  da hannu d’aya , d’ayan hannun kuma yana shan wani drink da yake cikin glass cup . 
 Time to time kuma yana ajjewa ya d’auki wayan da yake gefan system d’in. Itama kuma na ‘yan mintuna ne zai ajje ya ‘kara d’aukar system d’in, haka yake na tsawan lokaci . 

Daga side d’in hagunsa, a wata sofa akwai wata budurwa itama da ba zata wuce shekara 25 ba . 

Tana da kyau sosai dan kyakkyawa ce , bawai irin kyawun yara ne da ita ba , matured beauty ne da kuma zallan confidence da yake kan fuskarta . 

Tana sanye da ‘kana nan kaya , wando black sai over size shirt me d’an girma , yana da multi covers layi a jiki. 

Ta tufke gashin kanta da wani purple ribbon me kyau . 

Itama kuma laptop ne a gabanta , take faman aiki a ciki , lokaci zuwa lokaci sai ta ‘bata rai, ko kuma taja ‘karamun tsaki kad’an . 

A karo na ba’a dadi ta sake wani tsakin. Yanzuma shi tayi hakan yasa saurayin nan ya d’ago kai yana kallanta , sai dai bai ce mata komai ba  ya mayar da hankalinsa kan system din . 

Sai da ta kuma jan tsakin da ya fi na farko tukunna Ahmet ya ajje system d’in yana kallanta .

İta kuma sai ta d’an turo lips d’inta gaba yana cigaba da typing d’in da take . 

“ Aylin ba zaki iya aiki ba tare da kinyi tsaki ba ? You’re busy hissing ! Ba zaki iya rufe bakin ki waje d’aya kuma kiyi focusing akan abunda kike yi ba ?”. Cikin sanyin murya yayi maganar , sai dai muryarsa tana d’auke da nauyi, da alama baisan hayaniya sosai . 

Aylin kuwa d’an d’aga masa gira tayi , tana kallan yadda ya d’an dafe kai yana ya mutse fuskarsa “ABI kasan fa aikin da nake , yanzu idan ban ‘karasa ba , komai ma zai iya faruwa dani , kai kuma ba ‘kwata na zakayi ba , gwanda ka barni nayi tsaki na kawai, ko zanji sanyi a cikin zuciya na .”

“ Ina magana kina mayar mun ko Aylin? Waya hanaki yin aikin tun farko? Kin tsaya charting, jin wa’ka taya zaki zauna kiyi aikin nan ? Kinsan Allah babu bai taya ki wannan aikin , idan bakiyi wasa ba kuma sai na saka ANNE ta ‘kwace wayar naki tunda itace take d’auke miki hankali .”

Jiyowa Aylin tayi ga baki d’aya tana kallansa “ Abi nice nake wasa kuma? Tun safe fa nake zaune a nan ina abu d’aya , yanzu baka ga ‘ko’kari na ba shine har kake maganar wai a ‘kwace mun waya akan wana dalili?”. Tayi maganar cikin turo baki da magana ‘kasa ‘kasa, ga iska da take harara a fakaice sai dai ba Abi take harara ba . 

“ Ai ba zai kin juyar da idanuwan ki ba , kiyi facing d’ina ki fad’a mun maganar da tazo bakin ki mana , tunda baki da kunya , duka aikin da bai wuce kiyi shi a 3 hours ba shine kike maganar kin gaji . 

Kinga yadda babu kowa a cikin falon nan ? Yanzu nan zan bubbuge miki fuskar ki , try me and see” duka maganganun da yayi mata da yaran Turkish yayi , sai wajan da ya saka turanci , gashi har yanzu muryarsa ba wai cikin d’aga hankali yake mata su ba , amma kalaman da yayi anfani dasu , ya nuna dagaske yake maganar da ya fad’a . 

Shiru Aylin tayi tana kallansa , kafin ta d’anja ‘karamun tsaki na ‘kasa ma’koshi , ta rufe system d’inta , da wayarta zata tashi , Ahmet ya janyo ta baya , har system d’in hannunta na fad’uwa , da mamaki ya kalleta , daga sama har ‘kasa kafin ya nuna mata kansa “ Aylin ni kike ma tsaki? Ki kalle ni kiyi mun tsaki kamar wani sa’anki sannan kiyi ‘ko’karin wucewa , ance miki nan wajan da zaki dinga wannan haukan ne ?”.

“ Abi wai mene ne haka? Dan nayi tsaki shikenan sai ka dinga fad’a mun magana san ranka , tsaki na , kuma da baki na nayi ba naka ba , idan bakasan ji ka toshe kunnuwanka ko kawai ka bar wajan , ni banasan fad’a kuma banasan a dinga yi mun fad’a. 

Dan yau rana d’aya mun zauna tare a falo shine komai kaga dama zaka fad’a mun me yasa ba zaka fad’a mun a gaban su Anne ba , sai yanzu daka ga iya mu biyu ne a cikin falon . Please
 ka dena d’aga mun murya , na san ‘yan cina fa , kar ka manta duka 2 years gap ne a tsakanin mu , not as if wai girma na kayi da yawa , shekara 2 ba wani shekaru bane let’s respect each other , na fad’a maka banasan fad’a kuma ni ba’a mun fad’a ko a gida .” Ta ‘karasa maganar nata tana d’auko system d’inta da ya d’an fad’i .

“ Daman taya za’ayi miki fad’a tunda kin zama spoiled brat . Fad’a kuma idan har kina gidan nan ne , kikayi abunda bai dace ba sai nayi magana , ba haka behavior d’in gidan nan yake ba , sannan ke ba zaki zo ki gur’bata mana gida ba , idan ba zaki iya zama da standard d’in gidan nan ba , ki koma inda kika fito .”

“ Abi kenan , kana bani mamaki , kasan banzo gidan nan dan na koma ba ko? Ka fi kowa sanin dalilin zuwa na nan , kuma zanjure komai indai burina zai cika , kai ma kuma duka wannan abun da kake na gane gidan nan ne bakasan zama na a ciki.

Kuma ba zan tafi ba idan har ba Anne bace tace nabar gidan nan 
” ta ‘karasa maganar tana barin falon . 

Kallanta Ahmet yayi har ta bar falon ga baki d’aya kafin yayi wani murmushin takaici yana d’an jan tsaki “ Zamuga yadda burin naki zai cika ai da wannan banzan behavior d’in naki spoiled brat kawai , I don’t even know why Anne zata kawo mana wannan Aljanar cikin gida .” Daga haka ya koma kan abun da yake wato aiki da system d’insa . 

Aylin tana komawa d’aki ta jefar da system d’in akan gado , ko tsoran fashewa ba tayi , wayarta kawai ta d’auka ta kunna data bayan ta saka wa d’akin lock , sannan ta cike kayan jikinta ta saka ‘Karalar riga da ta wuce bom bom d’inta kad’an. 

Harta ribbon d’in da yake kanta sai da ta cire , ta saka hannu tana ya mutsa gashin kanta kad’an . 

Sannan ta shiga WhatsApp bayan messages da yawa sun gama popping up a wayanta , sannan ta shiga archive , inda yake da wasu numbers d’in da kuma group da ta ajje su . 

Wani group me suna No Stress Zone 😎ta shiga , lokacin an tara more than 50 messages , ga tagging d’inta da akayi kuma . 

Har wani murmushi ne ya kamata , tayi saurin gyara zamanta , sabida group d’in yana d’aya daga cikin abun da ya canza mata rayuwa ga baki d’aya , sabida irin abubuwan da suke ciki wanda ba kowa yasani ba sai iya su da suke cikin group d’in. 

Ganin charting d’in baya mata yadda take so , ta tashi ta kashe hasken d’akin ta koma kan gado, har da lullu’ba da duvet sabida ‘kure Ac d’akin da tayi , ga kuma wa’ka da ta saka , tana ji a cikin kunnanta . 


A cikin falo kuwa Ahmet yana cikin danna system d’insa bayan kusan 1 hour da barın Aylin falon , aka sake bud’e ’kofar . 

Kallan time yayi da sauri kafin ya kalli ‘kofar yana jiran wanda ya bud’e ’kofar ya shigo . 

A hankali wani sassanyan murya ya furta “ Assalamu Alaikum.” Sallamar bata fito sosai ba , alamar ko wacece tayi sallamar bakinta bai gama bud’ewa sosai ba , kafin  wata kyakkyawar yarinyar ta le’ko ta window . 

Ya Allah , Kyakkyawa ce sosai har tafi Ahmet kyau, tana da haske sosai , da wani kalar idanu masu kyau , ga ‘karamun baki na yara da allah ya bata red colour sai hakwaranta da suke da gaf a tsakani na yaran da basu soma fanfara ba . 

Gashinta an tufke su waje biyu , an saka pink baby ribbon , le’kowar da tayi jigarta ya d’an nuna shima kuma pink d’in ne . 

Ahmet yana jin muryar wanda tayi sallamar yayi sauri ya ajje system d’insa yana nifo ‘kofar muryarsa cike da fara’a ita kuma yarinyar tayi saurin komawa , daga inda yake yana jiyo sautin dariyar ta da take ‘kyal’kyalawa dashi alamar zallan farin ciki da yake d’auke a muryarta . 

Shima tsayawa yayi daga d’ayan side , yadda ba zata gansa ba , a dai dai lokacin da ta le’ko kanta har ta soma cewa “ Assalamu 
” da muryarta na ‘yan yara yayi saurin kamota , sai ta soma dariya tana zillo lokacin da yake cewa “ Na kamaki.” 

Wani dariyar yarinyar ta sakeyi amma ya ‘ki sakinta sabida d’agata sama da yayi yana d’an mata cakulkuli. 

Da muryarta dariya take fad’in “ Memet , Memet ( Ahmad , Ahmad ).” 

Sai a time d’in ya tsaya , yana kallanta shima a yanzu fararan ha’kwaransa sun fito sosai “ Nunuuu ! Ina Anne.” 

Hanyar shigowa ta nuna masa da d’an mitsitsin finger d’inta , tana d’an rugumar wuyansa, kafin tayi maganar suka jiyo muryarta “ Sai yanzu kasan dani ko Abi? Hankalinka yana kan Nunu tunda ta shigo baka kulani ba sai yanzu daka nutsu”.

Murmushi yayi mata yana takowa inda take , har yanzu kuma bai sauke Nunu data kunkumesa ba kamar ance za’a kwace mata shi . 

Side hug ya bawa Anne, sannan ya sakar mata kiss a kumatunta “ Haba Anne , kishi kuma zaki soma da Nunu? Kinsan in tananan hankalina baya zuwa wajan kowa , ko Nunu?.”

Ya kalli Nunu ita kuma ta d’aga masa kanta, tana ‘kara washe masa hakwaranta kamar ta fahimci maganar da yake yi .”

“ Yayi muku kyau, ni bani waje na zauna , sabida kunga d’ana bayanan shiyasa kuka ware ni , akwai lokaci nima da zan rama .” 

Bin bayanta Ahmet yayi, akan kujerar da ta zauna shima ya zauna , ya d’aura Nunu a cinyarsa , ita kuma ta wani lafe a ‘kirjinsa . 

“ Tuba muke Anne
” ya kuma fad’a yana kai mata wani kiss d’in a kumatu , ita kuma ta d’an harare sa . 

Kyakkyawa ce sosai , ßuna kama da Ahmet , dan kamar photo copy d’in juna , gashi sam bata tsufa ba , babu wanda zai kalleta yace ta haifi Ahmet sabida yadda jikinta yake da kyau , ga Abayar da yake jikinta ya haska fatarta sosai . 

“ Abi kai kad’ai kake zaune a falon ina Aylin? Karkace mun ta fita.” 

Ta’be bakinsa yayi kad’an “ Tana d’aki bata je ko ina ba , kinsan how spoiled she is 
”

“Kai dai Abi bakasan fad’an kirkin yarinyar nan , yanzu in na biye maka sai ka ta zayyano mun lefuka hamsin da tayi maka, Nunu taso muje a canza kaya 
” Tayi maganar zata d’auki Nunu.

Cikin sauri Nunu ta ‘kara ri’ke Ahmet tana fad’in “ Memet.” A shagwa’be .

Shima hugging d’inta yayi yana wa Anne dariya , shiyasa Anne ta tashi ta basu waje . 

“ Nunu kinga Anne ta tafi ko, so kike ta kai mu ‘kara?”.

Kanta ta girgiza a hankali alamar a’a , sannan ta turo masa d’an mitsitsin bakinta gwanin ban sha’awa . 




________________

ABUJA 

Mishal tana zuwa ‘kofar da zata sadata da cikin gidan ta dakata , camera d’in wayanta ta soma shiga ta duba fuskarta , thank god idanta baiyi ja ba , sai shinning d’in hawayen kukan da tayi . 

Sai da ta soma dai daita fuskarta tukunna ta danna wani blue d’in abu, cikin ‘kan’kanin lokaci yayi scanning d’inta , sai babbar ‘kofar ta bud’e . 


Akwai ‘karamar tafiya daga ‘kofar , zuwa kofar da zata sadaka da ainahin ‘kofar falon , tazarar tafiyar duka taku 30 ne . 

Nan d’in ma same procedure Mishal tayi anfani dashi wajan bud’e ’kofar . 

Ga baki d’aya ranta babu dad’i , ita bata yi niyar zuwa ba , ga kuma abunda Uncle Moh shima yayi mata , sai taji zuwan ya ‘kara fita ranta . 

Tana bud’e ’kofar falon ta soma jin hira da dariya yana d’an tashi kad’an kad’an. 

A hankali tayi sallama bayan ta nufi inda take jin hiran. 

Falon yana da girma sosai , yasha kayan alatu na zamani, duka furnitures d’in da akayi anfani dashi ba na nan bane . 

Modern , elegant design. Komai yayi kyau sosai.

Akwai 2 different kind of Sofas a ciki, sai falon ya zama kamar guda biyu ne a waje d’aya . 

Ko wacce kujera design d’inta daban, center d’inta daban da kuma carpet d’inta , ga babbar Plasma da take jikin bango da kuma abubuwan decorations . 

Wajan dinning shima an ‘kawata sa sosai . 

Ga kuma wani waje da akai a cikin falon kamar wajan hutawa , shima kuma yana da kyau sosai .

Dukan su kuma suna wajan a zazzaune .

Maza uku ne da kuma mata biyar , ciki har da Aunty Shukura da take faman dariya tun lokacin da taga Mishal . 

Ita kuma Mishal ta harareta kad’an tana d’auke kanta. 


Wani guy da yake kama da Uncle Moh ne ya d’aga mata hannu, amma bai kai Uncle Moh haske da kyau ba sabida shi d’in kankat ne wajan kyau. 

Fuskarsa akwai murmushi sosai, sa’banin Uncle Moh da baya ma murmushin kwata kwata . 

“ Oyoyo Mimin mu
 ai har na kusa zuwa nayi bikon ki , Shukura tace mun kince bakyasan zuwa . Mune kuma bakya san gani ko kuwa?”. 

‘Dan turo lips d’inta Mishal tayi kad’an ,amma kawai murmushi a face d’inta tun lokacin da taji yayi magana .

“ Yaya Sadiq ka ‘kyale Aunty Shukura , ni bamuyi haka da ita ba . Beside gashi nan ma ai nazo.”

“ Kinzo ko aka zo dake ?” Wani da yake gefen Yaya Sadiq ya fad’a yana kashe mata ido d’aya.

Sai duka falon aka saka dariya .

Shukura ta kallesa ta furta “ Uncle Saleem wallahi kamar ka sani , babu wanda yake karya taurin kanta kamar Uncle Moh shine dai dai ita . 

A kwance fa na tarar da ita tana karatun novel zata soma yimun fili’in batasan hayaniya . 

But kalleta yanzu, tayi tunanin Mamy zan fad’awa shiyasa na ‘kyaleta ai.”

Na kusa da Uncle Saleem da tun d’azu baice komai ba ya kalleta , tare da nuna mata side d’insa da babu kowa .

“ Have a seat Mimi , rabu dasu kinji?.” 

Babu musu ta ‘karasa wajansa ta zauna, kafin ta saki ajiyar zuciya kad’an “ Thank you Uncle Abba , you’re the best
”


“Mu were the worst Kenan?”. Cewar Yaya Saleem yana d’an le’kota.

‘Dauke fuska Mishal  tayi tana d’an d’auke kanta , ganin yadda suke ‘ko’karin yi mata taran dangi. 

‘Yan matan da suke zazzaune duka kyawawa ne , wasu zasuyi mate d’aya da Aunty Shukura , biyu daga ciki kuma za suyi mate da Amalili, sai d’aya da za tayi 30 years a cikin su. 

Ko babu kamanni a tattare dasu , amma akwai jini , wanda zai saka kaga kamar ßuna kama. 

Duk cikin su kuma babu mummuna ,  kyawawa ne duka kamar a familyn su akai wahayin kyau , daga mazan har matan , kuma suna da kyan ido duk da idon Mishal da na Uncle Moh ya fita daban da nasu .


“ Mishal wai me akai miki ne , not like you at all, yau ko d’an tankawar ma bakya yi.” Wata budurwa da take kusa da Aunty Shukura tayi magana me suna, Ameerah.

“ Dole sai nayi magana tukunna zaki zauna a falon ? Please you guys ku barni banasan ciwan kai.”

“ Suwa ne zasu saka ki ciwan kan ?” Cewar Ameerah.

“ Duk wanda yayi magana 
” Mishal tayi maganar tana d’an hararan Ameerah .

“ Okay a kai na zaki huce kenan? Toh bani na kar zoman ba , rataya aka bani
” cewar Ameerah.

“ Whatever
.” Itama Mishal  ta bata amsa .

“ It’s okay Mimin mu, duka wannan abun, ba abun tashin tashin bane . Yanzu ina Uncle Moh d’in yake? Ya shigo ko ya koma?.”

Kafin Mishal tayi magana , d’aya daga cikin ‘yan matan ta furta “ Aunty Feedy , ai ki bar Mimi, kullum bakinta baya zama waje d’aya , indai bata ya’bawa mutun magana ba .

Wai ku ai tana d’an raga muku ne , amma babu wanda ta raina kamar ni da Ameerah . Kuma in batayi wasa ba sai mun fad’awa Uncle Moh yayi mana tsakani.”

“ Ke kuma , ‘yar iya waya saka dake kuma? dake Aunty Feedy tayi magana ko dani? Waya saka bakin ki anan?”

Da sauri Aunty Feedy ta kalli budurwar sannan ta girgiza mata kai cikin wasa da d’an dariyar da yazo mata ta furta “ Zara banasan tsokana , ku ‘kyale mun Mimi na haba, kowa sai faman caccakarta yake .

Ina ruwanku ma idan Uncle Moh ne ya kawota ko bashi ba?”.

“Dan Allah kubar tsokananta haka . Ya isa tunda bata so.” Sai yanzu d’aya budurwar tayi magana, wacce suke kira da AUNTY BABY,  kusan duka ta girmi ‘yan matan, shiyasa kowa yabi umarninta yayi shirun. 

Su kuma su Aunty Shukura suka cigaba da hiran da suke dasu Uncle Saleem. 

Ajje wayar hannunsa Uncle Abba yayi yana kallan Mishal da ita kad’ai sai faman shan ‘kamshi take . 

A hankali ya soma magana yadda su biyu da suke zaune waje d’aya ne kawai zasu ji.

“ Mimi?”. Yayi maganar cikin concern.

“ Naam Uncle Abba .” Itama Mishal ta bashi amsa tana kallansa. 

“ Me ya faru? Ko Uncle Moh ne?”.

“ A’a Uncle Abba ni babu abunda ya mun.”

“ Toh yana ina ? Nasan dai shine ya kawo ki ko?”.

Kanta ta jinjina masa , da fingers d’inta ta nuna masa hanya , kafin ta furta “ A cikin Mota na barshi.”

“ Okay stay here , ki rabu dasu Ameerah banaso kina mayar musu da maganar da yazo duk bakin ki kinji? Ko kina so su Ameerah suje su had’aki dashi?”.

Kafin Mishal tayi magana Ameerah tayi karaf ta amshe . “ Me Ameerah tayi Uncle Abba naji an ambaci suna na..” Sai hiran ga baki d’aya ya tsaya kowa yana jiran yaji amsar da Uncle Abba zai bayar.

“ Mene ne kuka wani tsaya kallo na ? Ko nima zaku tsats tsareni da tanbayoyi ne ?kamar yadda kukai mata?.”

“ No Uncle ba haka bane fa , naji ka kira suna na shiyasa
.” Cewar Ameerah

“ Ke kad’ai ce Ameerah?” Uncle Abba ya tanbayeta yana zuba mata idanuwansa.

Sai tayi saurin girgiza masa kai kafin ta furta “ Toh kayi ha’kuri Uncle..” 

“ Yeah that should be nice of you” sannan ya mayar da kallansa kan Mishal. 

“ Bari naje na dawo Mimi 
” 

“ Shikenan Uncle Abba ! Take care 
” Mishal ta bashi amsa tana sakar masa murmushin ta .

Yana fita Zara ta taso ta zauna a kusa da ita , tana d’an d’aga mata girarta guda d’aya . 

“ Dagaske wai Mimi  ba zaki fad’a mana ba ko Uncle Moh yana gidan nan sai wani faman sha mana ‘kamshi kike yau
”

‘Karamun rankwashin wasa Uncle Saleem ya kai mata shima yana mi’kewa tsaye “ Gulma Zara ! Gulma dai babu kyau 
”

“ Uncle Saleem ai ba gulma bane , kawai tanbayarta nayi , ai da gulma za muyi ba zama mu bari kaji ba .”

“ Naji uwar magana .” Uncle Saleem ya bata amsa yana kallan Yaya Sadiq .

“Yaya Sadiq ba zaka fita ba ko anan zaka zauna?”.

“ No Saleem ! Jira nake ai ka gama surutun naka kafin mu tafi , tunda abun naku turn by turn ne .”

Gira biyu Saleem ya d’aga masa , kafin ya shafa kansa kad’an. 

“ Yi ha’kuri Yaya Sadiq , duk wannan yarinyar ce .” Ya nuna Zara da ta d’an murgud’a masa baki kad’an.


“ Ka ma fad’i gaskiya , duka yaushe Zarah tayi magana ma, kai dai mu tafi kawai .” yaya Sadiq ya bashi amsa shima .

Da haka suka fita daga falon ,yayi saura ‘yan matan kawai da suke hira abun su. 


PARKING LOT 

Tunda ta fita daga cikin motar bai sake motsawa ba , yananan a yadda yake . 

Sai kansa da ya jinginar akan kujerar da yake , ya lumshe idanuwansa duka biyu, yana sauke nunfashi a hankali a hankali. 

Gashi  idanuwansa biyu , amma da alama yana tunanin wani abune a cikin ransa .

A haka aka d’auki dogon time , har zuwa fitowar Uncle Abba da ya nufo motar . 

Yana zuwa side d’in driver seat ya nufa , sannan yayi knocking ‘kofar sau biyu. 

Uncle Moh da yake ciki , bai amsa masa ba kuma bai motsa daga inda yake d’in ba .

Ganin hakan yasa Uncle Abba ya zagaya d’ayan side d’in, ya shiga cikin motar, bakinsa d’auke da sallama .

Babu musu Uncle Moh ya amsa masa sallaman a hankali yana bud’e idanuwansa akan Uncle Abba da shima yake kallansa .

“ Bacci kake ne Uncle Moh? Yau kuma ko zaman motan ne yake maka dadi’?”cewar Uncle Abba , yana kallansa da full concern akan fuskarsa.

Hannu Uncle Moh ya saka a gefen wuyansa , ya d’an shafa kad’an kafin ya bashi amsa da “ No ! Why ?”. 

Cikin girgiza kai Uncle Abba ya furta “ No am just asking ne , na d’auka ma zaka shigo ne , even though nasan a wannan time d’in rigimar Mimi ce kawai zata shigo da kai nan by this time .”

“ Tayi wani abune yanzu?” Uncle Moh yayi maganar yana zubawa Abba idanuwansa masu kai fi.

“ Babu abunda tayi , amma ka saka sai tsokanarta ake tayi, nasan yanzu ta cika tafi fam, duk wanda ya ta’bota akansa zata wuce , bakinta kuma bayajin control , sai ta fad’i abunda take san fad’a 
”

“ Hmmm
” Kawai Uncle Moh yace , sabida tuna yadda tabar motar a yanzu . 

Bai tsaya ‘bata lokaci ba ya kunna motar , Uncle Abba kuma ya furta “ Za muyi nisa ne ?”.

“ No why?” Uncle Moh ya fad’a . 

“ Nasan su Saleem da Sadiq yanzu zasu fito su
” bai ma ‘karasa ba ya hango fitowar su suma suna nufar motar , sai ya canza maganar sa zuwa “ Gashi nan ma sun fito
” 

Uncle Moh bai kalli wajan ba , har sai da suka ‘karaso. 

Daman sunyi tunanin yana driver seat tunda motarsa ce . 
Kai tsaye side d’in suka nufa , shi kuma ya d’an sakko da glass d’in window d’in yana kallan su .

“ Uncle Moh
 ina wuni “ cewar Sadiq yana mi’ka masa hannu.

Babu musu Uncle Moh ya mi’ka masa nasa “ Sadiq kana lafiya?”.

“ Lafiya ‘kalau ! Saukar Yaushe kuma?”. 

Shiru Moh yayi masa lokacin da yake shaking hannun Saleem da shima yake mi’ka masa hannun . 

Shima tashi fuskar cike da fara’a lokacin da yake gaishe da Moh.

“ Uncle Moh ! Barka da dare , ya hanya ?”.

“ Alhamdulillah Saleem , ya kake .” 

“Lafiya kalau Uncle Moh.”

Kallan Sadiq ! Moh yayi , lokaci d’aya Sadiq ya d’an d’auke kansa yana sun kuyar da kansa a wayance a wayance .

“ Kafun na amsa maka , ka tabbata ka ta nadi duka amsoshin tanbayana . Now ku shiga motar mu tafi.” Yayi maganar cikin command .

Uncle Abba da yake gefensa ya kalle su , yana jinjina musu kai lokacin da suka had’a ido. 

Babu ‘bata lokaci Saleem da Sadiq suka shiga bayan motar , shi kuma Moh ya kunnata, cikin wani speed suka fita daga cikin gidan. 

A cikin gida kuwa 
..
 Tuni Mishal ta ware , wani new chapter d’in hira aka bud’e . 

Ita da Zarah da Ameerah . 
  Aunty Shukura da Aunty Feedy da kuma Aunty Baby su kuma sun koma main falourn suna hira ‘kasa ‘kasa , kamar wani abun suke tattaunawa a tsakanin su .


Position d’in zaman su a yanzu Ameerah tana zaune akan carfet ta d’anyi crossing legs d’inta . 

Ita kuma Amalili tana daga kwance , ta d’ora kanta akan cinyar Ameerah, tana d’an danne danne a wayanta . 

Zarah kuma tana facing d’in su itama kuma wayar ne a hannunta . 

Can kuma sai ta d’an d’ago ta kalli fuskar Mishal , har ta d’auke idanuwanta sai kuma ta sake kallanta . 

“ Wait Mimi , ina abun hancin ki ne?” Ta fad’a tana d’an ta’ba nata hancin.

Sai time d’in Ameerah ta d’an jiyo da fuskar Mimi dan ta duba itama . 

Babu musu kuma Mimi ta kalleta .

Cikin I don’t care tare da turo bakinta kad’an cikin rashin damuwa ta furta “ Uncle Moh ne ya amsa 
”

Cikin zaro ido Zarah ta ce “ Amma bai miki fad’a ba ko?”

“ Kema kinsan idan har ya gani sai yayi fad’a me yasa zaki barshi ma ya gani, idan dama bawai kinyi niya ya gani ba .”cewar Ameerah .

‘Dan ta’bota Zarah tayi , da hannu tana bata alamar ta bari mana , amma Ameerah ta ta’be bakinta kamar bata ga abunda Zarah take mata ba .

Mishal kuwa daga kwancen da take ta kalleta , kamar zata tanka mata, sai kawai tayi ‘karamun ‘kwafa , ta mayar da fuskarta saitin Zarah.

“Kema kinsan halin Uncle Moh , ko bai mun fad’a yanzu ba definitely sai yayi mun tunda duka wannan abubuwan bayasan ganin su , ni na manta ma dashi a fuskana shiyasa na manta bancire ba .”

Kanta Zarah ta jinjina mata , tana d’an shafa zuciyarta alamar relief . “ Insha Allah bazai yi ba , duk da bani da wannan full confidence d’in.”

“Is normal fa
.” Mishal tayi maganar tana d’aga kafad’unta, amma zuciyarta fall tsoran gamuwar ta da Uncle Moh take, idan yace zai mata fad’a . Yanzu ma ya lafiyar kura balantana ma taga nama tayi karin maganar tana ‘kara ta’be bakinta kamar abun baiyi wani shaking d’inta ba .

“ Maganin ki kenan
 gobe ma ki sake ..” Ameerah bata kai ‘karashen maganar ta ba, Zarah da Mishal suka kalleta duk su biyu .

Sai a lokacin Mishal  ta mi’ke zaune , tana bin Ameerah da wani banzan harara, kafin taja tsaki ta cigaba da danna wayar hannunta .

“ Kedai Ameerah bakiji dad’in halin ki ba wani lokacin , yanzu mene ne abun farin ciki idan Uncle Moh d’in yayi mata fad’a? Me zakiyi gaining a ciki?”

“ Babu abunda zanyi gaining Zarah , amma gaskiya ce sai na fad’a , in ke kina jin tsoran gaya mata ni sai na fad’a mata , sai dai taji haushi na , kuma babu yadda za tayi dani d’in ba .”

Wani murmushi Mishal tayi tana bin Ameerah da wani irin kallo . 

“ Abinki ya isheni haka Ameerah, tun d’azu sai faman fad’amun magana kike ina ‘kyale ki, kin san halina wallahi kika kaini bango ba zamu kwashe lafiya da ke ba. 

“ Mimi rabu da ita duk bata kai haka ba, zo mu fita waje mu d’an sha iska abun mu dan nasan su Yaya Sadiq by now basa cikin compound d’in nan .”

Without second thoughts Mishal ta amince suka mi’ke, daga ita har Zarah babu wanda ya kalli Ameerah suka nufi hanyar barin falon . 

Sai a lokacin su Aunty Baby suka kalle su. “ Ina zakuje haka?”

“ Aunty Baby zamu d’an za gaya compound ne , kinsan zama waje d’aya sometimes is so boring .”cewar Mishal.

Ganin su biyu a tsaye Aunty Baby ta mayar da kallan kan Ameerah da take danna waya kamar bata san dasu ba .

“ Ku kad’ai za kuje?” Tayi tanbayar har lokacin kanta yana kan Ameerah da bata d’ago ba .

Su kuma da “ Yess.” Kawai Zarah ta amsa mata , sukai ficewar su ba tare da jiran jin wani second thoughts daga gareta ba . 

Lokacin da suka fita compound d’in gidan, sai da Mishal ta rufe idanuwanta , ta bud’e hannayenta duka biyu tana sha’kar iskar da take kad’awa. 

Hakan kuwa yana d’aya daga cikin abunda take so a duk lokacin da dare yayi. 

Sai kuma ta kalli can side d’in da Uncle Moh yayi parking d’azu ganin babu motar sa a yanzu ta saki ajiyar zuciya mai ‘karfi. 

Bata aune ba , Zarah ta d’an ta’bota da wasa “ Kina dubawa ko Uncle Moh yananan ki fece kenan?”

“ Na fece ko mu fece?” Amalili ta fad’a , sai dukan su kuma suka soma dariyar kansu . 

âž»

To be continued
 đŸ”„


BLACK QUEEN đŸ€đŸż
***