MISHAL

Page 5/ page 6

by @ayshagaladima22

MISHAL



By BLACK QUEEN đŸ€đŸż
***



Book 1 
         page 5/ page 6

9 P.M.

Har zuwa wannan lokacin Mishal da Zarah suna filin gidan suna sha’kar yanayin weather garin. 

Kasantuwar dare ne , sai yanayin garin yake bada wani cool vibe me dad’i. 

Kusan sai da suka zagaya compound d’in gidan , ga securities ga kuma hasken fitilu a ko wana ‘bangare na gidan. 

Idan sun ga dama su tsaya su d’anyi hira , idan sun ga dama kuma suna tafiya suna hira abun su . 
 Basu lura da yadda lokaci yaja sosai ba , sai da wayar Zarah ta soma ringing ta kalli mai kiran kafin ta cewa Mishal “ Aunty Feedy ce .” 

Kanta Mishal ta jinjina mata , suna cikin tafiya Zarah ta d’aga kiran.

“ Zarah kuna ina haka? Ba dai fita kukai ba ?”. Aunty Feedy ta fad’a cikin wayar .

“ No Aunty Feedy muna compound ne , ba nisa mukai ba .” Itama Zarah ta bata amsa .

“ Kuna tare da Mishal kenan?” Aunty Feedy ta sake tanbayar ta .

“ Yes muna tare 
” cewar Zarah
.

Daga can ‘bangaran Aunty Feedy ta d’anyi shiru kamar tana yi wa wani magana a cikin falon da take , kafin ta cewa Zarah . “ Okay Aunty Baby tace ku dawo ciki , almost 9 yanzu , any moment from now zaku koma gıda 
” 

“ Okay shikenan , gamunan..” shine amsar da Zarah ta bata kafin tayi hanging call d’in.

“ Kinga har sun soma neman mu, wai 9 yayi mu koma ciki, kinsan halin Aunty Baby ko?”. Cewar Zarah..

“ Ke kuwa zata koma gidanta mana, ke baki da aure amma kin manta Aunty Baby na dashi, ko kina so ta kawo miki rainan AMEER da AMEERA ?”. Mishal tayi mata tanbayar cikin jiran amsar ta .

“ No no no ! Kinsan ina da san yara amma kuma bani san raino. Ko ni na haifi Baby ke zan kawowa kiyi mun rainan sa , kinsan i don’t like stress 
.” Zarah ta bata amsa tana kashe mata ido d’aya, fuskarta kuma ta sake fad’ad’a da murmushin da take yi.

‘Karamun harara Mishal tayi mata , kafin ta kai mata kallan sama da ‘kasa tana cigaba da tafiyarta , kafin ta bata amsa “ In kin ga dama kice ni zan d’au miki cikin ma , ‘yar rainin wayo. Tunda ance miki Nanny ce ni.”

“ No vex mana Mimin Mamy da Baffanta.” 

“ Nabi Vex da gudu, common malama ni yi mun shiru.” Mishal ta fad’a lokacin da suka ‘karaso ‘kofar da zata sadasu da falon. 

Cikin sanyayyar muryar su sukai sallama , sabida yadda suka ji falon yayi shiru ba kamar d’azu ba . 

Yanzu an kwashe ga baki d’aya chop chop d’in da aka kawo d’azu, komai ya sake yin neat , babu abunda yake tashi a cikinsa sai ‘kamshin turaran wuta. 

Aunty  Shukura , Aunty Baby da Aunty Feedy dukan su basa cikin falon , sai Ameerah kawai da take kwance akan 3 sitter , ta d’ora kanta akan pillow , tayi crossing legs d’inta ,  ta saka waya a kunnanta alamu sun nuna waya take sabida yadda bakinta yake motsawa kad’an kad’an , amma kuma ba’a jin mai take cewa sabida tayi very low da muryarta, yadda iya na cikin wayar ne kawai zai iya jinta . 

Daga kwancen da take ta kalli su Zarah, kafin ta d’anyi magana kad’an tana kashe wayarta . 

Sai a lokacin ta amsa sallamar da sukayi. 

“Ameerah ina su Aunty Feedy kuma?” Mishal ce tayi tanbayar tana dan kallan falon ko zata ga inda suke . 

Da hannu Ameerah ta nuna mata stairs kafin ta mi’ke zaune . “ Basu dad’e da hawa sama ba , nasan suna d’akin Aunty Feedy, naji Aunty Baby tace zata amsa sa’ko a wajanta, ita kuma Aunty Shukura  tace tanaso tayi magana  da both of them , shiyasa suka wuce sama dukan su .” 

“ Ahhhh ahhhhh ! Ameerah kinyi yarinya da yawa , shiyasa kunnenki ba zai d’auki karatun manya ba 
” cewar Zarah 


A maimakon ta kalli Zarah da tayi magana sai ta kalli Mishal da take ‘ko’karin zama “ Kema dai kinsan wa zaki cewa haka, amma ni kam na wuce kicewa yarinya duk da muna da shekaru d’aya amma ko banza soon za’ayi aure na , wasu fa ko samarin ma ba su dashi duk kyaun su
.” 

Kamar wacce tayi magana da dutse haka Zarah da Mishal sukai banza da ita , har sai da ta magantu ta sake fad’in “ ko ba haka ba?” Yanzu ma sukai mata banza kamar basu san abunda tace ba . 

Hakan yasa Ameerah ta d’an ja siririn tsaki dan ta tsani tayi magana a shareta. 

*

Suna zaune a haka su Aunty Feedy suka sakko ‘kasa suna hira da dariya kad’an kad’an akan conversation d’in da suka fito sunayi. 

Lokacin 10pm na dare har ya kusa yi sabida daga shigowar su Mishal zuwa time d’in da suka sakko yanzu an shafe kusan 40 minutes . 

“ ‘ Yan ‘kanne na ba zaku kwanar mana ba fisabillahi?”Aunty Feedy tayi maganar cikin kashewa su Zarah ido. 

Mishal ta soma mi’kewa tana gyara veil d’inta , dukan su suka soma dariya musamman Aunty Feedy da ta nufo side d’inta . 

“ Yanzu Mimi gudun gida na kike sai kace wata ‘yar kishiya? Idan kikai aure so kike mu soma gudun gidan ki tunda bakya zumunci ko?”

“ A’a Aunty Feedy duk ba wannan bane, nifa na fad’a muku bana san hayaniya , duk wanda yake san zumunci ba ga waya ba 
”

“ A ta’kaice dai zamu saka miki ciwan kai ko?” Aunty Baby tayi maganar tana d’an kawo mata hararar wasa .

Sai a lokacin Mimi ta d’an turo bakinta tana guna gunai amma ba’ajin me take cewa .

Hakan yasa Aunty Shukura tayi murmushi tana tsayawa a side d’inta itama “ Aunty Baby ku dena tsokananta haka , ita kad’ai ma gudun kanta take , balantana ma ace taje wani wajan . Muma mun zamar mata dole ne babu yadda zata yi da mu 
 yanzu haka Driver yazo yana compound .

Aunty Baby ke ba hanya d’aya zamuyi dake ba , mu yanzu Mamy ko Baffa zasu soma kiran mu tunda 10 ya kusa.”

“ Ai mu ca akai miki su Mamyn basa san mu ko?”

“ No vex Aunty Feedy, yanzu idan kuka soma musu keda Aunty Shukura har mukai gobe baku gama ba . Mudai mun tafi
.” Cewar Ameerah.

‘Kyautar harara Aunty feedy takai mata ita kuma tayi saurin hugging d’inta tana dariya . 

Mimi kuwa idanuwanta har sun soma lumshewa dan duk inda 10 yayi toh tayi bacci, sabida jikinta mutuwa yakeyi a wannan time d’in.

Shiyasa bata tsaya bin conversation d’in su ba tayi hugging Aunty Baby, sannan tayi hugging Aunty feedy ma , tana fad’in “ am sleepy now 
.. Good night you all .” 

The same hug suma suka kai mata, Tayi fitowarta waje bata tsaya jiransu su taho tare ba . 

Lokacin da ta fito compound already akwai 2 benz ba’ka’ke da sukai parking a kusa kusa, ko wace mota tana nan ‘kal’kal da ita , tasha wanki babu alamar datti ko ‘kura akan su kwata kwata. 

‘Daya daga cikin motar ta nufa , cikin sauri driver ya fito , jikinsa sanye da fararan suit , sai ba’kin takalmi, da kuma ba’kin belt, shigarsa ßak ta rich drivers . 

Cikin girmamawa ya gaishe da Mimi sannan ya bud’e mata back seat . 

Itama da fara’a ta amsa masa kafin ta shiga . 

Yana rufe ‘kofar ta sauke ‘karamar ajiyar zuciya sabida yadda taji ta soma yin relax babu surutu ko hayaniya a inda take ga baki d’aya . 

Ko 2 minutes ba’ayi ba su Zarah suka fito, itama kuma Zarah motar da Mimi ta nufa ta shiga , Aunty Baby kuma da Ameerah suka shiga d’aya motar. 

Ganin Driver ya tayar da mota Ameerah kuma bata shigo ba ta furta “ Malam Sani , Ameerah bata 
‘Kara
.”

Bata ma ‘karasa ba Zarah ta rigata “ No we can go, tace yau a gidan Aunty Baby zata kwana gobe ko jibi sai ta dawo . Wai mu fad’awa Mamy.”

Ta’be baki Mimi tayi “ Mu fad’awa Mamy ko ta fad’a mata ? Baki muka fita ko kuma ‘yan aike ta mayar da mu? Yadda bata fad’a mata ba lokacin da ta fito wallahi babu mai sakani fad’a, saura kema naji bakinki , ai tana da waya sai ta kirata ta fad’a mata , we’re not her messenger.”

“Mimi it’s not a big deal”.

“ You’re telling me is not that big Zarah ? Kin manta Mamy yadda take so strict akan fita without notice? Wallahi banyi laifi ba , ba zatasa a huce akai na ba .” Mimi ta ‘karasa magana tana ‘kara jinginar da kanta a bayan motar. 

Babu abunda Zarah tace sai dariya kawai da tayi . 

A haka both motocin suka fita, sannan ko wacce tayi separate way d’inta dan ba hanya d’aya suka bi ba . 

*
Not too long suka dawo gida, sabida duka 20 to 22 minutes ne ta zaran tafiyar da sukai. 

Mimi sai da ta kalli wani side a gidan , ganin babu motar da ya fita da ita , ta saki wani ajiyar zuciya. 

Itama Zarah ta kalli side d’in  a hankali ta furta “ Thank God Uncle Moh bai dawo gida ba . 

Zo muyi sauri mu bar wajan nan kar tsautsayi ya had’a da mu.”

Ba musu Mimi tayi mata knodding kanta , suka wuce cikin gida.

Falon sai faman tashin ‘kamshin turare yake, an ‘kara tsaftace shi , komai na cikin falon kuma an sake goge sa sosai da sosai , so Masha  Allah. 

Dukan su basu zauna a falon ‘kasa ba , kowa ya nufi hanyar d’akinsa . 

Mimi tana shiga d’aki sai da ta kwanta a kan gado na kamar mintuna 15 , ta rufe idanuwanta kamar mai bacci tana hutawa . 

Sai da taga baccin yana neman d’aukarta dagaske , ta mi’ke ta cire kayan jikinta , sannan ta wuce toilet. 

Bata ji’ka kanta ba , dan akwia wani hula na leda da ta saka wanda zaiyi protecting gashinta daga ji’kewa , sannan ta kunnawa kanta warm water , har wani lumshe idanuwanta take sabida yadda ruwan yake ratsata . 

Ta dad’e a cikin ruwan kafin ta soma wanka da sabulanta masu tsadan haske , su kad’ai sai tashin ‘kamshi suke . 

Atleast sai da tayi more than 25 minutes a toilet , bayan wanka da ta gama sai da ta ‘kara kunnawa kanta wani ruwan na musamman. 

Sannan ta d’auki mini pink towel ta d’aura a ‘kirjinta , duka da kad’an ya wuce cinyarta . 

Sai kuma ta d’auki wani dogo ta lullu’ba ga baki d’aya jikinta . 

Tana fitowa , sai ta soma tsane ruwan jikinta ,sannan ta bawa jikinta 5 minutes sabida ta ‘kara bushewa da kyau , sannan ta soma Night routine d’inta da ta saba duk dare kafin ta kwanta . 

After ta gama duka shafa abubuwan skin care d’inta , 
Sannan ta d’auki humra masu ‘kamshi da dadi ta shafa , ta ‘kara da body milk khumra. 

Ya Allah . Kunsan yadda turarukan maiduguri yake da d’inbin ‘kamshi musamman idan Kasamu turare a wajan wacce ta iya ba’a magana. 

Toh wannan ma turarukan da tayi anfani dasu ‘karshe ne wajan dad’i . 

Har wani sanyi sanyi zaka ji zuciyarka tana yi dan ya bad’e ga baki d’aya d’akin, uwa uba kuma wacce ta saka a jikin nata . 

Tana gama wa ta d’an taje kanta kad’an , sannan ta d’auko night dress d’inta na camisole maroon colour , hannun rigar siririne sai kuma wandon da yake d’an ‘karami duka da kad’an ya rufe mata bom bom d’inta . 

Tana duba wayanta taga da charge almost 70 , ta ajjeta a gefen pillow d’inta , sannan ta kashe light, ta bar d’akin so dummy, sannan ta kwanta tana sauke a jiyar zuciya. 

Bata wani jima ba bacci ya d’auketa



**
4:50am Mishal ta farka daga baccin da take , tana d’an mi’ka kad’an, sai ta kalli gefen gadon, anan ta tarar da Joy kwance . 

Bata wani damuna ko tsorata dan ta riga ta saba tashi ta ganta kwance a wajan.

Sai dai ta d’auki kusan mintuna 5 tukunna ta mi’ke ganin ko wana lokaci za’a iya kiran sallah . 

Sai da ta d’an kama ruwa tukunna tayi alwala da brush da kuma d’an abun da ba’a rasa ba a cikin toilet tukunna ta fito .

A lokacin Joy bata cikin d’akin, shiyasa bata tsaya dogon tunani ba ta suturta jikinta , ta tayar da sallah .

Nafila ta soma yi kafin sallar asuba . 

Da ta idar , tayi azkar d’inta , da karatun al-qur’ani na d’an lokaci dan ta dad’e sosai akan dadduma har sai da hasken safiya ya soma yayewa tukunna ta ajje al-qur’anin ta nannad’e daddumar itama ta mayar da ita muhallinta . 

Kan gadon ta soma gyarawa, ya dawo kamar ba’a kwanta akansa ba, sannan ta gyara d’akin ta share, ta wanke toilet d’inta . 

Tayi wanka sosai, as usual tabi routine d’inta na morning skin care , sannan ta shirya cikin simple material gown, dark purple sai ado adon rose flower da yake jiki light purple da kuma dark yellow, da d’an abun bishiyarsa green kad’an a jiki. 

Material din yayi kyau , kuma simple babu wani ado a jiki da simple material d’an akai anfani. 

Da’kyar ta iya taje kanta sabida yadda yake bata matu’kar wahala sosai. 

Sannan ta d’auro light purple d’in mayafi ta d’aura akanta yadda gashin kanta bazai fito ta baya ba . 

Little lip gloss sai faman shinning yake a bakinta . 

Tayi kyau sosai da sosai, Golden eyes d’inta ya fito sosai duk da bata saka kwalli ba. 

Ga dogayan eye lashes da take dasu , ita kad’ai sai faman ‘kamshi take .

Tubarkallah Masha Allah . 
Kyau iya kyau Allah ya bata , irin kyaun da ko da kud’in ka sai da rabanka . 

A d’akin akwai inda akayi sa specifically sabida takalma. 

Kuma ciki duk takalma ne different designers . 

A ciki ta d’auki white flat shoe , ta d’auki wayarta tayi hoto kad’an kala kala, sannan ta sake fesa turare kad’an, ta fito daga cikin d’akin . 

Bata sakko ‘kasa ba , sai ta bi wani hanya , bayan d’an ‘karamun corridor akwai ‘kofa a wajan . 

Tana bud’ewa ga baki d’aya wani part d’in ne ya fito daban, har yafi wanda ta baro kyau da tsaruwa. 

Kayan ciki duka modern design interiors ne aka saka , ko ina yayi kyau . 

Bayan falon da yake wajan, akwai stairs shima , da zai saukar da kai falon ‘kasa .

Ga tashin ‘kamshin da yake faman yi. 

Direct ‘kasan ta sakko, bayan falon da yake ‘kasan, ta bud’e wani ‘kofa irin doguwar nan . 

Nan d’in ma akwai wani mini falon amma bashi da girma sosai , kayan ciki kuma duka milk colour ne har kujeru da carfet . 

Wani ‘kamshi da sanyi ya daki hancinta , har sai da ta saki ajiyar zuciya , kafin tayi sallama a hankali tana shiga cikin falon

.



Mutane hud’u ne zaune kan kujera sai Yaya Sadiq da kuma Aunty Shukura da suke tsaye gefen dining, Yaya Sadiq yana ri’ke da cup na ahlan wa sahlan, ga black tea a ciki da kad’an ya wuce half . 

Daga cikin mutanan da suke zaune a falon kuma akwai Uncle Saleem, Sai kuma wasu manyan dattawa guda biyu, maza kansu da d’an furfura kad’an alamar manyanta, sai kuma mace itama zatayi 45+ a shekaru , tana sanye cikin leshi me kyau da sul’bi, hannunta guda d’aya carbi ne da take faman ja lokaci zuwa lokaci.

Wajen matar Mishal ta soma zuwa bayan tayi sallama , fuskarta cike da annashuwa tayi mata side hug kafin ta furta “ Mamy ina kwana..”

Wacce ta kira da Mamy murmushi tayi mata itama , sannan ta mayar mata da hug d’in da tayi mata , fuskarta cike da annashuwa ta sakar wa Mishal kiss a goshi , cikin kulawa ta furta “ Mimi har kin tashi .”

“ Na tashi Mamy na .” Cewar Mishal , kafin ta juya kusa da d’aya mutumin da ya fi kusa da Mamy , har yanzu fuskarta da fara’a cikin girmamawa ta furta “ Baffa ina kwana, fatan kun tashi lafiya .”

Shima Baffa murmushi yayi, fuskarsa cike da kulawa ya furta “ Mimi na ya kike .”

“Lafiya ‘kalau .” Ta bashi amsa , sai d’ayan mutumin da yake kusa da Uncle Saleem da shima ta gaisar .

“ Uncle Bashir , ina kwana .”

“ Lafiya ‘Kalau .” Ya bata amsa babu yabo ba fallasa daga nan  ta kalli Uncle Saleem da shima yake kallanta “ Uncle Saleem ina kwana.”

Ya amsa mata da “ Lafiya ‘kalau Mimi
” daga nan kuma ta kalli Sadiq da Shukura tana fad’in “ Yaya Sadiq ina kwana , Aunty Shukura ina kwana .” Lokaci guda .

Duka suka kalleta , suna amsa mata da lafiya ‘kalau Mimin mu. 

Mi’kewa tayi daga wajan Mamy ta nufi wajan su, har zuwa lokacin kuma Yaya Sadiq yana ri’ke da cup d’in hannunsa.

Cikin tsokana ta kallesa tana le’ken kofin hannunsa “ Yanzu Yaya Sadiq dad’in me kake ji idan kasha black tea d’in nan ? Baya saka jin yunwa ?.” 

“ Yunwa kuma Mimi , sai kace irin cikin kine dani? Kullum cikin cin junks food .”

“ But atleast yafi black tea d’in nan da kake sha .”

“ Says who? Kullum shiyasa bakya ‘kara ‘kiba , yanzu ina hureki fad’uwa ‘kasa zakiyi fa .”

“ Aunty Shukura kina jin dai abunda yafe fad’a mun amma ba zaki saka baki ba ko? .”

Hararar wasa Shukura tayi mata , tana d’aukar ’karamun tray d’in da ta gama shiryawa “ Lokacin da kika tsokanosa ai bakiyi shawara dani ba .”

“ Kedai kawai dan saurayin kine shiyasa zaki shigar masa .” Mishal tayi maganar ‘kasa ‘kasa yadda ba zasu jiba , amma Yaya sadiq ya jita, shiyasa ya sakar mata ‘karamun ran’kwashi aka , ta dafe tana fad’in “ Ashhhhh Yaya Sadiq .”

‘Dan matsowa yayi kusa da ita , yadda zata ji me yake cewa shi kad’ai “ Wallahi ki kiyaye ni , idan ba haka ba yanzu sunanki ya tafi wajan Uncle Moh 
”

“ Ah shikenan kuma bazan fad’i abunda yake rai na ? Ai gaskiya na fad’a kuma ai shima Uncle Moh yasan gaskiya na fad’a kuma ko ka fad’a masa sai yaji ta baki na eheee , kasan dai ba kayi mun sharri wajan sa .”

“ Oh Allah ! Tunda baya wajan , bakın naki har ya bud’e ko? Sannu Mimi , anjima zaki maimaita wannan maganar.”

Gwalo Mishal tayi masa , Tayi saurin barin wajan, shima murmushi yayi me had’e da dariya , yana dawowa cikin falon .

Kallanta Mamy tayi lokacin da take shan tea d’in hannunta “ Mimi kinyi breakfast kuwa ?”.

Cikin girgiza kai ta furta “ A’a Mamy , banyi ba tukunna .” 

“ Toh maza kije ki samu abu ki saka a cikin ki banasan jin No as your answer kinji?.”


Kallanta Uncle Saleem yayi yana d’aga mata gira “ Wannan yarinyar ai bata cin komai da safe , sai dai ta sha ruwa ta tafi ta danna waya .”

Cikin turo lips Mishal ta furta “ Kai Uncle Saleem banda sharri .”

“ oh nine ma zan miki sharri ko?”. Yayi maganar yana d’an zaro ido kad’an .

Cikin marairaicewa ta furta “ Uncle Saleem dan kaga Uncle Abba bayanan shiyasa kake mun haka ko?”.

“ Eh din anyi d’in.”ya bata amsa.

Kafin tayi magana Uncle Bashir ya kalleta har yanzu fuskar tasa ba yabo ba fallasa .

“ Mimi ya makaranta ? Ba dai kya tsayawa yin wannan shiriritan naki da shagwa’ba kamar wata yarinyar goye ko?”.

Mamy da Baffa ne kawai suka kalleta banda su Uncle Saleem da basu ma maida hankali akan maganar ba . 

‘Karamun ya’ke kawai tayi masa kafin ta furta “ Aa Uncle Bashir .”

“ Okay Good .” Ya bata amsa kafin ya cigaba “ Ki zauna ki nutsu kiyi karatun da ya dace karki biye wa ‘kawaye ko kuma samari , abunda yafi dacewa yanzu daku karatu ne , na fad’awa Ameerah ma. Kar naji kar na gani ku bari idan time d’in ku yayi sai kuyi abunda ya dace Allah , Allah yayi muku albarka .”

Yanzu kam ‘karamun ya’ke tayi, da ‘kyar ta iya ce masa “ Amin.” Sai dai kana kallan fuskarta zaka gane bata ji dad’in maganar ta saba .

Shiyasa ko zama ba tayi ba , ta d’auki excuse zata fita daga falon , sai shima Saleem ya fito , daga nan Sadiq da Shukura suka biyo bayan su , yayi saura Baffa , da Mamy da kuma Uncle Bashir da yanzu fuskarsa take d’auke da fara’a .

Ganin sun fice duka Uncle Bashir yayi gyaran murya yana kallan Baffa da yake shan shayi abunsa , shi da Mamy kamar basu san me ya faru ba .

“ Yaya da fatan dai ban ‘bata muku rai ba ? A maganata .”

“ Haba Bashir mene ne abun ‘bata rai , ai lokaci zuwa lokaci ya kamata a dinga ja musu kunne sabida yadda rayuwar nan take , musamman idan sunje makaranta babu idan kowa akan su.”

Karaf Uncle Bashir ya amshe “ Nima abunda na gani kenan Yaya , dan ma Ameerah ba’a nan ta kwana ba , ai so nan ga baki d’ayan su na had’a su na ja musu kunne, danni sam zamanin nan  na yanzu har mamaki yake bani , sai kaga yara suna ‘kanana sun lalace kuma duk sakacin iyayen sune , da suke barin su suke abunda suka ga dama .”

“ Haka ne bashir , Allah ya kare mana zuri’a baki d’aya.”

Da “ Amin” Uncle Bashir ya amsa , sabida yaji dad’in amsar Baffa , ganin Mamy bata tanka musu ba tun d’azu , yasa ya waiwayo kanta “ Hajiya Babba naji kinyi shiru ?.”

‘Karamun murmushi Mamy tayi masa tana kallansa , kafin a hankali ta furta “ Ai kun riga kun fad’i abunda ya dace na fad’a , Allah ya shirya mana su ga baki d’aya .” Ga baki d’aya suka amsa da Amin , kafin su canza hirar zuwa wata maganar da ban. 

Mishal kuwa tun kafin tayi nisa Uncle Saleem ya kirata , shiyasa ta d’an dakata da tafiyar da take , tana waiwayo wa . 

Lokaci d’aya suka ‘karaso da Yaya Sadiq da kuma Shukura da take kallanta . 

Daga nan suka jera su hudu har suka fito daga wajan. A falon sama suka zazzauna , Uncle Saleem ya kalleta ganin fuskarta , ba kamar yadda ta shigo d’azu ba. 

“ Mimi kina da saurin saka abu acikin rai , yanzu d’an maganar nan da Uncle Bashir yayi , har ya ‘bata miki rai? Shid’in bai isa yayi miki fad’a ko tuni ba ? And ba wai yanzu ne farau ba kinsan indai yana zaune a waje sai yayi tunin makarantar , inda sabo ai yaci ace kin saba da maganar sa ko.”

“ Uncle Saleem ni ba maganar sa ne ya ‘bata mun rai ba , amma imagine , kullum ni kad’ai yake fad’awa haka kawai yana wasi wasin tarbiyya na . 

Bai ta’ba had’ani da Ameerah yayi mana haka ba , gwanda gwanda ma Zarah .

But why me all the time? Ko Baffa da Mamy basa mun irin haka , infact ko Uncle Moh baya mun irin wannan
”

“ Toh kiyi ha’kuri ’yar gidan Uncle Moh , zuwa yanzu yaci ace kin saba ..”

“ Amma ai da Uncle Moh na nan ba zai fad’a mun haka ba.”

“Maza toh jeki kai masa ‘kararsa kice Uncle Bashir ya ‘bata miki rai.” Cewar Sadiq yana mata dariya shida Shukura .

“ It’s not funny Allah Yaya Sadiq ku dena mun dariya , in ba zaku lalla’bani ba kawai ku ‘kyaleni kunga tafiya na .” Zata bar wajan Uncle Saleem yace “ Share wad’an nan , ba’a abun kirki dasu , yanzu me zakiyi ?”.

“ Zan had’a tea ne .” Tayi maganar tana tafiya daga inda Sadiq yake ya d’an d’aga murya “ Nima zansha” itama Shukura ta furta “ Nima karki manta Dani .” Ko jiyowa Mishal ba tayi ba , tayi wucewar , sai a time d’in Uncle Saleem ya harare su . 

“ Abun naku ya koma tsokana , Allah yasa ta fad’awa Uncle Moh , wallahi dukan ku ba zaku ji da dad’i ba in har ya sani , just pray kar yaga mood d’inta , and see.”


“ Toh ai kune wani lokaci kuke biyewa Mimi , ni banga abun jin haushi a nan ba .” Cewar Shukura .

“ Uhm uhm fa . Uhm uhm fa Shukura , na dai fad’a muku
” suma daga nan suka canza hirar su zuwa wata hirar da ban dan waje ma suka samu suka zauna . 


Mishal kuwa asalin main falo ta dawo dan ta ‘kara ‘kuluwa da dariyar su Yaya Sadiq . 

Babu kowa a falo, sai ta wuce kitchen d’in falon . 

Yana da girma sosai kamar wani falo guda , ga kayan electric da ko wanne yake cikin muhallinsa . 

An ‘kawata kitchen sosai . 

Direct tea maker ta nufa , ta had’a tea me ‘kamshi da flavour , ta saka a cikin wani cup me murfi.

Shi kad’ai ta had’a, ta fito daga cikin falon , zuwa compound d’in gidan , tana sha’kar iskar safiya da take busowa da ‘kamshin fulawa da masu kula da ita suke faman ta’bawa . 

Direct building d’in da ta kalla jiya ta nufa , akwai security a jikin ‘kofar . 

Bata tsaya saka Pin d’in ba ta saka fingers d’inta , take a wajan ‘kofar tayi scanning hannunta , ta bud’e ita kuma ta shiga . 

Babu abunda ya soma dakar hancinta sai turaran Uncle Moh , ga sanyin Ac da ya had’e da turaran waje d’aya , duk sha’kar nunfashi sai ka sha’ka dashi sabida dad’i . 

Ajiyar zuciya Mishal ta sauke bayan ta sha’ki ‘kamshin turaran , kafin ta sako ‘kafanta cikin falon kamar mara gaskiya. 

Omo cikin falon komai da ba’ki akayi sa . Tun daga manyan panels da akayi an fani dashi a jikin bango , zuwa marbles tiles da suke ‘kasa ba’ka’ke ne , harta da ceiling da yake can saman falon ba’ki ne shi sai ‘kananan fitila daga saka ta ciki , suke bada hasken fari . 

Daga can ciki idan ka shiga cikin falon sosai akwai ba’ka’ken glass da suka kai har sama wanda zaka iya gano abun da ake a gefen ba tare da na waje yasan kana gani ba 


A tsakiyar falon akwai wani katon L-shaped sofa mai launin dark grey, mai matu’kar fad’i da taushi. An jera masa cushions masu launin baki da toka, yayin da a gabansa akwai wasu ‘kananan kujeru masu duhun launi. A gefen hagu kuma akwai wani dogon sofa mai launin baki, wanda yake kallon tsakiyar falon.

Daga tsakiyar kujerun akwai ‘kananan coffee tables da aka yi da duhun marble mai she’ki. A wasu daga cikinsu akwai wani irin ‘karamun  fireplace na zamani mai ɗauke da wuta a cikinsa, wanda yake fitar da d’an haske mai dumi a cikin duhun falon.

Daga ‘kar’kashin sofan an shimfid’a wani babban rug mai launin toka , wanda ya karya duhun da ke cikin falon , sai dai a kallon farko idan kayiwa falon , zakayi tunanin komai na ciki ba’ki ne sabida yadda suke da duhu . 

Idan kayi can gaba akwai babban dinning area , inda aka ajiye dogon dining table mai duhun launi tare da kujeru masu yawa . A bayan teburin akwai wani katon decorative wall da aka yi masa kama da marble mai ɗauke da zane-zanen halitta, wanda hasken chandelier ɗin da ke rataye a gabansa yake haska sa .

Daga gefe kuma ana ganin wani doguwar staircase , da zaka hau har zuwa sama , matakan staircase d’in kuma suna da haske a ‘kar’kashin su , shiyasa yanayinsa yake da gwanin sha’awa da burgewa . 
   Still gefen staircase d’in anyi shi da glass d’in black metal , wanda ya ‘kara masa salo mai kyau na zamani . 

A benen sama akwai open balcony mai glass railing , wanda yake kallon falon daga sama . 

Abun burgewa da jan hankali kuwa yadda aka had’a ba’ki , dark grey , marble , glass da ‘karamun haske . 

Babu wani kayan ado masu yawa a ciki amma duk abunda akayi anfani dashi a falon duk mutum me ido idan ya kalla sai ya sake kallan su . Sosai kuma ya dace da mutumin da baya son hayaniya . 

Sai da Mishal ta gama baza idanuwanta ta ko ina ta ‘karewa falon kallon ‘kurilla , a hakan ma ba komai na cikin falon take iya gani daga bakın ‘kofa ba , ganin babu shi  a falon , ta saki ‘karamun ajiyar zuciya , sannan ta rifo ‘kofar , a hakan ma cikin sand’a ta ‘karasa shigowar . 

Akan sofa ta zauna , ta bud’e tea d’inta . 

Ko rabi bata shaba, wayan hannunta kuwa a gefen kujerar ta ajjesa sannan ta kwanta , ko fargabar yazo ya tarar da ita ba tayi , even though ba wannan ne karo na farko ba idan an ‘bata mata rai take zuwa tayi zamanta sabida tasan bayanan, duk shigowar da take kuma bai ta’ba kamata ba , shiyasa yanzun ma ta saki jiki sosai, har bacci ya d’auketa a falon. 

Bayan kusan mintuna 56 tana bacci Uncle Moh ya shigo cikin falon , cikin takunsa me cike da izza  , da kuma nauyi da yake saka mutum ya lura dashi ko da bai d’ago kai ya kallesa ba. 

Harta Mishal da take bacci sai da ta gyara kwanciyarta lokacin da ‘kamshin ya daki hancinta , baccin ta ya soma nauyi shiyasa bata ankare dashi , dan da idanta biyu babu abunda zai hana ta kasa firgicewa idan ta jiyo wannan ‘kamshin a cikin hancinta . 

Kayan training ne a jikinsa , fitted performance T- shirt black colour da ta fito da murd’ad’d’an hannunsa , sai Comfy Sweatpants light ash . Kunnanta da ba’kin wireless earbuds , sai hydration bottle da yake hannunsa shima ba’ki da kuma farin Performance sneakers . 

Gashin kansa ya d’an rikice kad’an sabida training , har sai da wasu kad’an suka d’an le’ko ta gaban fuskarsa suka bada wani saban style d’in gyaran fuska . 

Duk da kayan training ne a jikinsa amma sunyi bala’in yi masa kyau , ga farar fatarsa da ta haska su , hannunsa veins d’insa duk sun fito sabida training .

Kallan falon yayi na wasu seconds ,  kafin daga ‘karshe idanuwansa ya sauka kan babban L- shaped sofa da take kwance tana bacci . 

Tea d’in da ta sha rabinsa yana nan akan table , wayarta kuma a gefenta . 

Fuskar Uncle Moh sam babu fara’a , dan tunda ya shigo haka fuskarsa take , ya had’a girar sama da ‘kasa , gashi daman kuma Allah ya bashi yalwar gashin gira ba’ka . 

Ga kuma idanuwansa masu kyau , da idan ya kuskura ya kalleka dasu kashin ka ya bushe , musamman idan mutum yasan bashi da gaskiya . 

Itama kallan second yayi mata ya d’auke kansa , kafin ya ta’be bakinsa kad’an , sannan ya nufi d’aya daga cikin sofa d’in ya zauna . 

Kana kallan fuskarta zaka ga babu sauran shagwa’bar nan da take yi , idanuwanta a rude suke , numfashinta yana fita da yana dawowa a hankali . 

Irin tana baccin hankali kwance babu wani fargaba , da alama sosai ma take jin dad’in baccin da take . 

Kallan time yayi , kafin ya kalli Mishal , sannan ya d’auko wayan sa yana daddan nawa , har zuwa lokacin kuma bai tashe ta ba . 

Mishal kuma babu abunda ya dame ta , baccinta take . 

Wani lokaci ta d’an motsa kanta , wani lokaci ta d’an gyara kwanciyarta . 

Sai da ya d’auki good 3 hours yana danne danne a wayan . 
Kafin ya fusgar da ‘karamun iska a bakinsa yana kallan time . 

Mi’kewa Uncle Moh yayi , bayan ya saka wayarsa a aljihu, bai bawa Mishal second look ba , ya wuce stairs . 

Kusan mintuna goma sha biyar zuwa ashirin ya dawo , da wani ‘karamun abu ba’ki da ya ri’ke a tafin hannunsa me d’an kauri kad’an . 

A dai dai kan Mishal da take bacci ya tsaya , ya kalli abunda yake hannunsa , sannan ya d’an d’aga girarsa guda d’aya kamai me tunani . 

A hankali ya matsa kusa da ita , sannan ya d’an sunkuya kad’an , ya kalli yadda take sha’kan bacci ta , tukunna ya ajje mata abun da yake hannunsa , ya had’e hannuwansa biyu kuwa a ‘kirji yana ‘kara had’e fuskarsa waje d’aya. 

A gaban idanuwansa abunda ya ajje ya shigo cikin rigarta.

Baiwar Allah tana bacci ta soma jin wani su’bul su’bul d’in abu yana mata yawo a sassan jiki, tayi tunanin ko mafarki take , ganin daga wannan waje abun sai ya koma wani wajan, sai faman ya mutsa fuska take . 

Jin abun ya koma ta cikinta tayi wanwar ta bud’e idanuwa a firgice tana ta’ba inda take jin motsi . 

Lokaci d’aya ta zaro ido tana sakin wani gigitaccen ‘kara sannan ta tashi tsaye tana tsalle . 

“ Wayyo Allah na , maciji, na shiga uku miciji a jikina .” Allah sarki Mishal cikin ‘kan’kanın lokaci ta firgice bata kula da Uncle Moh da yake bayanta ba , wani tsalle da ta daka maciji ya fad’o ‘kasa ba’ki ‘kirin dashi d’an ‘karami , itama kuma ta daka tsalle tana hayewa kan kujera tana cigaba da ambatan sunan maciji dan ji take har yanzu macijin na jikinta , ga hawaye da ya soma wanke mata fuska , ganin babu sarki sai Allah ta soma ‘ko’karin zuge zip d’in rigarta , a lokacin taji saukar kakkausar muryarsa a bayanta .

“ IF YOU DARE 
.”

A gigice Mishal ta jiyo , bayanta dan tayi tunanin gizo kunnuwanta sukai mata , amma ganin Uncle Moh tsaye a wajan sai ta sake riricewa , gani tayi ga baki d’aya shima d’in ya koma mata maciji. 

Shiyasa ta ‘kwalla ihu tana fad’in maciji sannan tayi baya zata fad’i a ‘kasa sabida suma da tayi a lokacin
..

( YASIN BAKA DA KIRKI UNCLE MOH 
.đŸ€­amma ina bala’in ’kaunar mugancinka 😭đŸ„č)

Sorry MimiđŸ€­đŸ€­đŸ€­đŸ˜­đŸ˜­â€Š..



____________

To be continued
 đŸ”„
INSHA ALLAH 
..


AISHA UMAR ( Black Queen)đŸ€đŸż.
WhatsApp num: ***