Page 7/8/9
MISHAL
By BLACK QUEEN đ€đż
***
MAI SAN A TALLATA MASA KAYANSA YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER ***
Book 1
page 7/page 8 / page 9
Da sauri ya riâkota , ganin da gaske suman tayi.
Daga inda yake a bayanta ya kwantar da ita akan kujera , kafin ya dâan ranâkwafo kadâan dai dai saitin fuskanta .
Bayan ya tabbatar da suman da tayi, ya nufi wajan dinning , akwai jug a samansa , akwai ruwa da yankakken slice lemon a ciki .
Dai dai rabin cup ya zuba ,sannan ya nufi inda take a kwance .
Da hannunsa dâaya ya dâan dâagota , sannan ya dâan ibi ruwan kadâan ya yayyafa mata a fuskarta .
A karan farko Mimi bata motsa ba , sai da ya dâan âkara yayyafa mata ruwan tukunna taja dogon ajiyar zuciya me dâan âkarfi tana saukewa.
âKirjinta sai faman sama da âkasa yake sabida yadda zuciyarta take faman bugawa da sauri sauri.
A hankali Mimi ta budâe idanuwanta , karaf suka sauka akan na Uncle Moh da yake kallanta .
Cikin dâan sauri ta kulle idanuwan , zata âkara âkwalla ihu , yayi mata âkaramar tsawa dai dai kanta .
â Ki shiga tai tayin ki , karki cika mun kunne .â
Ba shiri ta sauke ajiyar zuciya tana gyara zamanta sosai, sannan ta budâe idanuwan akansa da ya buga mata wani kallo .
Ba shiri ta dâauke kanta a kansa tana dâan turo baki cikin âkunâkuni.
â Uncle Moh ina kwana .â Ta gaishe sa , cikin muryarta da ya nuna sam bata da gaskiya , gashi tama âki kallansa bayan dâauke fuska da take .
Bai ma bi takanta ba ya bar wajan da cup . A dai dai dinning table ya ajje, shi kuma ya wuce upstairs bayan ya dâauko macijin da take wa ihu .
Tana ganin ya bar wajan , ta dâan harari hanyar da yabi , cikin âkasa âkasa da murya ta furta â Mutum sai shegen fadâin rai , mugu kawai da nasan kana nan da babu abunda zai hana na shigo part dâin nan ai , sai wani faman harhadâe rai kake kamar tarwadâa.â Ta dâauki cup dâinta da wayarta ta bar part dâin ga baki dâaya dan tasan idan ya dawo ya tarar da ita a falon ba âkaramin fadâa za suyi ba .
Tana fita part dâin su Zara ta nufa . Babu kowa a falo sai Momyn Zara da kuma wata sister dâinta Aunty Saudat .
â Momy ina wuni.â Cewar Mimi.
Cikin dâan zaro ido Momyn Zara ta furta â Manya manya , daman ana ganin ku? Yau Mimi na cike file kawai kice tunda na ganki a part dâin nan .â
â Haba Momy ko jiya na shigo fa , kin dai manta ne .â
â Babu wani mantawa da nayi Indai kece Mimi zanga lokacin da zaki canza hali, kullum dai kina dâaki abinki, idan ba da Zara ko Amira ba , baâa ganin ki a cikin gidan nan.â
â Kai Momy âŠâ Mimi ta dâanyi murmushin rashin gaskiya kafin ta kalli Aunty Saudat .
â Aunty Saudat ina wuni, ya gida .â
â Lafiya Kalau Mimi , ya gida , nazu ai na gaisa da Mamy tace kina dâaki , itama bata ganki ba .â
â Allah sarki ina ji shi yasa bamu hadâu ba .â Sai ta mayar da kallanta kan Momyn Zara.
âMomy bari naje wajan Zara.â
â Toh Mimi.â Da haka ta wuce dâakin Zara.
â Assalamu Alaikum .â
â Waâaikumussaalam mara mutunci sai yanzu zaki zo? Har dâakin ki fa na shiga ban ganki ba .â
â Kefa matsalata dake bakin ki ya fiya sauri wallahi , daga shigowata kin wani soma cacaca da surutu ki bari na zauna ma tukunna , kafin ki soma âkananan maganar taki.â
â Daman Mimi ai dole kice mun ina âkananan magana mana , Abeg ina kika je kika zauna na duba banganki a dâaki ba , ko dai part dâin Uncle Moh kika je ?â.
Shiru Mimi tayi mata , ta âkarasa ta zauna akan stool dâin da yake gaban mirror dâin dâakin.
â Ya akai naji ki shiru haka ? Meya faru?â
âMe kika gani?â Itama Mimin ta tanbaye ta.
â No naga kawai kinyi shiru ne not like you , ko wani abu ne yake damun ki?â.
â Nope babu abunda yake damu na , yanzu ma daga part dâin Uncle Moh nake , nayi tunanin baya ciki ma na zauna bacci âŠ. Aushe yana nan shiyasa na samu na gudo tunda naga ya hau sama , kafin ya dawo yaci zalina , mugu .â
â Ke uban me ya kai ki part dâinsa , bayan sarai kinsan halin kayansa .â
â Hmm kema kinsan idan su Aunty Shukura sunanan ba zasu taâba âkyale ni na huta ba , ga su Uncle Saleem duk zuwa za suyi su dameni.
Part dâin Uncle Moh ne kawai nake safe , shima kuma da nasan bai fita ba Allah bazan je ba .â
â Kuma bai miki komai ba ?â
â Hmm bar mugu maciji ya saka mun, kinga ni dena yi mun ma maganarsa, karki sa zuciyata ta dinga tafarfasa , su Ameerah basu dawo ba ?â.
â Anya baâa can zata kwana ba ? Dan nidai har yanzu batai mun maganar zuwa baâŠâ
âDan dâaga kafadâa Zara tayi daga inda take , kafin ta cigaba â Wallahi Ameerah idan ta samu comfort a wani waje toh mantawa take da gida , kinsan halinta .â
âDan sauke ajiyar zuciya Mimi tayi a hankali tana fadâin â Hmmm âŠâ kafin ta dâan jiyo da stool dâin sosai .
â Hmm kinga ajje maganar Ameerah a gefe , yanzu tashi muje muyi wani abu muci , yunwa nake ji , ko kinci abinci already?â.
âNo banci ba wallahi yanzu nake shirin kiran wayanki fa âŠ. Amma kafin nan wallahi you look so off yau , ko wani abune ?â
âyunwa ce fa kawai Zarah. Dan Allah taso muje muci abinci , kafin nayi collapsedâŠ.â
â Okay dear âŠ.â Cewar Zara .
Ga baki dâaya suka fito daga falon , suka wuce kitchen .
Ba wani special abu sukai ba , pancake ne akai masa decoration da fruit da zuma , sai Omelette da toasted bread da sukai , sai drinks da sukai kala biyu , dâaya fruit smoothie dâayan kuma blueberry drink , sannan suka sake wucewa dashi dâakin Zara.
â Sisi me yaki ke gani , anjima muje saloon mana , kwana biyu ba mu fita ba , or mu fita muje musha fresh air mana , ice cream , junks kingane ai ⊠ko ya kika ce ?â Cewar Zara
âDan shiru Mimi tayi kamar me tunani kafin daga bisani ta furta â Wajan âkarfe nawa kenan zamu ? Kinsan halin su Uncle Abba yanzu sai suce kar mu dadâe.â
â Mimi ki âkyale su Uncle Abba dâin nan suma ai kullum fita suke , a kwanakin nan baki ga basa dawowa da wuri ba .
Nikam na gaji da kullen nan da ake mana , kawai mu cewa su Mamy zamuje saloon , daga nan sai mu wuce mu dâanyi shopping , atleast before 7 sai mu dawo gida, lokaci su Uncle Moh ai duk basu dawo gida ba .â
â Uhm Uhm fa Zarah.â
â Ke dan Allah Mimi , yau dai rana dâayan ko ba zaki ba nayi tafiya na ? Kinga sabida halin nan naki ne bama fita yawo sosai most of the time in ba saloon ba ko kuma wani fita mai mahimmanci .
Just once in a while letâs enjoyed our self BabyâŠâ
â Okay letâs enjoyyyyyyyyyyyyyyyy.â Mimi ta fadâa da âkarfi bayan ta dunâkule hannunta ta saka dai dai saitin bakinta kamar lasifika .
Suna hira suna jin abincin su , basu san lokaci ya ja sosai ba sai da wayar Zarah ta soma kiran sallah , a nan ne Zarah taga biyu har yayi , ita kuma Mimi ta miâke zata tafi part dâin su tasan Mamy na nemanta yanzu .
â âYan mata kinga tafiya na nasan yanzu Mamy tana can tana nemana tun da safe bata sake sakani a cikin idanunta ba .â
â Toh âyar Mamy ai da yake ba Mamyn ki bace ke dâaya .â
â Na yaushe kuma ? Ke wallahi idan na tsaya biye miki , har laâasar tayi ina nan , kinga tafiya na bye bye . See you âŠâ da haka Mimi ta fice daga dâakin, lokacin da ta sauko âkasa har lokacin Momy da Aunty Saudat suna nan a inda suke .
â âYar Mamy har angaji damu?â Momy tayi maganar cikin tsokana .
âDan murmushi kawai Mimi kafin ta bata amsa â Aa Momy âŠâ
â Okay Dear a gaishe mun da MamyâŠâ
Da â Tohâ kawai Mimi ta amsa kafin ta wuce part dâin su dâin.
Tana shiga , dâakin Mamy ta wuce direct .
A hankali ta âkwanâkwasa kofar dâakin sau biyu, kafin ta murdâa handle dâin tana dâan turo âkofar kadâan , sannan ta dâan leâko da kanta ciki kadâan kamar wata Baby.
Cikin siririyar muryarta ta furta â Assalamu Alaikum.â
â Waâalaikumus Salam âŠâ daga cikin dâakin Mamy ta amsa mata , kafin ta âkara da â MimiâŠâ
A hankali Mimi ta amsa mata â Naam Mamy .â
â Shigo ciki mana , kika tsaya daga waje.â
Ba musu Mimi ta âkarasa budâe âkofar , kafin ta shigo ga ba dâaya .
Mamy tana zaune akan gadonta tana duba waya, shigowar Mimi yasa ta dakata da abunda take yi , sannan ta nuna mata gefen gadon da hannu alamar tazo ta zauna .
Da sauri Mimi ta âkarasa gefen gadon, amaimakon ta zauna sai ta kwanta , sannan ta dâora kanta , akan cinyar Mamy dâin .
â Mamy sannu da gida .â
â Yawwa âYar Mamy , sai yanzu kika tuna dani kenan?â.
â Aâa wallahi Mamy , bacci nake so nayi dâazu kuma kinsan indai su Aunty Shukura sunanan ba zasu taâba bari na nayi bacci ba , a part dâin Uncle Moh kawai zan iya bacci na hankali kwance .â
â Tsaurin idanki ya miki yawa ai , na rasa wa kika dâauko , ga tsoro ga kuma neman rigima , kinsan sarai yana nan amma kika wuce part dâinsa , idan ya sakaki kuka kuma Kızo ki taâbata rai .â
â Wallahi Mamy bansan yana cikin gidan ba shiyasa naje , kema kinsan inda na sani babu abunda zai kaini can dâinâŠâ
â Yanzu ai daga can dâin kike ko?â.
Girgiza mata kai Mimi tayi â No Mamy daga part dâin su Zarah nake , yanzu ma ke nazo dubawa sannan nayi sallah ..â
â Kinci abinci toh ?â
â Eh Mamy naciâŠâ
â Oya tashi kije kiyi sallah toh .â Mamy ta dâaga ta daga cikinta , shiyasa Mimi ta dâanyi dariya â
yanzu zan tafi Mamy ba sai kin kore ni ba .
Amma zuwa anjima zamuje saloon nida Zarah, kinji Mamy?.â
â Ku kuma haka tunanin ku ya baku kuje saloon da yamma, of whole day sai da yamma zakuje saloon?â.
â Kai Mamy akwai rana garin ne fa shiyasa muka ce zamuje da yamma .â
â Okay yaushe zaku dawo?â
â Kafin Magrib insha Allah Mamy sabida ana gama mana zamu dawo.â
â ah toh dan babu ruwana idan kuka dawo late , zaku hadâu da uncles dâin ku ..â
Cikin sauri Mimi tayi hugging dâinta â Shiyasa nake sanki Mamy na .â Kafin ta tashi da sauri tana dariya sabida yadda Mamy dâin take faman tureta a jikinta itama tana dariyar .
Babu âbata lokaci Mimi ta wuce dâakinta dan tayi sallah .
Sai da ta soma jingina bayanta da jikin door dâin , sannan ta sauke nannauyar ajiyar zuciya .
Agogon dâakin ta kalla ganin 2 har da 15 , tayi saurin wucewa toilet .
Bata jima sosai ba sabida alwala kawai tayi ta tayar da sallahr azhar dâinta . Tana idarwa kuma tayi azkar da dâan adduâoâi kafin ta kwanta a kan daddumar, tana lumshe idanuwa kamar me bacci .
Tsawan mintuna biyar tana nan a haka , kafin ta soma jin hannu a kanta alamar ana shafa mata shi.
A hankali ta budâe idanuwanta da suka soma lumshewa , ta dâora su akan Joy da take gefenta.
Cikin gyaran murya Mimi ta furta â Joy sai yanzu zan ganki? Ina kika je haka ?â.
â Na tsaya yin wani abu ne Mimi shiyasa ma kika ganni shiru , yanzu ma na gama abunda nake shiyasa na taho wajan ki .â Joy ta âkarasa tana tsirawa Mimi idanu.
Itama Mimi da take kallanta ta dâan dâaga mata gira guda dâaya â Mene ne kike kallo na haka kuma Joy?â.
â Mimi kinje part dâin Moh ko?â.
â Eh naje ⊠kema kinsan halin su Aunty Shukura zasu takurawa rayuwata ne .â
â Haka ne kuma . Ina zaku je ke da Zarah?â
â SaloonâŠâ Mimi ta bata amsa tana miâkewa zaune .
âSaloon da ina kuma?â Joy ta sake jefa mata tanbayar , idanuwanta har yanzu akan Mimi .
â Saloon ne kawai , sai may be ice cream da zamu tsaya mu siya , amma shima sai mun soma tabbatar da time tukunna kar muyi dare .â
â Sai kuma ina da ina zakuje?â.
â Thatâs all Joy⊠me yasa yau tanbayarki tafi ta ko da yaushe yawa ? Daga wannan tanbayar sai wannan.â
â Wa zai kai ku Saloon dâin?â Joy ta share tanbayar Mimi , ta hanyar sake jefa mata tata tanbayar .
â Driver ne .â
â Toh kar ku dâauki Driver , Zarah ta kai ku.â
â Amma ba lalle Mamy ta bari sabida yamma , and if yes ta bari , idan dâaya daga cikin su Uncle suna na ba zasu bari mu fita mu dâaya ba , kin san da hakan.â
â Na sani amma kuyi tafiyarku ku kadâai , sannan karki manta da maganata , ba kowa ne zai miki magana ki amsa ba , kar ki kula kowa a waje kinji?â.
â Kullum sai kinyi wannan maganar kamar ina kula wasu idan na fitan âŠ.â
â Har yanzu Yarinya ce ke Mimi, wasu abun gwanda ki bar su a rufe , wata âkila yau rana ta dâanyi miki zafi , amma daga baya zaki ji sannintaâŠ.
Kuma kiyi haâkuri da Moh tunda shi dâin Uncle dâin ki ne , baki da kowa kamar shi duk duniyar nan .â
â Kullum maganar ki kenan Joy , kin manta yadda baya âkaunata yanzu âŠâ
â Duk da hakan baki da kamar shi , kamar yadda shi dâin ma bashi da kamar ki duk duniya âŠ.â
â Shi mugun ko?â
â Koma me zaki ce kice , kuma ki riâke maganata guda dâaya , a duk lokacin da matsala ta tun kare ki, ya zamo mutum na farko da zaki soma neman taimako a wajansa , koda kuwa me zai faru , ko na kuwa zai kashe ki ne , ya zama number na dâaya ..â
Yanzu kam taâbe baki Mimi tayi , dan in ana haddace magana toh ta dadâe da hadda ce wannan maganar tsawan shekaru âŠ
â Toh shikenan naji maganar ki Joy .â
â Bawai iya ji zakiyi ba har da dâauka zakiyi ⊠akwai abunda zanyi yanzu shiyasa bazan biku ba , amma ki kula , ki kula Mimi⊠ki kulaaaa sosai âŠâ yanzu harda dâan taâba kafadâunta Joy tayi da dâan âkarfi , bata bari Mimi tayi magana ba ta âbace ga baki dâaya daga dâakin.
Ita kuma Mimi jingina tayi da jikin gado a inda take , tana ta maimaita maganar Joy âŠ
A duk fitar duniya idan har ba tare da Moh zata fita ba , toh tabbas sai Joy ta fadâa mata wadâan nan maganar , ba wai wannan ne karo na farko ba.
Tun daga tsawan shekarun da ta san Joy , har zuwa yanzu a duk fitanta wannan shine abu na farko da Joy take sake tunatar da ita , har yanzu kuma batasan dalilin hakan ba .
Moh kuma? Shine number 1 controller a rayuwarta , duk fadâan sa shine kuma number safe zone dâinta , kasancewar he was once a father to her âŠ
Tunanin hakan yasa ta dâan sauke ajiyar zuciya , bayan ta kuma tuno abunda ya hadâa su dâazu sai ta dâan turo bakinta waje kadâan tana fadâin â Mugu kawai âŠâ. a fili .
Sannan ta dâauki wayarta ta shiga instagram tana dâan duba abunda yake faruwa, sannan ta shiga game .
Tana cikin game dâin ne number Zarah da tayi saving da Besty ya shigo wayarta alamar shigowar message.
Bata tsaya âbata lokaci ba ta shiga cikin message dâin.
â Mimi please karki yi late fa , ana idar da sallah ki fito , tun yanzu kiyi wanka , kar kiyi delayed a hana mu fita kinji? Habibttyđâ.
Kafin tayi reply wani message dâin nata ya sake shigowa â And Ameerah ma tace zata bimu are you okay with that?â.
Kafin tayi reply wani message dâin ma ya sake shigowa ..
â Tace daman tana shirin zuwa kuma wata friend dâinta da suke waya dâazu itama zata je sai mu tafi duka tare ⊠kinji ?â..
The fourth message â Please say something..â
Mimi tana gama karanta messages dâin ta dafe kanta kadâan kamar me tunani , kafin tayi mata reply .
â Am okay with Ameerah amma mene ne hadâin mu da zuwan friend dâinta ? Nikam am out gaskiya âŠâ
Tana tura message dâin ko 1 minute baâa cike ba Zarah tayi mata reply .
â Haba mana Mimi , kar Ameerah taji ba dadâi , dan dai zuwa saloon is not a big deal mana , please⊠This once for my sake ! Please..â
â Nidai am out , mu haâkura next time sai muje ..â tana turawa sai ga kiran Zarah .
Zarah bata bari tayi magana ba ma ta soma roâkanta â Please please please Mimi⊠already na fadâawa Momy da Abba dan Allah mana , kar kısa Ameerah taji so offended mana .
Mene ne a ciki tunda ba dadâewa zamuyi ba ? PleaseâŠâ
Numfashi Mimi ta sauke kadâan kafin ta furta â Okay itâs fine..â
Daga cikin wayan tana jiyo ihun Zarah , kafin tayi mata reply â Ko kefa Mimi , thatâs why I love you ⊠bye bye karki manta ki shirya da wuri please nima zanyi abu ne sai na shirya kinji?.â
â Okay ..â Mimi ta bata amsa tana kashe call dâin.
Daga nan kuma book dâinta na jiya ta dâauka ta soma karantawa, har ta soma mantawa ma da fitan sabida yadda labarin da take karantawa ya shiga kanta sosai .
Sai da aka soma kiran sallar laâasar tukunna ta ajje book dâin.
Wanka ta somayi tukunna tayo alwala , just doguwar riga ta saka a jikinta , sannan tayi sallah .
Tana idarwa kuma ta soma cin karo da message dâin Zarah .
Bata tsaya bi ta kansu ba , ta soma shiryawa âŠ
Lotion dâin, daily skin care dâinta , da little bit lipstick da ta saka , sai dâan giranta da ta taje kadâan ..
Sai a lokacin ta soma tunanin kayan da zata saka , kafin daga bisani ta budâe side dâin materials dâinta .
Wani pink material ta dâauko , jikinsa akwai ado , ga kuma rawa da santsi da yake dashi .
Yana da dogon hannu, daga âkarshe akwai dâan roga a jikinsa sai kuma dâan kadâan dâin material da ya dâan rufe mata fingers dâinta amma ba duka ba .
Baâa wani adon dâinki a jikin saba sabida irin free gown dâin nan tayi.
Sai dai kayan sunyi mata kyau sosai , gashi babu ko hoda a fuskarta , sai zallan natural beauty dâinta .
Mayafin da tayi anfani dashi baby pink ne kamar kayan , sai zobe guda dâaya da ta saka a finger dâinta.
Takalmin âkafarta white ne , tare da mini fashion bag dâinta shima white .
Mimi tayi kyau , to the extend that , duk wanda ya kalleta sai ya sake kallanta , ba daga maza ba har daga matan idan sun kyalleta sai sun sake , ga idanuwanta da suka fito sosai Masha Allah .
Indai ana maganar kyau toh Mimi sai dai tace Alhamdulillah dan Allah ya gama yi mata komai .
Perfumes dâinta from different brands ta feffesa, shima kadâan ba sosai ba yadda zai hau .
Sannan tayi selfie kamar guda hudâu haka a cikin wayarta .
Before ta dâauki wayanta , Zarah tayi mata kira na kusan uku kenan âŠ
A last kira dâin yanzu ne ta dâauka tana fadâin â Ganinan sakkowa ! Give me one minutes My lady âŠâ
Daga cikin wayar Zarah ta furta â Kin tabbata kin shirya ko tsokanata kike? Ina kika ajje wayar ki ma , tun dâazu nake kiran ki , da baki dâauki wannan call dâin ba da kin ganni cikin bedroom dâin ki.â
â Yeap naga kiran ki, idan na tsaya dâaukan call dâinki zaki dakatar dani daga shiryawa , so yanzu da na gama ai gashi na dâaga .
Yanzu zaki ganni na fito , zan yiwa Mamy a little Bye ne âŠ. See you in a minutes âŠâ
â Thatâs my girl ! Nima yanzu zanyi wa Momy magana , till we caught up ⊠yaaa bye âŠâ
Ita ma Mimi tace mata âbyeâ kafin ta kashe call dâin .
âDakin Mamy ta nufa sai dai kash , lokacin da ta shiga Mamy bata cikin dâakin, ta dai ji motsin ruwa kamar tana toilet , shiyasa kawai ta âkyaleta tunda already ta fadâa mata dâazu , amma kuma ta mata dropping text through her phone .
Tasan zuwa yanzu idan bata fito ba Zarah zatai ta daminta da call
Shiyasa kawai ta fito compound dâin .. saura kadâan siyi kiciâbis da Zarah da take nufo part dâin nasu itamaâŠ
Kayan jikinta riga da wando ne , wandan plazo , sai red top dâinsa .. da kuma white veil , tayi simple makeup, ga kuma nude dâin janbaki da ta saka , tayi kyau sosai sai dai ba kamar Mimi ba ..
â Woowww ! Mimi kinga kyaun da kikai kuwa ? You look so gorgeousâŠwallahi âŠâ
â please karki soma ! Kema kinyi kyau dâin , idan kuma kika tsaya complement su Yaya Sadiq suka shigo , ni babu ruwana , I will just go back âŠ. Simple âŠâ
â Okay fine ! Letâs go daman key dâin Yaya Sadiq na dâauko . Muyi muyi mu dawo tun kafin ya cinye ni dâanye na , kuma babu mai âkwata na .â
â Okay but Ina Ameerah .â
â Oh zamu dâauke su a hanya ne , kafin mu âkarasa salon dâin ..â
â Okayâ Kawai Mimi tace , kafin su nufi wata baâkar Benz da take gefen compound dâin, baâka tass tasha wanki babu âkura akanta .
Zarah tana driving seat Mimi kuma tana gefenta , kamar wata innocent girl haka Zarah ta fita daga cikin gida cikin low speed , sai da ta tabbatar ta fita daga cikin duka gate dâin gidan tukunna taja motar a high speed .
Basuyi long tafiya ba Ameerah takira wayar Zarah ta fadâa musu inda zasu dâauke su.
Duka daga inda suke 5 minutes ne ya kai su , Ameerah tasha matsatsan âkananan kaya , tayi dâaura mayafinta , tayi gyaran gashi kadâan daga waje wanda ya nuna kwantaccen gashin kanta , amma tayi kyau itama ba lefi , ga tauna da take yi dâai dâai abunta .
Kusa da ita kuma akwai wata chubby girl , fara kalar Zabiya , itama âkananan kaya ne a jikinta , but babu dâan kwali sai attachment dâin kanta da ta tufke waje dâaya , bayan heavy makeup da yake fuskar su , har da baâkin sun glass suka saka .
Mimi da Zarah sai da suka kalli juna lokacin da suka ga su Ameerah cos basuyi tunanin kalar friend dâin da zasu fita saloon da ita kenan ba .
Zarah ce ma ta dâanyi mata yaâken murmushi tana cewa â Hiiâ sabida itama â Hiâ da ta ce mata .
Mimi tun daga â Hi â da tace musu bata kuma musu magana ba , gwanda dâayan friend dâin da take dâan yiwa Mimin magana , da taga sheâs not interested kuma sai ta dena mata magana.
Daman Ameerah data shigo cikin motan bata ma yiwa Mimi magana ba sai Zarah .
Ita kuma Zarah ji tayi motar tayi mata wani iri ba kamar yadda suka fito ba , that makes her to put a little song , da ya canza mood dâin motar , harta Mimi da ta soma vibe dâin waâkar tare da Zarah , ita kuma Ameerah ta soma da friend dâinta , dan har an fijin muryar su a cikin motar .
20 minutes ya kai su saloon dâin da suke san zuwa .
Yana da matuâkar girma , kana ganinsa ba irin simple saloon dâin da zaka je ka bada âkananan kudâi bane .
Wannan daga yanayin tsaruwarsa kadâai ya tabbatar da sai wadâan da suka isa ne tukunna zasu iya shiga cikin wajan.
A cikin compound dâin wajan Zarah tayi parking motar , duk suka fito .
Tun daga bakin wajan ake ve musu welcome Maâam har suka shiga ciki.
Basu tsaya a dai dai receiption ba suka hau sama , nan ma sai da aka budâe musu VIP .
Wajan an âkawata sa da kujeru sai kace falo , masu kyau , gashi sai faman tashin âkamshi yake .
Anan aka tarâbesu, aka kawo musu drinks masu sanyi da snacks ..
Already akwai list of services da ake a wajan , kowa ya zaâba wanda yake so .
Kusan a lokaci dâaya zaâayi musu sabida Ćuna da maâaikata komai kuma cikin tsari ake yi harta âkawar Ameerah sai da ta cire wig dâinta , nan gashinta ya fito aushe ba wani gashi bane da ita .
Tunda Mimi ta cire veil dâin kanta ta kasa dâauke idanuwanta akan gashin ta , sabida mamakin yawan gashin da take , mamakinta kuma ya kasa rufuwa har akan fuskarta , dan sai da Ameerah ta dâan harareta tukunna ta waske ..
An musu gyaran gashi sosai da sosai , yadda wajan yake da kyau haka âbangaran service dâin su yake da kyau shima .
Sai wajan 5:40pm aka kammala musu kowa ya mayar da veil dâinsa , sukai payment sannan suka fito .
Da aka shigo mota ne Zarah ta kalli Mimi .
â Letâs get some drinks mana âŠâ
Jinjina mata kai Mimi tayi alamar toh , kafin Zarah ta kunna motar su fice daga cikin saloon dâin.
â Okay ladies ! Ina zamu je yanzu ?â
â Just mu samu kusa kusa mu siya drinks dâin sai mu wuce gida kinga kar magrib tayi mana a gida , it wonât be nice for all of us ..â
â Yeah I know Mimi but atleast apart from drinks , mu siya ice creams ko junks ne mu tafi dashi gida , me drinks zai yi mana shi kadâai ko?.â
â Zarah leave her ! Itama na gulma ne , tanasan zuwa but kamar sheâs innocent take so ta nuna âŠ.â Cewar Ameerah .
âDan juyowa Mimi tayi ta kalleta daga inda take from head to toe, kafin ta furta â Excuse me âŠ?â
â Excuse you for what.?.â Itama Ameerah ta bata amsa tana yatsına fuska .
Mimi za tayi magana Zarah tayi saurin rigata â Please Ameerah itâs okay tunda har ba tayi miki magana ba , just ki fadâi raâayin ki itama ki bari ta fadâi nata âŠâ.
â Wai mene ne abun fadâa anan..â cewar Kawar Ameerah , tayi maganar cikin iyayi ta wani shaâke muryarta kamar wacce akayi wa dole sai tayi magana .
Kafin ta juyar da muryarta zuwa turanci tana kallan Ameerah â Please Dear is okay ! Kowa fa opinion dâinsa ya fadâa and beside , itâs not a bad thing âŠ. Ko ya kika ce ?â.
â Okay is fine Cynthia ⊠donât mind meâŠâ cewar Ameerah , hakan yasa , Cynthia ta kalli Mimi daga bayan da take , tana sakar mata wani killer smile , da turanci ta furta â Please kema kiyi hakuri , okay?â .
Kamar wacce tayi magana da gawa , haka Mimi ta mayar da ita , ita bata amsa bata ba , kuma bata nuna mata alamar tasan me take yi bama , a haka tafiyar motar yanzu ma ta kasance babu surutu sosai a tsakanin su .
30 minutes ne ya kai su Frosty Pops âŠ
Ameerah da Cynthia ne suka soma sauka cikin motar dan basu ma jira su Zarah ba suka shiga .
İta kuma Zarah tana âkoâkarin fita ta kalli Mimi ganin har time dâin Mimi bata yunâkura ba .
â Mimi ya kika zauna ? Ki taso mu shiga mana ..â
â No zan zauna anan ⊠kuje ku dawo..â
â Badai abunda Ameerah tayi bane ya âbata miki rai ? Common Mimi , weâre here to enjoy please, kin riga kinsan halin Ameerah âŠ
Dan Allah taso mu shiga kar dare yayi , idan kika zauna ke kadâai ba zanji dadâi ba .â
â Kema kinsan bata isa ta âbata mun rai ba , kawai I donât feel like going shiyasa ma kawai nace kuje .â
â Okay fine nima na fasa zuwa , idan sun fito sai mu koma gida.â Cewar Zarah tana komawa seat dâinta.
â Common Zarah.. mene ne haka kike ?â.
â Ke mene ne haka kike? Tunda ba zaâa fadâa miki magana ba kowa yayi abunda ya fi mishi , kince ba zaki shiga ciki ba good for you , nima nace ba zan shiga ba itâs also fine for me âŠâ
Kallanta Mimi ta tsaya yi kafin ta dâanyi murmushi tana dukan kafadâanta da wasa â Shikenan , letâs go, amma bazamu zauna ba , nasan a ko wana time yanzu Mamy zata iya kiran mu wallahi.â
â Na yadda ! Letâs go.â
Kanta Mimi ta jinjina mata , suka fito daga motan so loving , kana ganin su kasan akwai shaâkuwa sosai ta musamman a tsakanin su , sun riâke hannun juna suna tafiya , like mostly bestiesâŠ.
Lokaci da suka shiga su Ameerah already sunyi placing order dâin abunda suke so , har sun samu waje sun zauna ma .
Cynthia ce ta fara ganinsu , sai ta dâaga hannu tana musu alamar su âkaraso .
Babu musu kuwa duk suka nufi table dâin, sai dai basu zauna ba hakan yasa Cynthia ta nuna musu kujerar da hannu tana fadâin â Guys ! Come and join us.â
Zarah za tayi magana Mimi ta rigata â No thank you ! Tunda ba wani dadâewa za muyi ba , we have to rush back âŠâ
â Me haka Mimi , daga cewa ku zauna , ko dan ba friend dâinki bace ? I donât think she sound offended uhmp?â.
â Hey pleaseâŠ. Hold it âŠ. Hold it back .â Cewar Mimi.
â Hey itâs fine âŠ. Ameerah you donât have to talk back âŠ.its my fault. Letâs just place da order and go back âŠâ
Ameerah za tayi magana Zarah ta matso kusa da Mimin â itâs fine Dear ⊠me kike so na amso miki ?â
â Ice cream or Boba tea ⊠Wanda dai zai fi sauri âŠâ
â I gat youâŠ.â Cewar Zarah , sannan sukai placing order dâin abunda suke buâkata .
Har lokacin kuma basu zauna ba ita da Zarah , Cynthia kuma an kawo musu abunda sukai order , Ameerah na danna waya , Cynthia kuma tana taking little pictures of what they order .
Few minutes back aka kawo order dâin su Mimi , already daman sunyi payment , karâba kawai sukai suka fito .
Kowa fuskarsa da yanayinta sai dai yanayin Mimi ya canza sosai daga yadda take , which ko ita ne aka tanbayeta meke damunta ba lallai ta fadâa ba .
Wana irin damuwa kawai ta tsinci kanta a ciki ba tare da tasan dalilin damuwar ba .
Kallan time dâin wayarta tayi 6 har da minti 30 .
âDan lumshe idanuwanta tayi tana sakin nunfashi kadâan , a dai dai lokacin da kiran Mamy ya shigo wayarta .
Babu wani âbata lokaci ta dâaga call dâin bayan ta sake rintse idanuwanta kadâan tana budâe su .
â Hello Mamy..â shine abunda ta soma fadâi lokacin da tayi picking call dâin.
Daga cikin call dâin Mamy ta furta â Saloon dâin kenan Mimi ? Sai yaushe zaku dawo ko har yanzu baâa gama saloon dâin bane ?â.
â Sorry Mamy , already angama mana , yanzu zamu taho gida ma , mun dâan tsaya a Frosty Pops ne , mu amsa ice creams sai mu âkaraso .âcewar Mimi kamar bata san yin magana .
â Frosty Pops kuma ? Shine zuwa saloon dâin naku ?â.
â No Mamy âŠâ Mimi ta sake bata amsa .
â Then baku ga time ba ? Ko ice cream dâin ne babu a gida , ko kun kira Uncles dâin ku since bq zasu siya muku ba?.â
â Mamy duk ba haka bane , kınsan yau akwai rana yanzu zamu taho Allah har mun fito daga wajan ma yanzu , gida zamu dawo direct âŠâ
â Kuyi sauri âŠâ Mamy ta bata amsa kafin tayi cutting call dâin.
Kallanta Zarah tayi â Me tace ?â.
â Kema kinfi kowa sanin me zata ce , tace mu dawo gida .â
â Ai shikenan letâs go âŠâ cewar Zarah .
Sai da suka nufi daf wajan Mota tukunna Zarah ta budâe bag dâinta zata dâauki key .
Sai dai babu key kwata kwata a ciki .
Sau biyu tana sake dubawa kafin ta dâanyi froze kadâan na dâan lokaci tana tunani..
â Tunanin me kike ? Ki budâe mana mota mu shiga .â Cewar Ameerah .
Itama kallanta Zarah tayi cikin tunanin ta furta â Banga key dâin ba.â
â Kamar ya baki ga key dâin ba ?â. Ameerah ta sake tanbaya .
â Yes abunda nace kenan .âcewar Zarah .
â Itâs fine Zarah bari na shiga na duba inda muka tsaya probably ma a wajan ne key dâin ya fadâi.â Cewar Mimi ba tare da ta jira reply dâin kowa ba ta bar wajan zuwa cikin wajan.
Tana shiga direct wajan da suka tsaya ta nufa , tana duba key dâin babu shi kwata kwata , har wadâan da sukayi placing order a wajan su suka tanbaya suma suka ce basu gani ba dan sai da suka duba matan suma .
Haka ta haâkura da dubawar tayi âkoâkarin fitowa .
Kamar ance ta kalli wani shara da yake gefen hanyar fita sai kawai idanuwanta ya sauka a kan key dâin.
Cikin mamakin yadda akai ya zo wajan ta dâauko shi tana dubasa sabida ta tabbatar da ko shi dâin ne .
â Yes key dâin ne ..â bata tsaya wani dogon tunani ba sabida tanasan komawa gida , kawai sai ta watsar da tunanin komai ta nufo su Zarahn tana dâaga mata key dâin.
â A ina kika gansa ?â Zarah ta tanbaya lokacin da take amsar key dâin.
âCiki mana probably daman nace miki may be a ciki ya fadâi , now weâre good to go right ?â.
âYesss DearâŠâ Zarah ta bata amsa , kafin ta kunna mota kowa ya shiga kamar dâazu Zarah da Mimi suna gaba , Ameerah da Cynthia suna baya .
_______ Ana cikin tafiya a hanya text daga unknown number ya shigo kamar zata share sai kuma ta duba message dâin.
â KI KULA DA KANKI âŠâ shine kalma hudâu da akai mata .
Sake maimaita kalmar tayi aranta, kafin tayi âkoâkarin shiga taga wane ne ya turo mata message dâin .
Babu number babu alamarta , duk yadda taso âkoâkarin nemo
Number ta kasa ga baki dâaya abun kamar wani almara .
Kallan Zarah tayi kamar zata fadâa mata , sai kuma ta share ganin ba su kadâai bane a cikin motar , sai da ta mayar da kallanta zuwa window .
Yadda motoci suke faman tafiya abun su , har hankalinta ya kai kan wata mota baâka me baâkin tinted da take bayan su .
Zarah ba wani over speed gudu take ba , motoci da yawa suna wuce su , amma abunda zai ja hankali yadda itama motar bata gudu sai dai motoci da yawa da suke wucewa .
Cikin zaâkuwa Mimi ba tare da ta kalli Zarah ba ta furta â Zarah dâan âkara speed dâin motar nan , ki wuce atleast 2 cars or more .â
â But why ?â. Zarah ta tanbaye ta .
â Itâs nothing , kedai kawai kiyi , just for chill âŠâ
Babu musu Zarah tayi kamar yadda Mimi tace .
İta kuma Mimi idanuwanta yana kan motar nan tana so taga ko zata âkara gudu ko zata tsaya a yadda take dâin.
Sai gashi kuwa itama ta âkara gudu sosai , ta wuce cars dâin da Zarah ta wuce , ta sake dawowa bayan Zarah dâin kamar dâazu .
â Zarah dâan âkarayı âŠâ
Kallanta Zarah tayi , ganin hankalinta na cikin mirror sai kawai ta sake yin yadda tace, itan ma tana dâan sakar mirror dâin, Wanda akan idanta baâkar mota ta dawo bayanta .
Sai suka kalli juna ita da Mimi .
Da ido Zarah tayi mata magana , ita Mimi ta dâan mata alamar itama bata sani ba.
Duka wannan abun Ameerah da Cynthia basu san me yake faruwa ba .
Cikin ganganci Zarah ta canza hanyar da suke bi , zuwa wani side dâin.
At the same time motar da suka gani itama ta bi side dâin.
Hankalin su ga baki dâaya ya tashi sabida basusan me hakan yake nufi ba , shiyasa Zarah ta âkara speed dan hanyar da suka bi yanzu sai ya dâan ja musu lokaci kafin su tafi gida tunda kamar baya suka sake dawowa a wani wajan .
Cikin tsoro Zarah ta furta â Wai wana mota ne haka Mimi?.â
â I donât know too ..â itama Mimi ta bata amsa .
â Wana car kuke magana akai ?â Cewar Ameerah .
Zarah da ta soma dibibi cewa ta furta â I donât know Ameerah , amma kamar akwai motar da take bin mu a baya ..â
Kusan lokaci dâaya Ameerah da Cynthia suka firta â Whattttttt..â
Ba shiri ko wani second thought Ameerah ta dâauki wayanta tana danne danne , cikin sauri sauri.
Mimi kamar tasan hakan zai faru ta jiyo ta kalleta â Ameerah amma ba fadâa zakiyi a gida ba ko?â.
â Kin riga kinsan amsar ai , zan zauna kawai mota na bin mu ban san ko wana mota bane , salan na rasa raina a banza .â
â Amma ai bamu confirming motar mece ce ba ko?.â
â To uwar bin diddigi ai sai kisa Zarah tayi parking motar sai ki fita ki tanbaye su ko su wane ne su .â
â Kai kai kai Ameerah kina da matsala wallahi sometimes.
Yanzu mene ne na bakar magana ke kwata kwata ba zaâa fadâa miki magana kawai ki dâauka ba , sai kin dinga ya âbawa mutum yadda kika ga dama me haka ? Ku bari mu koma gida safe mana .â Zarah ta dâanyi maganar a âkufule âŠ
Cikin âkaramar murya Cynthia ta kalli both Ameerah da Mimi â Please kuyi haâkuri mu koma gida safe , idan ya so daga baya sai kuyi magana âŠâ
Maganar Cynthia kuwa kamar âkara ziga Ameerah yayi , dan har dâagowa tayi sosai daga jin ginin da take tana fadâin â Safe ? How can we be safe when someone is literally following us ?.â
â Amma ba mu da tabbacin hakan, zargi ne kowa yake , weâre not that sure .â Cewar Zarah .
â Then stop the car and letâs confirm !â.
â Youâre insane Ameerah ! Baki da hankali abi?.â Cewar Mimi .
â Ina zanyi hankali tunda kece kike rabawa , ai baki bani nawa kasan ba shiyasa bani dashi .
The fact that kina gaban motan ma , atleast tun tuni ya kamata ki duba kiga in weâre safe , but your mind is somewhere else âŠ.
Banzan kallo Mimi tayi mata yanzu sabida yadda ta gaji da halin Ameerah yau â Am feed up with your nonsense now Ameerah .
Do your worst please , wait me kike so ma nace miki? Ajje ni kikai da ko wana movement akai sai na kawo miki? Tunda job kika bani?â.
â Nothing ! Iâm just saying âŠâ
â Ameerah please!â Zarah ta ka tseta daga abunda take âkoâkarin cewan .
Amma ina sai da Ameerah tayi magana .
â Zarah baki ji abunda ta gama cewa ba yanzu , wallahi sometimes idan Mimi tayi abu har mamaki take bani , sai kace tafi kowa .â
Sake jiyowa Mimi tayi ta kalleta kafin ta furta â Excuse me ?â.
â Yes kinji ni sarai ai abunda nace .â
â Ameerah wai me kike so ne ? Tun dâazu neman abunda zaki jangwalo ni kike , what do you want please! Me nayi miki ?â
â Ni ai bance kin mun wani abu ba , I can talk and i have the right to talk abi.â
â Yes you can talk yadda kike so Ameerah , but for now please stop talking to me ..â
â Ke zaki iya magana nice bazan yi ba sabida kin haife ni am under you ko ?â.
â AMEERAH .â Zarah ta fadâa da âkarfi .
A wannan lokacin sai da motar ta dâanyi zig- zag sabida juyowar da Zarah tayi ta kalli Ameerah lokacin da ta ambaci sunanta .
Cikin sanyi da tsoro Mimi ta furta â Becareful Zarah .â
Gyara hannunta sosai Zarah tayi , cikin calm voice tace wa Mimi â Mimi dan Allah ki rabu da ita haka , hankali na yana âkoâkarin rabuwa biyu kinga abunda ya faru yanzu .â
â Fine ! Na bari .â Cewar Mimi tana mayar da kanta saitin Window .
Sai da Ameerah ta sake magana , amma both Zarah da Mimi shareta sukai , kamar basu san tanayi ba , sai a time dâin Cynthia ta dâan taâbata alamar tayi shiru , sannan ta nuna mata âkaramun note message da tayi a wayanta .
Ameerah tana gama karantawa ta dâan ja âkaramun tsaki , sannan ta koma ta zauna sosai akan kujera .
â Zarah I think mu shiga more crowded place , ko mu tsaya a police station tunda wajan nan babu cars sosai .â Cewar Cynthia .
â Yeah kin kawo good idea .â
Cewar Zarah kafin ta âkara speed dâin motar har sai da Mimi ta furta âZarah⊠please slow down a little.â
âBa dai yanzu ba .â
â Zarahâ Mimi ta kuma ambatan sunanta .
â Mene ne ?â.
â Kalli mirror .â
Babu musu Zarah ta duba mirror su kuma su Ameerah suka juya bayan mota dan suga me yake faruwa .
Motar yanzu guda biyu ce , bayan wadda take bin su , da kuma wata da ta fita girma , baâki da kuma duhu sosai .
Kafin dâaya daga cikin su yayi magana wata âbakar motar ta sake âbillowa , suka zama su uku, amma sun saka motar da take bin su Mimi a tsakiya .
Sai Zarah ta âkara speed dâin motar su , kafin ta tsakiya tayi over speeding , sai dâaya daga cikin motocin da sukazo tayi over speeding.
Ya zamto motar su Mimi na gama , sai dâaya daga cikin SUV CAR sai âbakar motar da take bin su , sai kuma dâayar SUV car dâin itama .
Amma yanzu sunyi mugun rage speed dâin su , sabida motar gaba da take tafiya a hankali har ya zamto su Mimi sun basu ta zara da dâan yawa .
â Wadâan nan motocin fa ?â. Cewar Ameerah .
Amma babu wanda ya bata amsa, hakan ya bawa Zarah damar âbulla titin da zai kai su gida , which theyâre now safe , babu wanda motar motocin kwata kwata a tare dasu .
Lokaci dâaya duka suka furta â Alhamdulillah âŠâ
Sai a lokacin Mimi ta lumshe idanuwanta , message dâin dâazu da aka ce mata â KI KULA DA KANKIâŠâ da kuma maganar Joy da ya fadâo mata arai .
âA duk lokacin da matsala ta tunkaro ki, ya zama mutum na farko da zaki soma neman taimako a wajansaâŠâ
Sai kuma ta furta â UNCLE MOH..â
Zuciyarta ta buga da âkarfi sabida wani tsoro da ya shiga zuciyarta .
Tana duba time dâin waya sai taga missed call dâin Mamy kusan uku , ga na Yaya Sadiq , Yaya Abba da Uncle Saleem, aushe ta saka wayar a silent ita bata ma sani ba .
Wani irin tashin hankali ne taji ya soma lulluâbeta , sabida batasan mai zai faru ba yanzu idan sun lol gida , musamman idan aka san abunda ya faru yanzu âŠ
â Innalillahi wa inna ilaihi rajiâun âŠâ shine kalmar da take faman nanatawa , bawai ganin missed call dâin su Mamy bane tashin hankalinta , ganin babu kiran Uncle Moh shine abunda yafi komai dâaga mata hankali.
Da more suna kusanta hanyar gıda , da more hankalinta yana âkara tashi, âyan yatsun hannunta har rawa suke .
Tana hango gate dâin gidan su kuma zuciyarta ta buga da mugun âkarfi, tanaji kamar zata fito waje , ga baki dâaya komai ya dena yi mata dadâi , haka kuma motar tayi shiru har aka budâe musu gate âŠ.
Cikin wani low speed motar ta shiga cikin, kai tsaye a compound ta tsaya .
Zarah tana kashe motar Ameerah da Cynthia suka fita daga cikin motar , basu tsaya yiwa Zarah ko
Mimi magana ba sai ice cream dâin su da ya riga yayi melting da kawai suka dâauka .
âDan binsu da kallo su Zarah sukai ganin sun nufi part dâin su .
Mimi kuwa har time dâin hannunta rawa yake shi kadâai .
â Are you Okay Mimi?â. Zarah tayi mata tanbayar dan itama taga yadda hannunta yake rawan.
Mimi bata amsa mata ba sabida hankalinta kwata kwata baya kanta .
â Mimi..â Zarah ta kuma kiran sunanta , tana dâan taâbota .
Sai a lokacin Mimi ta furta â Uhm?â
â Are you okay ?â. Zarah ta kuma
jefa mata tanbayar .
âYeah yeah am fineâŠâ cewar Mimi tana âkaâkalo murmushin da ya kasa zama a kan fuskarta .
â Am sorry Mimi ! Nasan Uncle Moh ku su Mamy zasu iya miki fadâa , but itâs not my intention da nasan hakan zai faru da bamu je yau ba, am sorry please .
Ko na biyo ku na fadâawa Mamy abunda ya faru .â
âNo Zarah kinsan zaki âkara âbata abun ne idan kika fadâa musu .
Donât mind Iâm fine ! Letâs go nasan sun san mun shigo , kar su ji mu shiru âŠâ
Da haka suka fito Zarah tana riâke da nasu ice cream dâin da yayi melting .
Shi ta dâan dâagowa Mimi kafin ta furta â Zan sa mana a fridge yayi âkanâkara may be zuwa gobe sai musha tunda yayi melting yanzuâŠ..â
â Okay âŠâ Kawai Mimi tace kafin su soma tafiya , amma babu mai magana a cikin su , har su kazo hanyar da zasu rabu, Zarah tayi part dâin su .
Itama kuma Mimi ta wuce nasu part dâin , zuciyarta yana dukan 100 100 bama 10 10 ba .
Tana zuwa entrance dâin building dâin su taji muryar Mamy .
âMimi..â
Cak Mimi ta tsaya , zuciyarta na sake bugayawa , bakinta har ya soma rawa , lokacin da take âkoâkarin amsawa Mamy â Naam Mamy..â
â Ina kuka tsaya Mimi? Last call da mukai kika ce mun gida zaku tako , which zuwa time dâin yaci ace na manta ma da dawowan ku gida .
Wani wajan kuka tsaya ko? Baki ga calls dâina ba ? Baki ga Sadiq ko Saleem wani yana kiran ki ba? Ina kika ajje wayan ki Mimi?â.
â Mamy âŠâ Mimi tayi maganar kamar za tayi kuka sabida yadda ta dinga jin tanbayoyin Mamy babu tsayawa .
Ajiyar zuciya Mamy ta sauke , kafin ta riâko hannunta suka shiga cikin falon .
Yaya Sadiq , Uncle Abba , da kuma Uncle Saleem suna ganinta suka miâke tsaye daga zaunen da suke , suna nufo inda take .
Uncle Abba ne ya riâko hannunta , har ya zauna da ita akan kujera , ganin yadda face dâinta tayi tsuru tsuru kamar bata gaskiya yasa ya sakar mata murmushi , sannan ya shafa âkirjinsa a hankali yana mata alama da ta kwantar da hankalinta .
Sai da Mimi ta sauke numfashi mai âkarfi tukunna Uncle Abba ya furta â Is fine ! Everything is fine . Karki wani dâaga hankalin ki .
Amma ina kuka tsaya Mimi ? Mamy tace ta kira ki kuna hanya amma kuma ya akai kuka dade ? Ko kun sake tsayawa a wani waje ne ?â Kanta Mimi ta girgiza masa alamar aâa sai kuma tayi tunanin abu dâaya.
Idan har ta âboye musu abunda ya faru toh tabbas za suji asalin maganar a bakın Uncle bashir ko Ameerah dan bazata taâba âboye asalin abunda ya faru ba .
Idan kuma basu ji daga bakinta yanzu ba , ba zasu ji dadi ba nan gaba shiyasa Mimi bata âboye musu komai ba ta labarta musu abunda ya faru har zuwa âkarshe .
Abu dâaya kawai ta âboye musu shine text message da aka turo mata.
Sai da suka gama sauraranta ga baki dâaya amma kuma babu wanda ya samu âkarfin gwiwar cewa komai na tsawan lokaci .
Kafin daga bisani Mamy ta furta â Tashi kije kiyi sallah , lokaci yana ta tafiya , daga baya mayi tafiya .â
Wannan kalma ta Mamy shi ya âkara dâaga mata hankali , ko ba komai tana so Mamy tace wani abu ko su Uncle Abba dâin amma babu wanda yayi magana .
Jiki babu âkwari ta wuce dâaki.
Wayanta kawai ta ajje akan gado ta fashe da kuka , dan batasan ya zata âkare da Uncle Moh ba idan ya dawo cikin gidan nan .
A inda take a nan ta durâkushe tana janyo pillow dâin da yake kusa da ita .
A hankali take kukan mara sauri, sai ruwan hawaye da yake saukowa babu âkaâkâkautawa .
â Ya Allah ! Na shiga uku ..â ta furta a hankali, tana goge fuskarta da tafin hannunta .
â Wata kaddara ce ta fadâo mun yau ?.â
Tanasan ta nutsu ta kwantar da hankalinta ko ta samu courage dâin yin sallah amma ta kasa , zuciyarta ga baki dâaya taâki tsayawa waje dâaya , tunani ne kala kala yake faman shige da fice a cikin ranta .
Hannunta ta kai kan wayarta da ta ajje aka gado .
Message dâin nan dai na dâazu ta sake budâe wa .
Yanzu ma sai da ta sake dubawa ko zata ga suna da number waya , but still yana nan an unknown dâinsa .
â Waye kai ?â Ta furta a hankali kamar mutumin yana ga banta .
â Me yasa kace na kula da kai na ?â Still babu mai bata amsar tanbayar da tayi .
Sai ga hawaye sun sakko mata daga both idanuwanta .
Contact list dâinta ta shiga , direct kan sunansa ta tsaya â UNCLE MOH âŠâ
Cikin chart dâin su ta shiga wanda sun dare ko shekara ma sosai .
Last magananta dashi kuma 6 month , kuma duka short message ne daga wajansa , dan reply dâinta yafi yawa da voice ba kamar shi da yake dropping 3 to
4 single words ba .
Shi kuma dâayan biyu is either warning ko kuma umarni baya wuce haka messages dâinsa .
Lumshe idanuwanta tayi tana shaâkar iska , maganar Joy kuma har yanzu yana sake mata yawa a kunne. .
Shiyasa ta samu courage dâin ta kirasa da kanta ta fadâa masa komai kafin yayi confronting dâinta ko taji sauâki sauâkin abunda yake ran nata .
Tana danna voice call , kafin wayar ta soma ringing tayi saurin katse wa .
â Me zan ce masa ?â Ta tanbayi kanta .
â Uncle Moh na fita ban fadâa maka ba , wasu motoci sun biyo mu har mukai late bamu dawo gida da wuri ba ?â. Sai ta girgiza kai alamar bai yi ba .
Ko kuma â Uncle Moh an turo mun message ance na kula da kai na ?â Ta ja wani numfashi tana sauke ajiyar zuciya â Bazan iya ba .â
Kafin ta samu damar sake yin wani tunani, taji an âkwanâkwasa âkofar dâakin.
Hawayen fuskarta ta goge da sauri tana fadâin â wane ne ?â.
Taji shiru baâa bata amsa ba sai sake âKwanâkwasa âkofar da kai â Knock knockâ
Babu musu yanzu taje ta budâe âkofar a hankali .
Mamy ce ..
Tana ganinta kuma ta kawar da kanta gefe
â Kinyi sallar da na saki?â
â Aâa Mamy .â
â Toh me kike jira ? Ko alwala kike so nayi miki ?â.
â No Mamy âŠâ
Da hannu Mamy ta nuna mata toilet â Oya maza tashi kije kiyi sallah my friend , ko so kike lokacin sallah ya wuce kina zaune ?â.
Sim sim sim Mimi ta wuce toilet , bata wani jima sosai na ta fito da alwalar ta .
Mamy tana tsaye a dâakin har ta tayar da sallah .
Sai da ta isar tayi addua tukunna Mamy ta samu waje ta zauna , bayan kamar mintuna biyar ta ambaci sunanta â Mimi.â
â Naam Mamy.â
â Zo ki zauna a kusa dani .â
Babu musu Mimi ta nufi inda take ta zauna , tana dâora kanta a kan cinyar Mamyn . Ita kuma Mamy ta soma shafa kanta , moment dâin ya dawo na uwa da âya .
â Kin zauna sai faman kuka kike akan abunda kinsan ba zaki kujewa ba .
Salan kanki yayi ciwo ko ?â
â Amma Mamy bansan me zai mun ba in yazo .â
â Shiyasa kika shigo gidan kamar wacce aka kashewa mutum? .
Ki nutsu wannan kukan da kike duk ya tsaya haka , banaso , koma dai mene ne ai ba zai cinye ki dâanye ba .â
â Mamy toh Dan Allah kiyi masa magana da kanki kinji?â.
Girgiza mata kai Mamy tayi â ko Baffan ki ba zai saurara ba balantana ma ni Mimi .
Kinga wannan Uncle dâin naki ? Zuciyarsa a ta fashe yake , in kinga yayi rangwami akan abu toh tabbas bakya ciki .
Amma idan har kina ciki , ni kaina bansan yadda zuciyarsa take juyawa ba lokaci zuwa lokaci .
Ki duba kiga a cikin yaran gidan nan , babu wanda maganar mintuna take hadâa shi dasu bayan gaisuwa amma ke yana miki magana , kuma har access dâin part dâinsa kike dashi wanda duk cikin gidan nan babu mutum dâaya da yake da wannan access dâin.â
â MAMYYYYYâŠ.â Mimi taja sunan a shagwaâbeâŠ.
â Zan sa a kawo miki abinci yanzu , amma karki kwanta bakiyi sallar ishaâi ba . Kinji ni dai ko?â
â Naji ki Mamy âŠ.â
â God bless youâŠ.â Mamy ta dâanyi mata kiss a goshi tana fita daga dâakin.
A inda take a zaune , tananan a wajan har dâaya daga cikin maid dâin su ta kawo mata abinci .
Bata da wani appetite sosai, amma kuma tana jin yunwa sosai , shiyasa ta dâan tsaâkuri abunda zata tsaâkura ta ajje ragowar a gefe .
Lokacin sallahr ishaâi nayi ta tashi tayi sallah , zuwa lokacin hankalinta ya soma kwanciya duk da kaso mafi yawa na damuwar yana danâkare a zuciyarta .
***** Tara nayi ta duba agogo , 10 ! 11 duk idanuwanta biyu ga bacci na janta gashi kuma tana tsoran tayi bacci Moh ya dawo cikin gidan.
An tafi 12 , 1 , 2 âŠâŠ. 2:30am aka budâe gate dâin cikin gidan lokacin bacci ya riga yaci âkarfin Mimi bata san ya dawo cikin gidan ba .
Black Mercedes Benz ce ta shigo cikin gidan da dâan speed dâinta , kai tsaye a wajan part dâinsa yayi parking ya fito.
Jikinsa sanye da wasu baâkaâken kaya, harta da p-cap da take kansa baâka ce , bayan colour skin dâin jikinsa babu wani abu me haske a jikinsa .
Gashi daga sautin âyan yatsunsa yayi rapping hannun da wani baâkin âkyalle .
A haka ya shiga cikin part dâin, yana zuwa sama ya wuce direct , bayan kamar mintuna 30 ya sakko , kayan da suke jikinsa sune dai a jikinsa bai canza su ba kuma bai cire p- cap dâin kansa ba ya fito ya wuce part dâin Mamy .
Har an kashe wasu daga cikin fitilun sashen sabida dare yayi sosai ya wuce sama .
Direct kuma dâakin Mimi ya nufa , baiyi Knocking ba , baiyi komai ba ya budâe âkofar dâakin ya shiga .
Fitilan dâakin a kunne take shiyasa ya hangota a âkarshen gadon dâakin, ta lulluâbe jikinta sosai sabida Ac da yake a kunne .
Sai da ya tsaya yayi mata kallo kamar na mintuna 5 sannan ya nufi gadon , ya yaye bedsheet .
Zumâbur Mimi da take bacci ta tashi sabida ta riga ta sawa ranta zai shigo dâakin a ko wana lokaci.
Suna hadâa ido dashi jikinta ya soma rawa , kuma shima yaga yadda jikin nata yake rawa , amma kuma babu dâigon hawaye ko dâaya a fuskarta dan neman hawayen tayi ta rasa a wannan time dâin .
Bata ganin cikin idanuwansa sosai shiyasa ta rasa a wana stage yake a yanzu .
Hannunsa dâaya ya miâka mata , babu musu ta miâka masa natan, ya janyota ta miâke da âkafafuwanta.
Da fingers dâinsa ya nuna mata ta saka dâan kwali , nan ma babu musu ya ja mayafin da yake bed ta yafa , har time dâin kuma bai saki hannunta ba , ya jata suka bar dâakin.
Mimi sai waige waige take , tanaso taga ko akwai wanda zai kwace ta , amma babu , ga kuka yaâki zuwan mata sabida yadda ta shiga tsakanin tashin hankali, haka Moh ya fita da ita daga cikin dâakin nan ba tare da yace da ita komai ba, ya wuce da ita part dâinsa âŠ..
âž»
To be continued⊠đ„
BLACK QUEEN đ€đż
***