MISHAL

Page 10/11

by @ayshagaladima22

***


MISHAL



By BLACK QUEEN đŸ€đŸż
***


MAI SAN A TALLATA MASA KAYANSA YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER ***



Book 1 
 Page 10 / page 11


Suna shiga part d’insa, door d’in bayan su ta rufe .

Mimi ji tayi kamar tayi ‘karyan suma ko zai rabu da ita, amma har yanzu bai saki hannunta ba . 

Hannunsa yana ri’ke da nata har sai da suka shiga tsakiyar falon tukunna ya saki. 

Akan 2 sitter ya zauna yana ‘balle ma’ballin gaban rigarsa guda d’aya , sannan ya jinginar da kansa akan kujerar na tsawan wasu sekonni.

İta kuma tana tsaye daga inda ya barta , babu umm babu um uhm da take sai ‘kif- ‘kifta idanuwa kawai da take . 

“ Zauna” yayi maganar cikin ‘kashan ma’kushi. .

Karaf kuwa maganar ta sauka akan kunnanta kamar dama jira take yayi maganar . 

Daga kujerar da take kallansa ta zauna , tana wani sunkuyar da kai, gashi baccin da take ji bawai isarta yayi ba . 

Tsaban tsoran abunda zai iya faruwa ne yasa taji kamar baccin ya tafi ga ba d’aya . 

Bayan kamar mintuna biyar ganin shi me mata magana ba kuma bai ce ta tafi ba ta soma guna guni cikin ‘kasan murya ta furta “ Ni kawai mutum ya hanani bacci . Yo ba kwanda in kwado na zakayi ba kayi kayi kwado na amma ka hanani bacci ka zaunar dani kamar me gadi
” Tana cikin wannan guna gunin ya furta “ Me kika ce ?”

Cikin sauri ta soma girgiza hannunta da kanta tana fad’in “ Ni babu abunda yace fa Uncle Moh ..”

“ Okay ! Kin natsu yanzu ?”.

“ Taya zan natsu bayan kana nan”. Tayi maganar cikin zuciyarta . A fili kuma ta girgiza masa kanta sannan ta amsa a rarrabe “ Na natsu Uncle Moh 
”

“ Okay follow me 
” ya mi’ke ya nufi kitchen itama kuma ta biyo bayansa fuskarta cike da mamakin zuwan nasu kitchen . 

Sai da suka shiga tsakiyar kitchen tukunna ya d’an matsa gefe , kamar bazai ce mata komai ba sai kuma yayi magana “ Cook something shaf shaf 
”

Baki a sa’kale , Mimi ta furta “ Uncle Moh dare yayi fa .”

“ Oh haba ?” Ya bata amsa yana kallanta . 

Kamar za tayi kuka ta furta “ Dan Allah Uncle Moh kayi hakuri in safiya yayi sai na dafa maka ko me kake so , amma yanzu tsakiyan dare ne.”

Ko bi takanta Moh bai yi ba sai ma cewa da yayi “ Healty food zaki dafa , am waiting.” Daga nan ya fice daga kitchen hankali kwance .

Wani irin harara Mimi ta bishi dashi kamar idanuwanta zasu fad’o ‘kasa . 

Sabida haushi da ta kaici ko ‘kwalla babu a cikin idanuwanta. 

Ji tayi ga baki d’aya kamar ta ‘Kona kitchen d’in ko hankalinta zai kwanta . 
Sai kuma ta sauke dogon , nannauyan ajiyar zuciya tana had’iye wani abu da ya tsaya mata a ma’koshi. 

Ta rasa ma me zata dafa dan ga baki d’aya idea d’in girkin ya d’auke mata aka tasan ba zata iya wani abinci sosai cikin daren nan ba aikuwa ta d’auko noodles guda biyu, da pepper , irin pepper d’in da kana gani kasan sunyi yawa a indomie guda biyu , ta d’auko fresh onions , har dasu green pepper da yellow pepper duka ta yanka , sannan kuma ta d’auko eggs guda biyar . Aka daga indomien su . Amma Kwan bawai dafawa tayi ba , ta soya sune had’e da indomien da tayi ja sosai sabida pepper da tasha . 

Kamar wacce tayi abun arzi’ki, ta d’auko tray ta saka plate d’in indomien, ta bud’e fridge ta d’auko fresh orange juice , da ruwa duka ta saka akan plate d’in da kuma fork .

Ita kanta tasan abunda tayi ba zasu ‘kare da kyau ba , amma sabida haushi da ya bata yasa ta çıka masa pepper d’in, sai abu biyu ya had’u ya tarar mata , ga shegen tsoro, ga kuma neman rigima . 


Simi Simi ta fito daga kitchen lokacin ya canza kayan jikinsa zuwa simple shirt fara , da kuma farin wando shima simple. 

Yana zaune kan kujera ga bansa kuma laptop ne , da kuma bottle of water da bai ma bud’e saba kwata kwata .

Hankali kwance yake operating laptop d’i nan kamar ba dare ba . 
Shigowar Mimi kuma bai dakatar dashi da abunda yake yi ba , har sai da tayi sallama tana ‘karaso wajan, da tray d’in hannunta. 

Muryanta har zuwa lokacin bai gama dawowa dai dai ba “ Uncle Moh ! Ga abincin naka 
” 

Da hannu d’aya ya nuna mata center d’in kusa dashi , babu musu ta ajje masa , ta juya zata wuce wajan long sitter ya kirata . 

“Come back here 
” 

Yanzu ma babu musu ta jiyo ta dawo inda take , tana ‘bata fuska kad’an kad’an sabida ya hanata yin baccin ta ga baki d’aya kuma lokaci sai tafiya yake . 

“ d’auko mun fork .” Ya umarta yana kallanta . 

Da sauri ta furta “ Uncle Moh akwai fork fa akan tray d’in, kallansa .”

“ Do as i said 
” yayi maganar cikin umarni.

Mimi bata kawo komai a ranta ba ta koma ta d’auko wani fork d’in, a gefen inda ta ajje na farko ta ajje na hannunta , kafin ta furta “ Ga fork d’in.”

“ Good .. zauna ki soma ci
” 

“ Ci kuma ? Ni bana jin yunwa .” Ta soma kokarin dogging, amma kallan da yayi mata yaƟa tayi shiru da bakinta .

Ita bata d’auki plate d’in ba , kuma bata matsa daha inda take a tsaye ba .

“ Bakiji abunda nace miki ba?”.

“ Uncle Moh Allah bana jin yunwa , bacci nake ji , kai na har ya soma ciwo.” Tayi maganar cikin marairaicewa . 

‘Dauke kallansa yayi daga kan laptop zuwa fuskarta , fuskarsa ba a had’e ba , sannan kuma ba’a sake take ba “ And who cares ?” Yayi tanbayar har lokacin idanuwansa na kanta . 

Ji tayi wani irin a zuciyarta , akan furucinsa , hakan yasa bata kuma ‘ko’karin yi masa musu ba , ta d’auki plate d’in indomien ta wuce dinning , ko kallan inda yake bata sake yi ba . 

Haka ta saka 1 spoon d’in indomien a bakinta , taji wani azababban test d’in yaji a bakinta, kuma daman kwata kwata bata ‘kaunar yaji sosai a abinci, lokaci d’aya taji ‘kirjinta yayi mata zafi sabida yajin da taci. 

Amma bata jiyo ta basa ha’kuri ba akan ya barta . Ta ‘kara kai indomien bakinta , nan d’in ma yaji, ‘kirjinta har ya soma yi mata suya, take hancinta ya soma tsiyaya shima , Allah ya temaketa akwai tissue a kusa da ita , duk spoon d’aya sai ta ‘kurbi ruwa , ga baki d’aya spoon 8 tayi ta ajje spoon d’in , sannan ta matsar da tray d’in abincin gefe , ta d’ora kanta akan dinning , wani irin kuka na zuwan mata . 

Abund take ji a ‘kirjinta amaimakon ya ragu sai ‘karuwa da yayi, hakan yasa kukan da take ya sake ‘karuwa , sai dai ba’a jinsa sosai sai shashshe’karta da kawai ake ji. 

Daga time d’in da ta wuce dinning idanuwansa na kanta har abincin da taci da kuma kukan da take duk akan idanuwansa , baiyi magana bane kawai, sai da tayi kuka iya yinta tukunna shima ya nufo dinning d’in. 

Yana jan kujera , ita kuma ta mi’ke ta bar wajan, bai jiyo ya kalleta ba ya zauna yana kallan abincin da yake gabansa. 

Kafin ya d’auki spoon ya soma cin abincin , kamar babu yaji , dan reaction d’insa bai canza ba ko a fuska , kuma baisha ruwa ba har ya gama cin indomie duk da shima bai cinye duka ba .

Mimi kuwa da ta dawo falon akan babban 3 sitter ta kwanta tayi rufda ciki, tana ‘kananan kukan da yake cimata rai, da kuma harshenta da take faman washewa ko yajin da take ji zai ragu. 

Shi kuma ya shiga wani d’aki da yake ‘kasa , bai dad’e ba ya fito da ‘karamun box akan dinning ya bud’e ya cira abu. Ba’a ganin ko mene ne a ciki sabida yadda jikinsa ya kare , sai motsin damtsen hannunsa kawai da suke motsawa . 

Sannan ya nufo inda take a kwance, yanzu fuskarsa ba’a had’e take ba , ya saketa sosai sannan ya ambaci sunanta “ MISHAL..”

“ Uhm” Kawai tace tana ta sowa zaune , dan yanzu ta dena jin tsoran abunda zai mata , kome ya ga dama ma yayi mata , babu ruwanta . 

Abunda yake hannunsa ya mi’ka mata , magani ne irin na tsotsa d’in nan da yawanci idan ‘kirji yana suyan nan ake sha, wato maganin ulcer .

Bata kallesa ba sai maganin da ta amsa kuma ta’ki ce masa sorry. A maimakon ma ta tsotsa maganin sai ta tattauneta ta had’iye, tana komawa ta kwanta .

Duka wannan abun da take yana tsaye a kanta , har da wani juya masa baya tayi , wanda hakan yasa yayi gajeran murmushi gefen la’b’ba . 

Unexpected ya juyo da ita daga juyamar bayan da tayi, Hakan kuma ba ‘Karamin tsorata Mimi yayi ba , sabida abun ya zo mata unexpected. 

“ Ni zaki juyawa baya ?” Yayi maganar cikin ‘kasan ma’koshi.

A hankali ta girgiza masa kanta “ A’a bacci zanyi shiyasa na juya .”

“Kalle ni” yayi maganar har lokacin yana a inda yake.

Babu musu Mimi ta kallesan .

“ Me akai miki?”. yayi tanbayar kamar mesan gano amsa a cikin idanuwanta .

Bata lokacin da idanuwanta suka buga masa wani harara ba , ita kanta batasan tayi ba sai daga baya . 

Shi kuma ya wani d’aure fuska, kafin ya d’an ta’be bakinsa kad’an yana barin wajan . 

Hakan ya bawa Mimi damar komawa kwanciyar da tayi . 

A hankali ! A hankali bacci ya soma d’aukarta me nauyi, shi kuma ya wuce sama bedroom d’insa . 

_____ 
‘ Karfe 4:20am Moh ya sake sakkowa ‘kasa , yanzu jallabiya ce a jikinsa milk colour, damtsen hannunsa ya fito sosai a cikin rigar. 

Inda Mimi take kwance ya nufa , baccinta take hankali kwance duk da ta d’an takure jikinta kad’an alamar jin sanyi . 

Dai dai gefen gadon ya d’an bubbuga , kafin ya ambaci sunanta “ Mishal
 Mishal
” 

Tace “ uhm 
” a cikin baccin da take .

“ Wake up
.” Ya furta a hankali. 

Ta kuma cewa “ Uhm
” 

Sai kawai ya furta “ Snake 
” 

Ai wannan kalmar a kunna Mimi ta sauka , ta wani bud’e ido a zabure, ta mi’ke , sai kawai taji jiri na ‘ko’karin kayar da ita , sabida ta tashi cikin gaggauwa , da ‘kyar ta iya kama damtsen hannun Moh tana sauke ajiyar zuciya. 

“ Scary cat , zaki sake ni ko sai na d’auko micijin?”.

Babu shiri Mimi ta sakar masa hannu tana d’an turo bakinta . 

“ are you trying to seduce me ?”. Yayi tanbayar bayan ya bada step baya sau d’aya .

İta kuma ta saki baki tana kallansa tama rasa abunda za tace. 

Shiysa ya katse mata tunani ta hanyar fad’in “ Lokacin sallah zai wuce , ki wuce kije ki canza wannan kayan and also pray.”

Da Tom ta amsa masa zata nufi Door yaga har lokacin bata wats tsakewa ga baki d’aya ba.

Hannunta kawai yaja ba tare da yace komai ya nufi wani corridor da yake part d’in . 

Da fari hanyar kamar jikin bango yake, dan ba zaka ta’ba sanin akwai hanya irin haka a wajan ba . 

Ita dai Mimi binsa kawai take bakinta cike da magana amma kuma bata da me bata wannan amsar. A haka dĂŒk hanyar da yafi itama nan za tabi, har taga sun tsaya a wani bango. 

Carfet d’in wajan ya gyara wa zama take ‘kofar ta bud’e , sai a lokacin Mimi taji tana san yin magana amma ya rufe mata baki ta hanyar bata dirty look d’insa me kad’a mata ciki. 

Simi simi ta shiga ‘kofar da ya nuna mata a hannu. 

Tana shigo ‘kofar ta rufe ruf
 ita kuma ta ganta a jikin falon su . 

‘Dan juyowa tayi tana kallon jikin bangon ko zata ga ‘kofar da ya bud’e mata amma ta kasa ma , duk ‘kwaf’kwafin da ta tsaya yi , taga hanyar ta kasa kuma a cikin falon nasu babu wani abu da zata iya cinka wanda zai nuna mata cewa abun bud’e ’kofar ne . 

Ganin bata da idea kawai ta wuce bedroom d’inta tunda time d’in babu wanda ya fito .

Tana shiga ta fad’a kan gado tana fad’in “ Wayyo Allah na 
” 

Kafin tayi saurin wucewa toilet kar lokaci sallah ya wuce ta . 

Sai da ta d’an kama ruwa tukunna tayo Alwala , ta zama ready , sabida few minute ne to sallah .

Lokaci nayi Tayi sallah ta , azkar , karatun al- qur’ani da kuma addu’ointa da ta saba duk safiya . 

Bata tsaya danna waya ba ta fad’a kan gado sabida bacci da take ji sosai da sosai 



__________

‘Karfe 8:30am ba’kar Mercedes Benz ta tsaya a wani tanfatsetsan gini, shi ba gida ba , shi ba company ba sabida irin girman da yake dashi sosai ga kuma tsayo . Glass d’insa shi zai nuna kamar company while , yanayin tsarin ginin ya nuna kamar gida . 

Wasu zaratan guys ne , a tsakar harabar wajan, kayan su ba’ka’ke, ko wanne da bindiga a jikinsa , bawai irin bingigogin ‘yan sandan mu na nan ba , irin sniper gun ne a jikin su , ba d’aya ba sannan kuma ba biyu ba , suna da hasken fata dukan su duk da rabin face d’in su ne a bud’e , rabi kuma a rufe ga glass da yake face d’in su shima ba’ki . 

Biyu daga cikin guy d’in nan ne , suka nufi Benz d’in da tayi parking . 

‘Daya ya bud’e driver side d’ayan kuma ya tsaya daga bayansa .

Takalminsa ne ya soma sakkowa ‘kasa , shima kuma farin sneaker ne da ba’kin wandonsa suka soma nuna wa , kafin ya fito da ga baki d’aya ainahin jikinsa . 

Rigar jikinsa fara ce ,  ya saka wireless earbuds a kunnansa . Murd’ad’d’an jikinsa yana sake bayyana .

Fuskarsa babu fara’a ko alamar rahama akanta . 

Ga baki d’aya mutanan wajan sai da suka shiga hankalin su, ji sukai ga baki d’aya yanayin wajan ya canza musu , babu wanda ya motsa daga inda yake tun bayan fitowarsa . 

Sai da ya nufi hanyar shiga build’ing d’in nan , guys biyun nan da suka nufi motarsa suka mota suka taka masa baya . 

Uncle Moh kenan , mutum mai matu’kar izza, iko uwa uba wani irin abu da babu wanda ya isa ya fad’a maka a tattare dashi , idan har ba shid’in ne ya fad’a ba , ko na kusa dashi bai isa ya fad’a wane ne shi ba . 

Cikin wajan falo ne sosai , mara tarkace , mara kayan alatu , amma yayi kyau tunda kujerun wajan foreign ne kuma masu tsada . 

Nan d’in ma akwai irin guys d’in waje masu bindigogi da kuma ba’ka’ken kaya . Reaction d’in da mutanan waje suka bayar , haka wad’an nan ma suka bayar da ganin shigowarsa , kuma ko wannan su sai da ya gyara tsayuwarsa. 

‘Daya daga cikin ‘kofar da take falon ya nufa , me kama da glass , yana zuwa ta bud’e kanta da kanta . 
Ya shiga cikin wajan tare da 2 guys d’in da har yanzu basu bar bayansa ba . 

Cikin wajen cike yake da kayan training, bawai irin simple 1 ba wannan manya manya ne dan full gym room ne, babu abun training mai mahimmanci da ba zaka samesa a cikin wajan ba . 

Daga gefe d’aya kuma akwai wani abu mai kama da na boxing d’in nan da ake nuka . 
Nan ya nufa d’aya daga cikin guy d’in nan ya mi’ka masa abu ya saka a hannunsa, sai a lokacin Moh ya d’aga idanuwansa mai ladaftarwa ya kallesa dasu.

“ Kungama aikin da na saka ku?” Yayi maganar a kausashe cikin amon murya me zafi.

“ Mun gama BOSS.” 

“ You can go..” Moh ya kuma basu umarni. 

Babu wanda yayi questioning umarninsa suka juya suka bar wajan, shi kuma ya soma dukan abun nan da yake a sa’kale . 

Duka yake masa ba irin na wasa ba , kamar wanda yazo filin gasan dambe haka yake dukan abun nan , babu ‘ka’k’kautawa. 

Dukan mintina biyar yayi abun ya soma fashewa dan bugĂŒn da yayi wa abun ba na wasa bane , a hankali d’igon jini ya soma d’iga, amma babu alamar zai dena bugun da yake. 

Last d’aga hannu da yayi zai bada wani punch, aka ri’ke masa hannun. 

Yadda ya juyar da idanuwansa yana kallan direction d’in wajan sai ya tsorata mutum, dan ga baki d’aya fuskarsa ta rine sosai da sosai har wani ja kunnansa suke. 

Wani kyakkyawan guy ne ya ri’ke hannun . Kyakkyawa ne amma bai kai Moh ba . Sai dai yana da yana da yawan fara’a akan fuskarsa sabida murmushi yake , yana kallan Moh da fuskarsa take a had’e . 

“ Ka bi a hankali karka kashe sa..”  guy d’in yayi magana har lokacin kuma akwai murmushi akan fuskarsa .

“ Let’s go off
.” Moh yayi maganar a fusge
 

A maimakon ya saki hannun sai ya ‘kara ri’ke wa yana yiwa Moh murmushin nan nasa mai karya zuciya . 

“ Yi hakuri Moh ! Karka kashesa 
 barshi haka 
 kaga ko motsi baya yi.”

“ I said leave me alone
” Moh ya kuma fad’a a d’an kausashe amma har time d’in gayen bai sakesa ba sai murmushi da ya kara yiwa Moh. 

‘Karamun tsaki Moh yaja yana sakin hannunsa , kafin ya juya zuwa bakın window shi kad’an sai faman kuci kawai yake . 

A nan ne guy d’in yazo wajansa , ya saka hannu ya dafa kafad’ansa. 

“Calm down! Calm down nima karka wuce akai na , naga kazo har wuya .” 

Moh yanayi masa wani kallo mutumin yayi dariya “ It’s fine ! Am sorry ! Nima wasa nake amma yanzu ba shine mai mahimmanci ba kasani ko? . 

Abunda yake da mahimmanci ya kamata mu tun kara ba wannan ‘karamun abun ba . Allow the guy to eat him alive 
  kurayenka ma kad’ai zasu cinyesa da ransa. Let’s focus please.”

“ Kasan you’re so annoying right ?” Cewar Moh .

Kansa guy d’in ya d’aga masa alamar yadda kafin ya furta “ Ina tunanin haka..”

Share maganar Moh yayi ta hanyar fad’in “ Yaushe ka dawo?”. 

“ Yau na dawo , ko gida ban shiga ba , na taho nan , naga kana ‘ko’karin yin kisan kai , wayana sai danger kawai yake nuna mun
. Guy you’re so damn unbelievable
”

“ Naji da ka dawowanka ka soma samun ciwan kai , gwanda ma ka wuce gida , kafin ka soma ‘bata mun rai 
” 

“ Haba Guy ! Babu inda zani , kasan ni d’aukan kama nazo yi, nasa ayi mana breakfast a gida 
 idan munje can ma ‘karasa maganar mu
 Kaga ko gida banje ba sabida kai 
.”


“ AL’AMEEN
” Moh ya fad’a yana kallansa.

Shi kuma Al’ameen yayi masa magana kawai da ido . 

Wani iska Moh ya furzar yana jan ‘karamun tsaki , kafin su jera da Moh su fito daga cikin gidan. 

Compound d’in cike da ba’ka’ken mota da alama tare dasu Alameen yake , wata ‘bakar mota da ta fita daban aka bud’e musu , sauran guys zasu biyo su, Moh yayi musu just 1 signal da hannu alamar su dakata , su kuma suka fice , Al’ameen a driver seat , Moh kuma yana seat d’in me zaman banza





âž»
A gida kuma , ‘karfe 11:30am hasken rana ya çıka d’akin Mimi, 
hakan yasa ta bud’e idanuwanta a hankali tana kuma mitsits tsikasu. 

Kallan time tayi kafin lokaci ya ja sosai tayi ‘karamar hamma tana mi’ka kad’an tare da fad’in “ Ya Allah 
.” 

Sannan ta mi’ke ta shiga cikin toilet. 

Wanka tayi sosai sannan ta fito ta soma skin care routine d’inta kamar koda Yaushe . 

Tana cikin saka kaya akai knocking ‘kofa sannan aka bud’e aka shigo.

Zarah ce ri’ke da waya , ganin Mimi a tsaye yasa ta furta “ La gashi ma ta tashi daga baccin.”
Banji me aka ce mata ba sai tace okay ta kashe call d’in sannan yazo wajan Mimi sukai side hug , Zarah tana fad’in “ I missed you my Besty , tun jiya kina raina.”

Ya ku’be jikinta Mimi tayi tana mata hararan wasa “ Ke dai ki fad’amun gaskiya ! Babu wani missing d’ina da kikai kuma ai kinsan d’akina ba sani ne bakiyi ba , da sai kizo mu kwana .”

“Wa ? In na mutu ai kai ni akai , ni kinga ran’kwashin da Yaya Sadiq ya dinga mun dan kawai na d’auki motarshi . Wai motarshi ba ta yara bace imagine , Momy kuma tana goya masa baya . 

Ai gwanda surutun su Ya Saleem akan tsautsayi ya had’a ni da Uncle Moh shiyasa na’ki fitowa ma sai da naji Ya saleem yace ya fita. 

“ Okay ni in mutuwa ne na muku kenan ko?”.

“ Noo ba haka nake nufi ba atleast ke jan wuya ce , kome Uncle Moh yayi miki kina d’auka ni wallahi suma zanyi ya buga mun wannan kallan nasa kamar wacce tayi sata haka zanyi tsamo tsamo. 

Yanzu ya kuka kare da su Mammy? Uncle Moh yayi miki wani abu?”.

“ Babu abunda zan fad’a miki , da labari kike so kiji da tun jiyan zakizo ai ayi akan idanki
 Abeg jare matsa na cigaba da shiryawa .

“Kai dan Allah Mimi, dan Allah fad’a mun..”.

“ Kema dai kinsa Mamy ba za tayi mun komai ba ko? Shi kuma Uncle Moh ko ganinsa banyi ba 
” cewar Mimi.

“ Dagaske kike wai ?”

“Da gaske nake mana , nayi tunanin zai nemeni amma bai ba , yanzu ba zuwa kikai kika ga ina bacci ba ?”.


“ Eh haka ne .”

“ So you see ba ? Babu abunda akai mun fresh na tashi , anjima kuma ki d’auko mana ice cream d’in mu 
.”

“ Thank God ! Wallhi da abun na kwana a raina Mimi har ina cewa dama ban barki ba aushe ke kinanan kina kwasan baccin ki.”

Murmushi dole Mimi ta kwakwalo sabida tuno abincin da Moh ya sa taci , sai kuma tayi saurin Kawai da tunanin dan bata ma san tuna shi dan har yanzu haushinsa take ji . 
Cikin zuciya ta furta “ Mugu kawai .”


“ Ni banbaki labari bama 
” cewar Zarah .

“ Me ya faru?” Itama Mimin ta tanbayeta. 


“ Kinsan wannan ‘kawar Ameerahn anan ta kwana ? Bama wai kwananta ne matsala ba , d’azu Uncle Bashir har Dady sai da ya sama a part d’in mu shi da Momy akan mun fita yawo wai su Ameerah da friend d’inta sunce nice nayi slow driving har wata mota ta soma bin mu, saura kad’an nayi loosing control, mu rasa ran mu .. can you imagine?.”

“ Wai har yake fad’awa Dady ke da kike gaba kina da lack of concentration, kamata yayi tunda agaba kika zauna ever here and there movement d’in motar ya zama akan idanuwan ki. 

Idan kinga fad’an da ya dinga yi mun , ko Dady da Baffa da na had’u dasu d’azu basu yi mun
 

Kinji wani tululun ba’kin ciki da ya cika mun ma’koshi , Allah ya temake ki ma bacci kike a time d’in , nasan da maganganun da zai fad’a ba kad’an bane . 

Daman kuma ba shiri kuke dashi sosai ba .”

“ Hmm Zarah kenan, idan ya fad’i laifin mu , ita kuma wana laifi yace Ameerah tayi ? Ko iya mu kad’ai mukai laifin?”.

“ Haka yace wai su ßuna baya, hankalin su bazai kawo wajan ba , daman alhakin safety d’in su ya kasance a hannun mu tunda mu ke driving . 

Hmmm Mimi manta da labarin Uncle Bashir , ‘kiri ‘kiri ya nuna Baffa da Dady mune masu laifi kuma kinsan Baffa bazai yi magana ba tunda bashi da fad’a gwanda gwanda ma Dady.”

“ Tunda yar sace yar so ba , ai dole ya fad’i haka
”

“ Hmm ke Allah ya taimaka Uncle Moh baya gidan a lokacin. 
Da anyi dramer, tazo muje muci abinci, already na gama girkawa ke nake jira daman zuwa nayi na tashe ki.”

“ Okay Zarah ! Bari mu soma zuwa na gaishe da su Mamy , nasan yanzu Baffa ya fita daga gidan.”

“ Mamy tana tare da Momy a part d’in mu , tunda can zamuje ai zaki had’u da ita.”

“ Aunty Shukura fa ?”.

“ Itama a part d’in mu na barta amma kamar fita za tayi a time d’in. Let’s go .”

Wayanta Mimi ta d’auka suka fito daga part d’in ita da Zarah , suka wuce part d’in su Zarahn. 

Babu kowa a falon su, shiyasa Mimi ta kalleta irin daman wasa kike mun ko?.

Sai Zarah tayi saurin fad’in “ Wallahi anan na barsu may be ko suna kitchen , ko suna upstairs , bari na soma duba kitchen d’in.”

Nan Zarah ta duba kitchen basa nan, sai suka hau sama nan d’in ma babu kowa a falon Momy. 

Sai Zarah ta wuce d’aya daga cikin d’akin da Momy take yawan zama a ciki tayi knocking sau d’aya , sau biyu 
 sai ga kiran wayan Momy ya shigo wayanta . 

Tana d’agawa sai ta furta “ Momy kuna tare da Mamy ne ? Mun shigo bamu gan ku ba , na d’auka kuna sama 
.” Banji me aka ce mata ba sai cewa da tayi “ Tom Momy .” Sannan ta dawo wajan Mimin. 

Aushe suna part d’in ku yanzu , sunce basai munzo ba sabida akwai maganar da suke tattaunawa, and i think it’s important, so kawai let’s chill Baby and enjoy , zuwa anjima sai ki had’u da Mamy , ‘yar Mamynta .” Zarah ta ‘karasa maganar tana murmushi . Ita kuma Mimi ta d’aga hannu cikin rashin damuwa , tana juyar da idanuwanta cikin d’aukar hankali. 

“ Wait amma me su Mamy suke tattaunawa?”.

“ Yaushe kika soma bin diddigi? Maganar su Mamyn kike so kiji yau kuma Mimi?”

“ No ba haka nake nufi ba , am just asking , nothing special , d’auko mana abincin mu , ni kin ganni zan jira ki a bedroom d’inki.” Mimi tayi wucewarta bedroom d’in Zarah , ita kuma Zarah ta wuce kitchen. 

Akan gadon Zarah ta d’an kwanta tana lumshe idanuwanta , at the same time kuma tana sake bud’ewa , kafin ta sauke nunfashi me d’an ’karfi . Sai kuma ta tuna daran jiya da kuma text d’in da akai mata , har yanzu ta rasa wane ne wanda yayi mata message d’in . 

Bata sani ba fa mace ce ko namiji duka bata da idea , daga nan kuma sai ta canza tunaninta zuwa wani tunani daban , bayan ta kawar da wanda take a yanzu, har Zarah ta shigo cikin d’akin. 

Tana ajje tray d’in hannunta Mimi ta furta “ Zarah .”

Kallanta Zarah tayi sannan ta furta “ Uhm?.”

“ Kin ta’ba ganin new number a wayanki? Like yana nemanki or something like that ?.”

Da mamaki Zarah ta kalleta , sani kuma ta furta “ Message kuma ? But why? Ni banga sabuwar number ba , any prob?
”

‘Dan shiru Mimi tayi , sai kuma ta furta “ Nothing , am just asking ..”

Matsowa kusa da ita Zarah tayi tana fad’in “ Kamar ya nothing , haka kawai ba zaki mun tanbaya randomly ba , akwai wani abune? Atleast we’re best friend you can share it with me , abi
.?”

Murmushi Mimi tayi tana fad’in “ Sannu Hajiya best friend ke dai zuciyar ki is bad , daga tanbaya har kin soma negative thinking? Abeg je ki d’auko mana ragowar abincin mu, na soma jin yunwa.”

“ Mimi are you sure ?”.

“ Yeap 
” cewar Mimi. 

Daga nan Zarah bata kuma cewa komai ba ta sake fita daga d’akin. 
Jim kad’an ta dawo da wani tray . 

Daga kan carpet suka ajje tray d’in sannan sukai serving junan su, Ɵuna ci Ɵuna maimaita abunda ya faru jiya which mostly Zarah ce take labarin sabida Mimi hankalinta is not here , yana wani wajan daban.



âž»
MOH POV

A cikin mota, Al’ameen yana driving , while Moh yana danna wayar hannunsa , lokaci zuwa lokaci kuma yana kallan window. 

“ Moh 
.” Shiru bai amsa ba .

“ GUY 
” Al’ameen ya kuma ambata , amma har time d’in Moh bai amsa masa ba. 

‘Dan murmushi Al’ameen yayi sabida hakan bai ‘bata masa rai ba tunda ya san ko wane ne Moh.

“ Tunanin me kake haka , ka share ni kamar bakasan da duniyata ba . Moh ! You’re actually bad .”

Kallo d’aya Moh yayi masa kafin ya furta “ Drive Malam..”

Yanzu kam har da d’an dariya Al’ameen yayi kafin ya furta “ Bakomai yanzu na zama Malam ,  yau ‘yan wula’kancin akai na suke , da nasan haka ne da nayi zamana kawai.”


“ Okay daman wa ka fad’awa zaka dawo hmm? Kawai nasan ka dawo dan ka saka mun ciwan kai 
”

“ Kai ma ka sani , babu mai iyawa da kai sai ni, am here for something if not , hanyata da kai babu had’uwa , you know that now.”

“ Oh really? Fatan zaka ri’ke maganar da kayi yanzu da kyau.”


“ Of course Boss 
” cewar Al’ameen.


“ Okay now let’s be serous , ka samo mun information d’in?”.


“ Yeah na samo , amma wannan karan abun is not easy kamar sauran
.

I bet baka bud’e email d’in ka ba , i send you some information though
 and it’s very important.. wannan karan da kai na yi, sabida banasan asamu matsala. But the guns , and everything yana gida.”


“ Yeah lokaci yayi , da zanyi komai da kai na , shiru na yayi yawa kwana biyu , na kwana biyu ban motsa jiki na ba .”


“ Easy Man
but zanyi dad’in game d’in nan , ko wane ne yake san wasa da wuta zai samu dai dai yadda yake so.” Cewar Al’ameen , lokaci d’aya ya canza daga mutumin me fara’a zuwa wanda bashi da fara’a kwata kwata . 


âž»

To be continued
 đŸ”„


BLACK QUEEN đŸ€đŸż
***