Page 14/15
MISHAL
By BLACK QUEEN đ€đż
***
MAI SAN A TALLATA MASA KAYANSA YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER ***
Book 1
Page 14 / page 15
âKarfe 6:40pm na yamma after Mimi tayi sallahr magrib, ta shirya cikin doguwar riga , mara nauyi irin na zaman gida, sai ta dâaura dâan kwalin kayan akanta, daga waje gashinta ya fito luf luf dashi sabida gyaran da ya sha a saloon.
Bayan lip balm kuma baya Ćaka komai a fuskarta ba , amma kwayar idanuwanta sai ta fito sosai kamar ta saka kwalli, gashi Allah ya bata kyautar su , ko ya ta âkiftasu, sai kaji wani iri a ranka ba daga mazan ba , har matan .
Main falo ta nufa , ganin babu kowa a ciki sai sanyin AC da kuma âkamshin turaran wuta da ya ke tashi ta wuce falon su Mamy.
Knock biyu tayi , ta murdâa handle dâin âkofar, bakinta dâauke da sallama .
â Assalamu AlaikumâŠâ
â Waâalaykumus salamâŠ.â Mamy ta amsa mata daga cikin falon.
Mimi tana shiga ta tarar da Baffa a kishingidâe akan carfet , hannunta dâauke da jarida , Mamy kuma na gefensa tana yanka masa fruit, sai suka bada wani vibe kamar na maâauratan da suke cikin tsananin soyayya .
Mimi tana ganin fuskokin su sai kawai murmushi ya âkwace mata a fuska, Mamy kuma ta gane murmushi mu take shiyasa ta dâan harareta tana fadâin â Idan kin gama kallan namu ai sai ki shigo, in kuma daman ba zuwa wajan mu kikai ba toh maza ki juya yanzu .â
Shagwaâbe fuska Mimi tayi, tana shigowa ciki sosai kafin ta furta â Kai Mamy , abun har da kora ?â.
â Eh na Kore ki dâinâ Mamy ta bata amsa ko kallanta ba tayi ba , sai a lokacin Baffa ya kalleta , da murmushi akan fuskarsa yana nuna mata kusa dashi.
Babu musu Mimi ta zauna a inda ya nuna matan, tana fadâin â Baffa na ina wuni? Ya hutawa kuma, na same ku lafiya ?.â
â Lafiya âKalau Auta na , yanzu nake tanbayar Mamyn ki ban ganki ba , tace itama batasan inda kike , ba ko yau dâin ma kin sake fita ne?â. Baffa yayi maganar fuskarsa cike da annashuwa ganinta .
â Aâa Baffa , lokacin da na fito already baka gidan shiyasa ba mu hadâu ba , kuma banasan kiranka kana office , nasan a time dâin may be kayi busy.â
â Mimi na akwai abunda ya kai ki busy ne ? Sabida wa ake fitan ba sbd ku ba? Saura kadâan ai ki ganni nazo biki a âkofar dâakin ki, ince tunda ke bani samu damar zuwa ba , ni bari nazo naji ko nayi wa âyar tawa laifi..â ya âkarasa maganar tasa cikin zolaya .
Cikin murmushi Mimi ta furta â Haba Baffa , ni na isa kazo biko na ? Ai da Mamy tayi sakwara dani..â hakan yasa daga shi har itan suka soma dariya suna kallan Mamy da ta taâbe musu baki tana cigaba da yanka fruit dâinta kamar batasan suna yi ba .
A tsokane Mimi ta furta â Mamy nima zansha fruit dâin..â
âDan âkaramun harara Mamy ta kai mata na wasa sannan ta furta â Kuma ba zaki sha ba , mijina na kawo wa , ai kinsan inda suke , sai kije ki yanka da kanki , ko kuma kema kiyi zuciya ki saka naki mijin ya yanka miki.â
â Kai Mamy har da gori? Toh na fasa sha, Kisha kayanki , Baffa kaji abunda tace mun ko?â.
â Kyaleta Autana , nima idan ba zaki sha ba , nima ba zan sha ba , dan wannan abun kam in an hanamu sai muje mu siyo namu ko?â.
â Ahhhhh Baffa ! Rufamun asiri âŠâ Mimi ta fadâa tana zaro beautiful eyes dâinta waje , gwanin ban shaâawa , yadda tayi da fuska kamar irin shock dâin nan , sannan ta dâora da â Ai babu ruwana Baffa , idan ba haka ba , ai kana fita zan hadâu da MamyâŠâ
â Ke wai me ya kawo ki ma nan ? Kinzo sai cika mu da surutu kike.â Cewar Mamy.
â Mamy wajan ku fa nazo , ku nazo dubawa mana , daman kuma ban hadâu da Baffa ba , kwata kwata yau.â
âToh ai yanzu kin ganshi har kun gaisa , ki wuce dâakin ki, after sallar ishaâi yau zaâai dinner duka a babban falon Baffa , saura kuma ki makara .
Duk wani âbata lokaci da kikasan zakiyi, toh ki yishi tun yanzu kafin time , bana san jin , ko ganin kece kawai babu a wajan , zamu âbata sosai .â
âDan shiru Mimi tayi, dan sam ita batasan wannan dinner da zaâa ce kowa yazo , dan tasan one thing lead to another zaâa soma zance.
Jin tayi shiru Baffa ya kalleta cikin kulawa â Autana tunanin me kike haka? Ko wajan ne baki san zuwa?â
Tun kafin tayi magana Mamy ta kalleta da ido , shiyasa ta girgizawa Baffan kanta , sannan ta bashi amsa da âba komai Baffa, Allah ya kai mu time dâin.â
Baffa ne kawai ya amsa da Amin amma but Mamy da Mimin babu wanda ya amsa.
Sai da ta âkara kusan mintuna 15 tukunna tayi musu sallama ta fito daga sashin nasu zuwa main falo, shima kuma bawai zama tayi ba, kitchen ta shiga ganin an kusa kallama komai sai kawai ta wuce dâakinta , tana tafiya tana danna waya.
Ko da ta shiga ma hankalinta yana kan wayar da take dannawa, sai hannun hagu kawai da ta saka tana rufo âkofar.
Tana cikin tafiya zata zauna taji gyaran murya a bayanta, cikin sauri ta dâago kanta saitin inda ta jiyo gyaran muryar.
Joy ce tsaye a waja , ta hadâa hannayenta biyu a âkirji tana kallan Mimi .
â JOYâŠâ Mimi ta fadâa cikin excitement, tana matsowa kusa da ita amma kuma reaction dâin Joy bai canza ba , har a lokacin tana kallan Mimi ne .
â Kin tsorata ne , ban tsammaci ganin ki yanzu ba .â
â Ai dole na tsorata ki Mimi yadda kika sun kuyar da kanki âkasa kina danna waya , ya zaâai kisan cewa ina wajan?â.
â Okay toh kiyi hakuri Joy ! Amma nayi kewarki sosai faâŠâ
â Nima nayi kewarki, Babyn MohâŠâ
âDan turo baki Mimi tayi kadâan kafin ta furta â Ki rasa wa zaki hadâa ni dashi sai Uncle Moh, kinsan muguntar da yayi mun kuwa , wannan mugunâŠ?â
â Kull kull Mimi ! A wannan duniyar ko zaki kira kowa da Mugu to banda Muhammad,sabida ta dalilin sa kika zo duniya , idan da ace baya nan , da wani zancan ake yanzu , da kuma babu Mimi yanzu, da kuma ba zaki taâba samun kwanciyar hankalin da kike ciki a yanzu ba.â
Dan kallanta Mimi tayi cikin rashin fahimta ta furta â Bayan ga iyaye na ? Taya ya zama siyar zuwa na duniya ? Ni fa wani lokaci baya gane miki joy idan naji kina magana a juye , kuma musamman a kan Uncle Moh , ko dai sanshi kike?â.
â idan ina sanshi zaki haâkura ki bani shi ne ?â Cewar Joy tana dariya âŠ
â Kamar ya ?â Mimi ta tanbaya in a confuse way âŠ.
â Nasan Baffa da Mamy iyayen ki ne , amma shima Moh dâin yana da matuâkar mahimmanci a rayuwarki , da dole shine bangon ki kafin ki soma tun karar kowaâŠ
Sannan ki guji âboyewa Moh abu, dan duk abunda mike kallan ki kawai yake dan a tafin hannunsa kike kamar wainar da ake juyawa, haka zai juyaki idan yasoâŠ
Sai dai kashhhhh yarinya ce ke har yanzu , har yanzu akwai abubuwan da lokacin sanin su baiyi ba , amma tabbas lokacin zai zo ko ba dadâe ko bajima .â
âToh Joy tun da kin sani ai sai ki fadâa mun, ba sai najira lokaci ba âŠâcewar Mimi.
Matsowa kusa da ita Joy tayi , ta dâan shafa kanta tana kallanta cikin kulawa â Kiyi hakuri Mimi , wannan ba hurumi na bane , ki bari idan lokacin dacewar sanin komai yayi zaki sani.
Sannan abunda ya kawo ni yanzu, kada ki kuskura ki cigaba da tsawaita bincike akan saâkon da ake turo miki ,ko hoto, ki barshi a yadda kika gani ko da ace baki sanarwa Moh ba , toh karkiyi kasadar wasa da rayuwar ki .
Yarinya ce ke , baki kai lokacin wannan ba , kuma ki dakatar da Zarah da ka kan ko wana bincike da tace zata taimaka miki.
Idan ba haka ba amaimakon gyara da binciken da kuke san yi? Toh komai zai lallaceâŠâ
â Joy kenan kinsan da message din?â
Karamar dariya Joy tayi kafin ta furta â na sani , ba ma ni kadâai ba Moh ya sani shima , bayan shi kuma akwai wanda ya sani dake dâin baki san ya sani ba amma shi kuma Moh yasani , shiyasa nace karki gaggawa akan komai da ya shafe kiâŠâ
Mimi za tai magana akai knocking a bakin âkofar .
Kafin ta bada izinin zuwa already Joy ta âbace ma .
Bataso zuwan ko wane ne a wannan time dâin ba sabida tana âbukatar amsa daga wajan Joy , amma kuma babu yadda ta iya .
â Come inâŠâ ta fadâa da dâan âkarfi kadâan .
Turo âkofar dâakin akai Aunty Shukura ce .
Mimi tana ganinta , tayi saurin rugumarta tana dâan dariya âkasa âkasa â Aunty Shukura yau ina kika shiga gabaki dâaya ban ganki ba fa .â
âDama ya zaâai ki ganni Mimi kullum ina dâaki , kina bacci baki da wani aikin yi sai bacci kinga kuwa ai dole ba zamu hadâu ba.
Yanzu ma Mamy ce ta aikoni , tace kina idar da sallah ki fito kar a zauna zaâaci abinci ace kece baki fito ba , zaku âbata.â
â Kai yanzu Mamy sai da ta aiko ki? Nima ta fadâa mun fa .â
â Ai tasan halin kayanta shiyasa ma ta fadâa itâs better yanzu kiyi abunda zakiyi, in zakiyi sallah , ki yi , idan kuma youâre off to maza ki wuce part dâin BaffaâŠ. Kinga ni tafiya taâŠâ
â Aunty Shukura ke ina zakije yanzu?â.
Fari Shukura tayi mata , kafin ta furta â YawoâŠ.â Tana barin wajanâŠ.
Cikin girgiza kai Mimi ta wuce toilet, bata ma wani dadâe ba , ta fito da alwala, saura few minutes to prayer , wayanta ta dâauka tana danne danne , kafin time dâin ya âkarasa.
Lokaci nayi tayi sallarta , ta kuma canza rigar jikinta zuwa more decent one itama kuma rigar ce amma tana da kauri, ta dâaura mayafin akanta , ta dâauko wayanta zuwa part dâin BaffaâŠ..
_____ Lokacin da ta shiga part dâin Baffa , kusan matan gidan duk suna nan , mazan ne kawai basa ciki .
Mamy da Momy da kuma Mama ( Maman Ameerah ) suna gaban babban dinning , da wasu maid kuma da ake directing dâin su akan yanayin tsarin dinning dâin..
Omo money na waterâŠ.. bang bang bangâŠ. ( đđ )
Wani massive dinning ne , ga dishes kala kala daban daban, ga fruits , ga juice komai zam zam, an tsara , ga aroma yana tashi ta ko wana lungu , âkamshin turare , âkamshin abinci, ga Ac⊠bang bang money na waterrrrrrrrrrrrâŠâŠ.
Cikin falo kuma Aunty Shukura , Aunty Baby , Aunty feedy , Zarah , Ameerah duka suna ciki suna shan hira abin su .
Shigowar Mimi ne yasa Zarah ta dâago mata hannu tana nuna mata side dâin da take .
Sai da ta soma zuwa tayi hugging dâin su Aunty Feedy , har da kuma Ameerah irin side hug dâin nan kafin ta zauna a kusa da Zarah.
Babu shiru kuma Zarah ta radâa mata a kunne â Any news ?â
Kanta Mimi ta girgiza mata alamar aâa , bata so kuma Zarah ta sake magana akai , kar wani abun ya fito fili shiyasa ta dâauke fuskanta zuwa hirar da su Aunty Feedy suke ganin sun sako ta a ciki .
Daga nan wani bang bang dâin hirar ya tashi a tsakanin ladies dâin, suna tsakiya da enjoying hirarsu su Uncle Saleem sukayi sallama .
Uncle Saleem , Uncle Abba ,da kuma Yaya Sadiq Ćuna gaba, bayan su kuma Baffa , Daddy da kuma Baba( Uncle Bashir kenan Baban Ameerah ) .
Sai da suka shigo falo sosai , Saleem ya dâan kashema Mimi ido , cikin tsokana ya furta â Tun daga waje nake tajin murya na tashi aushe muryar Mimi ne ya karadâe mana gida..â
â Uncle Saleem kai dai kaso kanka ne wallahi , kowa yana magana amma muryata kawai kaji ⊠Haba pity me mana âŠâ bata bashi damar yin magana ba ta kalli su Baffa da suka zauna akan kujera.
Baffanta ta soma gaisawar ya amsa mata cikin kulawa , sannan ta gaishe da Daddy shima dai kamar Zarah yake faran faran abunda kuma suna kama da Baffa sosai, dan sai da ya dâan tsokane ta kowa yayi dariya kafin ta gaishe da Uncle Bashir .
Shi kuma babu yabo babu fallasa ya amsa mata gaisuwa kuma ciki ciki.
Mimi bata damu ba tunda already ta saba da irin wannan amsar tasa .
Su Uncle Abba ma duka sai da ta gaishe su , anan ta lura da bayan cikin falon . Kuma ba saban abu bane , yawanci baya zuwa wannan family dâinner dâin , dan baya dawowa ma gıda a time dâin.
Tunda ya rakota part dâin su bata sake ganinsa ba . â Uncle Hope youâre fineâŠ?â Ta raya a cikin zuciyarta⊠ganin tana âkoâkarin fadâawa dogon tunani tayi saurin kawar da tunanin.
Mamy ce ta âkaraso cikin falon sabida komai ya kammala , kuma daman abunda tazo sanar dasu kenan .
Ga baki dâaya aka wuce dinning .
Su Aunty Feedy ne sukai serving abincin kowa .
âKaâida ne kuma idan suna cin abinci ga baki dâaya a lokaci dâaya basa hira ko magana har sai sun kammala .
Hakan ne ya kasan ce a yanzu , dan babu wanda yayi magana , sai âkarar cokula da aroma dâin abinci ne kawai yake tashi.
Suna gama ci , maid suka kwashe komai suka gyara su kuma all family members suka koma falo ana hira .
Su Baffa suna hira da su Daddy , su Mamy ma suna hira da su Momy, Aunty feedy da Aunty baby da kuma Aunty Shukura suma hira a tsakanin su .
Su Uncle Abba ma haka , sai Mimi , Zarah da kuma Ameerah da suke hira , duk da ma âkarfin hirar Zarah ce dan duk ta fisu magana a cikin su.
Ana haka ne , Ameerah ta dâan ja tsaki akan wata magana da Zarah tayi har tana cewa â Ke dadâi na dake wani lokaci Zarah kamar baki waye ba , we are in Gen- Z generation now .â
â Sannu wayayya âŠ.â Cewar Mimi tana dâan kashe mata ido guda dâaya .
â Ai bakiyi âkarya ba , sabida babu wanda zai ganni yace mun ba wayya ba , Alhamdulillah shiyasa samari sai zubowa suke kamar ruwa.â
â Ameerah wai for just single day , ba zaki iya zama baki maganar saurayi ba ? Saurayi this , saurayi that, wa yake da interest akan jin samarinki my girl?â. Cewar MimiâŠ
â Are you jealous?â Shine abunda Ameerah ta soma cewa Mimi.
â Jealous kyyyyyâŠâŠ for that matter akan boyfriend! Jealous not for me âŠ.â Itama Mimi ta bata amsa .
â Ke dai ki fadâi gaskiya , not for once ban taâba ji wani ya kira ki ba , kinga akwai probability dâin jealousy a wajan ki , sai dai kawai in zaki âboye , idan kin rasa kuma I can introduce one for you âŠâ inji Ameerah .
Yanzu kallanta Mimi tayi cikin serousness , kafin tayi âkaramun murmushi â Idan zaki kawo wadâan nan shirmen maganar nayi , kisan a inda zakiyi su , banaso na matsa wajan da ni dake duka ba zamu ji dadâi ba , letâs respect each others decisionâŠâ
â OppssssâŠâ cewar Ameerah za ta cigaba Zarah ta furta â Dallah ya isheki haka kuma Ameerah , komai samari , dan Allah ki karkato duka ka su ayi muku aure sai mu yadda da soyayyar da kuke naga for once babu wanda yazo gaisuwa har a san dashi a gida , Abeg âŠ. Hira muke yanzu ba hirar samari ba .â
â Daman Zarah ai ke bazaki taâba ramun kanki ba sai na wani , na tabbata da Mimi ce tayi maganar samarin da you will give your all a cikin maganar, but because sheâs against it , shiyasa kema kikai magana,,whatever kuma babu wanda zai hanani fadâan abunda nayi niyar fadâa , I have my own mouth so , I will talk the way , I want and no body can stop me âŠ.â
â Yeah mun sani , sai kiyi âkoâkarin kiyi adding more sensed cikin maganar kiâŠ. Mtsww .â Mimi tayi maganar tana miâkewa tsaye , shiyasa bata fiyasan muâamala da Ameerah , sabida a duk lokacin da suka zauna , 1 way to another zamu samu matsala kuma babu me hakurin yin shiru a cikin su , ita Ameerah ta iya yaâbawa mutum magana duk yadda tazo mata which ita kuma Mimi mata dâaukar wannan abun.
â Ina zuwa Mimi?â Suka tsinkayi muryar Dadyn Zarah , hakan yasa kowa na cikin falon ya kalleta .
â Dady dama zanje dâaki na ne .â Ta bashi amsa tana kauce kallanta da irin kallan da Mamy take jefa mata na irin zaki sani dâin nan .
â Yanzu kuma daka gama cin abinci? Ko mune bakyasan yira damu.â
âAa Dady ba dadâewa zanyi ba , yanzu zan dawo .â
â Okay su Zarah su raka ki mana .â Shima ya bata amsa da full murmushi akan fuskarta .
Kallansu Zarah tayi, babu shiri Zarah ta miâke , sai kuma ta kalli Ameerah da take danna waya kamar batasan me aka ce ba .
Basu âkara bi ta kanta ba suka wucewar su.
Sai da suka shiga part dâin su Mimi! Tukunna Zarah ta kyalkyale da dariya tana kallan Mimi.
âDariyar me kike kuma , kika tasani a gaba kina dariya ?â
â Dole ai nayi dariya Mimi, kina gudun ayi miki fadâa sai kikai saurin cewa zaki dawo , toh wallahi kiyi kiyi , kiyi abunda zakiyi , kafin Mamy tazo , kınsan idan tazo ba zaki ji da dadâi ba tunda kullum cikin dâaukar excuse kike duk lokacin da zaâa hadâu sai kinsan yadda zakiyi ki zama daga cikin kowa , yan gidan har sun soma shafa miki lafiya suna kyale ki.â
â Mtsee Ameerah ce ta bani haushi, banasan na zauna ina biye mata magana su Baffa suna zaune a wajan, dan wani maganar idan ta yaâbomun bana tunanin barinta haka nan shiyasa naso dawowa na dâaki , amma yanzu tunda nacewa Dady zan dawo ai dole na dawo kafin raina yaâbaci a hannun Mamy.â
â Yes amma bari mu gama maganar mu sai mu koma , any improvement akan binciken mu?â.
â Kiyi shiru Zarah , baâanan ya kamata muyi maganar ba , muje dâaki na ..â
âokayâ Zarah tace mata suka wuce bedroom dâin Mimi.
Suna shiga Zarah tayi saurin kullo âkofar sabida sheâs more eager to hear abunda Mimin zata ce mata .
Ganin rashin natsuwa fuskarta da saurin da take , har saida Mimi ta tsargu ta furta â Calm down mana saurin me kike haka Zarah.â
â Hmm ba zaki gane bane so nake mu gama abun nan , hankali kwance , kar wani abu ya faru sabida wannan ai baâabun yin shiru bane .
Indai bamu gano me tura message dâin nan ba , da kuma dalilin dayasa yake turowa hankalina bazai kwanta ba .â
â Hmmmmmâ Mimi ta sauke wani gajeriyar numfashiâŠkafin ta soma bincike .
âBanyi binciken komai ba Zarah , and wani zuciyar yana ce mun kawai na bar zancen nan, i donât want any issue in yaso ko wane ne yake turo message dâin Inya ga dama ya nuna kansa, idan bai ga dama ba kuma yayi ta zama anonymous, I donât care âŠ.â
â no ! I wonât support you in this gaskiya Mimi , magana ake akan rayuwarki , babu wanda zaki fadâawa wannan maganar ya zauna haka, is better idan mu ba zamuyi ba , mu fadâawa either Baffa ko kuma Uncle Moh.â
â Hmm Zarah kinsan indai muka fadâawa Baffa wannan maganar ba âkaramun shiga damuwa zai yi ba , and Uncle Moh zafinsa yayi yawa, kar muje mu yanke hukunci nan take , kuma alhalin akwai misunderstanding , danni har yanzu ina dâaukar abun nan ne kamar prank , ban wai yadda dashi ba 100 percent , because hotan da aka turo na ido na ne , kuma flower dâin da yake cikin picture dâin shima nawa ne. , wannan is likely like prank wallahi Zarah.â
â Nidai I donât believed wannan prank ne Mimi ! Donât âŠâ
â Beside ! I have to think about maganar da Joy tayi mun, kar nayi rushing âŠâ
â Wace ce kuma Joy?â Zarah tayi maganar in disbelief .
Sai yanzu Mimi ma ta gane ta ambaci Joy dâin shiyasa ta waske maganar ta â Manta da ita , zamuyi maganarta wani time dâin.â
â See you simple question ne kawai sabida nasan all friends dinki and I donât know wata joy shiyasa na tanbaya .â
â Joy friend dita ce Zarah , amma baki santa ba .â
â So you have a best friend a gefe da ban sani ba me suna Joy?.â
â Wai mene ne haka kike canza maganar Zarah ? Nace ki bari wani time dâin zamuyi maganaâŠâ
â Okay Tom shikenan ya kamata mu koma yanzu , kar Mamy taji mu shiru but you have to think akan maganar da nayi miki yanzuâŠâ
â Fine ! I will âŠ.â Mimi ta bata amsa daga haka suka bar maganar suka wuce part dâin Baffa again.
Shima shiga kowa na cikin falon ya sake kallansu, wannan karan kuma har da Ameerah .
â Kun dadâe me kuka tsaya yi?â Cewar Uncle Saleem , amma shima cikin wasa yayi musu tanbayar .
â Uncle Saleem duka mintunan mu nawa ? Ko dai kayi balaâin missing dâin mu shiyasa kaga lokaci baya sauri ?â. Cewar Zarah .
â Abeg commot for here âŠ.â Shima Uncle Saleem ya bata amsa yana kallan Uncle Abba da yake masa magana.
âHuhmmg hugbnmâ ABBA ( Baban Ameerah ) yayi gyaran murya hakan yasa kallo ya dawo wajansa ga baki dâaya .
Sai da ya dâan gyara zamansa, kafin ya kalli Ameerah da take dâan nesa kadâan dashi .
â Ke Ameerah.â Ya ambaci sunanta cikin iko da isa .
Cikin sauri ta furta â Naâam Baba?.â
â Me yasa kullum idan kika zauna da Mimi sai kunyj rikici a tsakanin ku , ba kamar idan sun zauna da Zarah ba ?â
âBABA itace batasan muâamala dani, naga kamar tafisan muâalama da Zarah .â
Da sauri Zarah ta furta â Kai Ameerah bakiji dadâin haâŠ.â Bata âkarasa ba Uncle Bashir ya furta â Yi mun shiru Zarah kinsan banasan wargi ki bari ita da na tanbaya ta bani amsa , kafin nazo kanki nonsenseâŠâ
Lokaci dâaya Zarah tani âkwalla ya tarar mata a cikin idanuwanta shiyasa ta dâaga ido ta kalli Dadynta shi kuma ya girgiza mata kai alamar kar tayi kuka .
Daga Dadyn har Baffan kallan Uncle Bashir kawai suke amma babu wanda yayi magana a cikin su , sai dai kana kallan Baffa kasan ransa ya soma âbacı bai nuna bane kawai .
Kara kallan Ameerah, Uncle Bashir yayi , yana jiran amsar da zata bayar.
â Baba itace bansan me take so ba , bazanyi magana guda dâaya ba sai ta soke ni , ta mayar mun da martani shiyasa bama ta zuwa part dâin mu ko muâamala dani , Indai ba wai zama ne ya hadâa mu ga baki dâaya ba .â
Uncle Bashir sai faman girgiza kai yake , Ameerah tana kai âkarshen maganarta ya furta â this is very unfortunate a gidan nan ace hakan yana faruwa a tsakanin yara .â
Ya kalli Mimi ya furta â this is very unfortunate, ace hakan yana faruwa Mimi, very unfortunate.â
âBaba maganar Ameerah fa ba gaskiya bane , itaceâŠâ
âYouâre very stupid Mimi, yanzu ina magana kina âkoâkarin mayar mun da magana baya, saâan kine ni?nace saâan kine ni?â.
Mimi ta budâe baki za tayi magana Uncle Saleem kawai yayi excusing kansa sabida maganar Uncle Bashir dâin ma haushi ta bashi ga baki dâaya, shima sadiq da Abba barin falon sukai, dan duk Wanda ya âkara zama a cikin falon haka Uncle Bashir zai sake âkunsa musu wani baâkin cikin.
Mamy kuwa yi tayi kamar bata cikin falon harkar gabanta kawai take da su Momy , dan babu wanda bai san halinsa ba akan mita da âkorafi idan ya zauna a waje.
Lokaci dâaya falon yayi shiru ga baki dâaya bayan Uncle Bashir ya gama mitar tasa .
Mimi kuwa tana zaune ne , amma
Ji take sabida haushi kamar ana tsikarar zuciyarta ne , ga baki dâaya haushin Ameerah da na Uncle Bashir ne kawai yake mata yawo a cikin zuciya .
Ga kalmar da ya fadâa mata tayi mata ciwo sosai wai â youâre very stupid .â Kalmar da tun da take Baffa da Mamy basu taâba ambatanta dashi ba , gwanda Moh yana ambata amma bata taâbajin zafi ba idan ya fadâa kamar yadda taji na Uncle Bashir , kuma a gaban kowa da kowa yayi mata tsawa .
Zarah ma tana nan a inda take a zaune , tunda ta goge hawayan idanuwanta, take hararar Ameerah kamar yadda itama Ameerah take hararar nata.
Ganin falon yayi shiru sosai Dady ya sauke numfashi, sannan ya kalli Uncle Bashir .
â Bashir âŠ.â
Sai dai kafin ya âkarasa , Bashir yayi saurin rigashi â Dan Allah Dady karka soma wani magana akan yaran nan , nazo nan ne a matsayin uba .
If i cannot correct what i see , then what exactly am I doing here ?
Yaran yanzu ga baki dâaya so suke ku canza alaâkar tarbiyar da mukai musu, idan bamu zauna tsayin daka ba , daga âkarshe mune zamu zo muna tauna ya tsa .
Shiyasa Ice tun yana âkarami ake tanâkwara shi, idan ya girma bazai tanâkwaru ba , sai dai ya âballe âŠâ
â Ka gama Bashir?â Shine abunda Baffa ya fadâa a wannan karan da tun dâazu bai ce komai ba .
Shiru Uncle Bashir yayi ba tare da yace komai ba hakan yasa ya kalli ga baki dâaya mutanan falon ya furta â Na sallame ku ga baki dâaya yaran, amma banda iyayen su suzauna.â
Da haka kowa kuwa ya miâke ya fito , daga Zarah har Mimi babu wanda ya kalli Ameerah balantana ma su nuna da zamanta a wajan, sai ma da suka kusa zuwa part dâin su Zarah ne , Mimi tayi mata good night da side hug , ita ta wuce part dâin su itama kuma Mimi ta wuce nasu.
A falo kuwa bayan kowa ya fita Baffa ya mayar da kallansa akan Uncle Bashir da yake faman cika yana batsewa shi kadâai .
â Bashir correction ba matsala bane , idan har zaka zaunar da yara kayi musu duk lokacin da sukayi kuskure , mahaifi ne kai a wajan su , amma ba dai dai bane , baka zauna ka nutsu kaji maganar both side ba ka yanke hukunci ko kuma kace lalle sai anbi abunda kace , sammm zamu zauna layi dâaya akan wannan abun ba.
Idan yara sunyi laifi ka zauna ka fahimce su , kaji abunda ko wana side zai zo ya fadâa bawai karan kanka ka yanke hukunci ba , kar yaran nan suga kana yanke hukuncin san ranka , har hakan yasa girman da suke baka ya fadâi , sabida yadda kake tsawatar musu, fadâa kuma baya gyara yaro kai ma kasan da wannan.â
Girgiza kai Uncle Bashir yayi , yana sakin wani murmushin âbacin rai kafin ya furta â Yanzu abunda nayi shine ba dai dai ba Yaya , aushe akwai ranar da zaka mun iyaka akan âyar ka , dan nasan sabida Mimi ne kawai ka saka bakinka a wannan maganar , sau nawa ina musu fadâa sai a wannan karan da zaka kareta .
Ga baki dâaya yaya kunbi kun sangarta ya rinya bata ganin kowa da mutumci, iskancinta kawai take san ranta kuma baku cewa komai , ni ai bazan zauna yaro yayi mun wannan iskancin ba banci ubansa ba .
Ga baki dâaya kan yarinyar nan rawa yake sosai kamar wacce maza suka budâe wa idanuâŠâ
â Aâah dakata bashir , kul karka kuma dan ganta âyata da bin maza , abubuwan da kake kuma ya soma isa haka , kana shigar mun hanci da yawa .â Cewar Mamy da ta zuciya , Baffa zai dakatar da ita , tayi saurin fadâin â Banni Baffa , bazan zauna yana âkoâkarin ciwa âyata mutumci ba a gaban idanuwana , tunda aka zauna bai aibanta âyarsa ba , dan haka babu wani dalili da zai zauna ya aibanta mun tawa yar , zai yarda da komai amma banda âkazafiâŠâ daga nan ta zaune wani nunfashin âbacin rai , tana kallan Bashir kamar yadda yake kallanta .
Murmushi me sanyi Baffa ya sani yana kallan bashir â Kaga irin abunda naka maka gudu ko? Ya kamata ka dinga zurfafa tunaninka kafin ka yanke wukunci..â
â A gaskiya Yaya ni banga wani aibu akan maganar da Baban Ameerah yayi ba . Yara idan baâa koya musu tarbiya âkoâkari zasuyi su âbaci , dole sai ana binsu da tsauri tsauri tukunna , amma gaskiya banji dadâin yadda Mamy tayiwa Abban Ameerah magana sabida na tabbata ba zata kalleka ta fadâa maka haka ba , a gafarce niâŠâ Maman Zarah ce tayi magana , kallanta kawai Mamy tayi , kamar za tayi magana sai kawai ta share maganar ba tare da ta ce komai ba . Momy , Dady da Baffa duka murmushi kawai sukai jin abunda Maman Ameerah tace , da mamakin yadda tabi bayan mijinta kuma âkarara .
A haka aka cigaba da muhawara , Baffa har sai da yaga maganar tana âkoâkarin zama babban abu , tukunna ya dâanyi gyaran murya yana kallan su ga baki dâaya .
â Ina tunanin tattaunawar ya isa haka , tunda dare yayi kowa ya kamata ya koma ya huta yadda ya kamataâ Sai ya kalli Dadyn Zarah â Dadyn Zarah , kai kam akwai tattaunawar mu ta dâazu da bamu âkarasa ba , sai ka dâanyi haâkuri ka jira munga , Momy Zarah fatan babu matsala hakan!â.
âDan dariya Momy tayi tana kallansu kafin ta furta â Ko nace ai da matsalan ma yanzu Dadyn Zarah zai bani kunya , ku ai baâa shiga tsakanin, Allah ya tashe mu lafiya ga baki dâaya .â
Ta miâke tsaye itama Mamy ta miâke tana kallanta â Bari na taho mu âkarasa Mommy , dan nima wucewa ta zanyi.â
â Allah ya taimaki gimbiya âŠ..â cewar Baffa , cikin tsokana , hakan yasa duk sukai dariya banda Maman Ameerah da kuma Uncle Bashir da yake a zaune kamar wanda aka dasa.
Kallanta Mamy tayi ba yabo ba fallasa ta furta â Maman Ameerah, Allah ya tashe mu lafiya .â
Da âkyar Maman Ameerah ta iya budâe bakinta ta furta â Toh Allah ya tashe mu lafiya .â
Daga nan Momy da Mamy basu sake bi ta kanta ba suka fito daga falon , hakan yasa itama sim sim ta wuce na ta part dâin.
Daddy da Baffa kuwa hirar su suka cigaba da yi , Uncle Bashir kuma yana zaune , fuskarsa babu wani murmushi , hannayensa dâaya akan armrest dâinsa , dâaya hannun kuma yana danna wayarsa lokaci zuwa lokaci .
Baice musu komai ba kuma bai shiga cikin hirar da suke ba , na tsawan lokaci, har sai da ya dâaga ido ya kalli Baffa , tukunna ya furta â Yaya , ni zan wuce âŠâ
âDan dâaga masa kai Baffa yayi â Toh Allah ya kiyaye hanyaâŠâ
Uncle bashir kuwa ya furta â Amin .â Yana miâkewa tsaye .
Da wayarsa da kuma key dâinsa da suke gefen kujera ya tattara yayi hanyar fita ba tare da ya kalli Baffa ko Dady ba .
âž»
âKarfe 12:30am na dare âŠ..
Daga cikin garden dâin, Uncle Bashir ne yake faman safa da marwa da waya a hannunsa yana faman lallatsata, shi kadâai sai faman zufa yake , da alama ko ma mene ne ya saka shi wannan zufar to yana da matuâkar alaâka da abunda yake yi a cikin wayar nasa .
Ya shafe sama da kusan hour dâay yana abu dâaya , ganin sauro ya soma jin ubansa ya wuce part dâinsa .
Sai da ya shiga falon, lokacin babu kowa a ciki, ya soma kwalla kiran â Salma ! Salma kina ina ne ?â. Magana kawai yake cikin ciccin magani , ko laâakari da dare ne bayayi, magana yake yi muryarsa a budâe .
Maman Ameerah da take cikin kitchen da sauri ta fito tana kallansa â Sannu da zuwa ai bansa ka shigo ba .â
â Ya zaâai kisan na shigo Salma , kina can kina shiririta , nace miki kuma kafin na dawo ki hadâa mun abinci da kuma shayi , wanne kikai a ciki ?â.
â Baban Ameerah abincin ya kusa kammala luwaâŠâ
â Haka kika iya salma , ni banga wani anfaninki a cikin gidan nan ba kullum sai dai kici kiyi kashi , bur bur amma abinci minti nawane kin gama ko ni nashiga kitchen ya ci ace na gama abunda nake yi , amma ke na lura duk san jiki ne yake dâawainiya dake, shiyasa duk naman jikinki ya fito sosai , babu wani shape dâin arziâki.â
Ăak Maman Ameerah ta tsaya , âyan kallan seconds ta bishi dashi, kafin ta sauke idanuwanta âkasa.
Ta saba , ta riga da ta saba da kalamansa tun ba yanzu ba .
Ta saba da yadda zai shigo gida haka kawai ya soma mita babu abunda akai masa musamman idan an âbata masa rai daga wani wajan.
Ta riga da ta saba duk da wannan halayen nashi .
Ta saba da duk abunda za tayi a matsayinta na âya mace bazai taâba birgesa ba , idan kuma kayi dan kanka ya kwaleka ko a gaban wane ne .
A sanyaye Maman Ameerah ta furta â Baban Ameerah wallahi tun kafin ka shigo nake kitchen, saura kadâan abincin ya nuna kayi hakuriâŠâ
â Tafi can, babu abunda kika iya sai dadâin baki , a kalli abunda dâazu ya faru , ni bar Yaya zai nuna wa san âyaya, matarsa kuma tana budâe baki tana âkoâkarin kare yarta , kanat tafi kowa san yarinyar , yarinya ido kamar na fatalwowi, amma har ni zaâa yi âkoâkarin ciwa mutunci , ke kuma ki shiga ki fita kamar yadda sukai suka kare mijin su kin kasa, kin wani zauna jagwab , kamar alala babu wani anfanin kirki da kika tsinana..
Yanzu kuma kin budâe baki zaki mun bayani, bayanin me zakiyi tunda bakiyi abunda na saki ba , kin soma yin nama kina ganin kamar kafadâata da taki iri dâaya ce ko? Wallahi Salma kina wasa dani ne , kina wasa dani kin manta banene Bashari ko? Toh ki cigaba zan cigaba da zuba miki ido kafin na dâauki mummunan mataki akanki.â
â Kayi hakuriâŠâshine abunda Maman Ameerah ta iya cewa shi kuma ko ajikinsa ya taâbe bakinsa, yana mata alama da ta tafi, kafin cikin umarni ya furta â Kiyi kiyi ki kawo mun abunda na saki banasan jira ko âbata lokaciâŠâ
â Tohâ kawai tace masa , jiki na rawa ta kuma komawa kitchen , shi kuma ya mayar da hankali kan wayarsa .
_________
âKarfe 3:07am na dareâŠ..
Gidan gaba dâaya ya yi shiru .
Babu motsin mutane, babu hayaniya , sai sanyin Ac da yake tashi a hankali cikin dâakunan gidan.
Fitilun corridors dâin a kunne suke sai dai haske me duhu ne da bazai takurawa duk wanda yaci karo da hasken ba a wannan lokacin.
A hankali cikin takun izza da iko Moh ya fito daga part dâinsa .
Yana sanye da shirt me launin dark grey sai wando black colour , hannunsa dâaya a cikin aljihun wandon sa dâayan kuma a waje .
Fuskarsa bata nuna komai , dan duk wanda ya kallesa babu abunda zai iya karanta daga yanayinsa .
Yananan so steady , kirar sama da âkasa da kuma sharp eyes dâinsa da suka fito .
Ya Allah ko baiyi magana ba , kyau yake .
A corridor dâin part dâin Mamy ya tsaya , sannan ya kalli agogon hannunsa â 3:08am.â
Ya dâan lumshe idanuwansa, ya dâaga kansa kadâan kallan wasu corridor na âyan seconni.
Kafin ya budâe âkofar part dâin , ba tare da wani babban sauti ba .
Bai tsaya a babban falo ba ya wuce , sama inda zai sadashi da dâakinta.
Yana zuma ko knocking baiyi ba ya murdâa handle dâin âkofar , ya budâe ta cikin rashin fito da sauti.
âDakin babu haske sai Dummy light , dan âkananan hasken bedside lamp ne kawai a cikin dâakin.
Ita kuma tana kwance akan gado, ta wani cukwikwiye bedsheet dâin waje dâaya sabida yadda zanyi yake ratsata.
Daga iya wuyanta kawai ta rufe zuwa âkasa da âbom âbom dâinta kadâan, rigarta kuma daga gefen cikin ya dâan budâe kadâan , kana iya hango cibiyanta.
Kallan yan seconds yayi mata ya dâauke , idanuwansa , kafin ya soma takowa zuwa gefen gadon.
A hankali ya saka hannu ya miâkar da âkafarta sosai , akan lankwashe su da yayi, sannan ya Ja bedsheet dâin ya rufe mata jiki ba tare da ya sake kallan jikinta ba , ya mayar da kallansa zuwa fuskarta , yadda take bacci hankali kwance batasan ma da wani a cikin dâakin ba .
Tun daga kan girar idanuwanta ya soma kallan step by step , zuwa circle balls dâin idanuwanta , da yadda ta lumshe eye lashes dâinta tana bacci, gasu tubarkalla zara zara dasu .
Next idanuwansa ya sauka akan hancinta, kafin ya mayar dashi kan âkaramun bakinta.
Tun daga kan zagayen bakinta har zuwa colour dâin bakin sai da ya âkarewa kallo, kafin ya saka one finger dâinsa yana gyara mata gashin da yake âkoâkarin rufe mata fuska.
Hannunsa da ya taâba tane, yasa ta dâan motsa , amma kuma bata budâe idanuwan ba sai sake âkudun dunewa da tayi kamar mage .
Bzzzzzzz notification ya shigo wayarta , yana kusa da wayar shiyasa ya kalli wayar , kuma ya karanta saâkon , kafin ya dâaga gira dâaya, yana wani murmushin leâban baki me hadâe da taune lips kadâan . Ya sake kallan Mimi na wasu lokuta, kafin ya dâan ranâkwafo kadâai ya ambaci sunanta â Mishal âŠ.â
Mimi kam bata amsa ba sabida baccin ta da take sha hankali kwance .
Yana âkoâkarin miâkewa ita kuma ta dâan muskuta, daga yanayin yadda yake zaune , fuskarta ya fadâo kan cinyarta , sannan ta wani turo lips dâinta waje kamar âkaramar yarınya.
Yana âkoâkarin zamewa amma ita Mimi sai fama âkara muskutawa take , batamasan tana yi ba .
â Ya Allah âŠâ shine abunda ya iya furtawa cikin âkasan maâkoshinsa.
âž»
To be continued⊠đ„
BLACK QUEEN đ€đż
***
***