MISHAL

Page 16

by @ayshagaladima22

MISHAL



By AYSHA GALADIMAšŸ¤šŸæ
***


MAI SAN A TALLATA MASA KAYANSA YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER ***



Book 1 
 Page 16 

A hankali ya saka hannuwansa guda biyu ya zame kanta daga jikinsa, sannan ya kwantar da ita akan pillow yadda ba zai tasheta daga baccin da take ba , sannan ya gyara mata blanket d’inta , ya mi’ke zuwa gaban mirror d’akin. 

Hannunsa duka biyu ya d’ora akai yana kallan madubin na tsawan lokaci , kafin ya mi’ke tsaye yana juyowa , sai dai jikinsa da ya jinginar da bayan abun mirror d’in, yana had’e hannuwansa suka guda biyu akan faffad’an ’kirjinsa. 

ā€œ MOHā€¦ā€ aka ambaci sunansa , hakan yasa ya d’aga idanuwa zuwa inda aka kira sunan nasa , JOY ce a tsaye tana kallansa , shima kuma baiyi Kızo ko mamakin ganinta a wajan ba , dan babu wani reaction nasa da ya nuna hakan. 

ā€œ MOH an kwana biyu, tun shigowar ka d’akin nan , ka duba ya Mimi take cikiā€¦ā€

ā€œ JOYā€¦ā€ ya fad’i sunanta a hankali yana kallan Mimi da take bacci hankali kwance .

ā€œ Nasan abunda bakaso a ambata Moh , amma kullum ā€˜kara girma take , baka tunanin lokaci yayi da zaka sauke wannan amanar ? Tayi maka nauyi sosai a zuciya , tsawan shekaru, ko sau d’aya ne ka bari zuciyarka ta amayar da abun da yake cikinta.

Mimi yanzu ba yarinya bace , shekaru take sake ā€˜karayı, girmanta , saninta komai yana hannunka, idan har baka yadda ba babu wanda ya isa ya maka musu, amma kai ma kana ā€˜ko’karin salwantar da yaruwarka akantata baya taka tafi tatan mahimmanci….ā€


ā€œ Ki cigaba da kula da ita kamar yadda kika saba Joy, ki tsaya a matsayin mai kula da Mimi, don’t try to lecture me againā€¦ā€ daga nan ya fice daga d’akin Mimi ko waiwayo wa bai sake yi ba . 

Ita kuma Joy tayi wani murmushin takaici tana kallan hanyar da yabi, kafin ta je ta zauna a kusa da Mimi tana kallan fuskarta kamar wacce aka ce idan ta tashi daga inda take , zata nemi Mimin ta rasa . 


____________
 THE NEXT DAY

After sallahr asuba Moh bai fita daga gidan ba , yau ko gym d’insa sai shiga ba ya wuce bedroom d’insa. 

Bayan yayi wanka, yayi aiki a system d’insa na tsawan 1 hour plus tukunna yasa hot green tea , ya kwanta .

In baka gansa ba sai kayi tunanin ko baya cikin gidan ne sabida ba zama yake a ciki ba all day . 


ā€˜Karfe 9 na safe … 

Sound d’in wayansa ya soma tashi, duk da sound d’in wayar bashi da ā€˜kara kamar tafiyar ruwan kogi haka ā€˜karansa yake . 

Sai da akayi kira biyu , a na ukun ne ya bud’e ido yana zama sosai akan bed d’insa , d’akin kuma so dummy. 

A speaker ya saka wayar, daga ciki yana jin yadda muryoyin su ā€˜kasa ā€˜kasa , kamar masu yiwa juya fad’a sai dai baice komai ba . Ya ajje wayar a gefen sa . 

Sai kuma yaji muryar Al’ameen a cikin wayar yana fad’in ā€œ Boss yarinyar nan zata ā€˜kona mun gida tabi ta dameni sai na kawo ta gidanka kuma na bata number d’inka , ni tun zuwan ka kamar ka kwance mata ā€˜kwa’kwalwa wallahi , she’s no longer the AYA I know, imagine, tana aiki tana tanbaya kai , wani MOH MOH sai kace caprison and beside that….ā€ Al’ameen bai ā€˜karasa abunda zai ce ba , Aya da tace can ā€˜bangaran ta amshe wayan tana fad’in ā€œ MOH MOH i can’t even reach you , nifa I want to talk to you , please Moh Mohā€¦ā€

Kamar masu magana da gawa, babu umm babu um uhm wayar kuma daman bata dai dai saitin sa shiyasa ya ajje ta a gefe, suna maganar su …

ā€œ MOH MOH please say something….ā€ Cewar Aya , da turanci take maganarta ga baki d’aya , turancin ma fluent British gashi maganar da sauri sauri yake fitowa ….

ā€œ MOH MOHā€¦ā€ ta sake ambata , shi kuma Moh kit ya kashe kiran daga inda yake a zaune . 

Hannunsa guda d’aya ya saka a goshinsa , yana ta’ba wa a hankali ahankali, idanuwansa kuma a lumshe suke , yayi hakan na tsawan lokaci, kafin daga bisani ya bud’e idanuwansa ya sauka daga kan gadon, zuwa toilet. 

Kunga cikin toilet d’in kuwa ? Sai kace ba toilet ba dan ko abinci ne ya fad’i mutum zai iya d’aukar abunsa ya ci, yayi kyau sosai , uwa uba yana da girma sosai da fad’i , interior d’in toilet d’in ma ba’a magana . 

A cikin toilet d’in akwai wani glass , da yake a tsagaye, na wajansa ba zai ga me na ciki yake yi ba . 

Rigar jikinsa ya cire , ā€˜ka’k’arfar muscles d’insa suka fito sosai , 8 packs d’insa suma sun zauna curcur , jikinsa a ā€˜kame yake ā€˜kam ā€˜kam sabida tsabar motsa jiki da yake yi. 

Abun mamaki cikin babu komai a ciki , daga jikin bango ya tsaya , ya danna d’aya daga cikin bangon wajen, ya d’an koma ciki kad’an, cikin ā€˜kananan seconds saman wajan ya bud’e , da kuma gefen inda ya danna , abun shower ne suka fito masu kyau, silver colour , new modern, wannan shafawa ma ake kamar screen , sai kai selecting abunda kake sanyi.

Shower Moh ya danna duk da shower d’in ma ya rabu kala uku, akwai ta sama , akwai ta gefe, akwai wanda zaka ri’ke a hannu, akwai kuma wacce take ā€˜bul’bulowa ta ā€˜kasa… 

Ta saman ya danna, amma warm … 
Take a wajan warm water ya soma sauka tun daga kan gashinsa, zuwa murd’ad’d’an jikinsa , da kuma wandonsa da shima ya soma ji’kewa. 

Ko moshi baiyi ba , sai idanuwansa da ya sunkuyar ā€˜kasa yana kallan yadda ruwan yake sauka a jikinsa yana wucewa… 

A hankali ya soma lumshe idanuwansa yana sake bud’ewa, sai kuma ya saka hannu akan gashin kansa yana d’an cakud’a su yadda ruwan zai shiga sosai a kan nasa. 

Wasu daga cikin gashinsa sun d’an yo gaba sun kwanta , wasu kuma har idanuwansa suke rufewa sai ya saka hannu ya mayar dasu baya tukunna suke kwantawa sosai. 

Ya dade ruwan yana sauka akansa, kafin ya kashe , ya fito da ji’ka’k’ken kayan nan zuwa cikin bedroom , direct kuma wayarsa da yake ajje ya d’auka , ya sake ganin kiran Al’ameen har guda biyu, sai bai kirasa ba ya tura masa short message, ya ajje wayan, sannan ya sake komawa toilet d’in. 


A ā€˜bangaran Mimi kuwa …..
Yau haka kawai taji zuciyarta ta tashi wasau, babu tunanin nan da take faman yi akan me tura mata text , sai ma mafarkin da tayi da yake faman dawo mata sabo, lokaci zuwa lokaci sai tai sauri ta furta ā€œ Mimi you chop sense abi?ā€. 

Yau ko ā€˜bangaran su Zarah bataje , da tayi wanka tayi duk abunda za tayi ta zauna a d’aki tana karanta English novel d’inta , sai da taji ta soma jin yunwa tukunna ta ajje book d’in, ko wayarta bata d’auka ba ta saka slipper d’inta ta fito zuwa down stairs ….

Uncle Abba yana zaune shi da Aunty  Shukura tana nuna masa abu a waya, shi kuma yana magana .

Shiya soma ganin saukowar Mimi, shiyasa ya d’an ri’ke ha’barsa kad’an yana kallanta ā€œ Mimi yau kuma kece da tashi da wuri haka? Za’ayi mana ruwa kenan?ā€.


Murmushin Mimi tayi tana gaishe sa ā€œ Uncle Abba ina kwana , ka tashi lafiya ?ā€. 

ā€œ Lafiya ā€˜Kalau Mimi, ya bacci kuma ā€¦ā€

ā€œ Wana bacci kuma Uncle Abba kasan ba wani bacci nake sosai ba kawai dai fitowar ne banyi da wuri ba , Aunty Shukura babu magana ko? Toh Ina kwana ?ā€.

Ta kalli Aunty Shukura da ta d’an ta’be baki ā€œ Mara mutunci na d’auka Uncle Abban kawai kika gani, ni ba zaki kula ni ba .ā€

ā€œ Yoo dan kin samu ma na kula ki, yau dai Uncle Saleem bayanan balantana ya shigar miki, Uncle Abba kuma kinsan yana side d’ina ko me zanyi , yana bin bayana ko ya kace Uncle Abba?ā€.


ā€œ Ai ba ma sai kin maimaita kanki ba , wannan maganar haka take, wace ce Shukura , bayan da Auta a gefe ….ā€ 

ā€œ Clock itttttttttt….ā€ Cewar Mimi tana yiwa Aunty Shukura gwalo.

ā€œWallahi ki bari na kamaki Shukura ai na danda’kaki a wajan nan , ni kike ma gwalo , wato tsuntsun kulle ya samu sake ko?ā€.

ā€œ ba komai , in ni tsuntsuwa ce kema ita ce , kinga ni Aku, ke tattabaraā€¦ā€

Da sauri Aunty Shukura ta kawo mata hannu , ita kuwa tayi saurin kufcewa tana mata gwalo , Uncle Abba kuwa dariya kawai ya tsaya yi.

ā€œ Zan kamaki ne aiā€¦ā€ cewar Aunty Shukura …

ā€œ Kinga tafiya ta ma , ni wajan su Mamy zan tafi , ga falon nan na bar miki , Uncle Abba bye bye , bari naje na gaishe da su Mamy.ā€

ā€œ Shikenan ā€˜yar Mamy a fito lafiya .ā€ Uncle Abba ya bata amsa . 

Ita kuwa Mimi ta wuce falon su Mamy, as always sai da ta soma knocking ā€˜kofar tukunna ta bud’e ta, kamar koda yaushe ā€˜kamshin turaran wutan Mamy da kuma sanyin Ac ne zai soma bugowa hancin duk wanda ya shigo. 

Itama Mimi sai da ta sha’ki ā€˜kamshin falon tukunna ta sauke ajiyar zuciya tana sallama . 

ā€œ Assalamu Alaikum ….ā€ Mimi tayi sallama. 

Baffa da yake zaune akan carfet ne ya amsa mata sallaman , babu Mamy a ciki shi kad’ai ne a shingid’e yana karanta jarida. 

Ganin Mimi ne yasa ya ajje jaridar, yana zare farin glass d’in da yake idansa .

Itama kan carfet d’in ta zauna tana d’an ran’kwafo kad’an . ā€œ Baffa na ina kwana .ā€

ā€œ Yar gidan Baffa kin tashi lafiya?ā€ Shima ya amsa mata cikin kulawa . 

ā€œ Lafiya ā€˜kalau Baffa, yau dai daraban zan ganka a cikin gida Baffa na d’auka ma har ka fita .ā€

ā€œ Ban fita ba Mimin Baffa, yau canai babu inda zani , har sai naga ā€˜yata ai , na gaji da wayan da Mamy take mun, kullum ita ce take ganin ki, ni bana ganin ki da safe shiyasa na’ki fita aiā€¦ā€


ā€œ Innaliallhi Baffa kayi hakuriā€¦ā€ Mimi ta fad’a tana dariya ā€˜kasa ā€˜kasan . 

Shima Baffa murmushi ne kwance akan fuskarsa , da babu murmushin nan , tun shigowarta ne murmushi ya fad’ad’a akan fuskarsa , kana kallan idon Baffa zaka ga tsananin ā€˜kaunar ā€˜yar tasa a cikin idanuwansa.

ā€œ Baffa ina Mamy ne , yau ko bacci take ne ?ā€.

ā€œ Taje part d’in su Zarah ne , amma nasan a kowana lokaci zata iya dawowa tunda ta d’an jima kad’an.ā€

ā€œ Shiyasa naji falon shuru, Baffa me zan girka ma yanzu , tunda kana gida .ā€

ā€œ Naci abinci Mimi tun d’azu , ke yakamata ki samu abinci kici yanzu, banasan wasan cin abincin nan da kike faā€¦ā€

ā€œ No Baffa zanci yanzu na d’auka kaima baka karya bane shiyasa zan mana tare , tea fa , ko coffee , ko wani glass of water ko drink babu abunda kake so yanzu?ā€.

ā€œ Babu Mimi na , kedai ki samu wani abu kici a cikin ki , tun kafin Mamynki ta soma complain kin rameā€¦ā€

ā€œ Baffa Indai wannan complain d’in ne ai kullum Mamy sai tayisa, sai dai bata ganni bane , bari naje naci abincin Baffa, Allah ya huta gajiya ā€¦ā€

ā€œ Amin Mimi na ā€¦ā€ cewar Baffa . 

Sai yanzu da zata fita ya d’auki glass d’insa ya mayar, har ta saka hannu ta bud’e ’kofar sai kuma ya kira sunanta . 

ā€œ Mimi..ā€

Babu shiri ta juyo tana amsawa ā€œ Na’am Baffaā€¦ā€

ā€œ Zo muyi magana kafin ki tafi.ā€ Ya bata amsa .

Babu musu Mimi ta dawo ta zauna a inda ta tashi , duk da ma tayi hasashe akan me zai mata maganar . 

Kuma hasashen nata ya zama gaskiya dan maganar Uncle Bashir ya somayi mata , kamar koda yaushe idan makamancin abunda ya faru jiyan ya faru a tsakanin su..ā€

ā€œ Mimi na kamar kullum ki zama me ha’kuri da kau da kai, idan wani abu ya faru, kinji ko? Banaso ki saka abu aranki, na sha fad’a miki amma zan sake kuma nanata miki.

Bashir d’an uwana ne , banaso ki dinga kallan abunda yayi miki a matsayin musgunawa ko kuma ā€˜kinki. 

Babu ko d’aya sabida kema jininsa , kuma ā€˜yar yayansa, a matsayin ki na yarinya kuma dole ki koyi hakuri akan irin wad’an nan al’amuran musamman da ya kasance kamar uba yake a wajanki. 

Tunda ni mahaifinki ne , toh shima tabbas mahaifin naki ne , ko ba haka ba ?ā€ Ya dakata yana kallanta. 

Kanta Mimi ta d’aga masa kafin ta furta ā€œ Haka ne Baffa ā€¦ā€

Cigaba da magana Baffa yayi ā€œ Kuma banasan zafin Bashir ya shafi Ameerah , tare kuka taso a tsakanin ku, inaso ki cigaba da mu’amala da ita, kamar komai bai faru ba , kamar yadda kike da Zarah haka kuke da Ameerah, a shekaru biyun nan, nima na lura da canzawar ku, ada kinfi zuwa shashen su Ameerah kuma ko da Yaushe kuna tare amm yanzu ala’karku da Zarah yafi wanda kukai da Ameerah ma . 

Yan uwan juna ne ku, karku raba kawunan ku, ina so ki kasance Miminki da na sani ada , me yawan walwala da fara’a wacce bata saka damuwa a cikin ranta, kuma ki gyara alamar ku da Ameerah banasan naji ā€˜kananan magana kinji? Ko yanzu idan har kin shiga part d’in su Zarah , toh ki shiga nasu Ameerah ma , kuma inaso idan kinci abinci kije ki bawa Bashir ha’kuri keda Zarah.

Nasan bakuyi laifi ba amma fushi yake da ku, kuje ku basa hakuri, sannan ku dawo normal yadda kike da Ameerah. 

Sannan kuma ki tabbata kinje kin gaishe da Moh, kina zuwa gaishe shi ma kuwa?ā€ Sai yanzu Mimi ta d’an turo baki tana wasa da hannunta 

ā€œ Baffa kasan fa halin Uncle Moh, yanzu ko inda yake bayansa nazo , kuma kullum cikin had’e mun rai fa yaye, har yanzu babu wannan fara’ar , kuma ya dinga harhad’emun gira fa ā€¦ā€

Murmushi Baffa yayi, sai yanzu ya sake zare glass d’in idanuwansa , yana ā€˜kara kallanta ā€œ Kalli cikin idanuwana Mimi.ā€ 

Babu shiri Mimi ta kallesa sai kuma ta sun kuyar da kanta ā€˜kasa. 

ā€œ Kiyi abunda nace miki kiyi , ko dukan ki zaiyi kije ki gaishe sa , infact in ma bayanan ki kirasa a waya , wannan umarni nake baki Mimi, beside that , idan har kullum zaki dinga gaishe da sauran Uncles d’inki me yake hanaki bakya zuwa gaishe sa uhm? Ko so kike na yadda da maganar da ake fad’a kina tsoran  Moh sosai?.ā€

ā€œ Baffa ba ya zama fa a gida kaima ka sani, kuma bana ganinsa a part d’in …. nan…shiyasa….ā€

Kallan da Baffa yayi mata ne yasa maganar ā€˜karshen ta fito a hankali kamar bataso tayi. 

ā€œ Amma idan ana so a takura miki can part d’in nasa kike ā€˜buya sabida babu me shiga , tsoran ki yake ji da yake barin ki kike shiga cikin part d’insa har kiyi bacci?, idan bayanan?.ā€

ā€œ Baffa….ā€

Hannu ya d’aga mata yana murmushi har lokacin ā€œ Zaki iya tafiya Mimi na , karki manta kuma kici abinci kinji ni ko? Banasan wasan cin abincin nan da kike haka .ā€

ā€œ insha Allah Baffa ā€¦ā€ ta bashi amsa jiki a sanyaye. 

Bata ma koma main falo ba ta soma wucewa d’akin Mamy ko ta dawo . 

Ai kuwa ta dawo d’in, dan a tsaye ta tarar da ita , ta bud’e wardrobe d’inta tana duban abu , shigowar Mimi ne ya dakatar da ita da abunda take yi d’in ,  ganin jikinta a sanyaye . 

ā€œ Daga ina kike , kika shigo mun d’aki salo salo kamar mara lafiya .ā€

Lips d’inta Mimi ta D’an turo kad’an, tana shagwa’be fuska ā€œ Mamy daga falon ku fa nake , naga bakya cikin, Baffa ne kawai a ciki.ā€

ā€œ Toh sai akai yaya?ā€ Mamy ta sake tanbaya tana kallanta . 

Ga baki d’aya maganar da Baffa yayi mata ta fad’a mata , ita kuma Mamy da take ri’ke da hannunta , ta saki ta sake komawa gaban wardrobe d’inta tana cigaba da abunda take .

ā€œ Mamy ba zaki ce komai ba ?ā€.

ā€œ Me zance miki Mimi? Kinsan dai ni ba Baffa bace , kina ā€˜kara shagwa’bemun wannan fuskar taki zaki ji ajikinki. Banyi lallacewar da zaki zo mun da ā€˜karamun iskanci nan ba , gwanda shi Baffa da yake biye miki idan kinyi abu, nan babu Baffa , tun wuri ki ā€˜bace mun da gani, kar ma ki ā€˜bata mun lokaci.ā€

ā€œ Mamy daman nasan bayansa zaki bi.ā€

ā€œ Idan banbi bayansa ba bayanki zanbi uwata Mimi?ā€.

ā€œ Kai Mamyā€¦ā€

ā€˜Dan sake dakatawa Mamy tayi da abunda take tana kallan Mimi d’in ā€œ Kinga ! Kinga tun muna mu biyu , ki fice mun daga d’aki na ā€˜karasa abunda nake , idan kika bari nazo inda kike wannan ā€˜karamun bakin naki sai na murd’esa idan yaso ya ā€˜kara girma , sai kace wata Babyā€¦ā€

ā€œ Mamyā€¦ā€ Mimi ta kuma ambata. 
Amma ganin Mamy ta soma nufar inda take , tayi saurin ficewa daga d’akin tana dariya . 

Itama Mamyn dariya tayi tana girgiza kanta ,sannan ta furta ā€œ Allah ya shirya mun ke Mimiā€¦ā€ daga nan ta cigaba da abunda take .


____
Bayan Mimi ta fice daga d’akin Mamy tana dariya , d’akinta ta koma sannan ta sake dawowa falo zuwa kitchen. 

Yunwar da take ji yanzu ya fara ā€˜karuwa sosai. Fridge ta soma bud’ewa tana kallan abunuwan da yake ciki, dan specifically bawai na kayan miya bane ko wani abun nama, yawanci tarkacen ciye ciye da kayan ā€˜kwalam a ciki, ice cream , chocolate and co .

ā€œ Yanzu me zan ci ni Mishal?.ā€ 
ā€˜Kwai ta d’auko guda biyu da slice bread , bread d’in guda uku ta cira ko wanne kuma ta raba shi guda biyu, ta d’ora manta a wuya, ta kad’a ʙwai , ta saka maggi, already ta yanka onion sannan akwai pepper ta d’iba kad’an shima , sannan ta soya bread d’in. 

Ta had’a Lipton amma green tea shima ā€˜karamun plate ta samu ta saka bread d’inta , ta d’ora kuma a mini tray tare da cup d’inta ta fito daga kitchen bayan ta d’auki wayanta zuwa d’akinta . 

Shigarta kuma yayi dai dai da vibration d’in wayar ta . 

Sai da ta ajje tray d’in tukunna ta kalli wayar , Zarah ce take kira . 
Murmushi tayi kad’an kafin tayi picking call d’in tana fad’in ā€œā€™yan mataā€

Daga can ɓangaran Zarah itama ta amsa mata ā€œ Na’am ʼyan maza ! How far .ā€

ā€œ i dey fine oo.ā€ Itama Mimi ta amsa mata , tana zama kusa da breakfast d’inta . 

ā€œ na d’auka kina can kina baccinki na fama ai .ā€

ā€œ Tunda ance miki ka sa ce ni ai dole na dinga bacci everyday , everytimeā€¦ā€

ā€œ Mimi to who knows ko ita ce? Kedai ba za’ayi shedar ki ba .ā€

ā€œ Abeg jare ʙyaleni naci abinci na.ā€

ā€œ Yau kuma? Gaskiya gulmarki yawa ne dashi wallahi Mimi..ā€

ā€œ Naji ɗinā€ Mimi ta bata amsa , sannan ta gutsiri soyayyan bread d’inta . 

ā€œ Gaskiya ne ā€˜yar Mamy , enjoy your self …. Wai tsaya ya ake cikine maganar binciken nan?ā€.

ā€œ Wana bincike?ā€

ā€œ Mimi kinsan akan abunda nake magana fa , akan number d’in da muka ce za…..ā€ Zarah bata ā€˜karasa ba Mimi tayi saurin katseta ā€œ Zarah please not nowā€¦ā€

ā€œ Why ?ā€. Zarah ta tanbaya . 

ā€œ Yanzu ba wannan ne ma a gaban mu ba Zarah , Baffa yace muje mu bawa Uncle Bashir ha’kuri , and kinsan halin Baffa , idan bamuje ba , ran mu sai ya ā€˜baci mu duka .ā€

A can d’aya ā€˜bangaran itama Zarah jinjina mata kai tayi ā€œ Nima Daddy ya bawa Mommy sa’ko akan muje mu basa ha’kuri , and ya zamuyi tunda sun fad’a , amma kinga Ameerah hmmm.ā€

ā€œ Zarah ki barta kawai da halinta babu bu’katar ma tayar da maganar , ta fad’a abunda ta ga dama , kuma bata isa ta samu muyi abunda take so ba , so cill. 

Bani 10 minutes na ā€˜karasa cinye abinci na yanzu zan fito muje part d’in nasu sharp sharp mu dawo.ā€

ā€œOkay dear bye ..ā€

ā€œ Byee tooā€ cewar Mimi kafin tayi cutting call d’in. 

Bata wani tsaya ā€˜bata lokaci ba , ta kammala abincinta , takai plate d’in kitchen , tunda tana tare da wayarta , no need to koma d’aki sai kawai ta fito daga part d’in su . 

Bata shiga part d’in su Zarah ba , number ta Kawai ta kira , Zarah tana d’agawa Mimi ta furta ā€œ Fito mu tafi Zarah ina waje .ā€

ā€œ On my way ..ā€ shine amsar da Zarah ta bata kafin ta kashe kiran itama. 


____ Mintuna kad’an sai ga Zarah ta fito daga part d’in su sanye da doguwar riga me kyau, ta saka scarf d’inta aka . 

Inda Mimi take ta ā€˜karaso , sukai wani hugging junan su , kamar ba sune suka gama waya yanzu , ā€œ
Yanzu muje kenan?ā€.

ā€œ Eh mana ..ā€ Mimi ta bata amsa . 

Suna zuwa Part d’in , falo suka shiga , anan kuma suka tarar da Ameerah akwance kan kujera tana danna waya , ita kad’ai ce a falon, sai tv da take kanta. 

Mimi ce ta soma sallama , duk da ba tayi dan Ameerah ta amsa d’in ba . 

Ameerah kuma bata amsa ba , sai d’an d’agowa da tayi ta kallesu ta sake mayar da idanuwanta kan wayarta da take dannawa . 

Kallan junan su Mimi da Zarah sukai kafin Zarah ta furta ā€œ Ameerah , ina Bashir , ko zaki mana izo wajensa?ā€.

Wani kallan gefen ido Ameerah tayi musu ta sake watsarwa gefe , ta kuma mayar da kallanta zuwa wayanta. 

Wani ā€˜kululun abune suka ji ya tsaya musu arai amma suka danne.

ā€œ Ameerah magana fa muke miki.ā€ Yanzu Mimi ce tayi magana .

ā€œ And so ? Kunzo kai na sai wani hayaniya kuke mun, bakusan inda zaku same sa bane , a beg please let be ā€¦ā€

Gyara tsayuwarta Mimi tayi sosai tana kallan Ameerah ā€œ Ameerah why are you so rude , like bangane miki bane kwana biyu , sai ki dinga wasu behaving kamar dole ne mu’amala damu, look it’s not by force , idan kinga dama dan Allah karki sake magana har mahad’i ya bayyana. Rubbish kawai .ā€ Mimi ta bar wajan, itama Zarah tai maka kallan tara saura kwata , suka nufi falon Uncle Bashir d’in. 

Sai da sukai knocking kamar sau biyu , daga ciki sukaji ya amsa da a shigo. 

Mimi ce a gaba ita ce ta soma bud’e ā€˜kofar ta shiga , Zarah kuma ta biyo bayanta . 

Ganin su da yayi ya d’an soma cika yana batsewa , har da gyara zama sosai . 

Kamar yadda Mimi zata gaishe da Baffa haka gaisheta . 

ā€œ Ina kwana Uncle Bashir .ā€

ā€œMe ya kawo ku?ā€ Shine tanbayar da ya soma yi musu ba tare da ya amsa gaisuwar ba .

ā€œ Mun zone mu baka ha’kuri , kayi ha’kuri.ā€

Sai a lokacin ya saki ransa har wani murmushi yake irin anzo an bashi ha’kurin nan . 

Zamansa ya gyara sosai akan kujera , ya jingina bayansa , tukunna ya kallesu su duka .

ā€œ Yanzu wane ne ya turo ku, ku bani ha’kuri nasan ba zuwan ku bane wannan , Daddy ne ko Baffa .ā€

Zarah za tayi magana Mimi tayi saurin rigata ā€œ A’a Uncle Bashir  basu bane , munga ranka ya ā€˜baci jiya shiyasa muka zo mu baka ha’kuri .ā€

Murmushin fuskarsa ne ya ā€˜Kara ā€˜karuwa sabida a duniya yanasan irin haka idan anzo basa ha’kuri ā€œ  Bakomai ai ku ā€˜ya’yana ne , Allah ya shirya ku ga baki d’aya .ā€

Suka amsa da ā€œ Ameen .ā€ Zasu mi’ke ya tsayar dasu ā€œ  Kuna mun kallon kamar nafi fifita Ameerah akan ku amma ku bakusan gatan da nake muku ba , kuma ku dena tunanin ko na tsane kune .

Ni ban tsane kuba sabida ku d’in ā€˜ya’ya na ne , iyayen ku yayena ne jini , dan haka babu dalilin da zai saka na tsane ku. 

Kuma ni halin kune banaso bawai kud’in ba kunjini?ā€.

ā€œ Eh Uncle Bashir mun gode .ā€ Zasu sake juyawa ya kuma tsayar dasu , hannu ya saka a aljihu ya ciro rapper  bandle d’in kud’i guda biyu d’an d’ari biyar biyar ya basu ā€œ Gashi ku saka kati wannanā€¦ā€

Daga Zarah har Mimi sai da suka ā€˜kame dan mamaki , kasa cewa komai sukai sai Zarah da taje amsar kud’in ta furta ā€œ Mun gode Uncle Bashir .ā€ Daga nan fit suka fice daga falon babu ā€˜bata lokaci. 

Ko da suka fito falon da Ameerah take , ko kallo bata ishe su ba suka fita daga part d’in ga baki d’aya gudun ma kar ya sake dakatar dasu .

Suna fita bayan sun d’anyi nesa da part d’in suka wani kwashe da dariya ga baki d’ayan su şuna kallan kud’in da ya basu .

ā€œ Omo yau Uncle Bashir ne ya bamu kyautar kud’i sabida mun bashi ha’kuri? Wonder shall never end ā€¦ā€


ā€œ Kema dai Zarah dole kiyi mamaki baki ga har da wani smiling yake ba ?ā€.

ā€œ But Mimi, Ameerah fa ?ā€

ā€˜Karamun tsaki Mimi tayi , ta d’aga kafad’unta kad’an ā€œ ita ta sani.ā€


_________________

To be continued… šŸ”„


Aysha Galadima šŸ¤šŸæ
***

***