Page 17/18/19
MISHAL
By AYSHA GALADIMAđ€đż
***
MAI SAN A TALLATA MASA KAYANSA YAYI MUN MAGANA TA WANNAN NUMBER ***
Book 1
Page 17/ page 18/ page 19 .
Mimi za ta bar wajan Zarah tayi saurin dakatar da ita ta hanyar riâko hannunta âToh kudâin fa ? Ko shima na ajje miki?â.
â No nidai babu ruwana , idan kinaso ki dâauka amma ina ganin zai fi kyau ki ajje , kar Uncle Bashir ya soma cewa ya bani kudâi , ahtoo dan yau yayi mana kirki ba hakan yake nufin zai mana gobe ba kema kinsan halinsa.â
âYar âkaramar dariya Zarah tayi tana juya kudâin a hannunta , cikin wasa ta furta â Ai wallahi sai na taâba su , ai ba roâkansa mukai ba , idan ma daga baya yazo yayi mana magana ni babu ruwana , kinga na rage zafin takaicinsa da mitarsa , kedai naki zan ajje miki duk lokacin da kike buâkatar su sai na dâauko miki .â
â Bazan ma buâkata ba , nidai na fadâa miki.âdaga haka Mimi ta soma tafiya , sai dai ganin saitin hanyar da ta nufa ne yasa Zarah kallanta da mamaki â Ina kike shirin zuwa ? Ba part dâin mu zamuje ba ? Kamar part dâin Uncle Moh naga kina nufa fa .â
â Yeah can zanje .
Zanje na gaishe sa ne .â
â Part dâin mu fa?â. Zarah ta tanbaya tana dakatawa daga tafiyan da take .
â No Zarah , yau bana tunanin zan shiga part dâin ku, may be dai zuwa anjima , yanzu idan na gaishe da Uncle Moh ina tunanin zuwa nayiwa su Mamy abincin rana da kai na ne , idan na zauna a part dâin ku kuma bazan san lokaci ya tafi ba.â Cewar
âDan jimm kadâan Zarah tayi kafin ta furtaâ Okay ooo ! Ni bari naje na ajje kudâin , idan yaso sai ki âkarasa part dâin Uncle Moh dâin.â
â Ke ba zaki ba kike nufi ?â
â Yeah kedai kije , I will talk later .â Cewar Zarah , bata bari ma Mimi ta sake magana ba ta juya zuwa hanyar part dâin su .
Itama Mimin kuma bata damu ba daman kuma tasan Zarahn zata iya guduwa idan tasan zata je part dâinsa wannan ba saban abu bane a wajanta.
Tana zuwa ta saka dâan yatsanta ta budâe falon .
Bayan sanyi da âkamshin turare babu abunda dâakin yake , gashi kuma kayan falon baâki ne , kuma 80% na filitun falon a kashe yake , kamar babu kowama kwata kwata a ciki.
Mimi sai da ta kunna filitan wayanta tukunna ta kunna duka light dâin falon , lokaci dâaya yayi tantar da hasken fitula .
Ba tayi tsammanin ganinsa a falon ba , kuma hasashenta yayi gaskiya babu Moh sai âkamshin turaransa kawai da yake ciki.
Turo baki Mimi tayi kadâan, batasan kuma ta hau sama dubashi, shiyasa Tayi deciding zata tura masa short message idan ta koma dâaki.
Amma bata fita daga falon ba , kwanciyarta tayi akan kujera sosai ta bararraje tana daddan na wayar hannunta , hankalinta yana kan reels da take kalla batasan da fitowarsa ba kwata kwata.
Kamshin turaransa kuma da take ji sai tayi tunanin falon ne tunda âkamshin turaransa falon yake a koda yaushe.
Moh kuwa , daga kitchen ya fito hannunsa dâauke da bottle water , da alama tun acan ya soma shan ruwan, sabida ragowar ruwan da yake cikin bottle dâin bai fi rabi ba .
Waya ne a kunnansa, tunda ya fito har ya zauna , bai ce komai ba itama kuma bai ce mata komai ba , infact ko kallan inda take baiyi ba .
Hankalin Mimi ga baki dâaya yana kan reels dâinta wasu kuma tana dariyarta hankali kwance .
Kamar âkiftawa da bismillah taji saukar muryar yana fadâin â Okay shikenan.â
Cikin wani 360 Mimi ta jiyo, dai dai shima ya kalleta , karaf idanuwansu ya shiga cikin na juna , da sauri ta miâke tsaye tana fadâan sosa kanta alamar rashin gaskiya.
â Uncle Moh ina⊠ina kwana?â.
â Abunda kikeyi in kin zauna a dâaki kenan?â Ya jefa mata tanbayar a maimakon ya amsa gaisuwar da tayi masa .
Cikin sauri ta furta â Aâa wallahi nazo gaisheka ne , naga bakanan sai na dâan kunna amma ba haka nake ba wallahi Uncle Moh.â
â Okay yanzu me kike?â Ya sake tanbaya yana zuba mata wannan idanuwan nasa masu kaifi.
âDan wasa ta somayi da hannunta dan ta rasa wana irin amsa ma zata bashi dan ya âkyaleta.
Tana tsakiya da wannan tunanin ya miâke tsaye yayi wucewarsa sama, ba tare da yace mata komai ba.
Ita kuma da kallo tabi bayansa, har sai da taga wucewarsa tukunna ta dâan taâbe bakinta â Mutum sai fadâin rai , idan ba zaka amsa gaisuwar nawa ba bashikenan ba amma zaka âkyaleni , a tsaye sai kace wani kara.â Ta kuma murgudâa baki , dama maganar cikin âkunâkuni tayi ta gudun karma yaji, sannan tayi wucewarta itama ta bar masan part dâinsa ba tare da tayi wani second through ba , ta wuce nasu part dâin.
_________
ISTANBUL âŠâŠ
Hira kadâan Ahmet yayi da Nunu da take faman yi masa shagwaâba, kafin bacci ya dâauketa.
Shi kuma ya sata a kafadâarta yana dâan tattakawa a cikin falon na tsawan mintuna 30 .
Sai da ya soma jin numfashinta a waje, alamar baccinta ya soma nisa tukunna ya kwantar da ita a dâaya daga cikin kujerun wajan, shima kuma ya zauna , yana dâan danne dannensa akan laptop dâin.
Kujerar da Aylin ta tashi akai ya kalla , lokaci dâaya ya dâan ja gajeran tsaki sabida takaicin halayanta da dâabiâunta da yake , wanda suka sha banban da halayen mutanan gidan nan ga baki dâaya, dan harta Nunu ba za tayi wani abunba idan Aylin tayi.
Bayan kamar hour dâaya , cikin falon yayi shiru dan harta Ahmet ya dakata da danna System dâin da yake , ya jinginar da kansa a kan kujera idanuwansa a rufe a kusa da Nunu, yadda yayi matuâkar nutsuwa kuma za kayi tunanin ko shima baccin yake , dan ko motsu mutsu ba yayi.
Aylin kuwa a dâakinta tana kwance âkarâkashin duvet, fitilar wayarta ne kawai yake haska fuskarta .
Bayan ta gama gudanar da tattaunawar da take da No stress zone đ bacci ya dâan soma fusgarta .
Batafi 30 minutes ba , vibrating dâin wayarta ya soma tsananta sabida bata kashe data dâinta ba kuma wayar yana dai dai saitin kunnanta.
Kamar wacce take expecting urgent message haka ta budâe idanuwanta farat dâaya , ta shiga WhatsApp dâinta.
Already 2 different WhatsApp ne da ita wanda ta shiga ya sha banban da wanda No stresss zone yake .
Kuma babu much number a cikin wajan, duka duka numbobin ciki ba zasu wuce 5 ba .
Kuma duka anyi saving dâin su da Jan heart me dâan dâori dâorin fari, bayan shi kuma babu ko suna a jikin numbers dâin.
Duka kallan 5 numbers dâin nan tayi , an tura mata message kuma a duka numbers dâin, musamman wata number da yake sama sama, an tura mata atleast 5 messages.
Idan ka kalli lokacin da aka tura zaka fahimci kuma yanzun nan aka turo su , sabida time dâin da suka shigo lokaci ya nuna.
Number âkarshe ta soma shiga , rubutun ciki ta karanta wanda akayisa da yaran Turkish , itama kuma tana gama karantawa tayiwa number reply da yaran Turkish .
Sauran 2 numbers da suke wajan sai da tabi duk tayi musu reply dâin messages dâin su , kafun ta shiga last number da aka rubuta â Aylin muna jiran sakamako daga gareki, dafatan komai yana tafiya dai dai kamar yadda muka buâkata ?â.
âDan taâbe baki Aylin tayi , at the same time kuma tana jan tsaki akan tuno abunda Ahmet yayi mata dâazu.
â Komai yana tafiya dai dai burin mu yana gaf da çıka, sai dai wani lokaci Ahmet yana mun barazana, kuma idan ya gano wanu abun, ga baki dâaya burin namu zai lallace tun kafin muje matsayin da muke san zuwa .â
_____________
Da tsakar daren ranar , misalin âkarfe 1 da rabi , Ahmet ya tashi daga falon da yake , dan ya dadâe sosai a cikin sa, already ya kai Nunu dâakinta , shi kuma ya canza kayan jikinsa zuwa baâkar jacket , sannan ya fita ta âkofar baya zuwa yankin sararin dok na gidan ( Private dock) .
Akwai sanyi sosai a ciki , ga kuma iskar teku sosai da yake tashi .
A cikin duhun daren wata babbar yacht baâka ta âkaraso gefen Private dok dâin da Ahmet yake , ba tare da ta kunna fitilun taba .
Wani mutum sanye da baâkaâken kaya ya miâkawa Ahmet wani envelop jikinsa da seal a jiki , bai ce masa komai ba bayan nan yayi juyawarsa yayi tafiyarsa , cikin âkanâkanın lokaci jirgin ya âbace bat a tsakiyar ruwan Bosphorus , sabida azabar gudun sa .
Daga saman benen gidan , Aylin tana tsaye daga jikin labule , idanuwanta duka yana kan Ahmet , tana jiran taga meya fito dashi , sai dai tun kafin mitinin nan ya fito ya bawa Ahmet envelop ta shaâki wani abu a hancinta da ya sakata atishawa masu âkarfi.
Kafin ta gama jero atishawar da take , ta saita kanta already Ahmet ya amsa envelope dâin , mutumin kuma ya juya , sai Ahmet kuma da yake tsaye , har zuwa lokacin bai canza position dâinsa ba .
Aylin ta jira iya jirawarta tanaso taga me Ahmet ya fito yi amma ganin bashi da alamar barin wajan , taja âkaramun tsaâki ta wuce dâakinta , itama .
*
A safiyar ranar laraba, hasken ranar istanbul yana sauka akan korayen ciyawun lambun gidan da kuma ruwan da yake zuba cikin foundation.
Yanayin gari yananan as usual yana da dadâin kasancewa , dadâi ga duk wanda ya ke irin wajen.
Anne tana zaune akan teburin kam h tana shan shayi, yayın da Nunu ke gudanar da wasanninta , a tsakiyar filin wajan, bayan an shinfidâa mata dogon abu sabida karta âbata kayanta .
Ahmet ya fito sanye da baâkin suit , ya nufi inda Anne take tare da bata kiss a goshi yana fadâin â Anne , zan tafi aiki , kina buâkatar wani abune?â.
Dakatawa Anne tayi daga shan shayin da take â Abi ! Tun yanzu ? Amma zaka dawo da wuri ko?â.
â Shine abunda nake fata kinsan yanayin aikin mu kullum canzawa yake .â Ahmet ya bata amsa, yana dâan ranâkwafowa sabida karya tsaya a kanta .
â Okay AbI ! Allah ya dawo dakai lafiya , amma karkayi wasa da cin abinci as always , get sometimes Kaci abinci sosai kaji?â
â Insha Allah Anne â shima ya bata amsa , kafin ya mayar da kallansa kan Nunu da hankalinta ga baki dâaya yake kan wasa da alama ma batasan ya fito ba .
âNunu yau ba magana?â.
Da sauri Nunu ta juya zuwa inda yake , tana ganin shi ta âkyalâkyale da dariya , sannan ta zubar da kayan wasa tana miâkewa tsaye .
A guje tayo kansa, saura kadâan ta fadâi, tana miâka masa hannuwanta alamar ya dâauketa.
Babu musu ya dâauketa yana dâan jujjuyawa da ita sai faman dariya take .
Bayansa ya juya mata kanta shiyasa ya dakata yana kallanta har lokacin kuma bata dena dariya ba , kyawawan hakwaranta sunanan a jere na yara.
â Memet ina zakaje? Nunu tayi magana cikin zallan muryan yara .
â Zanje aiki ne Nunu, kuma kinga baâa zuwa da yara shiyasa da naje da ke.â
âMemetâŠ.â Tayi maganar kamar za tayi kuka . Anne bata bari Ahmet yayi magana ba ma ta amsa Nunu tana nuna masa hanya â Maza wuce kayi tafiyarka, in kuma ka fasa zuwa aikin ne sai ka fadâa mun tun yanzu .â
Murmushi Ahmet yayi , yana kallan Nunu da tayi masa narai narai da ido kamar za tayi kuka .
Sai da yayi pecking dâinta a goshi kafin ya furta â Rabu da Anne kinji Nunu, idan na dawo sai mu fita yawo kuma ba zamuje da Anne ba kinji?â.
Cikin sauri ta jinjina masa kanta, kafin ta kwanta a kafadâar Anne tana dâan shash sheâkar kuka , Ahmet zai taâbata Anne ta masa wani kallo haka dole ya haâkura ya barta , a wajan yayi tafiyarsa.
Sai da Anne taga ya fita ga baki dâaya tukunna ta dâan soma tafin dâinta â Ya isa Nunu na âŠ. Zan baki sweet kinji?âda haka Anne ta samu ta lallashi Nunu har tayi shiru ta cigaba da wasan da take .
Bayan kamar hour 2 , itama Aylin ta fito , sanye da riga da wando , rigar tata , irin open shoulder dâin nan ne da ita ana ganin har gadon bayanta, sai gashin kanta da ta tufke a bayanta , wandan jikinsa jeans ne amma da kadâan ya wuce gwiwar âkafarta , hannunta waya ne kawai sai cup cikin sa akwai wani juice me kamar strawberry da yake ciki da kuma block da aka zuba a ciki.
Taku take dâadâdâai sai faman zuba âkamshin turare take , kamar wacce tayi wanka da turare , haka ta nufi inda su Anne take .
Sabida âkarfin turarenta tun kafin ta âkaraso sai da Anne ta dâago kanta yana kallanta .
Ita kuwa Aylin sai faman murmushi take saki tana âkara wani yangan cewa.
Tana zuwa ta miâkawa Anne hannu â Anne bari na dâauke ta âŠâ
Cikin sauri Anne ta dakatar da ita da hannu, kafin ya kalli shigarta , ta kuma sake kalla,
kafin kuma ta kalli Aylin dâin again â Aylin wannan wana irin turare kika saka da yawa haka , sannan baki duba kanki ba kafin ki fito nan wajan?â.
âKarewa kanta kallo Aylin tayi daga sama har âkasa , sannan ta kalli Anne alamar bata fahimci maganarta ba .
â Anneee..â
Da hannu Anne ta nuna mata ta juya , fuskarta babu yabo babu fallasa â Koma ki canza wannan kayan Aylin, idan kuma su kike san sawa sai dai
ki zauna a cikin gida, banda yawo haka with me around .â
â Anne normal dress ne fa , kinsan kuma sune kayan da nake so , banasan canzawa please Anne , beside a gida nake baâa waje ba fa .â
Kallanta Anne tayi kafin ta furta â Okay now maganar wa zaâajiâ.
âDan shiru Aylin tayi tana sake saâke cikin zuciya , kafin ta furta â Bari naje na canzaâ. Da haka ta juya ta bar wajan zuwa dâakinta.
Tana zuwa akan gadonta ta fadâi tana fadâin â why why whyâŠâ cikin huci alamar ta âkulu, siririn tsaki taja, ta shiga No stress Zone dâin su ta soma hira da friends dâinta , duka bata dadâe ba na mintuna 30 tayi , ta tashi ta kunne dâakinta ta saka lock .
Cikin wardrobe dâin kayanta ta fito da wata jaka, magunguna ne da yawa a ciki da kuma Allurai, haka ta zari allurar nan ta kama jijiyarta ta tsiya , sannan ya sha wani tablet , da kuma wani syrup . Cikin sauri ta samu abu ta dâaure hannayenta biyu.
Baâai cikakken mintuna biyu ba Aylin tayi mugun fita daga hayyacinta, idan wani yazo yaganta a yadda take sai yayi tunanin mutuwa za tayi sabida yadda tayi mugun shidâewa nunfashinta ma kadâan kadâan yake fitowa, sabida fita hayyaci da tayi , har wani birgima take , bata kallan gabanta , duk inda ta fadâa haka take birgima a wajan nan .
A wannan yanayin da Aylin take ciki zaka gane ba lafiya dâaya take a wannan lokacin .
Daga nunfashinta ya dawo zai sake jikicewa , jikinta yayi mugun rauni, kamar wacce aka cire wa duka âkarfin jikinta aka mayar zuwa kasala, haka take dawo.
Har jikin gefen gado taso riâke wa sabida ta dâan samu balance but still ta sake fadâuwa âkasa.
Wayarta da take kan gado sai faman vibrating take , message dâin No stress Zone ta ko ina shigowa yake babu tsayawa .
Sai dai kuma ina Aylin bata san ma sunayi ba , a haka idanuwanta suka rufe ga baki dâaya , if not sabida jijiyar gefen kanta da take har bawa mutum sai yayi tunanin ko mutuwa tayi a wannan time dâin dan ko motsin kirki ba tayi ga wuyanta da ya dâan juya kadâan.
A lambu kuwa Anne batasan abunda yake faruwa ba , ya dadâe kuma a zaune a wajan tana kallan Nunu da take wasa , har zuwa wani lokaci , kafin ta dâauketa zuwa cikin gidan, tayi mata wanka itama tayi wanka ta canza kayan jikinta, ta dâauki keys suka fita daga gidan ita da NunuâŠ.
________ âKarfe 7:00pm na dare Ahmet ya dawo gida , sai faman miâkar da hannunsa yake alamar gajiya, time to time kuma yana dâan juyar da kansa , akan kujera ya zauna , yana fadâin â Ya Allahâ⊠a fili , yana wani lumshe idanuwansa na dâan sakenni kafin kuma ya sake budâewa yana âkarewa falon kallo .
Babu kowa and baiyi expecting ganin kowa ba a time dâin shiyasa ya wuce dâaki, shaf shaf yayi wanka, ya canza kayansa zuwa âkananan kaya marasa nauyi , sannan ya wuce kitchen .
Sai da ya saka apron tukunna ya soma fito da abubuwan da zai buâkata .
Roasted Herb Chicken ya somayı , sannan ya girka Almond Rice Pilaf , Roasted Potatoes and Vegetables , Fresh Strawberry Juice da kuma Turkish tea .
Duk shi yayi wadâan nan girkunan kamar wani professional chef , kuma kwata kwata bai âbata kitchen dâin ba sabida wata macen ma ba zata koya masa tsafta ba .
Duk abunda ya âbata sai da ya wanke , ya saka abincin a warmers ya bar su a kitchen dâin, juice dâin kuma ya saka a fridge , ko dâaya babu abunda ya zuba ya fito dag kitchen dâin.
Lokacin 10 saura , haka ya zauna a falo yana dâan danne dannensa.
Jin an taâba âkofa ya mayar da kallansa kan âkofar.
Bell dâaya aka danna ya miâke ya nufi door dâin , bai tsaya wani âbata lokaci ba ya budâe âkofa .
Nunu ce da Anne .
Tana ganin Ahmet ta âkwalla wani âkara mai hadâe da dariya tana fadâin â MemetâŠâ
Shima dariyan yayi kafâin ya dâauketa â Wannan ihu haka Nunu so kike ki cirewa Anne dâita kunne ?â
Nunu kam ko kulashi ba tayi ba sabida yadda ta âkara ruâkunâkumeshi kamar ance mata zaâa âkwace mata shi.
Hanya ya bawa Anne , ta shigo kafin ya sakar mata kiss a goshi.
â MemetâŠâ Nunu ta kira sunansa cikin siririn muryarta na yara, alamar kuma ta gaji daga yanayin maganarta.
â Naam , Nunu.â Ya bata amsa yana kallanta.
âYan mitsi mitsin hannunta ta saka guda biyu ta kama cheeks dâinsa , har sai da yayi saurin cire hannun nata sabida ya dâan ji zafi duk da âkananan hannunta amma haka ta cakumi fuskansa.
â Nunu waya koya miki kalar wannan muguntar kuma ?â.
â Idan ka tsaya biyewa Nunu zaku kwana a tsaye , rabu da ita kawai .
Ya nagan ka kai dâaya , ina AylinâŠâ
Kallan Anne yayi cikin confuse dan baiyi tunanin tana cikin gidan ba shiyasa ya kuma cewa Anne â Aylin?âŠâ
â Yes Aylin ko ta fita ne?â Itama Anne ta tanbayesa.
â Anne kinsan halin âyar ki , ni tunda na dawo ban ganta ba kuma banga giftawar taba , so may be she went out .
Yanzu ba maganar Aylin ba , Anne kije kiyi wanka muci abinci , already na girka ke kawai yake jira .â
â Jazakallah AbiâŠâ cewar Anne kafin ta kalli Nunu â Nunu zo muje a canza kaya.â
â Anne yawo zani da Memet..â
â No Nunu sai anci abinci tukunna, maza kije Anne tayi miki wanka , muci abinci sai muje yawo kinji?.â
Ba musu ta dâaga masa kai ita kuma Anne ta dâauketa suka wuce upstairs .
Shi kuma ya wuce ya fito da warmers dâin ya gyara dinning yayi serving komai yadda yana zuwa ci kawai zaâayi.
Basu wani dâauki dogon time ba suka sakko sanye da wasu kayan, Nunu sai lumshe ido yake , kana ganinta kasan ta soma jin bacci shiyasa Ahmet ya soma serving dâinta abincin.
Infact a baki ya dinga bata , har sai da ta âkoshi tukunna ya soma ci.
Kafin ya gama cin nasa har tayi bacci akan kujera, da ido Anne ta nuna masa ita, murmushi kawai yayi ya dâauketa , zuwa dâakin Anne .
Anan ya kwantar da ita ya fito ita kuma Anne ta zauna a falo tana jiran fitowarsa .
Daga gefenta ya zauna yana dâan kallanta .
â Anne ya aiki kuma ? Fatan komai yana tafiya dai dai .â
â Fine Abi Alhamdulillah.. Amma Abi Aylin kwata kwata bata bar maka message ba ta fadâa maka inda zata ?â.
â Kai Anne kin fiya sa damuwa a rai . Aylin yarinya ce ne wai , ba yau ta soma fita bata fadâa ba , so why yanzu kuma kike so ki sakawa kanki damuwa ?â
â Ba haka bane Abi , I donât know kawai ina jin wani feelings daban , bansan ma wana iriâŠâ bata âkarasa ba Ahmet yayi saurin tsayar da ita.
â Anne please banasan ki soma sawa kanki damuwa akan wata Aylin.
Duk Inda yake ma zata dawo ai ba âkaramar yarinya bace , beside any moment ta ga dama fita take , zan zauna a falo har ta dawo , yanzu ki wuce dâaki ki dâan samu huku kema dare yayi , kuma kina tashi da wuri âŠâ
âAhmetâŠ.â
â Trust me Anne babu komai , gwanda kije wana Nunu kinsan motsi kadâan tayi taga babu kowa shikenan baccin nata zai wartsake, donât worry about Aylin da safe zaki gantaâŠâ
Ajiyar zuciya Anne tayi a hankali kafin ta furta â Shikenan Abi , sai da safe .â
â Sai da safeâŠâshima ya bata amsa , da haka ta wuce bedroom dâinta . Shi kuma sai da ya dâauki 30 minutes ya tabbatar da Anne ba zata fito ba shima ya wuce dâakinsa abinsa , wanka kawai yayi ya kwanta bacci abinsa .
_________________
ABUJAâŠ..
Kwanaki suna ta tafiya , yau ya kasance Saturday , kuma kusan kwana biyar kenan da zuwan Mimi part dâin Moh, daga lokacin bata sake saka shi a cikin idanuwanta ba , kuma ba saban abu bane a wajanta , dan ita har ta manta ma da babinsa harkar gabanta kawai take yi.
A cikin biyar dâin nan Mimi bata sake saka Ameerah a cikin idanuwanta ba , sai dai suna yawan waya da Zarah kasantuwar tun zuwa da sukai bawa Uncle Bashir hakuri , Zarah ta tafi gidan Aunty dâinta ( âkanwar Mamanta) , taso Mimi ta bita , amma Mimi taâki yadda shiyasa ta tafi ita kadâai .
âKarfe 3:00pm Mimi tana zaune a dâan balcony dâin dâakinta , me dâauke da 2 chairs haka da dâan table dâin su mai kyau , ta saka kayan zaâki sosai a gabanta tana sha , har da su ice cream, fruit , kayan tarkace na ciye ciye dai da yawaâŠ
Akwai kuma system akan table dâin sai dai ba dannawa take ba , tananan a ajje , wayar hannunta take dannawa tana kallan Mini series dâin nan na Ai.
Series dâin sosai yake mata dadâi at the same time kuma yana enjoying kanta da kayan zaâkin da suke gabanta.
Sau biyu ana knocking âkofar dâakinta hankalinta yana kan kallon da take batasan anayi ba .
Ana ukun ne aka budâe âkofar.
âKarar budâeta ne ya janyo hankalin Mimi zuwa cikin dâakin.
Ameerah ce ta shigo sanye da material tayi rolling da kayan material dâin jikinta , babu laifi ta dâanyi kyau abunta , kallanta Mimi tayi , ta cigaba da kallanta , ita kuma Ameerah ta âkaraso balcony dâin tana sallama .
Babu musu Mimi ta amsa mata sallamar tata amma kuma bata kuma ce mata komai ba daga wannan sallamar.
Ganin haka yasa Ameerah ta samu waje ta zauna tana dâaukar dâaya daga cikin sweet da suke wajan , kafin ta kalli Mimi â Yan mata babu magana ne?â.
Ita Mimi tsayawa kallan mamaki ma ta somayı mata kafin daga bisani ta furta abunda yake cikin zuciyarta â Ameerah anya baki da aljanu kuwa ?â.
â Me kika gani?â Itama Ameerah ta tanbayeta.
âNaga lamuran naki ne kamar da shafan aljanu, yau aganki normal gobe kuma a ganki ba dai dai ba , imagine rashin mutumcin da kikai mana last week daga tanbayar ki Uncle Bashir , but here youâre now , talking nicely kamar bake ba.â
â Hmm Mimi kenan , ba zaki gane ba , da kinsan yadda nake ji a zuciyana da baki mun wannan maganar ba⊠anyways am sorry if i hurt you in any wayâŠâ
â Haka ake bada haâkuri Ameerah?â
â Toh so kike na tsugunna âkasa ina taâba kafafuwanki ina cewa Aunty Mimi kafin ki haâkuraâŠâ
Gajeran tsaki Mimi tayi â You will never change Ameerah .â
â Naji dâin. By the way nikam are you free now?â.
âYes why ?â Mimi ta amsa mata .
â Cake nake so nayi, will you help me a little bit ? Kinsan ba wani sosai na iya saba .â
âKice abunda ya kawo ki kenan bawai kinzo neman yafiya ba .â
â Kai Mimi kinfiya janyo magana wallahi dagaske har zuciyata nake baki wannan haâkurin, just atimes ki dâan dinga mun uzuri , cause you will never understand me âŠ.â
âDan shiru Mimi tayi , sai kuma daga bisani ta furta â Yaushe kike so muyi cake dâin?â.
Da sauri Ameerah ta bata amsa da â Yanzu âŠâ
Yanzun ma sai da ta âkarayin shiru kamar me tunani sai kuma ta furta â Okay letâs go , but help me tidy this place ..â
Babu musu Ameerah ta soma ta yata suka kwashe duka junks dâin, wajan ya dawo normal kamar yadda akesan waje me tsafta ya kasance .
Lokacin da suka sakko âkasa already Mamy tana main Falour kuma zuwan Ameerah sai da ta soma hadâuwa da Mamyn a falo , kafin tazo bedroom dâin Mimin.
Kallan su Mamy tayi cikin so ta furta â âYan mata na sai kuma ina?â.
â Mamy zan taya Ameerah aiki ne a part dâin su ..âcewar Mimi.
Kanta Mamy ta jinjina mata alamar toh , su kuma suka fita zuwa part dâin su Ameerahn.
Lokacin da suka shiga kitchen already Ameerah ta fito da komai da suke buâkata, haka suka zauna hadâa cake dâin su suna hira kamar basu ne kwanaki suke saâinsa a tsakanin su ba .
Sunyi cakes sosai, dan bayan cup cake sai da sukai slice , Ameerah ta hadâa whipping cream, ita kuma Mimi ta hadâa chocolate cream da suke so.
Sun dâan jira sosai a kitchen , kafin su ka gama suka koma falon su Ameerah sabida cake dâin ya dâan sha iskaâŠ.
â Wayyo âkafataâŠ.â Ameerah ta fadâa da dâan âkarfi, ita dai Mimi sauke ajiyar zuciya kawai take dan ita ma dâin ta gaji ba âkarya , a hankali ta furta â Nima wallahi na gaji.â
Gyara zamanta Ameerah tayi sosai tana kallan Mimi â Amma kinsan Allah , cake dâinnan yayi dadâi kawai wahalarsa ne bashi da dadâi, duk jikinka ya bi ya gaji, ba gaira babu daliliâŠâ
â kinji bayana kuwa Ameerah? Ga baki dâaya ya âkame wallahi⊠kinsanâŠ.â Shiru Mimi tayi daga abunda take san cewa sabida notification dâin da ya shigo wayarta , bata ma tsaya karanta abunda yake cikin notification dâin ba ta kalli Ameerah â Ameerah kinyi sallah? Almost to 6â
A hankali Ameerah girgiza mata kai tana dâan sauke wani numfashi â Wallahi naga time Mimi , jikina ne sai naji duk na kasa, duk lokacin dana yunâkura sai naji bana jin dadâin jikina.â
â Ameerah sallar? Baki da lafiya ne?â
â No lafiya na âkalau , zauna bari naje nayi sallar ko kuma may be kafin na idar ki duba cake dâin, kinji? Am coming backâŠâ
â Okayâ Kawai Mimi tace mata, ita kuma cikin sauri ta wuce bedroom nata .
Sai da Mimi ta sake âkara mintuna kusan guda biyu tukunna ta wuce kitchen dâin, already daman sunyi packing cakes dâin yadda suke so, Abubuwa kadâan kawai Mimi ta dâan gyara ta kuma gyara kitchen dâin tsaf tsaf ⊠a haka Ameerah tazo ta sameta.
â Yan mata tunda an gama cake bari na wuce dâaki na make i rest âŠâ
â Ba zaki zauna muci cake dâin ba?â.
â Wallahi Ameerah ga baki dâaya âkamshin baking dâin nan ya riga ya gama shigar mun ciki, shiyasa bazan ma iya ci yanzu ba, ki bari zuwa gobe sai naci.â
â To zaki tafi dasu ne ko kuma na ajje mana ? Dan nima sai zuwa goben zan ci yanzu bana jin cin shi.â
â Yes ki ajje mana a wajan ki, i have to goooooo.â
â Okay kai wa Mamy wannan..â Ameerah ta dâauko wani babban cake tana miâkawa Mimin.
Babu musu Mimi ta amsa, ba zato ba tsammani taji Ameerah tayi hugging dâinta tana sauke nunfashi kadâan â Nagode sosai MimiâŠ.â
â Youâre welcome dear âŠâ
Cewar Mimi , kafin ta fito daga kitchen dâin zata fita , sai kuma ga Uncle Bashir yana shigowa , ganin Ameerah da Mimi sun fito tare da ga kitchen murmushinsa ya fa dâadâa tare suka gaishesa da Ameerah , ya kuma washe musu baki sosai kamar bashi ba . â Aâahhhh yau manya ne a sashen mu?â Yayi maganar yana kallan MimiâŠ..
â Abba cake mukai nida ita..â cewar Ameerah âŠ
Irin daga yanayin yadda ya furta â Dagske âŠâ zakaji muryarsa irin so excited dâin nan , dan har ita Mimi sai da ta dâan kallesa, hakan yasa ya dâanyi gyara murya kadâan yana fadâin â Ya dace hakan, ya kamata ku dinga hadâa kanku a matsayin ku na âyan uwaâŠ.â Da haka yayi wucewarsa .
Ita kuma Mimi ta kalli Ameerah ta dâanyi mata waving alamar bye bye , kafin ta fita daga sashen zuwa nasuâŠ
Tana zuwa direct dâakin Mamy taje ,tana zaune akan kujera tana danna waya.
Shigowar Mimi ne ya dakatar da ita da abunda yake , ta kalleta tana amsa mata sallamar da take mata .
â âYan mata na sai yanzu?â.
âDan shagwaâbe fuska Mimi tayi tana zama a gefen Mamyn â Mamy wallahi na gaji sosai âŠâ
âDuka hour dâin ki nawa da zaki ce kin gaji? Idan an miki aure haka zaki dinga wannan lallacin?â
â Kai Mamy ki bari lokacin auren yazo mana amma yanzu ki barni na huta , ga cake dâin ki ma inji AmeerahâŠâ
â Har dani?â.
â Yes Mamy bari naje na dâan watsa ruwa , jikina wani yam yam yake munâŠâ da haka ta miâke ta fita daga dâakin Mamy zuwa nata .
Tana zuwa wanka ta somayi da ruwan dâumi, ta dadâe sosai kuma a cikin toilet dâin kafin ta fito ta shirya cikin doguwar riga mara nauyi sosai, akwai kettle âkara daman a dâakin , ta hadâa tea me kauri tasha, nan da nan ta soma hamma , gashi daman ba sallah za tayi ba , Ac kawai ta âkara ta kulle ko ina dâakin ya zama dummy , kafin bacci ya dâauketa me dadâin gaskeâŠâŠ..
*____
Bata wani jima sosai tana bacci ba duka baccin hour 2 tayi , aka soma knocking dâakin.
Bata budâe idanuwanta ba sabida baccin da take yana mata dadâi sosai .
Sake knocking âkofar akai , nan ma babu feedback Mimi bata budâe idanuwanta.
A hankali taka budâe âkofar dâakin .
Mamy tsaye , jikinta sanye da hijab , ga kuma carbi a hannunta da take dâan ja .
Ganin yadda dâakin yayi dubu sosai , taje ta kunna hasken dâakin.
Nan da nan idanuwanta suka sauka akan Mimi da ta âkudun dune jikinta tana bacci.
Haâbarta ta riâke tana fadâin â Lalle an gaishe ki MimiâŠâ
Bakın gadon ta âkaraso tana ambatan sunanta â Mimi ! Mimi ! Mimi âŠâ
Sai a lokacin ta furta â UhmmâŠâ
â Oya tashi maza maza an gama abinci, ki sakko kuma ki wanke face dâin nan naki, karki bari mu zaman jirankiâŠâ
Cikin magagin baccin Mimi ta furta â No Mamy kuci abincin ku bana jin yunwa sabida nasha tea kafin na kwantaâŠâ
â Shi tea dâin abinci ne da zai riâke miki ciki? Common my friend minti goma na baki ki sakko, idan kuma kika tsaya âbata mun lokaci zaki hadâu dani.â Da haka Mamy ta bar dâakinâŠ
Mimi sai da ta kwashe mintuna uku a kwance ta kasa tashi , da âkyar ta samu ta yunâkura ta wuce toilet , bayan ta tsaftace jikinta, turare kawai ta fesa shima kuma kadâan.
Bata dâauki wayanta ba ta wuce falon MamyâŠ.
Bakinta dâauke da sallama .
Dukan su suka amsa mata , daga Mamy sai Baffa sai kuma Aunty Shukura da Yaya Saleem âŠâ
â An gama baccin ?â Baffa ya tanbaye ta , yana nuna mata kusa dashi.
Babu musu ta zauna tana dâan naike masa â Aa Baffa ban gama ba Mamy ce ta koroni wallahi.â
Kallan Mamy , Baffa yayi ganin yadda yayi cikin cikin kamar batasan dasu a wajan ba yasashi ya girgiza kai kawai yana murmushi.
Itama Aunty Shukura da Uncle Saleem dâin duk murmushi sukai dan babu mai ja da maganar Mamy.
Da haka suka wuce dinning, Mamy da Aunty Shukura sukai serving dâin su dinner , babu wanda yayi magana kuma tunda aka soma cin abinci, dan wannan alâada ne basa magana kuma suna cin abinci at the same time , sai dai ayi guda dâaya , idan an gama ayı dâaya .
Basu dadâe akan dinning dâin ba suka koma falo ga baki dâayan su , su suna hira .
Mamy da Baffa , Aunty Shukura da Uncle Saleem, ita kuma ta salallaâba ta fice daga falon kuma duk sun ganta yi sukai kamar basu ganta ba .
Tana shiga dâakinta yau ko wayar ma bata dâauka ba ta dâauki system ta haye kan gado, yau Korea take san kalla.
Kuma shi dâin ta saka , tana kallo abunta , har sai da taga lokaci yaja sosai tukunna ta kashe ta kwanta sabida dare yayi sosai a time dâinâŠ.
âKarfe 3 na dare gari yayi shiru sosai, banda dâan sanyi sanyin yanayi babu abunda yake tashi daga compound dâin gidan , sai dai hasken fitilu a wannan karan ya dâan ragu ba kamar yadda ake kunnasu tar tar ba .
Daga can jikin bishiyar dabino da yake bayan compound dâin gidan ya soma ko kuma ya soma takowa .
Baâa ganin ko wane ne balantana kuma ya gane jinsinsa, hankalin kowa bazai zo wajan ba sabida daga bayan compound dâin gidan nen wajan store rooms kuma duk gidan wajan ya fi komai rashin haske .
Akwai yalwar jiyawa da ta dâa kwanta a wajen, da kuma sauran bishiyu bayan ta dabino da suke wajan.
Kayan jikinsa ko jikinta baâki ne daga sama har âkasa , kuma bawai matsats tsuba, kamar suffar hijab ko kuma babban mayafi da aka yafa âkatoto a wajan.
Harta takalmi irin cover shoe dâin nan ne baâki shima .
Da sauri sauri yake tafiya ko take tafiya a hanyar wajan, tana/ yana tafiya , yana/tana dâan warge wargen hanya har yazo âkarshen bishiyun da suke wajan.
A wannan time dâin duk wanda yazo wajan nan ba âkaramun abun girgiza wa bane, dan ko da rana ba wajan zuwa bane sabida ba anfani ake da wajan sosai ba balantana kuma yanzu da tsakar dare lokacin da mafi yawanci ake bacci dan hutawa rai.
Can bayan store room mutumin ko matar ya tsaya, hannunsa ko hannunta akwai wata baâkar leda da ta riâko shi / ko ya riâkota a cikin abunda ya lullubewa jikinsa .
Ahankali mutumin ya tsugunna, hannunsa da ya dâan fito dashi akwai baâkar safa ajiki doguwa har zuwa gwiwar hannu.
Ledar jikinta ya ajje a âkasa ya budâe abunda yake ciki.
Tarwadâa ne manya manya guda biyu a ciki jikin su an dâadâdâaure su tamau da wani farin zare , bakın su kuwa an âbulasu da wasu allurai haka .
Sai da mutumin nan ya soma haâka rami âkarami a wajan, ya saka kifi guda dâaya tare da wasu allurar da suke cikin baâkin ruwa a roba , ya dâauko guduma da yake cikin leda ya soma caccakawa a jikin kifin nan , da ransa da komai, kifin sai wani irin abu yake har ya mutu, dâayan ma desame thing abunda akai musu kenan, sannan aka âkara hadâa rami sosai aka binne su a ciki a rufe ruf, aka kuma gyagyara kamar baâayi komai a wajan ba dan koma wanene yayi wannan abun sai da ya shirya , bai bar ko ledar kifin ba haka ya hadâa da ita ya bar wajan, bayan ya gyara komai a muhallinsa.
WASHE GARI âŠâŠ
Da wuri Mimi ta tashi daga bacci dan sosai tayi bacci jiyan, yanzu ma sai 8 ta tashi.
Sai da ta gyara dâakin ta wanke toilet tukunna tayi wanka zuwa doguwar fitted gown dâin atampa read colour , ta dâaura dâan kwalin kanta zuwa irin V shape dâin nan ana ganin gashin kanta kadâan, dâaurin yayi mata kyau kuma ya fito da kyan fuskarta sosai, golden eyes dâinta sun fito tar dashi , haka kawai taji tana san saka zoban hancinta, a tunaninta tunda a kwanakin nan bata ga Moh ba , toh yau dâin ma ba ganinsa zatai ba dama kuma shi kadâai ne ya hanata sakawa idan yananan.
Ta dâanyi wa bakinta lining kadâan, ta saka lip balm âŠ
Mimi tayi kyau sosai , dâinkin kuma da tayi ya sake fitowa da kyakkyawar surar jikinta, har da dâan âkaramun âkashin wuyanta shima da ya fito sosaiâŠ
Gashi kuma ta saka âyar âkaramar sarâkar chain, dâan kunnenta ma dâan karami ne amma yadda tayi balaâin kyau xaka dâauka gasar zata shiga ko kuma irin fitan nan za tayi mai mahimmanci , ga kuma uwa uba turaran da ta saka sai faman tashin âkamshi yake .
As usual taje ta gaishe da su Mamy ta fito daga sashen su, taga kuma su Uncle Saleem suma kuma sun dâan tattaâba kira kafin ta fito compound dâin gidan.
Har yanzu akwai ragowar iskar safiya da take dâan kadâawa kadâan kadâan a compound dâin gidan .
Bawai tafiya take ba , no tana tsaye ne a dai dai saitin sashin su, tana kallan movement dâin masu aiki da kuma wadâan da suke wucewaâŠ
Ta dâauki mintuna kamar 30 haka sai ta koma falon âkasa ta zauna ita kadâai, har ta shiga game tanayi, a haka Ameerah tazo ta tarar da ita , hannunta dâauke da wani âkaramun packâŠ
Kallanta Mimi tayi, kamar yadda Ameerah itama take kallanta .
Tana zuwa ta miâka mata , daman kuma ga spoon akai,babu musu Mimi ta amsa ta budâe cake dâin su ne da sukai najiya , Mimi har da sauke dâan ajiyar zuciyar relief kadâan dan tun dâazu take sake saâken me zataci da safen nan.
Spoon dâin farko ta soma testing kafin ta kalli Ameerah â Amma yayi dadâi fa banyi tunanin zanyi dadâi har haka ba .â
â Yeah nima da nayi testing dâinsa I wasnât expecting that , daman shi nazo kawo miki, ina zauri akwai abunda zanyi see you later âŠ.â
â Byeeee âŠâ cewar Mimi ganin har ta juya , ita kuma sai ta cigaba da cin cake dâinta .
Ko rabi bata ma yi ba taji muryar Zarah ta dâan âkwalla mata daga bakın âkofa⊠â BestyyyyyyyâŠâ
Cikin sauri Mimi ta kalli âkofa ganin Zarah ce kuwa da gaske .
Babu âbata lokaci sukai hugging dâin juna â Nayi missing dâinki Mimi, tun jiya nace zan dawo nayi miki suprise amma look ban ma dawo ba sai yanzuâŠ. Allah nayi missing dâin kiâŠ.â
â Yeah nima nayi missing dâinki Zarah ya hanyaâŠ. Wai tun yaushe ma kika dawo ?â.
â Ban jima da dawowa ba , kaya na kawai na ajje na taho butâŠâ sai Zarah ta kalli Mimi..
â But what ?â Itama Mimi ta jefa mata question ganin tana binta da kallo kamar me san tanbayan abu.
â Naga Ameerah ta fito daga part dâin ku , ko wajan Mamy tazo?.â
â No waje na tazo ta kawo mun cake dâina ne âŠâ
Cikin disbelief Zarah ta furta â Cake kuma? Kuma Ameerah ce ta kawo miki? Like ban gane ba , daga tafiya yaushe kuka shirya har ta soma kawo miki cake?.â
â Daman tun da ni ai bana gaba da ita and you know that, wani lokaci halinta ne banaso , shiyasa muke yawan Samun misunderstanding , but yeah she apologized babu buâkatar cigaba da faman daman tun farko itace take fadâa dani bawai nice nake fadâa da ita ba and yanzu da ta dawo dai dai babu buâkatar tasar da maganar da ya wuce kinsan halina .â
â OhhhhâŠâ shine kawai abunda Zarah tace , shiyasa Mimi ta kalleta sosai tana sake maimaita abunda Zarahn tace â Ohhh? Shine kadâai abunda zaki ce?â.
â Nop abun ne yazo mun unexpected but itâs fine , tunda ta baki haâkuri âŠ.
Bari na koma dâaki nayi wanka kinga ko zama banyi ba nasan Momy na jira na , we will talk later okay?â.
â Okay âŠ.â Itama Mimi ta bata amsa , tana komawa kan kujera , while ita kuma Zarah ta fita zuwa nasu part dâin.
âKarfe 1:30pm Uncle Abba ya shigo sashen su Mimi, yana ganin Mimi ya sake fadâadâa murmushinsa â Ah ah yau kuma kece a falo? Gaskiya kam yau su Mamy sun ciri tuta a gidan nanâŠâ
â Haba Uncle Abba kai ma tsokana ta zata somayi kamar Uncle Saleem?â
â Hahahahh tuba nake Mimin Baffanta.
Toh me kike ke dâaya a falo ko yau kina da apointment dâin hadâuwa da wani ne , naga kinci wannan ado haka? Yau babu Zarah babu Ameerah kuma a wajan ki.â
â Uncle Abba ni babu wanda nake expecting kawai dai yau ina jin zaman falon ne , Ameerah tana part dâin su itama kuma haka Zarah bata dadâe da shigowa ba âŠâ
â Kedai fadâamun gaskiya ko Uncle Moh kike jira ?â.
Saura kadâan Mimi ta âkware da yawun bakinta, dan tanbayar tasa ma ya saka sai da zuciyarta ya buga sosai â Haba Uncle Abba please ka dena tsokanataâŠâ
âDan murmushi Uncle Abba yayi, kafin ya miâke tsaye , âna dena amma kije Moh na part dâinsa yanzu , ni fita zanyi da na raka kiâŠâ
A dâan tsorace Mimi ta kallesa â Uncle Abba ni kuma ? Ko wani abun nayi masa?..â
âKo dâaya Mimi ki daiyi sauri kinga dai jiran ki yake , kar ki âbata masa time ba zaku kwashe da kyau ba .
Infact tashi mu tafi tare , ke sai ki tafi part dâin nasa, ni kuma sai na fitaâŠâ
â Uncle Abba bari na canza kaya na âŠâ
â Inyee kwalliya zakiyi?â
Da sauri Mimi ta furta â No âŠâ
Hakan yasa yace â Oya toh taso mu tafi yanzu kar ma kice zaki koma sama let go.â
Batasan yin musu dashi shiyasa ta miâke tsaye da wayarta a hannu, saura kadâan ta hadâe tafiyarta, haka kawai take jin mixed feeeling a tattare da ita .
Kusan jerawa sukai tare Uncle Abba sai da ya rakota har zuwa part dâin amma bai shiga ba ya koma , ita kuma finger print dâinta ta saka âkofar ta budâe , tafin hannunta har rawa yake mata, ita kanta batasan dalilin hakan ba .
Babu kowa a falo as always , falon so dummy babu haske sai sanyi da kuma âkamshin turarensa.
Akan kujera ta zauna , tsawan mintuna biyu, sai taji zaman har ya gundure ta , sai ta shiga kitchen ta dâauko ruwa , shima kuma ta budâe za tasha taji kuma bata shaâawar âkara shan ruwan.
Falo ta sake dawowa , ganin bai sakko ba kuma kar taje ta sake wani lefi, ta yi shahada kawai ta hau Ćamansa cikin sandâa kamar wata mara gaskiya , har zuwa falon sama .
Falon sama yafi na âkasa hadâuwa nesa ba kusa ba sannan kwata kwata shima babu wani tarkace a cikinsa amma fa dukiya ta girgiza a cikinsa , sai dai muce Masha Allah .
Yanzu kam a falon saman ta zauna , tafi mintuna biyar shima bai fito ba , har ta kasa natsuwa tayi âkoâkarin dubawa yananan ko bayanan, nan dâin ma cikin sandâa take , kamar irin wacce bata so aji takun âkafarta ko asan da ita a waje ga baki dâaya , gashi har time dâin jikinta bai dena mata rawa ba , mixed feeling da take ji bai dena ba .
Sai da ta taâba handle dâin one of the room kamar zata budâe sai kuma tayi sauri ta fasa , ta jima sosai tana tunanin abunda za tayi, sai taji an dâan taâba handle dâin, kafin tayi wani âkwaâkwâkwaran motsi aka budâe âkofar ga baki dâaya .
Wani âkamshi me dadâi ya doki hancinta, irin âkamshin da ta dadâe bata ji saba, sai da ta sauke ajiyar a hankali kafin ta dâaga idanuwanta zuwa saitin âkofar da aka budâe.
Babu shiri ta sauke idanuwanta sabida jikinta da ya dâan soma rawa .
âCome inâŠ.â Ta ji saukar muryarsa cikin husky , cold and scary voice nashiâŠ
Irin muryar da babu wanda ya isa yayi musu akai.
Idanuwanta suna âkasa ta bisa zuwa dâakin..
Daga can tsakiyar dâakin ta dakata tana dâan wasa da hannunta .
Dogon wando ne a jikinsa baâki, sai baâkar singlet da ta kama jikinsa, duka muscles dâinsa sun fito rudâu rudâu, cikin cikakkiyar mazan taka .
â Come here âŠâ taji muryarsa kamar kiftawar iska sabida yadda yayi maganar ciki ciki.
Hadâiye yawan bakinta Mimi tayi da âkyar , batasan me yasa zuciyarta take bugawa haka ba tun lokacin da ta shigo part dâin , kuma ta kasa fassara ko wana irin feeling ne gashi ganin Moh da tayi ya âkara dagula mata hankalinta.
A hankali ta dâaga idanuwanta zuwa saitin da yake , ba ita yake kalla ba , shiyasa ta dâan samu damar âkarewa bayansa kallo.
Gani tayi ya âkara mata haske , gashin kansa kuma ya âkaru , kamar ba Uncle Moh dâin da ta sani ba , gashi yau harta da yanayin maganarsa sai taji ya canza mata, cikin sauri ta alaâkanta hakan da rashin ganinsa da batayi kwana biyu bane ya janyo take ganin hakan.
A hankali ta âkara takawa zuwa cikin dâakin, ya zamana gaf dâin da yake tsakanin su bashi da yawa sosai ⊠â Uncle Moh ⊠ga ganiâŠâ ta fadâa a hankali.
Baice mata komai ba kuma bai tanka mata ba , hakan yasa ta kuma fadâin â Uncle MohâŠâ batasan lokacin da ta shagwaâbe murya ba , tana jin muryarta yana dâan rawa kamar za tayi kuka .
Jiyowa yayi a hankali zuwa inda yake , sannan ya soma takowa wajan da take, hakan yasa itama ta dâan soma ja baya , tana dâan yarfe hannuwanta, dan gani tayi ga baki dâaya ya wani canza mata kamar bashi ba , yadda tasan shi kwata kwata sai taga saâbanin hakan yau, musamman idanuwansa kaifin su da take ji har ya wuce misaliâŠ.
Tsayawa yayi , yayi folding hannuwansa a âkirjinsa lokaci dâaya yana kallan yanayinta , sai kawai ya juya zuwa dâaya daga cikin kujerun da suke dâakin â Come here nowâŠâ ya fadâa a hankali.
Babu musu ta âkarasa gaban kujeran , sai ya dâanyi tapping hannunsa a gefen kujerar da yake , nan dâin ma babu musu ta zauna kamar yadda ya umarta . Wani karamun box ya dâauko ya budâe cikin sa irin first aid box dâin nan ne , a ciki har da su scissors âkaramı da sauran abubuwa da ake buâkata masu mahimmacin a cikin first aid dâin box dâin.
Da mamaki ta kallesa , batasan lokacin da bakinta ya furta â Uncle Moh, baka da lafiya ?â.
Baice mata komai ba yadâan dâaga gefen rigar , take a wajan wani bandage fari ya fito a wajan⊠batasan ya akai ba , sai kawai ta tsinci hannunta da kaiwa zuwa gefen cikinsa tana taâba wajan , tana manta wane ne a gabanta ga baki dâaya.
Kallanta yayi da idanuwansa, da suka narke sosai kamar mai jin bacci, yana kallan yadda take kallan ciwan nasa.
A hankali cikin âkasan maâkoshi ya furta â Canza mun..â
Babu musu ta dâaga masa kai, har sai da yanayin yadda ta amsa da wuri ya bashi mamaki sai dai yanayin fuskarsa bai canza ba daga kallan da yake mata..
âKara dâaga singlet dâin yayi sosai , 8 packs dâinsa yana fitowa sabida a dai dai nan wannan bandage dâin yake .
A maimaikon ta soma cire bandage dâin sai ta tsaya kallan bandage dâin dan bata ma san taya zaâai ta cire shiba.
Ya fahimci hakan, scissors ya samu ya dâan yanka bandage dâin jikin nasa , yadda zai mata hayar budâewa .
Kallansa tayi a karan farko , sai wani siririn hawaye ya sauka a kumatunta.
â Uncle Moh wa ya ji maka ciwoâŠ?â
Lumshe idanuwansa yayi , ya sake budâewa akanta , har lokacin bata dâauke idanuwanta ba akansa kamar wacce take jiran amsar da take son ji daga garesa.
Kallan bandage dâin yayi sannan ya kalleta , ganin taâki dena kallansa sai kawai ya dâauki hannunta zuwa kan bandage dâin , ita kuma a garin ta janye hannunta sai ta dâan ja da âkarfi , hakan yasa Moh ya lumshe idanuwansa, ita kuma tayi saurin saka ihu sabida jinin da taga ya soma fita daga jikinsa .
Hannu ta saka tana âkoâkarin tare bandage dâin ko jinin ya tsaya, shi kuma idanuwansa yana kanta , ganin batama kallansa , gashi kokari take ta shidâe daga jinin da taga yana fitowa ..
Hannu yasaka a dai dai âkugunta , ya janyo ta sosai zuwa jikinsa .
Hakan yasa ta dawo hayyacinta tana âkoâkarin âkwacewa amma kuma ya âKara riâkota yaâki bata ko wani damar da zata âkwace..
A dai dai saitin kunnan ya furta âwhy are you nervous?â Kamar me radâa .
Ita kuma sai taji wani irin shock a jikinta , tama rasa me zatayi, kamar ba Uncle Moh bane wannan, canza shi akai, da tace zatayi âkoâkarin kwacewa ta âkarfi sai ta fama masa ciwo hakan yasa ta fashe masa da kuka sosai, shi kuwa Moh a jikinsa sai ma kansa da ya dâora a kafadâun nata yana sauraran yadda take jero kukan.
_________________
To be continued⊠đ„
Aysha Galadima đ€đż
***
***