MISHAL

Page 22

by @ayshagaladima22

MISHAL



By AYSHA GALADIMAđŸ€đŸż
***


BOOK 1 
Page 22

Tana shiga part d’in su Zarah ta tarar da Momy tana waya . 

Momy bata kashe kiran ba, sai dai ta d’an saukar da wayar daga kunnanta kad’an. 

Kafin Mimi tace komai ta furta “ Tana d’akinta” cikin ‘katsan murya sannan ta mayar da wayar kunnanta . 

Mimi kuma kamar wayar da take mai mahimmanci ne sai kawai ta jinjina mata kanta , sannan da wuce saman da niyar idan ta sakko ‘kasan lokacin may be Mommyn ta gama wayar sai ta gaishe ta . 


Da ta shiga d’akin Zarah a ‘kudundune ta tarar da ita cikin blanket tana sha’kar bacci abunta , ga uban Ac da ta kunna ..

Remote d’in Ac Mimi ta soma d’auka sabida sanyin  da Ac yayi har yayi ‘ko’karin wuce misali .

Tana ragewa kuma ta soma yaye blanket d’in Zarah , tana fad’in “ Sai a tashi ai gari ya waye , ace har yanzu baki tashi daga bacci ba.  

Da alama dai jiya bakiyi bacci da wuri ba ko?”. Mimi ta ‘karasa maganar tana janye ga baki d’aya blanket d’in, hakan yasa Zarah taja ‘karamun tsaki ba tare da ta bud’e ido ba ta furta “ Dan Allah Mimi ki ‘kyale ni nayi bacci . Bacci nake ji
” ta kuma janyo blanket ta lullu’be. 

Ri’ko ’kugu Mimi tayi tana kallanta “ Yanzu dai ba zaki tashi ba kenan?”.

Daga cikin blanket d’in Zarah ta bata amsa “ Yes bazan tashi ba , in kin gama baccin ki ni yau ban gama ba , allow me to rest jorrrrr
.”

Kafad’a Mimi ta d’aga tana fad’in “ Fine ! Asha bacci lafiyaaa
.” Ta fito daga d’akin. 

Lokacin da ta sauka ‘kasa Mommy ta gama waya shiyasa ta gaisheta , cikin d’an mamaki Mommy ta furta “ Yau kuma tafiyar wuri za’ayi mana kamar muna korar ki?”.

“ No Mommy bacci take ne shiyasa na barta ta gama baccinta .”

“ Wana irin bacci kuma , har yanzu bata tashi ba bari naje na taso miki ita .”

“ A’a wallahi Mommy ki barshi ,daman nima akwai abunda zanyi yanzu ne , zanje na ‘karasa yanzu ! Sai anjima agaishe da Daddy.”

“ Tom shikenan Mimi , zan fad’a masa sa’kon ki kema in kin koma kice ina gaishe da su Mamy , kinji?”. 

“ Insha Allah zan fad’a musu
” da haka Mimi ta fito daga part d’in su Zarah ta koma part d’in. 

Sai da ta bud’e fridge ta d’auko wani fruit juice me sanyi da cup tukunna ta wuce d’aki, tazo zata shiga taga sai faman gyara , d’akin kusa da ita ake , baki kawai ta ta’be ta wuce nata bedroom d’in. 

_________________

‘Karfe 12:51pm aka soma kiran wayan Mimi, daman wayan na hannunta , even thought taga ba’kuwar number sai kawai ta d’aga . 

Tana fiki wacce taji tayi mata sallama ne yasa ta d’an kalli wayar , sai kuma ta mayar da wayar kunnata . 

“Aya ce” muryar Aya ta kuma dokan kunnanta . 

“ OhKay ?
.” Shine abunda Mimi tace , zata kashe kiran Aya da take d’ayan side d’in ta furta “ Ina cikin gidan mu, Moh Moh na kira ki, zaki nuna mun d’aki na , ina jiran ki 
.” Da turanci tayi magana tunda ba wai iya hausa tayi ba .

Yanzu ma “ Okay 
” Mimi tace , tana 
‘kara gyara gwanciyarta , kamar ba zata sauka ‘kasa ba , amma tsoranta kar taje Moh yana cikin gidan, kuma ya ga bata fito ba ya ‘bata mata rai , shiyasa kawai ta saka takalmi ta sakko ‘kasa .

Yau ma Shirt ne a jikinta da Jeans , tayi kyau sosai kamar kullum
.

Tana saukowa ta tarar da Aya a tsaye a cikin falon, tana sanye da Baggy cloth d’inta riga ba’ka da kuma wando ba’ki, sai P- cap da ta saka a kanta tunda gashin kanta a aske yake, da kuma silver d’in sar’ka da shima yake wuyanta , harta da shoe d’in ’kafarta ba’ki ne , banda kamanninta da yake na mata , shigarta ga baki d’aya ta maza ce


‘Dan ‘kara ta’be bakinta Mimi tayi kad’an , tana ‘karasowa ciki. 

Aya da take tsaye, ta sakar mata murmushi ta soma takowa inda “ Kinyi kyau sosai Mimi
”

“ Me yasa kike ya’ke, ai Uncle Moh d’in bayanan ki dena pretending
” cewar Mimi.

‘Dan waigawa Aya tayi taga da wani take magana sai taga babu kowa a falon iya su biyu ne kad’ai a ciki, ta nuna kanta da d’an ‘yatsa tana fad’in “ Pretending me ? You’re very stupid 
.” 

“ Hey wait ! Karki zo gidan mu kice zaki fad’a mun magana , ca akai zaki zo ki zauna damu ko? Ga gida nan ki zauna , kiyi abunda yake gaban ki, nima kuma zanyi nawa 
” cewar Mimi tana mata kallan sama da ‘kasa.

Lokaci d’aya dariyar Aya ta ‘bace ‘bat a fuskarta, kamar wacce batasan wani abu wai shi murmushi ba , ta nuna Mimi da d’an yatsa , in a serious turn da ita kanta Mimi sai da tayi mamaki da irin seriousness d’in da ta dawo lokaci d’aya . 

“ If not because you’re Mimi
 da bakinki ba zaki sake fad’a mun wannan maganar ba . Be careful”.

Sai kuma ta dawo normal Aya d’inta tana sakin murmushi a fuskarta bayan ta matso kusa da Mimin da take kallanta “ Na gaji nuna mun d’akin da zan zauna and yes karki damu , Moh Moh bayanan , amma duk da haka zan iya yin maganin ki a cikin gidan nan , be have your self My Little Mimi
”

“Who do you think you’re ? Da zaki zo gidan mu kice zaki fad’a mun maganar da kike so ? Wace ce ke ? Dan zaki zauna a nan ba hakan yake nufin , ko me kika ga dama zaki mun ba , better stay out of me , I told you
” cewar Mimi 
. 

Sai da ta gama fad’an abun da zata fad’a , tukunna Aya ta sakar mata murmushi, kamar ma bataji abunda Mimin ta fad’a ba . “ Show me my room
.” Shine abunda ta fad’a , kallanta Mimi tayi from head to toe , itama tana sakar mata nata murmushin, kafin ta d’auki wani number tayi dialing ana d’agawa ta furta “ Hauwa zo falo , ina jiran ki..” Sai ta kashe wayan. 

Daga nan babu wanda ya sake magana a cikin su, har tsawan mintuna uku da Hauwa kulu tazo . 

Tana zuwa taje wajan Mimi , cikin girmamawa ta furta “ Aunty gani.”

Murmushi Mimi tayi mata , kafin ta nuna mata Aya da take tsaye , da ido “ Nuna mata d’akin da kika gyara d’azu
.”

Sai kuma ta kalli Aya ido cikin ido, kafin ta ta’be bakinta “ Behave your self , idan kuma ba haka ba I will show you who is Mimi, ko wannan ya kawo ki bazai hanani yi miki abunda naga dama ba , Tomboy kawai
.” Ta juya zuwa d’akin ta da yake saman itama , haka ta bar Aya da sakin baki tana kallanta . 


Mimi tana shiga d’aki ta ja tsaki yafi sau biyu , ji take kamar ta sha’ko wuyan Aya “ Ni zatayi wa bara zana ? Hmmm lalle zan nuna miki who is Mimi
.”  Daganan ta cigaba da sabgar gabanta , har ta manta da wata wai ita Aya a cikin gidan . 



‘Karfe 3:10pm na yamma kiran Mamy ya shigo wayanta , har ta soma bacci ringing d’in ya tashe ta , ganin Mamy ce yasa ta d’aga call d’in. 

Tana d’agawa kafin tayi magana taji umarnin Mamy “ Zo nan Mimi” daga nan aka kashe wayar. 

Bin wayar tayi da mamaki , tana tunanin dalilin kiran Mamy irin haka, amma bata kawo komai a ranta ba ta saka takalmi ta sauko ‘kasa , dan ko d’akin da Aya ta sauka bata kalla ba . 

Tana shiga falon Mamy , tun a bakin ‘kofa ta tsaya , ganin Aya a zaune a falon suna hira da Mamy kamar irin sun dad’e da sanın juna. 

Kallan da Mamy kawai tayi mata yasa ta sha jinin jikinta, haka jiki ba kwari ta shiga falon tana fad’in “ Mamy sannu da dawowa bansan ai kin dawo ba .”

“ Dama taya za kisan na dawo sabida kin zama ishashiya
.”

“ Wallahi dagske nake miki Mamy bansan kin shigo ba..”

“ Naji ! Yanzu ni kad’ai kika gani a falon ?”.

Kallan Aya tayi sai kuma ta kalli Mamy dan dagaske bata gane abunda Mamyn take nufi ba .

“ Ke yanzu Mimi yaushe zaki’yi hankali , sarai kinsan da ba’kuwa a gidan zaki tafi ki barta , har da wucewa d’aki, ni zaki tozarta ?”.

Even though Aya bata fahimci maganar Mamy , ganin yadda lokaci d’aya Mimi ta d’an bata rai sai da tayi murmushi.

Ita kuwa Mamy ‘kara had’e fuska tayi , tayi maganar da turanci yadda Aya d’in zata gane abunda take fad’a . 

“ Tace tana so ta zagaya taga compound d’in gidan nan , nasan kuma babu abunda zakiyi yanzu, saura naji sa’banin abunda nace miki?”.

Yanzu ma ‘bata fuska Mimi tayi sosai tana kallan Mamy “ Haba Mamy, taya zaki ce mun ni zan rakata compound d’in, bata da ‘kafa ne ko kuma gasu Hauwa mana kice musu su raka
..” bata ma kai da ‘karasa zan canta ba Mamy ta mi’ke tsaye tana fad’in. 

“ Ni ai ban isa dake ba , bari naje na rakata da kai na , kinyi dai dai ai kin balaga, komai ma zaki iya fad’a mun yanzu.” 

Cikin sauri Mimi ta furta “ Wallahi ba haka nake nufi ba Mamy , da tazo baki ga yadd take wani ‘kafafa bane, dan Allah kiyi ha’kuri , wallahi zan rakata kinji Mamy
”

Ko kallan inda take Mamy ba tayi ba , ta kalli Aya da take kallan su ganin da turanci suke maganar kuma ta fahimci komai kawai magana ne ba tayi ba . 

Murmushi Mamy tayi mata , sannan ta furta “ Taso muje na nuna miki wajajan da kai na .” 

Babu musu Aya ta mi’ke bayan ta jefawa Mimi wani kallo da ita kad’ai tasan ma’anar kallanta , ita ta soma ficewa daga falon, Mimi zata ri’ko hannunta Mamy ta daka mata tsawa duk da ba sosai tayi tsawan ba amma sai da taja baya ganin ran Mamyn ya ‘bace sosai .

“ Idan kika kuskura kika kuma mun maganar zaki je sai na ‘balla ki a nan wajan, tunda ai yanzu na zama sa’arki , wasa da nake dake kike ganin ban isa da ke ba ko kuma kafad’un mu ya kai , ki fad’a mun abunda yazo bakin ki.

Zaki sani dani kike magana ai shashasha
”


Sunkuyar da kanta tayi ‘kasa , cikin jin haushin kanta ganin ran Mamy ya ‘baci ta furta “ Dan Allah kiyi ha’kuri Mamy.”

Mamy zata sake magana , Mimi tayi saurin fad’in “ Dan Allah kiyi ha’kuri Mamy.”

‘Dan kallanta Mamy tayi na wasu sakanni kafin ta d’an yi ‘kwafa “ Then wuce ki wuce kiyi abunda nace , idan kuma kuma zaki sake mun musu ne yanzu sai na tafi da kai na .”

“ A’a zanje Mamy
” da haka Mimi tayi saurin bin bayan Aya , sabida kar  Mamy ta canza shawaranta . 

Tana fitowa ta tarar da Aya a tsaye , kamar yadda take kallanta itama Aya kallanta tayi , babu yabo babu fallasa Mimi ta furta “ Let’s go.” Daga nan babu wanda yayi magana , har suka fito filin compound d’in gidan. 

Mimi sai faman danne zuciyarta take , tama rasa yadda za’ai tayi wa Aya , bayanin gidan su, gashi yanzu idan ta musa ran Mamy ne zai ‘kara ‘bace wa, hakan da Aya ta gani ne yasa ta d’anyi murmushi ta dafa kafad’anta , cikin sauri Mimi ta zare jikinta tana hararanta , Aya kuwa ko a jikinta ta furta “ Kwantar da hankalin ki , ba cinye ki zanyi ba , naga gidan naku yana da girma sosai , basai munyi nisa sosai ba , zaki iya fad’a mun su wane ne a cikin part d’in, ya ma isa haka .”

“ Wai me yasa kike san ki soma fara takura wa rayuwa ta ne ? Daga ganin ki jiya , ga baki d’aya kin bi kin shiga rayuwata , me kike nema ne ?”cewar Mimi.

“ Bana bu’katar komai daga gareki Mimi, nazo nan ne naga yadda kike rayuwa, kuma the more naga kinaso ki ya kice ni a rayuwar ki , ni kuma the more zan ‘kara shiga rayuwar ki , ko kina so ko bakya so Aya is part of your life .”


“ Akan wana dalili?” Cewar Mimi..

“ Sabida ina ‘kaunar ki magana , tunda nazo gidan nan kike tamun abu, if not because of your mother , na tabbata bazanyi magana haka da ke ba , kin bi ga baki d’aya kin takura kanki akan abun da bashi ba . 

Infact me nayi miki like wannan fushin dani? Sabida Moh Moh ko kuma sabida kin ture ni naji ciwo? Bani ya kamata naji haushi ba? Me yasa keçe kike yin ‘kananan attitude?.”

Ajiyar zuciya Mimi ta sauke a hankali , dan ita kanta batasan ma dalilin da yasa take wannan abubuwan ba , shiyasa ta sake furta “ Amma ai bansan kina wajan ba , taya zaki zo kiyi hugging d’ina ba tare da na sani ba , kina kira na wani Baby
”


“ Hahahha ba wannan ne dalili ba Mimi, har yanzu ke yarinya ce wannan zafin naki yayi , kuma na sake yadda ke nairon Moh Moh ce , sai naga kamar ga baki d’aya attitude Moh Moh a tattare da ke , kuma kinsan wana shawara zan baki” Aya tayi maganar cikin wasa kafin ta cigaba “ Karki d’auko halin Moh Moh , idan ba haka ba zaki sha wahala fa , sai ‘bata ranki kike sabida yace ki bada ha’kuri jiya ,nima lokacin da na ta’ba yin shigen laifin ki, lokacin ina asalin Aya d’ina very arrogant, nazo zanyi masa taurin kai , ga baki d’aya ya d’auke ni zuwa dustbin. Imagine ?.”

‘Dan murmushi ne ya kufcewa Mimi, ita kanta batasan murmushin zai zo ba , hakan da Aya ta gani yaßa ta d’an ja mata hanci kad’ai sai kace wata yarinyar ta furta “ Ko kefa , yanzu zaki faddad’amun wajajan ku?”. 

Kanta Mimi ta d’aga mata sai ta furta “ Part d’in mu, the next one kuma shine part d’in su Zarah , sai part d’in su Uncle Saleem, part d’in su Uncle Bashir , and then Uncle Moh
”Tana gama fad’in haka tayi shiru .

Kallan mamaki Aya tayi mata “ Haka ake bayanin waje Mimi? Taurin kanki yayi yawa , kamar ma kina so kifi Moh Moh taurin kai 
”

“ Meyasa kike ce masa Moh Moh?.” Cewar Mimi


“ Sabida ya saka mun Aya mana , shiyasa nima nake ce masa Moh Moh.” Cewar Aya. 

“ Toh me yasa kikazo gidan mu? Ko sabida Uncle Moh?”.

“ Meyasa zanzo sabida Moh Moh kuma ? Nazo nan ne sabida ke ba sabi dashi ba
. Tsaya tsaya ma, me kike tunani tukunna ? Kinsan ala’kata da Moh?”

Kanta Mimi ta girgiza mata alamar a’a.

Cikin jinjina kai Aya ta furta “ Daman ai nasan bazai fad’a miki ba , but ni zan fad’a miki, but for now akwai inda zani idan na dawo i will talk to you 
”

Zata juya Mimi tayi saurin fad’in “ Then meyasa kikazo nan sabida ni , bayan ban sanki ba ?.”


“ SABIDA NIDIN AUNTYN KICE
” shine abunda kawai Aya ta furta, yayi wucewarta zuwa ba’kar motar da take d’an nesa dasu kad’an
.

Bin hanyar da Aya tabi tayi da kallo , badan wani abu ba , sai dan rashin fahimtar inda maganar ta , ta dosa, ga baki d’aya sai taji kamar gizo ma kunnanta, yake mata ba shine abunda Aya d’in take fad’a bane , kamar wani abu ta fad’a wanda ba wannan kalmar ba . 

Zuciyarta ga baki d’aya ta’ki accepting abunda Aya ta fad’a dan bata gane wace Auntyn take magana ba , Aunty wace iriya? Sai dai hankalinta ga baki d’aya ya fi bata akan cewar ita d’in budurwar Moh ce shiyasa tace Aunty, kamar yadda Uncle Moh , yace ta dinga kiranta da Aunt Aya 


Bata da wanda zai bata wannan answer sai dai Ayar idan ta dawo, shiyasa Mimi ta wuce part d’in su Zarah kafin ta dawo. 

Tana shiga part d’in su ta tarar da Zarah da Ameerah suna hira, ga d’an malele da suka saka a gabansu suna sa, cikin mamaki Mimi ta furta “ Abun ‘yar san kai ne ? Yanzu zaku sha d’an malele babu wanda zai kira ni a cikin ku?”.

“ Meyasa zamu kira ki, bayan yanzu kamar bakyasan ana ta kura miki? Naga ko magana idan akai miki sai ki soma kakkaucewa bakyasan magana bakyasan magana. Ya kike so muyi dake ?”. Cewar Zarah tana kai spoon d’in d’an malele bakinta . 

“ Lalle ma Zarah , naga d’azu har zuwa nayi na tashe ki, kika ce mun bacci kike na ‘kyale ki,  har kina da bakin magana ma?”. 


“ Toh da nace bacci nake why not ba ki jira ni ba? Ni haka nake miki Besty naga ai ko baki tashi daga bacci ba , haka nake zama na zauna jiran ki amma ke dan nace ki ‘kyaleni sai ki wani tafi , sai nace ba Bestyn ki ba?” Ta ‘karasa maganar tana d’an kaiwa Mimi hararar wasa .


Itama ‘karamun tsaki Mimi takai na wasa tana hararar Zarah. 

Kallanta Ameerah tayi “ Mimi ki taho musha d’an malelen mana , na d’auko miki spoon?”. 


“ No Ameerah yau bana sha’awar sa wallahi.”

“ Kedai ko sabida abunda na fad’a ne? Amma kinsan dai wasa nake miki ko?”. Cewar Zarah.

“ Toh kice ma dagaske kike mana , kiga yadda zanyi rugu rugu dake ,kudai kusha d’an malelen ku.” Daga haka tayi shiru, Zarah har ta bud’e baki za tayi magana sai Ameerah ta d’an girgiza mata kanta alamar a’a hakan yasa Zarah tayi shiru, sai dai hankalinta ga baki d’aya yana kan friend d’in ta ganin kamar ta tafi dogon tunani.

Suna gama shan d’an malelen su, Zarah ta d’an fad’a jikinta tana dariya “ So now fad’a mun tunanin me kike haka? Tun d’azu kin wani zauna kin yi shiru kina faman tunani, tunanin me kike?”.

Ajiyar zuciya Mimi ta sauke kad’an , haka kawai ta tsinci kanta da girgiza musu kai alamar bakomai , sai kuma ta bud’e baki ta furta “ Babu komai fa, ji nayi kai na kamar yana mun ciwo.”

“ Mimi yana ciwo ko kamar yana ciwo?”. Cewar Ameerah .

“ May be ciwan dai yake , I don’t even know.”

“ Kinsha magani?” Sukai tanbayar kusan a tare . 

‘Dan kallansu tayi na few seconds sai kuma ta furta “ yes nasha , thank you guys .”


“ Yaushe kika sha maganin?” Zarah ta kuma tanbaya . 

‘Dan d’agowa Mimi tayi ta kalleta tana fad’in “ Zarah yaushe kika zama journalist ? Wannan tanbayar sai kace me yin interview ?”.

“ Toh ai naga ke d’ince dole sai da haka da bamu tanbaye ki ba , ai da ba zaki ta’ba fad’a mana ba .”

“hmmm” kawai Mimi tace.

Ita kuma Ameerah tana sake kallanta suka had’a ido sukai murmushi wa juna , sai ta mi’ke tsaye tana fad’in “ Bani naje part d’in mu nasan a kowa na time Mama zata iya nemana , take care of your self Mimi , Allah ya ‘kara sau’ki.”

“ Amin Ameerah , thank you dear .” Cewar Mimi , da haka Ameerah ta fita tana musu waving d’in hannu. 

Tana fita Zarah tayi saurin kallan Mimi “ Mimi wai me yake damun ki ne ? Ni na rasa me yake damun ki wallahi kwana biyu, kamar bakyasan fad’amun abu .

Ko akan number d’in nan ne kike ta mun kauce kauce bayan ma na ha’kura da bincikar number yanzu tunda kince bakyaso , kuma nace ki fad’awa Uncle Moh shima sai wani kauce mun kike.”


“ Zarah dan Allah mubar maganar nan haka , kai na ciwo yake da gaske , I have to rest , daga baya sai muyi magana .”


“Okay toh ki kwana a d’aki na mana , ko yanzu da kanki yake miki ciwo, kina nufin haka zaki koma part d’in ku? Bayan akwai d’akuna anan?”.

“ Zarah kinfi kowa sanin yadda nake san kwana a d’aki na , and don’t be offended I’m feeling more safe and happy idan ina bacci akan gado na wallahi, and you know that..”

“ Kedai kawai kice mun bakyasan bacci a nan part d’in , ba sai kin kawo wani dogon excuse d’in ki ba . 

“Nima karan bani na yasa nayi miki tafiya nasan ba kwanan zakiyi ba”

Ri’ko hannunta Mimi tayi kafin ta furta “ Amma kinsan ba haka nake nufi ba ko Zarah ? Am just telling you the fact ne , ke when last kika ga na kwana ko a d’akin Aunty Shukura ne ? I so much love sleeping alone .”


“ Fine is okay 
” cewar Zarah. 

Kallanta Mimi tayi ganin kamar bata ji dad’i ba , yasa ta sauke dogon ajiyar zuciya , sannan ta furta “ Shikenan zan kwanta anan d’in, amma karkizo ki hanani bacci ko kuma ki dameni.”

Da sauri Zarah tayi hugging d’inta , cikin dariya ‘kasa ‘kasa ta furta “ That’s my girl
 karki damu bazan dameki bama wallahi”  da haka suka hau sama , Mimi ta kwanta a bed d’in Zarah , ita kuma Zarah ta kashe mata fitila ta fito daga cikin d’akin sabida karta dameta .


Tana fitowa a hankali ta d’anja ’kofar sabida karta dameta . 

Lokacin da take saukowa daga stairs  ita kad’ai take tanbayarta kanta “ Wai me yake damun Besty ne ?” Kafin ta bawa kanta amsar da take so , wayarta yayi ringing , tana ganin me kiran ta d’aga tana fad’in “ Hello Ameerah.”

Daga can ‘bangaran Ameerah ta amsa mata “ Naam Zarah , ya kan Mimi? Da zan kirata sai kuma banaso na dameta , shiyasa na ki kawai.”

“Wallahi Ameerah yadda ta fad’a mana hakan ne dan nima tunda tace mun kanta ne yake ce ciwo bata kuma ce mun komai ba .”


“ But Zarah sai naga kamar akwai wani abu a ranta ko?.”

“ Gaskiya ba na ce ba , amma tunda tace kanta ne yake ciwo , toh kawai mu barshi a hakan , idan tana so dakanta zata fad’a mana abunda yake damunta ..”

“Shikenan Zarah , sai anjima bari naje wajan Mama.”

“ Okay dear .” Zarah ta kashe wayan.


_____ A d’akin Zarah kuwa , tunda Mimi ta kwanta take faman juye juye akan gado, maganar Aya ne kawai yake dawo mata da take ce mata “ Nidin Auntyn kice.”

Ga baki d’aya ta rasa wace irin Aunty take nufi, kuma ta rasa wa zata tunkara da maganar har ya bata amsa . 

Still kasa ha’kuri tayi sai da ta furta “ Wace Auntyn ?.” A fili sai kuma ta rufe idanuwanta a hankali tana sake bud’e su , haka kawai ta soma hango yadda Aya take mata murmushi , da kuma seriousness d’in da take zama lokaci d’aya . 

Batasan ya akai ba , batasan dalili ba taji gabaki d’aya haushin Aya da take ji a cikin zuciyarta , ya gushe , burinta kawai ta dawo ta fad’a mata wata Auntyn take nufi , kuma me yasa ma Uncle Moh zai ce ta dinga kiranta Aunt at the first place

..




_________________

To be continued
 đŸ”„


Aysha Galadima đŸ€đŸż
***





***