MISHAL

Page 23

by @ayshagaladima22

MISHAL



By AYSHA GALADIMAđŸ€đŸż
***


BOOK 1 
Page 23

Tana cikin tunanin da take aka ‘kwan’kwasa ‘kofar. 

Da farko bataji ba sai da aka sake, kafin tayi magana kuma aka bud’e ’kofar . 

Zarah ce , hannunta d’auke da wani mini tray , ana saka plate a ciki da kuma cup , even though an rufe su , daga gefen bed ta ajje tana kallan Mimi . 

“ Har yanzu bakiyi baccin ba ?”.

“ Wallahi banyi ba Zarah , ji nayi ga baki d’aya ma bana jin baccin yanzu , ‘ko’kari nake in the next minutes na sauko ‘kasa , sai ga ki kuma.”

“ Ke dai Mimi kice kawai kin kasa bacci ne a d’aki na ne , d’akin ya zamar miki dodo ba zaki iya bacci ba sai kin koma bacci , ai shikenan. .”

“ Yanzu kuma wa ya kawo wannan maganar , ni yaushe na fad’i haka, kina ‘ko’karin samun 
magana a baki alhalin ba haka bane ba . 

Please ki dena fad’in irin wannan maganar , sai ki dinga sawa ina jin wani irin haba Zarah mana .”


“ Mai da wu’kar , wasa nake miki, gashi nan Mommy tace na kawo miki fate ne, tasan kuma kinasan shi, ni kai na ta hanani amma ta baki , wai ‘yarta kawai ta sani, kuma nima dan ban dad’e da cin abinci ba wallahi da tare zamu sha abun nan.”

Hararar Mimi tayi tana tashi zaune sosai , sannan ta d’auki tray d’in ta bud’e .

‘Kamshin faten sosai yayi mata dad’i, shiyasa bata tsaya ‘bata lokaci ba , ta wuce toilet ta wanke bakinta, sannan ta dawo
ta soma shan faten. 

Zarah kuma na gefe tana kallanta. Sai da ta kusan shanye
ga baki d’aya faten, tukunna ta ajje spoon tana fad’in Alhamdulillah. 

Drink d’in da ya ke kan tray d’in shima sai da ta sha kusan tabi ta ajje, tana faman lumshe ido sabida yadda taji ta ‘koshi .

“ Kinsan Allah Zarah , ina gama sha da naji ciki na Alhamdulillah na ‘koshi sai kuma na soma jin kamar bacci baccin zanyi..”

“ Kya dai ji da gulmar ki , daman yunwa kike ji, amma mukace kizo kisha d’an malele kika ‘ki , yanzu tsabar gulma sabida fate ne ai gashi kinsha


Kinga tafiya na, idan kin gama baccin sai ki kirani, in kuma na sake dawowa d’akin nan , kin gama bacci , dan sai na tashe ki daha baccin da kike .” Da haka Zarah ta d’auki tray d’in ta fita dashi, itama kuma Mimi tayi murmushi kawai, batasan ta kwanta daga cin abincinta , shiyasa ta d’an shiga wayarta tana dudduba abu , kafin bacci ya d’auketa, ga baki d’aya .



‘KARFE 9:10pm na dare 
.

Zarah da Mommy suna zaune a falo suna hira , sai kawai suka ga shigar Aya cikin falon su .

As always , tana sanye da Baggy clothes , shigarta sak ta maza da ta saba , ta fito a Tomboy d’inta sosai. 

Da mamaki duk suka tsaya kallanta , sanin cewa basu santaba , sai ma Mommy ce da ta d’an yi murmushi tana fad’in “ Sannu da zuwa wa kike nema?.”

Aya bata ce mata komai , sai ma falon nasu da ta ‘karewa kallo ga baki d’aya , ganin bata amsawa Mommy , Zarah ta mi’ke tsaye tana fad’in wace ce ke? Kuma wa kike nema?”. 

Kallanta Aya tayi, haka kawai Zarah taji wani iri da ta kalleta , har tana ‘ko’karin yi mata tsiwa amma da ta kalli idanuwanta sai taji ta nemi masifar da take ‘ko’karin yi ga baki d’aya ta rasa . 

“ Ina Mimi?.” Shine abunda Aya ta soma tanbaya kenan , cikin British accent d’inta . 

Both Mommy da Zarah kallan juna sukai , hakan yasa itama Mommy da take zaune ta mi’ke tsaye , itama ta canza harshen nata zuwa turanci tana tanbayarta “ Wata Mimi kike nufi?.”

“ Mimi nawa kuke dashi agidan nan ?” Itama Aya ta jefa mata nata tanbayar. 

Murmushi Mommy tayi kad’an , tana nuna mata waje “ Samu waje ki zauna toh , Mimi tana sama , bacci take amma nasan ko wana lokaci zata iya tashi tunda ta d’an dad’e tana baccin.”

Murmushi Aya ta sakar musu ba kamar d’azu ba da fuskarta babu yawo babu fallasa “ Okay kamar yaushe ta kwanta baccin ?”.

Mommy bata amsa mata ba sai Zarah da ta kalla, hakan yasa itama Aya d’in ta kalli Zarah .

“ Wai wace ce ke kike ta
mana wannan tanbayar?.” Cewar Zarah but in a low turn ta ‘karasa maganar sabida irin kallan da taga Aya d’in tayi mata . 

A karo na biyu  Aya ta kuma tanbayar “ Yaushe Mimi ta kwanta bacci.” 

Zarah za tayi magana , Mommy ta harareta , “ Ki amsa abunda aka tanbayeki, kinsan banasan musu ko? Yaushe Mimi ta kwanta bacci .”

“ Mommy bata wani jima ba fa , wajajan la’asar ne ta kwanta bacci , kuma naga kanta ne yake ciwo shiyasa ban tashe ta d’aga baccin da take ba .”

Ha’ba Momy ta ri’ke kafin ta furta “ Innalillahi , Zarah amma dai baki da hankali ko? Duka tsawan lokacin nan baki tashe taba , har zuwa yanzu da take bacci?”.


Kallanta Zarah tayi itama kafin ta furta “ Mommy ai gani nayi tana jin baccin kuma kanta ciwo yake , kınsan babu dad’i a tashi wanda kansa yake ciwo yanzu ciwan kan sai ya iya dawo mata , gwanda idan ta tashi da kanta zai fi”.

‘Dan Nunfasawa Mommy tayi , kafin ta mayar da kallanta kan Aya.
“ Tana sama , amma bari na saka taje ta taso miki ita.”

“ Zan iya binta ?” Cewar Aya ba tare da tayi acknowledging maganar da Mommy tayi da farko ba .

‘Dan shiru Mommy tayi tana nazari, bayan ta ‘karewa Aya kallo daga sama har ‘kasa , tasan kuma wana irin gına suke ciki, haka kawai mutum baya shigowa randomly idan har besan d’an cikin gidan ba , gashi Aya kuma ba tayi kama da irin bad mutanan nan ba . 

Daga ‘karshe Mommy ta jinjina mata kanta , tana kallan Zarah , “nuna mata inda Mimin take .” 


“ Amma Mommy
.”

“ Ya isa Zarah, nuna mata inda take , in kuma ba zaki je ba , ni na nuna mata da kai ba.”

Kallan Aya , Zarah tayi kafin tace mata “ Lets go.” Tana juyawa .

Babu musu Aya tabi bayanta zuwa sama. 

Zarah na gaba, Aya kuma tana mara mata bayan, har zuwa d’akin Zarahn . 

Suna shiga suka tarar da ita tana bacci har lokacin. 

Sai da Aya ta ‘karewa ga baki d’aya d’akin kallo , tukunna ta nufi gadan , bata tsaya ‘bata lokaci ba , ta d’an bubbugi gadon kad’an tana fad’in “ Mimi ! Mimi
” Mimi bata tashi ba . 

A karo na biyu Aya ta kuma fad’in “Mimi
”

Cikin bacci ta amsa da “ Hmmmm 
” 
Zaunawa Aya tayi a gefen gadon, tana d’agota ga baki d’aya daga kwancen . 

Babu shiri Mimi ta bud’e idanuwanta da suke cike da bacci a d’an firgice , tana ‘ko’karin ja baya da sauri.

Aya bata sake taba sai ma fad’in da tayi “ Ke nice , bud’e idanuwanki sosai ki kalleni.” 

Babu musu Mimi ta kalleta , ganin Aya ce dagaske yasa ta d’an sauke ajiyar zuciya a hankali , da muryar bacci ta furta “ Kin tsoratar dani.”

“ Na tashe ki , baki tashi ba shiyasa ai na jijjiga ki, baccin me kike haka, kinsan ‘karfe nawa?”.


“Please ki ‘kyaleni, bacci nake ji wallahi sai naji ma kamar yanzu kwanta baccin, am so tired
”

“ Ke kalleni nace miki, ki wartsake tun yanzu, baccin me kike yi haka 9 har ta wuce , sabida baki da abunyi sai ki zauna kiyi ta bacci, haka aka koya miki?.”

Da mamaki Mimi ta sake kallan Aya tana fad’in “ 9 kuma?”.

A maimaikon Aya ta bata amsa sai ta kalli Zarah da ta tsaya kallansu , ganin yadda suke magana sosai alamar sun san juna , which Zarah tasan tunda  take batasan Mimi da wannan friend ba , kuma tasan ba wasu friends ne da ita ba , mamakin hakan yasa ta kasa cewa komai tunda suka shigo d’akin.

“ Zarah ‘karfe naw?” Ta tsinkayi muryar Mimi 


Wayar Mimi da take bedside Zarah ta d’an kunna, tana kallan time sai ta nuna wa Mimi wayar tana fad’in “ Past 9..”

Sake zaro ido Mimi tayi tana fad’in “ Shine baki tashe ni ba, kika barni ina ta bacci haka sai kace me baccin asara .”

“ Kefa kika ce mun kanki yana ciwo kuma nasan ba sallah zakiyi ba shiyasa ban tashe ki ba.”

“Hmmm “ kawai Mimi tace , tana amsar wayar nata, sannan ta yun’kura ta tashi tsaye , bayan ta amsa mayafin kanta da Aya ta mi’ka mata. 

Ba tama d’aurashi akanta kamar d’azu ba rolling kawai tayi, ta juyo saitin Zarah zata mata magana , Aya ta ri’ko hannunta zata fita da ita daga d’akin, Mimi tana ‘ko’karin ‘kwacewa amma kuma ta kasa sabida mugun ri’ko da Aya tayi mata , cikin sauri ganin zasu fita daga d’akin ta furta “ Bari na saka takalmi na.”

Tsayawa Aya tayi ta saka ta kalmin kafin ta cigaba da tafiya , hannunta yana cikin nata , har suka sauko Zarah tana bayansu itama , ko bari Mimi tayiwa Mommy magana ba tayi ba taja hannunta suka fita daga part d’in da sauri .

Suna daf da shiga part d’in su Mimi tayi nasarar ‘kwace hannunta , a zuciye ta furta “ Me haka kike mun? Sai faman ri’ke mun hannu kike kamar wani abu ya faru? Sai wani jana kike 
.”

Ganin yadda ta ‘bata rai yaƟa Aya ta sakar mata murmushi tana matsowa kusa da ita “ Fine ! Am sorry bazan sake ri’ko miki hannun ba , so now let’s go 
”

Shiru Mimin tayi mata , ba tare da tace komai ba , kuma bata matsa daga inda take ba , hakan yasa Aya tayi kamar zata ‘kara ri’ko hannun ta, ita kuma ta janye tana wucewa part d’in su , haka Aya kuma ta mara mata baya . 

Tana shiga part d’in su , Uncle Saleem da Aunty Shukura ßuna zaune falo suna hira, amma har su d’in bata kalla ba ta wuce d’aki kuma ta sa lock ta ciki sabida karma a shigo mata d’akin. 

Ita kad’ai sai faman jan tsaki take, tama rasa me zata cewa Aya ga baki d’aya daga zuwanta , tana nema ta takurawa rayuwarta . 

Takaicin yadda ta ri’ko hannunta tana janta ne yafi komai ‘bata mata rai , gashi ta kasa ya kice abun ma aranta ga baki d’aya , shiyasa ta wuce toilet ta watsa ruwa , ko abunda take ji a ranta zai tafi. 

Da ta fito daga toilet d’in ta d’anji dama dama , shiyasa ta d’auki Al-qur’ani tana karatu tunda ta samu tsarki a time d’in. 

Ta d’an jina tana karatu har sai da taji relief sosai a zuciyarta , sannan ta d’an shiga wayarta shima irin fisha d’in nan bata wani dad’e a ciki ba , taga both message d’in Zarah da Ameerah , amma duk ciki babu message d’in wanda ta bud’e sabida she’s not in the mood a lokacin ga baki d’aya . 

A haka yinin daren ya ‘kare mata , yau sai da ta kai past 12 tukunna ta kwanta bacci . 


‘Karfe 5:01am ta farka daga bacci, tana mi’ka a hankali , kamar yadda ta saba ko da yaushe bayan tayi abunda za tayi a ban d’akine , ta fito tayi sallah , azkar da kuma Karatun al-qur’ani. 

Haka kawai taji tanasan komawa bacci tunda gari bai gama wayewa ba .

Daddumar da tayi sallah ta soma nannad’ewa , ta cire hijab d’in ta kenan , akai knocking ‘kofar d’akin. 

A tunaninta Mamy ce tunda itace take yawan zuwa a irin wannan lokacin, shiyasa bata tanbayi wane ne ba , ta bud’e ’kofar. 

Aya ce a tsaye , cikinta sanye da kayan gym, sai kuma p- cap da ta d’ora akan fuskarta . 

Mimi tana ganinta , da ido tayi mata alamar lafiya ? .

Aya kuma amaimakon ta amsa mata , sai kawai ta shigo cikin d’akin tana ‘kare masa kallo ga baki d’ayansa . 

“ ‘Dakin ki yayi kyau sosai , kin iya za’bar colour , yanzu canza kayan jikin ki mu fita training.”

“ Training?” Mimi ta d’anyi tanbayar da shock a fuskarta .

Aya kuwa ko damuwa ba tayi ba da reaction d’in Mimi ta furta “ Yeah training , kiyi sauri ki shirya mu tafi , hour d’aya ne damu , banasan ‘bata lokaci.”

“ Okay akan wana dalili ma zan biki? Meyasa kuma ke ba zaki iya zuwa training ba sai dani? Excuse me ? Kinsan kuwa an ina kike ? Naga tun jiya sai abu kike kamar kin fi kowa , na kasa gane miki, ko sabida kince ke Aunt d’ina kamar yadda kike i’kirari hakan ne zai sa kiyi duk abunda kika ga dama a cikin gidan nan ? Or sabida ana rabuwa da ke shiyasa kike ganin kamar zaki iya komai?.

Please fitar mun daga d’aki, kuma ki sani bani na kawo ki cikin gidan nan ba , idan kinasan abu sai kije wajan wanda ya kawo ki bawai ni ba ..

Kizo ki fitar mun daga d’aki , zan kwanta , da sassafen nan ba zaki zo ki dinga sakani ciwan baki ba , abunda kikai jiya ma na share ki, toh karki ce zakiyi mun shi yau .

Let’s respect each other , yanzu kizo ki ficemun daga d’aki, karki bari nayi loosing temper d’ina
”


“ Okay idan kinyi loosing temper d’in me zakiyi ? Uhm me zakiyi ?”. Cewar Aya . 

Kafin Mimi ta samu damar magana Aya ta sake rigata “ Kina ‘bata mun lokaci , ki shirya zamu je gym lokaci na tafiya .”


“ Bani da lokacin ki , Aya kike kowa , kina ‘bata mun lokaci , zan kwanta idan baki da abunyi ni ina dashi
” cewar Mimi tana d’an matsawa gefe ta baya Aya hanya alamar ta wuce .

Aya kuwa tsayawa kallanta tayi , da fari kamar ba zata ce komai ba , sai kuma ta sake cewa “ Mimi ki shirya mu tafi , idan kuma ba zaki tafi ba , zan jaki muje da kai na , bani da ha’kurin da zan tsaya  â€˜bata lokaci ina ta maimaita miki magana.”

‘Karamun tsaki kawai Mimi tayi, ta kashe fitilar d’akinta , tayi kwanciyarta , hakan yasa dan dole Aya ta fita daga d’akin, bayan ta janyo ‘kofar , even though bata rufe ‘kofar duka ba . 

‘Dan d’agowa Mimi tayi ta kalli ‘kofar bayan ta fita , sai kuma ta soma jan tsaki sabida takaici, bayan kamar mintuna biyar tana runtse idanuwanta sabida tayi bacci , sai tayi ringing d’in wayarta . 

A hankali ta bud’e ido tana duba screen d’in wayar nata , Mamy ce .

Bata tsaya ‘bata lokaci ba tayi picking call d’in. 

Tun kafin tayi maganar ta ji saukar muryar Mamy a kunnanta “ Ki sauko ‘kasa ina jiran ki.” 

Kafin Mimi tace komai ta kashe wayar . 

Ba ‘bata lokaci Mimi ta sauko ‘kasa , sai ta tarar da Mamy a tsaye , sanye da hijab sai kuma Aya da take zaune akan kujera . 

Tun kafin ta ‘karaso wajan Mamyn tayi sensing dalilin kiran Mamyn tunda taga Aya a wajen , amma mamakinta ya kasa ‘boyuwa akan fuskarta . 

Ta rasa dalilin da yasa Mamy lokaci d’aya zata biyewa bare , wacce ga baki d’aya kwananta d’aya a cikin gidan , kamar irin sun dad’e da sanin juna sosai d’in nan . 

“ Mamy ina kwana .” Cewar Mimi tana d’anyi mata side hug . 

A da’kile Mamy ta amsa mata da “ Lafiya Lou , Mimi baki ji abunda Aya tace miki ba?.”

“ Mamy me tace miki ? Danni bansan komai ba .”

“ Toh Mimi ‘karya za tayi miki? Ba tace ki shirya kuje training ba amma daga ‘karshe me kikai ba , kashe fitila kikai kika barta a cikin d’akin, haka daman kike tar’bar ba’ki?”.

“ Haba Mamy kema ya zaki dinga biyewa wannan? Duka jiya jiyan nan tazo ba , kema kin sani Mamy babu gym da nake zuwa , infact Mamy ko kin manta matan gidan nan basa zuwa training , wai kuma da safe lokacin da kowa yake kwanciya , sai zuwanta zata fito da wani kili bibi ,idan ta gaji da zama ai sai taje tayi yawonta ita kad’ai, but she’s just behaving any how a
” bata ‘karasa ba Mamy ta tsayar da ita . 

“ idan kin gama surutun naki sai ki wuce kuje training d’in, idan kuma baki saba yi ba daga yau zaki fara, bana bu’katar maimaita kai na , ko ki canza kayan da suke jikin ki , ko kuma kije dasu haka , wanne kika za’ba a ciki? 

Kuma maganar wa za’aji ? Maganata ko kuma maganar ki?”. 


“ Hmmm aa Mamy maganar ki za’aji” cewar Mimi bayan ta d’an sauke nunfashin da take ji kamar yana ‘ko’karin kufce mata .

“ Then koma kije ki canza kayan karki wuce minti goma , banasan musu kuma , kiyi abunda na saki.”

Kallan Aya , Mimi tayi ido cikin ido sai kuma ta d’an taune gefen lips d’inta tana fad’in “ Tom Mamy.” Sannan ta juya zuwa sama . 

In a short time ta canza kayan jikinta zuwa riga da wando, da kuma hula da ta saka . 

Mimi tana kallan Mamy sai tayi mata murmushi sannan ta kalli Aya itama da take mata murmushin “ Mu tafi ko?”. 

Hakan kuwa akai Aya ta jera da ita suka fita, Mimi kamar abun arzi’ki yadda ta fito irin normal d’in nan , daman kuma akwai gym a cikin gidan da mazan suke zuwa tunda duk cikin matan babu me zuwa Gym sai yanzu da Aya ta ‘kir’kiro wannan abun. 

And again Aya bata san an ina direction d’in Gym d’in yake ba , shiyasa ta bi bayan Mimi ganin tana nufar wani direction , duk a tunaninta a nan area gym d’in yake . 

Mimi kuwa tana sane tabi hanyar, ganin Aya tana bin nata , dai da tayi doguwar tafiya tukunna , tazo wani part na masu Aiki sa aka dad’e ba’a anfani dashi , tuntuni  kuma yana can ‘karshen gidan dama.

Mimi tana zuwa wajan, ta gama ‘karewa ga baki d’aya building d’in kallo , an d’auki shekaru masu yawa bata zo wajan nan ba, babu ma masu zuwa sabida ba anfani ake dashi ba sai time to time da ake d’an gyarasa ..

Mimi tana gama kallan ginin ta juya zata bar wajan Aya ta d’an ri’ko hannunta da mamaki akan fuskarta “ Bangane ba ? Ina wajan Gym d’in yake ko daman anan akayi sa?.”

Banza Mimi tayi mata tana cigaba da tafiya amma haka Aya ta ‘kara shan gabanta, “Kice wani abu, sai faman yi miki magana nake , amma kuma kina raina mun hankali , babu wanda yake mun abunda kike mun , kuma a haka ina rabuwa dake kin kasa ganewa, karki ‘bata mun rai Mimi , ina wajan Gym d’in yake? Ki wuce muje ki nuna mun wajan , kafin ranki ya ‘bace .” Yadda take magana sai kace wata uwarta , gashi cikin umarni take maganar kamar itace ta haifi Mimi d’in.

Iya sha’ka Mimi ta sha’ki maganar Aya , amma sai ta kawar da kanta ta cigaba da tafiya . 

Itama Ayan kuma sai ta d’anji haushin abunda Mimi tayi mata , ganin tana faman mata magana amma ta shareta . 

Hannunta biyu tasa tana ‘ko’karin dawo da Mimin ba, mistakenly agarin dawo da ita sai ta d’an janyo ta da d’an ’karfi, ita kuma Mimi bata ri’ke balance d’inta ba sai ta d’an fad’i a ‘kasa. 

Da sauri Aya tazo zata mi’kar da ita tana fad’in “ Kiyi ha’kuri ba da gangan nasa kika fad’i ba , dakatar dake nake ‘ko’karin yi sai kika fad’i kuma
” bata ma kai ‘karashen maganar nata ba , Mimi tana d’agowa ta gyara mata mari , ji kake tasssss a kumatun Aya . 

Wani irin firgita Aya tayi sabida zafin marin da taji, da duk hannuwanta tasa ta dafe kuncinta, idanuwanta har sun d’an taru da ‘kwalla kad’an dan sosai taji zafin marin, wanda zata iya rantsewa ba’a ta’ba marin irin haka ba da yazo mata a bazata kuma unexpected ba . 

Rai a ‘bace Mimi ta nuna ta da yatsa “ Na rantse miki da Allah idan har baki shiga hankalinki akai na ba , zan yi mugun sa’ba miki, haba mana kin bi kin ishe ni, kin had’a ni mahaifiya ta , na ‘kyale ki, kin hanani kwanciyar hankali shima na ‘kyale ki, kin had’ani da Uncle Moh shima na ‘kyale ki, uban wacece ke da zakizo har cikin gida na ki nuna abunda zanyi? Am asking uban wace ce ke ? Idan baki fita harkana ba wallahi ko shi wanda ya kawo ki cikin gidan nan bai zai ‘kwace ki ba , stupid kawai
.” Mimi taja wani dogon tsaki ta bar wajan . 

Aya ta dad’e a tsaye a wajan, har yanzu marin da Mimi tayi mata bai sake ta ba , gashi ‘yan yatsu biyar d’inta sun fito sosai akan fuskarta , sabida tana da hasken fata .

Mimi kuwa tasan yanzu idan ta koma part d’in su zata iya had’uwa da Mamy , kuma Mamy zata iya tanbayarta ina Aya take , ko ina Gym d’in da suka ce zasu je , shiyasa bata koma part d’in su ba , idan kuma taje part d’in su Zarah a yanzu tasan bacci suke , idan kuma idan su biyu ita da Mommy zasu iya tanbayarta ba’asin wace ce Aya wanda a yanzu babu worst mutum da batasan a anbaci sunansa kamar Aya d’in. 

Ba zata iya zuwa part d’in su Ameerah ba shima sabida wani aikin ne , idan suka had’u da Uncle Bashir shima zai iya ci mata mutumci ko ya fad’a mata maganar da zata ‘bata mata rai , bata da choice sai dai taje part d’in Moh, amma kai tsaye bata je, part d’insa ba sai da ta soma duba wajan motocinsa taga kamar an fita da mota guda d’aya daga yanayin gap da aka bari na mota d’aya , bata confidence d’in cewa shine ya fita ko akwai wanda ya fita , duka calculation d’inta ne , bata kuma da wani choose haka ta ha’kura ta wuce part d’insa .

Tana shiga taga ga baki d’aya fitilun falon a kashe suke , ba’a kunna ko guda d’aya ba , a hankali ta sauke ajiyar zuciya irin ta relief d’in nan , kafin ta salalla’ba a cikin duhun nan , ta nemo kujerar da zata zauna. 

Tana jinta a 2 sitter ta sake sauke wani ajiyar zuciyar. Ta ma’ki bari zuciyarta tayi tunanin ko Moh yana part d’in ko bayan, tunda ta samu ta kwanta take faman jera ajiyar zuciya dan iya sha’ka ta sha’ki Aya yau , kuma tayi rantsuwa a zuciyarta , idan har Aya ta kaita bango yau, toh tabbas ba zata ji da dad’i ba sai dai ko me za’ayi mata a gidan yau sai ayi mata , tana cikin wannan tunanin bacci ya soma d’aukarta sama sama 


______ Sai kashhhhhh baccin nata baiyi nisa ba , aka sake bud’e ’kofar falon , da fari ‘kara shigewa cikin kujerar tayi kamar tana bacci, amma ganin an kunna fitila, an tsaya kuma akanta, yasa ta d’an bud’e ido tana fad’in “ Uncle Mo
” maganar nata ya tsaya mata , ganin Aya ce a tsaye akanta , ta ri’ke hannuwanta a ‘kirji tana kallan Mimi d’in . 

Ko kusa Mimi batayi mamakin bud’e ’kofar da tayi ba, tunda har zai iya kawo ta cikin gidan, dai ya bata pin d’in part d’insa ai ba abun mamaki bane . 

A hankali ta mi’ke zaune , kamar yadda Aya take kallanta , itama kallan nata tayi “ Lafiya kika zo kika tsaya mun aka?.”

“ Mimi tanbayana ma kike lafiya ? Bayan mari na da kikai shine zaki zo nan ki kwanta , kinsan wace ce ni da zaki mara ? Dan nazo gidan nan shine kome kika ga dama zaki yi mun? Kinsan wace ce ni nace miki?.”


‘Dan dariya Mimi tayi mata me kama dana takaici tana kallan Aya daga sama har ‘kasa sai kuma ta jingina da kujera sosai mostly yadda Moh yake zama , a kai kai ce ta furta “ And ke d’in wace ce ? Ok ok ba sai kin fad’a mun ba nasan amsar , ke d’in ba komai bace kuma bakowan kowa bace, face wacce ba zata iya siyan gidan da zata zauna ba , sai dai ta dinga manne wa maza sabida su bata wajan zama , misali gashi nan a gida na kike , ma’ana ba zaki iya kama gidan naki ba because you’re so stingy , dan haka ke d’in ba komai bace , kuma ba kowa bace .” 


In a speechless way Aya ta furta “ Mimi kamar kina so ki had’ani da kalmar karuwa”

Hannu biyu Mimi ta d’aga , in I don’t care manner ta furta “ Ban fad’a ba , amma tunda ke kika fad’a da kanki , babu abunda zance sai dai nayi accepting abunda kika ce , and by the way please idan kin gama ‘kamewa zaki iya matsawa mun daga kai, idan kuma baki gaji da tsayawa , ki d’an matsa gefe sai ki cigaba da tsayuwar da kike, dan turaren ki yana hawamun kai, ko mazan gidan mu basa saka irin wannan turaren me ‘karfi.”

A wannan time d’in muryar Aya tayi sanyi, idan ka kalleta ma dole kaga alamar hakan a fuskarta da alama maganar Mimi tayi mata zafi sosai , cikin sanyi ta furta “ Mimi you’re insulting me ?


“Ni ban zage ki ba and yes idan haka kike tunani then fine please ki matsa ki bar
.” Fassss taji an d’auke fuskarta da mari , da farko tayi tunanin ko Moh ne ya mareta , ganin babu kowa a falon sai Aya da take gabanta wacce take d’an wuci , hakan yasa ta gane ita ce d’in ta mareta , itama bata tsaya ‘bata lokaci ba ta daddage a inda ta mareta d’azu ta sake ‘kara mata wani marin. 

Fuskar Aya tayi d’ad’au , ya tsu takwas sai da suka fito , Mimi kuma ya tsu biyu ne suka kwanta a mata a fuska , amma basu fito sosai kamar yadda na Aya ya fito ba . 

“ Mimi mari na fa kikai? Ni Aya kika mara?.”

“ Oh ba za’a iya marin ki ba, shine ni kuma aka ce miki fuskana ta mari ce da zaki mara ?”

“ Mimi wallahi sai kinyi dana sanin mari na da kikai, a yanzu ba sai anjima ba , kina ganin kamar na katse miki freedom d’in ki sabida na saki kiyi abu ko? Zan nuna miki akwai gap a tsakanin mu, ni ba sa’arki bace .

Baki da kunya Mimi, kuma zan dakatar dake daga wannan rashin kunyar taki .

Bana bu’katar tsayawa magana dake yanzu amma tabbas marin da kikai mun sai kin bani ha’kuri akansa 
” da haka Aya ta wuce ta bar part d’in rai a ‘bace.

Ita kuma Mimi waje ta samu ta zauna, tana jin yadda zuciyarta take faman bugu sosai da sosai , ta san tunda ta mari Aya , ba lalle Mamy tayi mata shiru ba, a’bangaran Moh ne batasan me zaiyi mata ba shi kuma , dan tunda har zai iya kawo Aya gidan nan toh tabbas budurwarsa ce , kuma bazai ‘kyaleta ba , haka nan sabida marin da tayi wa budurwarsa .

1 hour ya wuce Mimi tana zaune a falon nan tama kasa komawa baccin da tace za tayi , second hour shima ya shiga , bata koma bacci ba kuma bata wuce part d’in su, a haka har lokaci ya ja , 11 na shiga bugun zuciyarta ya soma tsananta , dan tasan anymoment from now Moh zai iya dawowa, kuma idan har yaga marin fuskar Aya batasan me zai yi mata ba . 

Tana tsakiya da wannan tunanin , aka bud’e ’kofar falon , ‘yan yatsun hannunta har wani rawa suke sabida ta gama gasgata cewar shi ne ya dawo . 

Kuma shid’in nen , sabida tun kafin ya shigo ‘kamshin turaransa ya rigasa shigowa, babu shiri ta mi’ke tsaye tun kan ya ganta akan kujera.

Moh sanye yake da farar riga me d’an fad’i, hannunta iya gwiwar hannunsa , sai wando shima fari , agogon hannunsa kuma ba’ki da takalmin ‘kafarsa shima da yake ba’ki . 

Normal simple dress ne a jikinsa amma kuma ba’karamun kyau yake yi ba a kullum , sai kaga kamar ‘kara masa kyau ake , gashin gansa ya kwanta a ta bayansa, sai kad’an da ya d’an tufke . 

Fuskarsa tananan kamar kullum ba’a sake ba , ga kaifafan idanuwansa me ladaftan da mutum. 

Itama Mimi idanuwansa ne ya ‘karasa wa jikinta yin rawa , sabida tasan bata da gaskiya , duk adduar da tazo bakinta yi take , tana ro’kan Allah , Allah yasa kar ya gano ta har ta fice daga part d’in, amma kuma addua ta bata amsu ba , dan a kallan farko da yayi mata , ya gane akwai wani abu da take ‘boyewa musamman yadda take kaucewa idanuwansa, kuma ya’ki d’auke idanuwan nasa shiyasa ta ‘karashan jinin jikinta sosai. 

Tana shigowa falon, cikin d’an rawa rawar murya ta furta “Hmmm Uncle Moh.. ina .. kwana.” Ita kanta batasan ya akai muryan nata yake faman rarrabewa ba koda tayi ‘ko’karin had’e kalmar waje d’aya . 

Bai amsa mata ba , kuma bai dena kallanta ba , har ya samu waje ya zauna , ita kuma ta sunkuyar da kanta simi simi , zata fita .

“Mimi dawo ki zauna.” Ta tsinkayi muryarsa . 

Sai da ta had’iye wani abu da batasan ko mene ne ba a wuyanta, tukunna ta juyo ta zauna a kujerar da yake facing d’insa , ta’ki yadda ma su had’a idanuwa .

“ Wannan kauce kaucen da kike na mene ne ? Me kikeyi , kike gujewa kallo na?”. 

Mimi tana jin wannan bayanin ta saki ajiyar zuciya ganin baisan komai ba . Sai ta d’an ‘ka’kalo murmushin ya’ke akan fuskarta da bai kai zuciyarta ba tana fad’in “ Uncle Moh ni babu komai fa , bacci nake ji shiyasa kuma kaina ne yake ciwo amma na sha magani , kuma
banasan hayaniya sai nazo part d’inka na kwanta , amma yanzu daman nake shirin tafiya d’aki nayi wanka tunda kaina ya dena ciwo yanzu.”


“ Idan kin gama storyn naki sai ki fad’a mun abunda kikayi, ko kuma ni na gano da kai na .”

Narai narai tayi da idanuwanta, kuma taci magani duk dan ya barta “ Nifa dagaske nake maka Uncle Moh, babu komai , kasan bazan ‘boye maka komai ba
”

Hannun sa d’aya yayi mata alamar tazo , sannan da idanuwansa ya nuna gefensa akan ta zauna . 

Ta gane me yace amma kuma batasan zama a wajan shiyasa ta furta “ Uhmm?”. 

Yanzu kam a kausashe ya furta “ Karki bari na kuma yi miki magana Mimi
” 

Simi simi ta mi’ke ta zauna a kujerar da ya fad’a amma ba a kusa dashi ba , shi kuma ja d’aya yayi mata tunda ba nauyi ne da ita ba ta dawo kusa dashi sosai, sai ta d’an wayance ta dafe gefen kumatunta da Aya ta mara karya gani, amma ya riga ya gani.

Hannunsa d’aya ya saka zai jiyo da fuskarta ta soka ‘ko’karin kaucewa kamar za tayi masa gardama .

“ Wallahi zan wanka miki mari ! Are you mad?.” 

Tanajin yadda yayi magana da wannan cold turn voice d’in nasa ta marairaice masa fuska tana sakin hannun nata . 

Shatin hannun da yake kan fuskarta ya ‘karewa kallo, har zuwa ‘kwayar idanuwanta da wasu ‘kwalla suka fito babu shiri sabida kallan da taga yana jefa mata.

“ Wane ne ya mare ki?” Shine abunda ya soma tanbaya , ita kuma tayi saurin girgiza masa kanta tana fad’in “ Fad’uwa nayi , babu wanda ya mare ni 
”

“ Oh 
” shine abunda yace ya mi’ke tsaye , tayi tunanin ya yadda da maganar nata zai wuce sama ne , sai ta ga ya ri’ko hannunta , tana ‘ko’karin tirjewa yayi mata wani irin kallo da yasa ta shiga taitayinta , ta riga ta sad’akar ma komai zai faru kawai ya faru bata da wani choice tunda Aya d’in ma ta mare ta ai.

Suna shiga cikin part d’in su a tsakiyar falon su tukunna ya saki hannunta , Abba , Saleem, Sadiq , da Shukura suna cikin falon suna zaune , da alama hira  suke , ko wannan su ya d’ago Kai ya kalli Mimi da wani kallo da itama bata gane kallan mene ne ba sai kuma suka gaishe da Moh. 

Kansa kawai ya d’aga musu, sannan ya samu waje ya zauna , ita kuma Mimi ta ‘bata fuska. 

“ Shukura kiramun kowa da yake cikin part d’in nan .” Yayi maganar cikin bada umarni . 

Babu musu Shukura ta amsa masa , part d’in Mamy ta nufa kai tsaye taje ta sanar da sa’konsa, sai kuma ya kalli Mimi itama “ Jeki kira mun Aya.” 

Babu damar tayi musu sabida kallan da yayi mata , haka ta wuce saman nasu sim sim kamar abun arzi’ki, ta tsaya a’kofar d’akin, knocking d’aya tayi , taji ba’a amsa ba , ta ta’be bakinta ta sakko ‘kasa , a time d’in Mamy ta fito , kuma taji idanuwanta akan Mamyn sai ta’ki kallanta itama , a inda ta tsaya d’azu anan ta tsaya , sauran kuma kowa yana zaune yana kallanta , cikin d’an turo baki ta furta “ Na kıra ta bata amsa ba .”

Baice komai ba ya d’auki phone d’insa , ringing d’aya ta d’auka “ Sauko ‘kasa .” Kit ya kashe call d’in . 

Ko cikakken 1 minutes ba’ayi ba , sai ga Aya ta fito, abunka da ba ‘yar Nigeria ba , gefen fuskarsa yayi sutu sutu, akan marin da Mimi yayi mata, ga baki d’aya suna kallan fuskar AYA sai suka kalli Mimi da itama ta shagwa’be fuskarta kamar za tayi kuka, at the same time kuma ta had’e rai, sai ta d’an d’ago fuskarta ta kalli Moh da ya sakar mata wani murmushi. 
Murmushin da kana gani kasan akwai ayar tanbaya akansa

.


_________________

To be continued
 đŸ”„


Aysha Galadima đŸ€đŸż
***



***