MISHAL

Page 29/30

by @ayshagaladima22

MISHAL



By AYSHA GALADIMAđŸ€đŸż
***


BOOK 1 
Page 29 / Page 30 + Bonus page .

Suna zuwa ‘karshen hanyar ta bud’e mata ‘kofar da zata sadata da part d’in su . 

Hannunta da yake ri’ke dashi ya kalla kafin ya d’an ran’kwafo ya sumbaci hannun, sannan ya sumbaci goshinta shima . 

“ Take care 
.” Yayi maganar cikin ‘kasan ma’koshi. 

Akwai tarin tanbayoyi da suke nu’kur’kusarta a ciki, tanaso tayi masa tanbayar amma kuma bataga fuskar hakan ba a tattare dashi, haka ta ha’kura ta wuce cikin part d’in su, wajan ya rufe ruff kamar babu wani hanyar da aka ta’ba yi a wajan. 

Tsayawa kallan falon ‘kasa tayi , babu kowa a falon , har fitilin ciki an rarrage su sabida dare da yayi . 

Jiki babu ‘kwari ta wuce d’akinta. 
Ahankali ta rufo ‘kofar d’akin, tana jingina jikinta da jikin ‘kofar d’akin . 

Fararan kayan jikinta ta ‘karewa kallo, sannan ta kalli hannun da yayi wa kiss, sannan kuma ta d’an shafa goshinta shima dai dai wajan da yayi mata kiss. 

Wani irin abu take ji a cikin zuciyarta, wanda ita kanta batasan mene ne ba , kuma ta kasa fassara abunda ya faru a tsakanin su. 

Tunani kala kala, sosai ya shiga yi mata yawo cikin kwanya , duk yadda taso ta gane wani abu, ta kasa , duk inda ta kama sai ta saki, ganin tana ‘ko’karin sawa kanta cikin kai , ta ha’kura da tunanin ga baki d’aya . 

Ta d’auki hula ta sa akanta, sannan ta wuce toilet tayi fitsari da alwala , bayan ta gama duk abunda za tayi , ta kwanta bacci. 

Baccin da sai da ta dad’e a kwance to kunna ya ‘kwace ta , sabida tunani ka sosai da yake shiga da fita a kwanyar kanta . 


***Washe gari sai da ta d’an makara , sabida batayi bacci sosai, gashi har an idar da sallah asuba .

Jiki babu ‘kwari ta mi’ke taje tayo alwala , ta tada sallar asuba, tana gamawa tayi Azkar da karatun Al-qur’ani duk da ba me yawa tayi ba, sabida baccin da take ji. 

Tana kammala wa ta zare hijab d’inta , yau ko ninkeshi ba tayi ba ta barsa akan daddumar da tayi sallah, ta koma baccinta. 


‘Karfe 9:15am na safe , aka soma ‘kwan’kwasa mata ‘kofa , sama sama taji knocking d’in amma bata bud’e idanuwanta, sabida har lokacin bata tashi daga baccin da take yi. 

Sake knocking akai a karo na biyu, bayan jikinta da ta d’an motsa babu abunda tayi. 

A knocking na uku ne aka bud’e ’kofar d’akin, sannan aka zo aka kunna fitilar d’akin duk tana ji.


Zarah ce a tsaye , hannunta ri’ke da cup sai faman turiri yake , ganin yadda Mimin ta ‘kudundune , ta duvet yasa ta ajje cup d’in hannunta , a gaban mudubi sannan ta nufi bed d’in tana d’an bubbuga pillown da Mimi take kai .

“ Bestie ki tashi ! 9 fa ya wuce , yau wana irin bacci kike haka ?”

Tabbas Mimi taji muryar Zarah, wanda idan a dane babu makawa zata tanka mata, ko ma ta bud’e ido, sai dai daga abunda tayi mata jiya bata jin wannan attachment d’in nata da take ji a baya. 

Ganin ta’ki dena damunta da surutu , Mimi ta bud’e idanuwanta tana mi’kewa zaune sosai, bakinta d’auke da addua 
.

Wani murmushin Zarah tayi mata , ganin ko kallan inda take d’in ma ba tayi ba.


“ Bestie baccin me kike haka? Tun d’azu fa nazo part d’in nan tun wajan 8 , naga kina bacci, yanzu har past 9 baki tashi daga baccin da kike ba , kallan har tea na had’a miki , sabida nasan zaki iya tashi da yunwa .”

‘Karamun murmushi Mimi tayi tana kallan Zarah , tama rasa abunda zata ce mata, bayan abunda ta gama yi mata jiya har tana da audacity d’in zuwa ta dinga faffad’a mata magana haka . 

Zarah zata kuma magana Mimi ta rigata “ Zarah please ya isa haka, gashinan already na tashi, shayi kuma thank you so much amma bana bu’katar shi.” Da haka ta mi’ke ta shiga toilet ta bar Zarah a tsaye .


Wani irin kwalla ne ya tarar wa Zarah a cikin idanu, sosai take jin zuciyarta tayi mata ba’ki, bakinta har wani d’aci d’aci yake mata , akan abunda Mimin tayi mata, which tana ganin kome zatayi wa Zarah bai kamata tayi mata haka ba sabida tun farko laifinta ne , da bata bari an kawo wata cikin gidan ba da duk hakan ba ta faru ba , kuma da bata nuna fifikonta akan ba’kuwar ba da kwata kwata ba zata yi mata abunda tayi jiya ba. 

Haka ta fita daga d’akin ba tare da ta d’auki cup d’in hannunta ba , zuwa ‘kasa .

A’kasan aushe Ameerah tananan itama , da kuma Aunty Shukura , sai Aunty Feedy da tazo. 

Ko wanne da cup a hannunsa da alama ßuna tea d’in ne a ciki. 

“ Zarah kin mi’ka mata tea d’in?.”

Da’kyar Zarah ta iya had’iye abunda yake bakinta , sannan ta d’ora kyakkyawan murmushi na ban mamaki akan fuskarta , tana jinjina wa Ameerah kai “ Eh Ameerah na bata tea d’in da kika had’a nace mata Ameerah ce ta had’a mata tea tace idan bata sha ba sai tayi gutsi gutsi da ita..”

“ Kefa kinfiya rashin mutumci, a gidan uban wa na fad’i haka . Aunty feedy ko kinji lokacin da na fad’i haka ?”. Zarah ta ‘karasa kalamanta tana kallan Aunty Feedy da take dariya . 

“ Nifa ba zaku sakani a cikin wannan sabgar taku ba , mutum yazo ya shiga tsakani ya ji kunya , ku bari idan abokiyar yin taku tazo sai tayi muku shara’a
”

“ Kai Aunty Feedy 
” Ameerah ta d’an ’bata fuska sai ta kalli Aunty Shukura . 

Suna had’a ido da Aunty Shukura ta d’aga mata hannu tana mata dariya “ Ameerah , I’m out 
”

“ Ai shikenan , tunda haka zakuce bari Mimin ta sauko zamuga maganar wa zata yadda .” 

‘Karamun gwalo Zarah tayi mata tana zama akan 3 sitter d’in da babu kowa akai. 


Bayan kamar mintuna 40, sai ga Mimi nan ta soma saukowa , tun kafin ta ‘karaso wani azababban ‘kamshin turarenta ya ziyarci hancin su , ba kamar Ameerah da take faman shinshinar ‘kamshin sabida yadda yayi mata bala’in ’kamshin .

Yau tayi kyau sosai, doguwar fitted gown ta saka red colour . 

Red colour d’in yayi mugun matching da skin colour d’inta , ga hula me V shape da ta saka gashin kanta ya d’an fito waje daga tsakiya , ta saka ba’kin kwalli, ta d’anyi lining d’in bakinta kad’an brown colour da kuma white lipstick da ta saka Mimi tayi kyau irin over over d’in nan ya Allahu. 

Tana shigowa  cikin falon Aunty Feedy ce ta soma tankawa “ Mimi wannan kwalliya da kikayi , kamar zaki je gasar kyau ? Ko dai zance zaki je ne bamu da labari ?.”

‘Karamun dariya Mimi tayi tana juya idanuwanta wanda ya ‘kara yi mata kyau sosai “ Kaji ki Aunty Feedy , idan gasar kyau zan shiga ai kuna gama gama a masu sani, zance kuma na rasa yaushe zanyi zance sai da sassafe ? Sai kace nice allazi soyayya?.”

“ Oho dai , waya sani abu a duhu, dan irin kune idan suka soma soyayya sai sun kusa haukata Mijin su sabida yadda zai bala’in san ku.

In ma dai akwai ake ‘boyewa , a temaka kar a rikita mana in law 
”


“ Uhm gaskiya dai kam Aunty feedy fad’a mata , idan tayi tsami za muji, kalli yadda take faman blushing , ita kad’ai sai faman murmushi take , Me I don’t trust her today o..” cewar Aunty Shukura itama tana kashe mata ido d’aya .

“ Aunty Shukura nifa bazan biye muku ba wallahi, ba zaku had’u ku d’inga tsokanata ba , dan kunga Uncle Abba bayanan balantana ma ya shigar mun..”

“ Toh Abban yazo mana , mu gani idan zai hanamu tsokanar ki
”

“ Aunty Feedy mai da wu’kar . 
Ina kwana , kin tashi lafiya ?”.

“ Lafiya ‘kalau Mimi ya kike?”. 

“ Fine Alhamdulillah
” sai kuma ta kalli Aunty Shukura itama “ Aunty  Shuky ina kwana.”

“ Ke rabani da wannan banzan sunan naki . Me wani Shuky ? Yau iskancin akai na zai ‘kare ?.”

“ Kai Aunty Shukura amma ai sai ki amsa gaisuwar kafin komai ya biyo baya .”

“Okay lafiya ‘kalau
”

Mimi zata yi magana Ameerah ta d’an mi’ke tsaye , toh gaskiya Aunty Feedy da Aunty Shukura an gama daku, mu da muke tare a cikin gidan nan yau ko kallan inda muke batai ba , kafin ma na manta abunda nake san fad’a nidai koma wana turare ne kika shafa a jikinsa ina so kafin a yi zancan kyaun da kikai, Aunty Feedy Zarah wai duk baku ji ‘kamshin turaran nan ba?.” 

“ Kinsan Allah Ameerah maganar turaran nake ta so nayi , tun saukowarta, ni kaina turaren ya mun ‘kamshi.” Cewar Aunty Shukura .

Aunty Feedy murmushi tayi tana girgiza kai “ ai bama sai nayi magana ba , dan ban fita daga gidan nan sai ta fad’a mun inda ta siyo dan nima ya mun ‘kamshi, in kuma ba zata fad’a ba ta bamu nata.”


“ Ameerah wallahi kinfiya bragging da yawa , turaran nawa ne baku san ‘kamshin sa ba? Kawai dai kun dad’e baki ji saba , kin tuna last year wani turare da nayi order na maiduguri?”. 

Kanta Ameerah ta d’aga mata alamar “ Eh..”

“ Toh shine 
” cewar Mimi.

‘Karamun harara Ameerah tayi mata “ Nidai ban yadda ba .”

Irin kallan da Ameerah tayi mata itama Mimi shid’in tayi mata “ Toh kar Allah yasa ki yar da mana , daman nace ina so ki yadda?.”

‘Kara hararanta Ameerah , har za ta sake tanka mata sai ta kalli Zarah da take faman yi musu murmushi tunda saukowar Mimin. 

“ Mene ne wai sai faman murmushi kike Zarah, ko magana ba naji ba kiyi ba , yau azumin magana kike kome? 
And Besty d’in taki ce baki gane ba ko kuma kyaun d’inta ne ya soma rud’ar ki?.”

Kafin Zarah ta bud’e baki tayi magana Mimi ta d’an doki kafad’un ta cikin wasa sabida tana kusa da ita “ Kema iskancin ki ba kowa ya ‘kyale ba, idan na biye miki haka zamu kai azahar muna cacar baki, bari naje na gaishe da Mamy , Allah yasa Baffa bai fita ba .”

“ Baffa yana nan , nazo muje?”. Cewar Ameerah.

“ Yeah why not ..”

Kallan Zarah da bata tanka ba Aunty Shukura tayi “ Zarah wai lafiyar ki ‘kalau kuwa yau? Ko fad’a kukai da Mimin ne ? Naga kin canza kamar ba Zarahn da na sani ba ?”.

“ Aunty Shukura ko d’aya fa , yau kai nane yake d’an mun ciwo shiyasa kika jini haka”

“ Amma da kika sauko ai ba haka kike ba? Taya tun d’azu ciwan kan naki bai canza ba sai yanzu?” Cewar Ameerah .

Kallan Ameerah, Mimi tayi “ Ki dena ma exaggerating abu , babu wani abu da ya had’a mun , karki ma wani tunani negative , tunda tace kanta ciwo yake toh may be ciwan kan take , and kowa akwai lokacin da yake so moody 
.”

Shiru kowa yayi , yana jiran jin me Zarahn zata ce , ita kuma Mimi batasan su Aunty Feedy suyi wani tunani daban akan Zarah idan ta fad’a musu actual abunda ya faru, shiyasa ta kalli Zarah kamar yadda itama Zarahn ita take kallo babu yabo babu fallasa “ Ki taso muje mu gaishe da su Baffan mana , in kuma ba zaki iya ba gasu Aunty Shukura nan sai su d’auko miki maganin ciwan kai , Allah ya ‘kara sau’ki..”

“ No bari na taso muje..” cewar Zarah tana mi’kewa tsaye . 
Daga nan babu wanda ya sake cewa komai , yan mata ukun suka jera zuwa part d’in su Mamyn.

Lokacin da suka shiga cikin falon , Mamy da Baffa ßuna zaune suna hira , shigowar su Mimin ne ya dakatar dasu daga hiran da suke . 

Wajan Mamy , Mimi ta soma zuwa , harda bata d’an side hug tana fad’in “ Mamy na ina kwana
” 
Hararan ta Mamy tayi kad’an tana fad’in “ Ni d’aga ni , karki ‘ballani haka kawai
”

“ Kai Mamy
”

Harararta Mamy ta kuma yi irin na wasan nan , ‘bata fuska Mimi tayi ta koma side d’in Baffa “ Baffa na ina kwana , ka tashi lafiya?”

“ Ai yau nayi tunanin ba tani kike ba , shiyasa na tsaya na jira naga nid’in zaki kulani ko wajan Mamyn kawai kikazo?”.

“Haba Baffa ni wajan ka nazo ma , ba wajan Mamy ba , bakaga yadda Mamy take faman ture ni ba , kamar irin na isheta d’in nan .”


“ Daman kin ishe ni mana , wa yace miki baki ishe ni ba?.” 


“ Baffa kaji ta ko?”. 

“ Rabu da ita Mimi, kin tashi lafiya ?” 

“ Lafiya kalau Baffa .”

Kallan su Ameerah Baffa yayi “ ‘ Yan matan Baffa , anya baku kuka bata shawarar zuwa ba ? Dan nasan halinta da shegen bacci.”

“ Ai Baffa kamar kasani kuwa
” cewar Ameerah tana dariya ‘kasa ‘kasa ganin yadda Mimi take jefo mata harara..

“ No wonder ! Zarah ke kuma ya naga kinyi shiru , tun shigowar ki ko akwai abunda kike so?”

“ Baffa babu abunda nake so wallahi 
”

“ Good..” cewar Baffa . 

Kallan Baffa , Mimi tayi “ Baffa please yau zamu iya fita haka mu d’an zaga gari?”.


“ Gari kuma Mimi? Amma ke da suwa zaku je ?”

“ Baffa iya mu uku, sai su Aunty Shukura kuma da zan tanbaya idan za taje .”


“ Yanzu Mimi in banda rigima irin taki taya zaku fita , iya ku kad’ai mata , ina lefin ku saka d’aya daga cikin Uncles d’in ku su raka ku, ko kuma suyi muku arranging fitar naku, amma bawai ku iya mata ku fita ba , ban yadda da wannan sakacin ba .”


“ Toh Baffa ! Yanzu idan muka tanbayesu zaka bari muje?”.

“ Why not , kuje tun wuri ku tanbaye su , kafin su fita , dan idan suka fita nidai babu ruwana a cikin wannan maganar.”

“ Okay Baffa mun gode bari muyi sauri 
”.

“ Tom Mimi idan kun tashi tafiya kuzo Mimi zata baku kud’in da zaku kashe , kuma banda ciye ciyen za’ki kunjini dai ko?.”


Cikin farin ciki duk suka amsa masa da “ Toh Baffa.” Daman kuma sun dad’e basu fita ba tun lokacin da suka je saloon d’in nan . 


Suna fitowa Ameerah ta d’ane Mimi saura kad’an su fad’i ‘kasa “ Kai Mimi kinji yadda naji dad’i daman na kwana biyu ban fita ba aushe yau akwai casu
”

“ Kin manta Club aka ce za’a je da zaki ce zamu sha casu?”

“ Kefa matsalata da ke Mimi wata rana kamar na wanke face d’in ki da mari , toh daman a iya club ake cashewa? Ai wallahi tunda Baffa ya amince muje , yau fita babu fashi , insha Allah dan ko ‘karyar rashin lafiya ne sai nayi sabida su Uncle Abba su dawo amma dai mu soma zuwa part d’in nasu .”

Kallan jikinta Mimi tayi “ Okay ku jira ni bari na saka top d’inta , idan na fita haka Mamy ta ganni rai na sai ya ‘bace .”


“ Okay but please kiyi sauri kinji?”

Kanta Mimi ta jinjina mata alamar toh , ta wuce sama sai alokacin Ameerah ta kalli Zarah . 

“ Zarah wai mene ne wannan abunda kike yi ne ? Na lura tun d’azu idan an kawo maganar Mimi sai ki dinga faman kakkaucewa , kamar bakyasan kiyi maganarta ? Bayan ba haka aka saba ganin ku ba , atleast ni muna fad’a wannan is a usual thing , kuma kowa yasan ba ko da yaushe muke ji tuwa ba but yet time to time muna shiri da ita , ba kamar ke da kowa yasan cewa kullum kuma tare ba , aga kuna irin haka , zaki sa kowa yayi questioning naki, tunda ita Mimi ko kusa bata nuna akwia wani abu a tsakanin ku ba .

Look idan bakyasan fad’an abunda ya had’a ku, am fine with it , beside i don’t even care , kawai ki samu ku dawo normal d’in ku yadda kuke , da ace dani take fad’a wannan who give a damn ? Kowa yasan zafin kan mu baya jituwa amma tun jiya kike behaving somehow .. 

Are you okay?.”

“ Hmmm Ameerah kenan , karki manta Mimi best friend d’ina ce so it’s normal dan mun d’an samu matsala , but I hate it idan mutum yayi abu ya nuna kamar besan ma yayi ba . 

Yanzu yadda nake d’aukarta a matsayin Bestfriend dina haka ta d’auke ni? No 
. 

Kawai am just a cousin to her abi, har cewa Mimi nayi zan dawo d’akin ta da kwana let’s be sharing thing together ta’ki yadda , amma shine yanzu zata kawo wata wai har ta zauna kusa da ita , it means she don’t trust me , toh me yasa zan dinga manne mata nima?”.


“ Zarah you’re Mad 
” cewar Ameerah , ba tare da ta kuma cewa komai ba tayi wucewarta , ta bar Zarahn a tsaye ita kad’ai. 


***** Lokacin da Mimi ta dawo , ta saka white light doguwar riga me fad’i akan rigar jikinta , it seems shine complete set d’in jirar. 

Daga Mimi har Ameerah babu wanda ya ‘kara biyewa Zarah even though tare suka nufi part d’in su Uncle Abba . 

Ganin ‘kofar wajan a kulle , Mimi ta furta “ Ameerah ko kiran su zamuyi idan Ɵuna nan? Ji yadda ‘kofar part d’in ya ake a kulle kuma duk cikin mu babu wanda yasan pin d’in wajan, ya zamuyi kenan?.”


“ Okay kinsan me ya kamata muyi”. Cewar Ameerah . 

Girgiza mata kai Mimi tayi tana jiran jin feedback d’inta . 

“ Okay  yanzu zan kira Uncle Abba , ke ki kira Uncle Saleem , Zarah kuma ta kira Yaya Sadiq muji ko d’aya daga cikin su yananan, idan ma basa nan ko Uncle Abba ne sai mu ro’ka if he’s less busy
.”


“ Okay bari na kirasa muji.” Cewar Mimi tana dannan wayarta itama Zarah Sadiq d’in ta kira sai dai duk sun mammatsa sabida suji dad’in yin wayar. 

Sai kuma ga baki d’ayan su , fuskokin su yayi looking so disappointed , suna cire wayoyin a fuska. 

Sai kuma suka ßaka dariya at the same time .

Zarah ce ta soma cewa “ Yaya Sadiq yace baya kusa , sai dare zai shigo cikin Abuja ma .” 

Ameerah kuma ta furta “ Uncle Abba kuma yace mun yana da meeting by 4 which is very much important
”

Sai aka kalli Mimi ana jiran jin me zata ce akan Uncle Saleem . 

Cikin dariya ta furta “ Ni ko sauraro na bai yi bafa kamar yana tare d friends d’insa , ya saka wayar a wajan Music.”

‘Karamun dariya Ameerah tayi “ Wallahi Uncle Saleem bashi da M wani lokaci? Toh yanzu yaya zamuyi? Haka zamu fasa fitar?”.


“ Toh ai we don’t have any option, sai dai mu tafi gardening kawai muyi ordering snacks haka , mayi party na can ? Ko ya kika ce?.” Cewar Mimi. 


“ I have a suggestion
..” inji Zarah . 

Kowa ya kalleta yana jiran jin abunda zata ce. 

Itama kallan su tayi kafin ta furta “ Why not tunda basa kusa, and we have time yanzu kafin anjima , muyi decorating garden d’in? Tunda duk muna da abubuwan, then sai muyi ordering snacks d’in , beside  sai mu barwa su Hauwa’u su gyara garden d’in, mu kuma mu girka wasu abubuwan da drinks haka kafin orders d’in mu yazo bayan sallahr isha’i ai kowa yana gida, it will just look like small gathering Abi?.”


“ Yeah it’s nice idea but in mukace zamuyi , akwai a lot of abubuwa and kamar ba zamu kai har zuwa time d’in ba 
.” Cewar Mimi.”

“ Like seriously? Mimi za’a iya akwai organizing abubuwan da za’a girka zamuyi yanzu , kowa ya d’auki nashi. Like kamar yanzu Mama , Larai ( Me aikin su Ameerah) , ga su Aunty Feedy , Aunty Shukura , shine ba zamuyi iya ba ? Just yanzu karma mu tsaya ‘bata lokaci tunda ba wani abubuwa masu yawa za’ai ba . 

Zan saka su Larai su gyara garden d’in and every decoration suyi tunda ba tun yau suka soma yi ba . 

Zan tanbayo mana , any available restaurant da zamu yi order d’in snacks atleast everything 50-50 , like Mini burger , samosa , mini chicken sandwich , prawn tempura , mini meatpie da kuma Chicken skewers.”


“ Yanzu duk wannan abun da kika lissafo ,kina tunanin zamu same su a yau ? Nifa gani nake kamar babu enough time wallahi , beside ba iya snacks za’ayi ba , drinks da food duk ya za’ayi da  su , cikin ‘kan’kanın lokacin nan?.”


“ Mimi ya kike abu kamar yau kika saba , kawai idan idea d’ina baiyi ba , ki fito fili ki fad’a , ba sai kin dinga wannan kauce kaucen ba it’s simple sai kice baiyi miki, looks bari ma kawai na wuce d’aki, duk abunda kukai deciding you can tell me .”

“ Dallah tsaya .” Ameerah ta d’an ri’ko Zarah da take san barin wajan , dan Mimi ko tanka mata ba tayi ba .

Hakan yasa Ameerah ta kallesu duk su biyu “ You guys idan abunda zaku tsaya yi kenan gwanda ai kawai ku fito fili ku fad’a mun, ya za’ai da na kamo nan wajan , ku zille idan ba zakuyi ba duka kawai ku fad’a mun haba wai mene ne kuke yi? Idan kuma a fasa abun nan ne duka kawai ku fad’a safiya ce yanzu fa ko 12 ba tayi ba amma kuna yin wad’an nan abubuwan
”

“ Okay it’s fine shaa zamu d’auki suggestion d’in nata , and sai mu girka abu simple simple ba masu yawa can sosai ba .”


“ yawwa ko kefa yanzu naji batu, Zarah ke kuma fa ?”.

“ Yeah nima na d’auka d’in , zanyi wa su Mommy magana in yaso zuwa lokacin nasan an gama duk wasu necessary abu da ake bu’kata.”

Daga nan sukai taking plan d’in abubuwan da ya kamata su tsara , kowa yayi part d’insa . 

Mimi tana zuwa Mamy ta sanarwa and  Mamy tayi supporting hakan which amaimakon a girka abincin dare anjima sai ayi abunda za’aci kawai in general , tunda akwai komai da komai, kuma akwai chefs a gidan ba d’aya ba , ba kuma biyu ba . 

Mimi is so much a fav of drinks , musamman natural drinks , shiyasa tun yanzu kar abu su ca’kud’e mata ta had’a tea and omelette tacı , sannan ta soma fito da abubuwan da za tayi drinks dasu tunda so take shaf shaf kafin azahar tayi making 3 drinks and with the support of Aunty Shukura da ta kira suka soma had’a drinks d’in su.

Pineapple and ginger juice , watermelon juice ,ice tea , Hibiscus/zobo mocktail , and best fav wato fruity juice . 

Su da suka ce zasuyi 3 drinks sai gashi sunyi har 5 drinks kuma da yake drinks d’in duk ba masu wahala bane , 2:15 sun kammala komai , sun saka a fridge sai suka kira Hindu( one of the maid ) tazo ta gyara kitchen d’in , su kuma suka wuce d’aki sabida suyi sallah. 

Mimi tana idar da sallah d’inta ta sake saukowa kitchen , Allah ya taimaka su Mamy za suje maid House kitchen suyi preparing wasu abincin a can. 

Haka Mimi ta sake dawowa kitchen, ta soma had’a cup cake , which shi kuma ya d’auketa lokaci , tunda har sai da ta ajje taje tayi sallar la’asar , kafin ta sake dawowa ta ‘karasa. Tana gamawa shima bata zauna ba tunda yamma ta riga tayi, anymoment from now magrib za tayi , tuni ta d’ora     Creamy pasta ta soma had’a coleslaw, even though ba shi kad’ai za tayi ba , har da garden salad da zata had’a kad’an. 

Duka wad’an nan abubuwan da tayi ba masu yawa tayi ba sabida bataso a bar su. 

Tana kitchen d’in nan akai sallahr magrib , bata ma sani ba , sai daf da isha’i tukunna ta kula da time , Alhamdulillah kuma ta gama ma abunda take . 

Da sauri ta wuce d’aki tayo alwala ta tada sallar magrib. Tana idarwa bata ma tashi daga daddumar ba , sai faman sauke ajiyar zuciya take dan babu ‘karya ta gaji , ‘kafafuwanta har sun soma tsami, ga yunwa da take ji dan tun tea da omelette da taci d’azu ba ta sake saka komai acikin cikinta ba . 

Tana zauna akan dadduma akai, kiran sallahr isha’i , shiyasa tayi sallanta, tayi shafa’i da wutri d’inta , tukunna ta shiga wanka. 

Ta d’an jima tana sakarwa jikinta ruwa, haka kawai ta tsinci kanta da smiling sabida tunano ruwan jiya da tayi, a time d’in ta tuna da kayanta da ta bari, a bayyane ta furta “ Allah yasa bai gansu ba .” Cikin toilet d’in . 

Da ta fito cikin simple Abaya ta shirya , sky blue tunda a garden za’a zauna da kowa da kowa , ya kamata tayi modest dressing.

Komai ta sa yarinyar nan, kyau yake mata, kamar dan ita daman aka yi su.
Lipstick kawai ta saka a bakinta , ta fesa turare sabida ta gaji babu wani abu da kuma zata iya sake yi a yanzu Indai ba cin abinci ba .

Fitowa tayi daga d’aki tana tunanin, me ya kamata tayi , taje ta d’auko kayanta yanzu ko kuma ta bari gobe da sassafe idan ya fita taje ta d’auka ?. 
Tana wannan tunanin ta kalli d’akin Aya, yau ga baki d’aya bata sanya ta a ido ba , “and may be kuma bata nan” Mimi ta raya cikin zuciyarta tana saukowa ‘kasa . 

Kitchen ta soma shiga ta tabbatar da komai intact yadda yake , sai ta d’auki waya ta kira Ameerah , nan Ameerah take sanar da ita already an kawo snacks d’in su da sukai already , har an fara kai komai da komai garden d’in tunda yanzu har 8 ma yayi , which alokacin ne ake saka tsammanin ganin kowa da kowa ya dawo cikin daga aiki duk da cewa wasu har sun dawo.

**Ta dad’e a compound tana tunanin taje ta d’auko kayan nata ko kuma ta bari zuwa da safe , amma kuma bataso yaga bra da pant d’inta 


Daga ‘karshe dai ta yanke hukuncin zuwa d’aukowa idan ta tabbatar da baya nan, amma indai taga part d’insa da haske , zata ha’kura zuwa safiya sai ta d’auko. 

Part d’insa da ta nufa aushe akan idon Zarah, dan a lokacin ta fito daga nasu part d’in zata je part d’in su Ameerah . 

Wani malulun ba’kin ciki ne ya tsaya mata a rai, taji duniyar ga baki d’aya tayi mata d’aci , har wani jiri jiri ta soma ji lokaci d’aya da taga Mimi ta nufi part d’in Moh. 

Dan ba wannan ne karo na farko da ta saba gani tana zuwa ba , part d’in da ko ita da take mutuwar sansa bata ta’ba shiga ba , ko taga yadda yake , amma haka Mimi take shige da ficenta a duk lokacin da ta ga dama . 

( Zarah kiyi ha’kuriđŸ„čđŸ„čđŸ„čđŸ„č Kishin AyyyyyyyđŸ„č😂đŸ•ș).


Mimi tana zuwa successfully Moh baya nan , fitila kad’an ta kunna a falon sabida da duhu, babu shiri ta ruga a guje zuwa d’akinsa , kar tsautsayi yasa ya dawo ya tarar da ita a d’akin batasan me zata ce masa ba . 

‘Dakin yana nan tsaf tsaf kamar ba’a shigarsa , ga ‘kamshin turaransa da yake faman bula’i a cikin d’akin. 

Bata ma tsaya ‘karewa d’akin kallo ba , tayi sad’af sad’af ta wuce toilet sabida tayi abunda za tayi kafin ya dawo. 

Tana shiga toilet , kaya yace d’auke ni Inda kika ganni. 

Babu kaya babu alamar su, ga baki d’aya sai da ta duba ko ina na cikin toilet d’in babu kayanta. 

Hannu ta d’ora aka tana fad’in “ Na shiga uku na 
”

Kamar mara gaskiya haka ta sake fitowa daga toilet d’in, ta d’an wawwaiga d’akin ko zata hango ta inda ya ajje su, amma babu kaya babu alamar su, bata da wani choice bayan ta ha’kura da kayan kawai , tunda gashi har taga 2 missed call d’in Ameerah da kuma 1 missed call d’in Mamy , tasan nemanta suke kuma tana sane ta saka wayan a silent yanzu . 

Mimi ta fito daga d’akinsa kenan, taga hasken falon ya ‘karu, d’an tsugunnawa tayi tana le’ko ’kasan falon yadda ba za’a ganta ba . 

Idanuwanta kawai suka ci karo da bayan Moh. 

Yana tsaye , ya juyawa inda take baya , da kuma waya a kunnansa, alamar waya take . 

Cikin zare ido tayi saurin ja baya , saura kad’an ta bige ‘kafarta. 

Sad’af sad’af ta koma cikin bedroom d’in, amaimakon ta shiga wani yadda idan ya fita sai ta fito ina , tunanin ta ya toshe sai ta sake ‘komawa d’akin tana faman safa da marwa tana tunanin yadda za’ai ta fice ba tare da ya ganta ba . 

Mimi har da cire takalmi sabida kar yaji ‘karar takalminta , ta ri’ke su a hannu, ta koma can baya wajan toilet yadda za tayi saurin yin reaction d’in buya karya ganta, ta nutsu kuma sosai, ta kasa kunne sabida taji takunsa. 

5 minutes d’in farko bata ji takunsa ba sai a next minute da alama kuma d’akin yake dosowa , ai babu shiri ta fad’a toilet tana waige waigen yadda za’ai ta rufawa kanta asiri ta ‘buya. 

Gatanta d’aya akwai wani doguwar wardrobe a ciki duka kuma bathrobe ne da kuma towel a ciki, wasu a sa’kale wasu kuma sababbi ne bama a cire su daga cikin ledar su ba. 

Cikin wanda suke a rataye ta shiga ta ‘buya kamar ‘bera , ko hango ta ba’ayi sabida yadda ta lafe a cikin wajan zuciyanta yana duka 100 100 bama uku uku ba . 

Ta d’auki kusan 20 minutes a cikin wajan nan sai taji an bud’e ‘kofa an shigo cikin toilet d’in, ko ina da take cikin kayan bata ganin wanda ya shigo dan har sunkuyar da kanta tayi,  ta ‘kudundune jikinta sabida masifar tsoran da ya kamata , ga kuma ßu Ameerah da suke faman kiran ta, ciki kuma har da Zarah . 

Da’kyar dai ta samu ta turawa Ameerah short message , sabida ta dena kiranta amma kuma Zarah bata dena kira ba , kamar me gasar call, da kiran farko yayi cutting take sake yin wani kiran , haka ta dinga jejjerawa Mimi kira , Mimi tana gani ita abun ma mamaki ya soma bata dan idan aka ce mata Zarah zata dinga wannan d’abi’un baza ta ta’ba yadda ba , but here she is tanayin yadda taga dama , amma a hakan Mimi tana mata uzuri ne , thinking ko akwai abunda yake damunta which she need a little bit of space.

Tana tsakiya da tunanin Zarah , taji an  kunna ruwa, a firgice ta soma nanata “ Innalillahi wa inna ilaihi raji’un , Innalillahi wa inna ilaihi raji’un” kamar wacce akayi wa mutuwa , sai kuma duk adduar da tazo bakinta, sabida ga baki d’aya ta har gitse , ita kad’ai sai zufa take yi na rashin gaskiya . 

Bayan kamar 20 minutes aka kashe ruwan, Mimi dai tananan a san dare a toilet babu uhmm babu uhmm uhmmm. 

Bayan kamar 5 minutes sai taji kamar an bud’e ‘kofa an fita , sai ta bata kamar 2 minutes sabida tanaso ta fito daga cikin wardrobe d’in ko ta samu ta sha’ki iska
..

Tana fitowa daga cikin wardrobe , idanta yayi mata mummunan gani, sabida Moh ne a tsaye daga gefen wardrobe d’in , yana sanye da towel a ‘kugunsa, sai kuma bathrobe amma bai rufe ta ba, hakan ya bawa faffad’an ’kirjinsa daman fitowa waje , ga kuma alamun yankan gwanaki da bai gama wucewa ba. 

‘Kirjinsa sai faman d’igan da ruwa yake . Gashin kansa kuwa sabida a ji’ke suke wasu duk sunyi gaba wajan idanuwanta. 

That man look so sexy , ga yadda idanuwansa suke gaman lumshewa , kamar wanda yayi shaye shaye ko kuma ace bacci, nan d’in ma kuma ruwan kanshi yana d’igowa a fuskarsa da take da ruwa itama .

A rud’e ta ‘kwalla ‘kara tana komawa cikin wardrobe d’in, daga ciki ta ‘kudundune , bathrobes d’in ciki, a dole zata kare kanta.

Hannu yasa ya mayar da gashin kansa da sukayo gaba, yana kallan inda ta shiga . 

“ Zaki fito ko nazo na fito dake ?”. 

Cikin shash she’kar kuka ta soma fad’in “ Wallahi ba da gangan na shigo ba , kayana nazo na d’auka, dan Allah kayi ha’kuri Uncle Moh.” Muryanta har rarrabewa yake sabid kuka da yake son fin ‘karfinta. 

Bai ce komai ba , hakan yasa ta kuma fad’in “ Don Allah Uncle Moh kayi ha’kuri wallahi bazan sake ba , Dan Allah, Dan Annabi.”


“ Mimi come out 
” yayi maganar cikin low turn voice , amma kamar ya sake ce mata ta zauna a ciki ta ‘kara ‘kwa’kwube  bathrobe d’in da suke wajan. 

A hankali ya soma takowa wajan, hannu yasa , zai cire yaji ta ‘ka’k’kame su da iya ‘karfinta . 

Daga inda yake ta waje , yasa hannu ya ‘ban’bare hannunta duk yadda take san ‘kwace hannunta ta kama bathrobe ta kasa sabida ba ‘karfin su d’aya ba , yadda yaga tana faman ciccijewa a ciki sai da ya d’an murmusa la’b’bansa kad’an .

Da hannu d’aya yasa ya had’e both hannayenta tukunna ya janyota da ‘karfi, a tunaninta ‘kasa zata fad’i , har ta rufe idanuwanta sai kawai ta jita a sama, da sauri ta bud’e idanuwanta, a kafadunsa ya sa’bata ya fito daga toilet , sai kawai ta sa kuka , dan tasan yau ta shiga uku tunda ta zauna a toilet har yayi wanka. 

Yana ajjeta aka gado tayi saurin mi’kewa tana girgiza kai “ Dan Allah, Dan Annabi kayi ha’kiri Uncle Moh wallahi ni ban kalle ka ba , ido na ma a rufe yake dan Allah kaji?.”

“ No kin kalleni mana, ba wanka kike so muyi ba ? Oya cire kaya maza maza basai kin ‘buya a toilet d’in ba next time..” 

Har ‘kasa ta tsugunna tana had’e hannayenta biyu , muryanta har ya soma ‘ko’karin dusashewa “ Kayi hakuri bazan sake ma , Dan Allah ! Dan Allah ..”.

Hannunsa ya mi’ko mata “ Bani hannun ki
” 

Amaimakon ta sake basa hannun sai ta ‘boye su a ‘kirjinta . 

Yana zuwa bama hannun ya ri’ke ba , ga baki d’ayanta ya d’aga ita kuma sai ‘ko’karin zillewa take . 

Hannu yasa ya matsar da kayan gaban madubi wasu har suna fad’uwa ‘kasa amma ko kallansu bai yi ba , ya d’orata akan wajan, ita kuma duka hannyenta Ɵuna kan face d’inta tama’ki yadda ta bud’e su.


‘Dan ran’kwafowa yayi dai dai fuskarta “Meyasa kika saka turare da yawa haka?.”

“ Uncle Moh Dan Allah kayi ha’kuri.”

“ Answer me ..” taji saukar muryarsa sai dai cikin soft yayi maganar . 

Ba tare da ta bud’e fuskanta ba, ta furta “ Babu kowa , gathering muka had’a nida Ɵu Ameerah kuma kowa yana garden yana jira na dan Allah ka bari naje kar Mamy tayi ta nemana.”

“ Karki sake saka turare me yawa haka . Okay 
” 

Da sauri ta jinjina masa kai amma ta’ki bud’e idon. 

“ So now back to business, ko ki bud’e idanki, muje muyi wanka da kike so , ko kuma ki bud’e idanki and do something that I will forgive you , or mu zauna haka har a gama gathering d’in.”


Mimi tayi shiru tana tunanin maganarsa, tasan ko tana aljanu ne bazata ta’ba gigin cewa za tayi wanka dashi, and dole taje gathering din nan sabida kowa zai je by now tasan kowa yana can yana jiranta . 

Her only choice yanzu shine taji mene ne second option d’in. 

Da kyar ta iya fad’in “ Mene ne second option d’in
”

Hannu yasa ya nuna mata lips d’insa, wani irin zaro ido Mimi tayi tana kallansa , shima kuma ya d’an bud’e idansa yana kallan nata .

Girgiza masa kai tayi alamar a’a sai yayi kamar bai ganta ba kuma tunda ya fad’a condition d’insa tasan dole tayi guda d’aya idan ba haka ba kuma zai yi abunda yace .

Sakin hannunta tayi , tayi ready yadda tana yi masa abunda yace zata gudu, yana kallanta amma bai ce mata komai ba . 

Unexpected yaji tayi masa peck d’in a baki zata sauka , yayi saurin mayar da ita yana fad’in “ I said kiss not peck
” 
Kafin tayi wani magana ya soma tsotse bakin yarinya. 
Ta saka hannu zata turesa , ya ri’ke both hands d’in nata. 

Sai da yayi yadda yake so, tukunna ya saketa, ba tare da ya sake kallanta ba sabida idanuwansa da ya lumshe , ita kuwa ta fita daga d’akin aguje . 

Har ta sauko ‘kasan gudu take , kamar wacce aka koro. 
Har ta wuce 1 sitter d’in falon taji muryar Aya . “ Little Mimi, be careful
”

Da sauri Mimi ta tsaya , tana juyowa a time d’in ne kuma Aya take mi’kewa tsaye , cikin sauri Mimi ta kawar da kanta , duk a tunaninta  Aya ta bane abunda Moh yayi mata . 

“ Moh yace na zauna na raka ki, should i follow you ?.” 

Kanta kawai Mimi ta d’aga mata alamar eh, dan ta kasa magana ma, aushe duk wannan abun Moh yasan tana cikin part d’in. 

Har ta fad’a tunani Aya ta d’an ta’bata, firgigit ta kalleta , ita kuma ta furta “ Let’s go
” 

Yanzu ma da kai Mimi ta amsa mata , ta fito cikin sanyin jiki dan ji take kamar har yanzu bakinsa yana kan nata. 


Garden suka nufa . 
Tun daga nesa suna hango yadda aka ‘kawata cikin wajen, su Mamy suna Zaune tare da Mommy da kuma Mama
 
Su Uncle Saleem kuma suna tare da su Baffa. Sai su Ameerah da zaune ga baki d’aya da sauran ladies d’in gidan, har da Aunty Baby da Kuma ‘yan cute yaranta Ameer da Ameerah. 


Garden d’in sosai yayi irin luxury outdoor family gathering d’in nan , duk da ayau akayi komai , amma komai ya had’u so perfectly. 

Daga kan ciyawan garden d’in da suka sha gyara aka shimfid’a manyan persian rugs masu laushi.  Sannan aka saka manyan cushions masu kyau da pillows masu laushi akan su, yadda wajan zai yi wa duk wanda ya zauna dad’i. 

Daga tsakiyar garden din an anjiye manyan low wooden trays masu kyau , wad’anda akayi musu ado da ‘kananan vases na furanni, candles da decorative pieces . 

Ba’a saka manyan dinning tables ba ko kuma kujera a wajan ba , komai an tsada shi yadda za’a zauna a ‘kasa irin so elegant moroccan inspired outdoor seating d’in nan. 

Gefe d’aya akwai long elegant food station , an rufe shi da fararen linen masu kyau, akai aka jera abincin da aka girka kala kala , cikin manyan dishes akwai grilled chicken, lamb chops, prawns, roasted potatoes , salad da sauran su. 

A kusa da su akwai trays na mini snacks d’in da akai , su cup cake, sandwiches ,spring rolls, samosas, chicken skewers da pastries.

Ga kuma manyan glass dispensers cike da colorful fruits drinks , passion - fruit mocktails, ice tea , watermelon juice da wasu drinks d’in. A kusa da su akwai glass na drinks , kankara , lemon slice da kuma fresh mint. 


An kunna golden garden light akan lawn d’in wasu daga cikin bishiyoyin da suke wajan. 
Wasu kuma an rataye su daga ßaßsan bishiyoyin, kamar ‘kananan glowing bulbs, sosai garden d’in yake da haske . 
A kusa da cushions kuwa har ‘kananan lantern masu haske aka saka , wajan sai ya bada calm , expensive atmosphere. 


Garden d’in yana da cream beige, da soft gold da green color palette, babu wani abu mai yawa a cikinsa. Decoration d’in wajan was so so very amazing . 

An yi decoration d’in waje yadda ya kamata, family ga baki d’aya ana hira, da wasa da dariya wasu kuma ßuna cin abinci, wasu kuma suna cin snacks da drink. 

İta kad’ai ce babu , sai Moh da ko sau d’aya bai ta’ba shigowa irin wannan abun ba . 

Ga baki d’aya shigowarta sai yasa kowa ya d’ago kai ya kalleta . 
Mamy tana shirin sakar mata harara sai ta ganta tare da Aya hakan yasa mood d’inta ya canza ya dawo normal . 

Zarah kuwa kallan sama da ‘kasa take bin Mimi dashi, idanuwanta kamar zasu fad’o ‘kasa sabida irin yadda take faman hararanta a fakai ce , tun d’azu take jiran taga ta inda zata ‘bullo amma sai yanzu take zuwa , babban ‘karin ba’kin cikin ma yadda ta ganta tare da Aya.

‘Dan juyowa Mimi tayi ta kalli Aya , ita kuma ta jinjina mata kai alamar taje
 

Mimi wajan su Baffa ta soma zuwa inda mazan suke, yau Uncle Bashir kwata kwata babu wannan had’e ran, fuskarsa wasai da fara’a lokacin da yaga Mimi, ita kanta Mimi ta d’anyi mamakin yau fara’arsa. 

Duka sai da ta gaishe su dasu ko wanne ya amsa mata da kulawa , sannan ta juya side d’in su Uncle Abba suma tayi musu barka da dare .


Sannan ta koma wajansu Mamy ta gaishe da su Mommy da Mama da kuma kanta Mamyn. Still kowa ya amsa mata with care . 

Wajan su Ameerah ta nufa , ta gaishe da Aunty Baby daman itace kawai basu had’u ba , sai kuma Ameer da Ameera da suka soma faman dabai bayeta. 

Aya tana tsaye a inda take babu wajan wanda taje kuma , bata zauna a cikin su. 

Sai da Mimi ta juyo ta kalleta , fuskarta da murmushi ta nunawa Aya d’in kusa da ita . 
Anan ne Aya ta matso ta zauna, ßu Aunty Baby sai faman kallanta suke sabida basu santa . 

Nuna Aunty Baby , Mimi ta somayi, tare da gabatar mata da Aya , anan Aya tayi mata murmushi sannan ta mi’ko mata hannu, babu musu itama Aunty Baby ta mi’ka mata nata tare da gaishe da ita , sai Aunty Feedy , which sukai the same , already tasan Shukura amma itama sunyi shaking hannunta , kafin ta mi’kawa Ameerah hannu ita har ta mi’ko mata tana murmushi , itama murmushi tayi mata, saura Zarah da ta tsaya , tunda ‘Mimi ta zauna bata kuma cewa komai ba . 

Sai kowa ya kalleta . Da’kyar ta iya mi’kawa Aya hannu, ita kuma tayi wani murmushin gefen baki ta ri’ke hannun, Zarah zata saki sai taji kamar ta ri’ke hannun ne shiyasa ta d’ago tana kallan Aya d’in. 
Wani irin kallo da Aya tayi mata sai da tayi saurin d’auke kanta dan ji tayi har zuciyarta na bugawa . 

Daga nan Aya ta sakar mata hannu. 

“Mimi let’s get something to eat , tun d’azu nake faman jiran ki sai yanzu kika zo kowa ya’kicin abinci sai snacks ance ba za’a ci babu keba .” 

Juyawa Ameerah ido Mimi tayi tana fad’in “ Thank you dear .”

Ameerah ce ta soma mi’kewa , Mimi itama ta mi’ke , Aya itama haka ganin Mimi ta mi’ke sai Aunty Shukura dan Zarah tana zaune ko alamar tashi batayi sabida a excuse d’in da ta bayar kanta ne yake ciwo.

Yadda Mimi dasu Ameerah suke serving Aya ta tsaya kallo , bata ta’ba komai na wajan ba , amma kuma each and every thing da yake wajan sai da tayi scanning d’insa da ido. 

Gashi kai kawon da Mimi suke , idanuwan Aya yana kai, mutum sai yayi tunanin ko su Mimin kawai take , kalla, but the actual truth is that , ko wana mutum da yake wajan Aya tana observing movement d’insa .

Mimi a babban trays suka zuzzuba masu abubuwa da yawa , idan yaso mutum sai ya d’auki Wanda yake so yaci tunda ga plate da kowa zai zuba abunda yake so , da kuma lemo , haka suka gama serving kowa suma kuma sukai serving nasu . 

Lokacin da Mimi ta koma cikin su lokacin itama Aya ta dawo anan ne su Aunty Baby sukai serving haka kowa a plate nashi. 

Mimi dakanta ta zubawa Aya amma Aya ta girgiza mata kai alamar ba zata ci ba . 

‘Dan shiru Mimi tayi tana kallanta , sai kawai ta mi’ko mata nata plate d’in tunda the same food ne , nan ma Aya ta’ki amsa , sai water bottle kawai da ta d’auka tana nunawa Mimin, amma shima bata sha ba ta dai bud’e shi ne . 

Hakan kuwa akayi ‘yan mata matan nan aka soma cin abinci, Mimi taci snacks sosai, sai kuma roasted chicken da taci da salad , da kuma fruit, bayan su bata kuma cin komai ba . 

Garden ga baki d’aya ya d’au family vibes , kowa yana cikin raha banda Aya da bata magana kuma bata cin komai amma 80% idanuwanta suna kan Mimi
.

Kusan 15 minutes haka , lokacin bama a gama cin abinci ba , Mimi ta d’an dakata, sai ta saka hannu a wuyanta kamar abu ya cijeta , babu komai , sai kuma bayanta da ta soma ji ya fara ‘kai’kayi zuwa hannunta .
Da sauri ta ajje spoon d’in hannunta Aunty feedy ce ma take tanbayarta “Mimi lafiyan ki kuwa.” Mimi bata ce mata komai ba , ta d’an soma shash shafa jikinta . 
Ga baki d’aya sai suka dena cin abinci, Banda su Baffa da kuma su Mamy da basusan abunda yake faruwa .

‘Dan hannunta ta saka a cikin tana d’an shafawa kad’an . 

Da sauri Aya ta ri’ko hannunta tana fad’in “Mimi? Mimi?” Amma kan Mimi a sunkuye yake tana ta faman shafa cikinta ,  ga baki d’aya kuma sai suka tsorata suka nufi kanta , hakan yasa hankalin kowa ya dawo wajan yana tanbayar me ya faru , Ameerah da Zarah kawai suke fad’in Mimi, Mimi. 

Duka kowa da kowa sukayo kan Mimi, A rud’e Aunty Baby ta d’an d’ago face d’in Mimi, lokaci d’aya suka ga gefen fuskarta ya kumbura sosai, ga wahalar numfashi da take faman yi, hatta lips d’inta ya kumbura . 

Ga baki d’aya wajan ya hautsine cike da tashin hankali, Mamy tana ganin yadda Mimi ta dawo ta yanke jiki ta fad’i sumammiya , hakan yasa familyn aka rabu wasu ßuna kan Mamy wasu ßuna kan Mimi. 

Aya bata tsaya ‘bata lokaci ba kawai ta sa’ba Mimi a bayanta , tama ‘ki bari kowa ya d’auketa, ko nauyin Mimi bata ji ta soma ‘ko’karin gudu da ita a bayanta , a haka kuma tayi dialing number Moh 
. 

Ringing biyu ya d’auka, cikin sar’kewar murya kawai take fad’in “ Mimi Mimi
.” Kitt taji an kashe kiran

.



_________________

To be continued
 đŸ”„


Aysha Galadima đŸ€đŸż
***



***