Page 31
MISHAL
By AYSHA GALADIMAđ€đż
***
BOOK 1
Page 31
Aya bata tsaya tunanin kashe kiran da Moh yayi ba, sabida tasan a wannan lokacin baya gıda.
Da sauri ta nufi motar ta , Ameerah da su Zarah suna mara mata baya, ga su Uncle Abba ma , amma taâki bari kowa ya dâauketa.
Da kanta ta saka ta abayan mota , zata shiga driver seat Uncle Abba yayi saurin amsan key dâin , bai ma tsaya jin me zata ce ba ya shiga driving seat , ita kuma Aya tayi saurin komawa bayan motar kusa da Mimi, Uncle saleem ma ya shiga gaba , suka tayar da motar .
Suna fita motar su Ameerah tana bin su abaya , Allah ya taimaka babu cinkosun abun hawa , tun da alokacin goma har da kusan rabi , any moment 11 za tayi .
Sosai Uncle Abba yake gudu , mintina 25 ne ya kawo su NIZAMIYE HOSPITAL.
Already kuma akwai wanda Saleem ya kira tun kafin su âkaraso asibitin, shiyasa suna shigowa cikin Hospital dâin , Drs suka dâauketa zuwa Emergency Department babu âbata lokaci.
Tunda aka shigar da ita Aya ta jinginar da kanta jikin bango, ko sau dâaya bata dâago da fuskarta ba . Su Uncle Abba duk suna tsats tsaye , kowa kagansa zaka ga tsananin tashin hankali akan fuskarsa .
Sunanan wajan su Ameerah suka zo kowa yaci kuka ya gode Allah sabida abu ne da yazo very unexpected wanda makamancin hakan bai taâba faruwa da Mimin ba .
Ameerah tare da Zarah suka zo da Aunty Baby da kuma Mama ( Maman Ameerah ).
Mintuna goma sha shida a tsakani sai ga su Mamy, itama suma tayi , tun lokacin da aka fitar da Mimi, Baffa ya yayyafa mata ruwa, tuni ta farka tana ambatan sunan Mimi, ganin batanan ta dâaga hankalinta dole akayo asibitin da ita , itama .
Daga family gathering abu ya koma hospital gathering, gashi bazai yu ga baki dâaya kowa ya zauna a asibitin ba , da âkyar aka lallashi su Yaya Sadiq , Aunty Feedy , Aunty Shukura , da kuma Daddy da Momy suka koma gida , daman Ameerah tuburewa tayi ba zata koma ba ita da Zarah da an matsa musu kuma sai su saka kuka .
Har yanzu baâa fito da Mimi daga Emergency ba, a nan wajan Alâameen yazo ya tarar dasu , su Zarah sai kallansa suke , sabida basu sanshi ba , ganin ya nufi Aya tukunna suka gane wajanta yazo.
Ganin yadda ta jinginar da kai a jikin bango, yana zuwa ya dâan dâago da ita , itama kamar wacce zata fadâi âkasa, ba tayi kuka ba amma idanuwanta sunyi jajawur , fuskarta kwata kwata babu annashuwa âŠ
âDan janta yayi zuwa nesa kadâan inda babu muta ne , take a wajan hawaye ya soma sauko mata akan fuskarta .
Cikin sauri ta saka both hannuwanta , ta rufe face dâinta tana kuka kamar âkaramar yarinya.
â Hey itâs okay kalli yadda kike kuka da kamar âkaramar yarinya, itâs okay za taji sauâki Aya ki dena kuka.â
â AMI ( sunan da take kıransa) Ami ina Moh Moh? Yanzu me zance masa ya samu Mimi da wana ido zan kallesa , kana ganin yadda na dinga roâkansa akan zanzo gidan na kula da Mimi, da âkyar ya amince amma kalli babu wani kula da ita da nayi, da na sani nima naci abincin idan yaso koma mene ne ya faru da ni amma ba ita ba , me zance masa.â
â Itâs Okay Aya , number na kika kira ba ta Moh ba , by this time nasan yana cikin zirgi, kinsan dalilin tafiyansa da dalilin da yasa yau ya baki amanar Mimi, ya kamata ki nutsu ki mayar da hankalin ki waje dâaya , kafin ya sauka daga jirgi in sha Allah zamu bashi tabbacin tana lafiya .â
âAmi be dadâe da fita ba fa , ace daga barinsa gida wannan abun ya faru wallahi ko wane ne ya saka ta a cikin wannan condition dâin bazamu âkyalesa ba , shima sai ya dâan dâana abunda muka ji, ko me Mimi taji wallahi sai sun nunka nata sau 1000âŠâ
â Ya isa haka Aya, kiyi âkoâkarin kwantar da hankalin ki, koma mene ne zai biyo baya ,bayan mun tabbatar da lafıyarta a yanzu , already na tura gidan kome a ka ci a wajan zaâa fito dashi in details kuma duk girki dakai sai an gano da abunda aka girka , letâs first wait for the Drs , Okay?.â
Kai Aya ta dâaga wasa wani hawayen na sake sakko mata .
Hannu yasa a aljihu ya dâauko handkerchief ya miâka mata, yana mata alamar ta goge idanuwanta.
Babu musu ta goge hawayen, tana sassaita kanta waje dâaya .
Yana gani ta dawo nutsuwarta, ya radâa mata wani abu a kunne na tsawan mintuna biyu , bayan su babu wanda yaji me yake ce mata sai Allahn da ya halicce su.
Daga nan kuma ya fice daga wajan ga baki dâaya, at the same time kuma su Zarah suna âkara binsa da kallo ganin babu wanda ya kalla duk cikin wajan yayi ficewarsa .
Aya kuma tananan a tsaye sai faman kai wa da komowa take , tanayi tana duba time . Mamy tana zaune akan kujera , ganin ban tausayi, ga baki dâaya tayi wani iri, a hakan ma su Uncle Saleem da su Baffa suna kwantar mata da hankali ne , amma ko ruwa ta kasa kaiwa bakinta, tayi dana sanin yadda da taron nan a zuciyarta ya fi sau dâari .
Bayan kamar mintuna 35 aka budâe Emergency Room dâin nan , ga baki dâaya sukayo wajan Drs dâin suna jiran su ji ya Mimin take .
Kallan su Dr yayi cikin nutsuwa kafin ya sassaita muryarta â Ya kamata ku nutsu Dan Allah , sabida ta hakan ne zaku fi fahimtar abunda nake so ku fahimta .â
â Dr me ya sameta?â Aya tayi saurin katsesa , dan so take taji ya Mimi take , bayan surutun sa ba .
Shima ya fahimci abunda suke san ji kenan shiyasa ya âkara gyara muryarsa bayan 2 Drs da suke gefensa suka jinjina masa kai .
â Alhamdulillah zamu iya cewa mun gano bakin zaran , which yanzu yarinyar an yi stabilise Éinta , and mun samu nasarar ceto rayuwarta , wanda da ace kun sake 5 minutes baku kawota ba zaku iya loosing dâinta.
Beside nasan dole kunsan tana da AllergyâŠ. Tabbas Allergy dâinta ne ya tashi kuma tashi me âkarfin jiki, shiya haifar mata da kumburin fuskanta , da kuma âkaiâkayi da take ji a jikinta da kuma ciwan ido.
Gaskiya kunyi babban Ćakacı , har kuka bari taci abincin da yake dâauke da one of shellfish , which I mean âkaguwa ( crab ) .
Shiya janyo mata wannan severe allergie dâin, mun samu mun dai dai ta komai , but tana buâkatar bed rest kamar na kwana hudâu, sabida ta dena jin âkaiâkayin ga baki dâaya , kuma akwai drug da zamu dinga bata zuwa time dâin, daga nan insha Allah babu wani matsala sai dai ku dinga kula da irin abunda zata ci ku tabbatar babu âkaguwa ko a cikinsa.â
Yana gama bayanin jikin kowa yayi sanyi a wajan , banda Aya dan in sun fahimta a cikinsa abincin da aka girka ne wani ya sa âkaguwan kenan? Tunda already kowa ya dadâe da sanin tana da wannan allergie dâin but more than 12 years bai taâba tashi ba sai a yanzu da kowa yake tunanin ta warke tuntuni.
Now tanbayar shine wane ne yasa? Bayan matan gidan da kansu sukai girki bawai order sukayi ba .
Kallan juna kawai sukai , kowa ya rasa abunda zai ce .
Aya ce ta kuma kallan Dr dâin â So Please Dr zaka iya fadâa mana wani kalan abinci, may be Main dishes ne ko snacks?â.
âFor now muna kan binciken Hakan ne sabida mun fi maida hankali akan ceto rayuwarta , yanzu zamu kai ta dâakin da zata huta ne , har zuwa lokacin da zata farfadâo.â
Mamy ce ta furta â Dr zan iya zuwa ganin ta , Dan Allah?â .
âYeah zaki iya idan har an mayar da ita dâakin da zata huta , but batasan hayaniya idan kuka ce ku duka ne zaku shiga , zaku dame ta ne kuma a condition dâinta na yanzu baâa buâkatar hakan kwata kwataâŠ.â
â Dr ba zata zauna a asibiti ba , zaâayi arranging duk abunda zata buâkata, zamu tafi da ita gida , she will be more safe , bazan yadda ta zauna anan ba.â
â Haba Aya , Meyasa zaki ce a tafi da ita ? Bayan tana buâkatar hutawa a wannan time dâin?â. Mamy ce tayi maganar.
Aya kuwa ko gici ba tayi ba â Yeah dole mu tafi da ita , a gida anyi âkoâkarin kashe ta , balantana ma asibiti , she has to be save , sheâs your daughter atleast ya kamata ki kula da lafiyanta at every cause .
I will never risk her life again.â
â Aya ina tunanin abunda Mamy ta fadâa haka ya kamata ayi , a bari Drs suyi abunda ya kamata , ko dan sabida Mimi , daga baya koma mene ne sai anyi bincike dan nima bazan taâba kyale wanda yaso ya cutar da âyata ba.â Yanzu Baffa ne yayi magana .
Dafashi Uncle Bashir yayi â Yaya ina tunanin tana da gaskiya , a dâauke Mimi daga asibitin nan , ko hankalin mu ga baki dâaya yafi kwanciya , ko ya kagani?â.
Tun kafin ma Baffa yayi magana, Aya ta juya wajan Dr â Kayi mana arranging komai, zamu tafi da ita , duk abunda ya kamata ayi , you should just do it properlyâŠ.. And âŠâ kafin tayi magana ta hango Alameen yana nufo wajan cikin takunsa na mazan taka , bayanda kuma wasu ridâa ridâan mutane ne , a bayansa kowa yaci baâkaâken kaya ga kuma kalolin bindigu da yake jikin su sai ya tsorata ka tunda ko murmushi basa yi fuskarsu tamau babu faraâa kamar yadda shima ta Alameen dâin babu faraâa.
Ga baki dâaya sai suka tsaya kallan sa dan mafi yawanci members dâin da suke wajan sun tsorata da ganin irin jibja jibjan mutanan ko basu fito fili sun fadâa ba, daga mazan har matan.
Alameen yana zuwa Dr ya soma tanbayar abunda ya faru ,nan Dr ya âkara fadâa masa abunda ya fadâa musu yanzu , Alameen ya jinjina kai â Yeah akwai Drs dâin da zasu cigaba da kula da ita , yanzu zaka fadâa mun every thing da ake buâkataâŠâ
â Who are you to her ?â Cewar Dr yana kallan Alameen .
Wani kallo Alameen ya kai masa tare da fadâin â Who are you to tell me who am i?â
â itâs my job and I think i have to asked .â
â Then youâre not in that position to asked me .â
Dr zai sake magana Aya tayi saurin ciro wani abu a aljihunta which Dr dâin ne kawai ya gani tunda tana facing dâinsa sosai .
Yana ganin abun da ta muna masa , yayi saurin ja baya, yana kallan Alameen.
â Sorry yanka yadade yanzu zaâai duk abunda ka fadâaâŠ.â Kana kallan yadda Dr dâin nan yayi magana lokacin da yake kallan Alameen a yanzu akwia alamar tsoro a cikin idanuwansa wanda ko su ragowar Drs dâin da suke bayan sa basu abunda ta nuna masa ba .
Su kuma Uncle Abba kowa ya saka masa question mark sabida basu san shi ba which kuma kamar yafi alaâka da Aya da yake magana.
Gashi daman face dâinsa , ba irin mutanan da ake kawo wa wargi bane, ba kuma mutanan da yake tare dasu , ga baki dâaya an rasa wanda zai iya yi masa magana a cikin su , idan aka cire Aya .
Baâai good 20 minutes ba aka gama cike ko wana abu da zaâa buâkata na Mimi, sannan aka fito da Mimi zuwa mota, a ciki kuma har da wannan Doctor dâin da kuma wasu guda biyu da suma suka sha jinin jikin su , sanin ko wane ne Alâameen.
Idan mutum yaga yadda harabar asibitin nan ya cika da motoci mutum sai yayi tunanin, ko siyar da motoci ake , SUV ce manya manyan gaske , ko wacce taci uban tinted glass , ga manya manyan maza masu jini a jika , da suke tsats tsaye, both farare da baâkaâke, ko idanuwansu baâa gani sabida baâkin glass da suka sanyawa fuskokin su, they looks so scary, a hakan ma kuma akwai sojoji da suke sanye da uniform dâin su , even though basu kai masu baâkin kayan nan yawa ba .
Ga baki dâaya abun ya bawa su Baffa mamaki , yes they are rich , but not that over rich da zaâa saka wadâan nan Suv dâin ba kamar wanda president yake waje.
Dan wannan ko SUV dâin President dâin Nigeria Albarka . Gashi babu wani patient ko wani a harabar wajan, apart from wadâan nan mutanan da kuma su Alameen da suka fito yanzu.
Aya tana right side , Alameen yana left . Ku Mamy da Baffa da suke iyayanta , basu kusanto ta ba , sabida wani irin zagaye hanyar da ake tafiya da Mimi akai. Kowa akwai tanbayoyi da yawa da suke faman nuâkurâkusar su a ciki, amma kuma babu wanda zai iya basu amsar tanbayar da su.
A gefe dâaya zuciyoyin su na cike da tsananin fargaban abunda zai je ya dawo, musamman idan aka gano wanda yayi wannan aika aikan, dan tabbas, wani ikon Allah ne zai hana koma wane ne baâkuntar lahira , idan har wanda ake tsoran ya bayyana ya bayyana.
Hmmmmmmm.
Motar da aka tafi da Mimi wata babban mota ne da zaâa iya kwantar da ita , tana da matuâkar kyau , if not a yanayin da ake ciki, babu wanda ba zai tsaya âkarewa motar kallo ba .
Anan aka saka ta , wani âkatan mutum ya shiga driving seat sabida alokacin shima yana a tsaye ne , Alameen ya shiga dâayan side dâin , Aya da Mimi kuma a cikin asalin bayan motar su biyu, Mimi tana kwance yana tana kusa da ita tana binta da idanuwa, bayan su babu wanda aka saka a cikin motar , kuma akwai wajan rufe bayan.
YES Alameen ya rufe wajan, dan harta shi da driver ba zasu ganta a bayan ba .
Anan motoci suka soma fita , SUV iya so SUV , an zagaye motar dasu Mimi suke ciki, harta hanyar wucewa ga baki dâaya sai da aka kashe one road sabida wucewar su.
Duk wani me mota ba ta hanyar yake bi ba , sabida yadda motocin suke da matuâkar yawa kuma baâkaâke kuma gashi dare yayi sosai a wannan lokacin .
Is a silent ride , daga cikin motar da su Alameen suke har zuwa sauran motocin da âyan gidan suke , kowa yayi shiru yana saâke saâke a cikin zuciyarsa .
Baâa dadâe suka âkaraso, su Mommy duk suna compound kowa yaâki shiga gida ana jiran dawowar su Mimin, tunda Zarah ta tura musu text dâin cewa gasu nan tawowa, shima kuma a âboye tayi dan ga baki dâaya a tsorace take , tun wani kallo da taga Aya tanayi mata.
Amaimakon a nufi part dâin Mamy da ita , sai aka nufi part dâin Moh da ita.
Part dâin da bayan Mimi da Aya , babu single mutum da ya taâba shiga cikinsa, idan aka cire Alameen, kuma babu wanda yasan ya tsarin cikin falon yake, bayan ginin building da suke gani , harta Mamy da Baffa basu taâba shigar wannan building dâin ba.
A nan akai parking, dai dai lokacin da wasu Benz guda biyu suma suka shigo cikin gidan. Ana fito da Mimi suma suna fitowa daga cikin motar su.
A mata ne su uku, ba yara bane , dukan su kuma zasu haura 40 , a ciki a kwai wacce zata iya kaiwa 50 ma , dâaga da jaka a hannunta , dâaya da Box wai wani âkatan box me kama da trolley da aka fito dashi aka shiga cikin part dâin Moh.
Duk wannan abun, daga Dr da suka saka Mimi amota , sai Alameen, Aya , da kuma matan nan da suka zo, sai kuma Baffa da Mamy da wannan ne karon su farko na shiga part dâin.
Bayan su babu wani mahaluâki na gidan da ya shiga ciki, kowa yana nan yayi cirko cirko gashi kuma an zagaye part dâin Moh ga baki dâaya .
Masu kuka tun Ćuna yi , har hawayen fuskar su, ya âkaâkâkafe sai dai kana kallan idanuwan su , kasan cewa sunyi kuka , duk gıdan ma bayan Ameer da Ameera babu wanda yayi bacci sabida tsoro da tashin hankalin yadda Mimi take ciki, uwa uba gasaban abu da suka gani yanzu wato Alameen.
Omo the guy is so damn hurt , yadda yake tafiyar da lamuran komai kamar ga baki dâaya members dâin gidan a tafin hannunsa suke , dan dole ka sara masa , tabbas shidâin Abokin Moh neâŠ. OMO the power is so damn⊠the audacity , the ordersâŠ.. baâa magana .
A âkasa akwai babban dâaki me girma sosai , anan aka kwantar da Mimi akai settling komai , da dĂŒk abubuwan da take buâkata , sai dai Alameen da Baffa basu shiga cikin dâakin ba , Mamy da Aya da kuma wadâan nan mutanan nan kawai suka shiga , bayan sun tabbatar da komai nata ya dai dai ta , babu wani matsala , suka fito daga dâakin.
Alameen ne ya kalli Mamy, ganin ta duk ta dâan rikice kamar tana cikin damuwa.
Murmushi yayi mata da ya tsaya iya kan laâbâbanta yana fadâin â Ya kamata kuje ku huta , yanzu tunda dare yayi, kema kuma kina buâkatar Hutu sosai , insha Allah zuwa gobe everything will be fine.â
Girgiza masa kai Mamy tayi cikin rashin amince wa â Aâa zan zauna anan gwanda na kula da abata kar a âkarasa mun ita .
â Babu wanda zai âkarasa miki ita tunda har tana cikin part dâin nan , she is safe , game da abincin da taci ma zamu gano bakin zaren shima .
Dole kina buâkatar Hutu ku duka .â Ya kalli Baffa da yake sauraran .
Cikin amince Baffa ya furta â Ga amanarta nan na baku ku kula da ita sosai dan Allah.â
âInsha Allahâ shine abunda kawai Alameen ya fadâa .
Aya juyawa tayi zuwa dâakin da Mimi take , su kuma sauran mata biyun suka fita , ya rage Alameen ne kawai a cikin falon, shi kuma akan kujera ya zauna.
Daga waje kuma Baffa ne ya bawa kowa umarnin komawa akwanta tunda dare ne , kuma bazai yu ace ana tsaye a wajan ba , har washe gari.
Haka dan dole babu wanda ya so, kowa ya nufi part dâin su, amma fa wannan securities dâin da suke gidan, babu Wanda ya motsa ginan yananan dabai baye da securities kuma babu wanda aka bari ya sake zuwa wajan garden dâin nan tun fitan su Asibiti.
Moment dâin daren ya kasance wani irin baâkon yanayi da baâa saba dashi ba.
Bacci ya âkauracewa kowa , yayinda tunani kala kala , yake faman yawo an âkwaâkwalwar mutane .
Gidan sosai yayi shiru , irin shirun da duk motsin da mutum zaiyi a wannan lokacin zai zama kamar ana jin abun da yake ne .
A part dâin Moh kuwa , hasken falon kawai aka bari a kunne .
Alameen yana zaune akan kujera, hannunsa dâaya akan armrest dâinsa, dâayan kuma yana riâke da wayarsa yana daddan nawa , da alama abu yake yi me matuâkar mahimmanci a cikin wayar .
Fuskarsa babu alamar gajiya , babu wani kuma da zai iya fassara yanayin fuskarsa , Idan har ba wanda yayi mugun sanin sa ba, idanuwansa sunyi ja sosai dasu, sabida abubuwa da yawa da suke cikin su.
Aya kuma tana zaune a gefen Mimi, ta âkura mata idanu, ko âkiftawa batasan yi , kawai tana kallan yadda fuskarta tayi fiyau lokaci guda , kamar ba ita ce dâazu take sakin murmushi ba , but here she is kamar matacciya .
Ko bacci bata ji, kuma bata da alamar kwantawar da alama itama tana cikin dâaya daga cikin wadâan da bacci ya âkaura cewa âŠ..
Thatâs how the day became so long , kafin kace me Next day har tayi.
Ana idar da sallar asuba, Mamy ta taho part dâin dan duba Mimi, lokacin Aya tana zaune a falon, tana jiran dawowar Alameen daga masallacin da yaje .
Sai ganin Mamy tayi , muryarta ko fitowa ba tayi, tayi sallama .
âDagowa Aya tayi, ta kalleta tana amsa mata , Mamy ga baki dâaya ta koma kamar mara lafiya , kallo dâaya kawai zaka mata kasan cewa yes tana buâkatar hutu itama sosai , kamar yadda Aya bata yi bacci ba , haka itama Mamy bata rintsa ba .
Mamy babu wani kalma da ya soma fitowa daga bakinta sai kalmar â Mimi..â Tana fadâin â Ta tashi ? Ya jikin nata?â.
âDan kamo hannunta Aya tayi ta zaunar da ita akan kujera , sannan itama ta zauna a gefen nata â Mimi sheâs fine, and muna da hope zata tashi, just pray for her , ki kwantar da hankalin ki.â
â Hmm Aya bazan iya ba idan har ba ganin Mimi nayi ta dawo hayyacinta ba , kun gano wanda ya janyo wannan abun? Sannan Moh yasan halin da take ciki?â.
â Karki damu zamu gano komai da komai, akan Moh ne bazan iya ce miki komai, kiyi haâkuri.â
â Meyasa ?â. Cewar Mamy.
âZai fi kyau ki idan har zaki iya tanbayar Alameen but bazan iya fadâa miki komai a kan Moh ba , shima muna saran ganinsa at any momentâŠâ.
â Uhmmmâ shine kawai abunda Mamy tace , kafin ta furta â Zan iya shiga naga Mimin ?â.
â Why not letâs go.â Da haka suka nufi dâakin da Mimi take a kwance , sosai yanzu fuskanta ya dâan soma dawowa normal , kumburin fuskan nata yana raguwa sosai.
A haka Mamy ta shiga ta ganka , duka 30 minutes tayi , suka sake fitowa da Aya .
Anan falo suka tarar da Alameen da kuma Baffa suna tattaunawa , inda Alameen yake cewa â Baffa kayi haâkuri bayan ku, babu wanda zai iya ganin Mimi har sai Moh ya dawo cikin gidan nan .â
â Yan uwanta ne , ya kamata dai ko yaya ne su shiga su ganta tunda sun damu da ita , kar ka manta Mimi fa âyata ce.â
Kansa Alameen ya jinjina masa â Yeah tabbas Mimi âyar kace , and bazan taâba hanaka zuwa ganinta ba , but maganar Mimi ake , maganar rayuwar ta, a wannin baya kadâan da suka wuce ta kusa rasa rayuwarta ne , daga cin abinci, cikin âyan uwanta, babu wanda yayi ciwan kai a cikin su .
They donât deserve to see and I pray wanda ya saka wannan crab dâin ba dâaya daga cikin family member dâin nan bane âŠ.â Daga nan yayi shiru yana dâan murmushi.
âKoma dai mene ne Mimi ai âyata ce ko? A wannan karan dole âyan uwanta su ganta koda ace sau dâaya ne , dole zamu gano dalilin faruwan hakan amma kuma lefin wani baya taâba shafan wani.
Ga baki dâaya hankalin kowa a tashe yake , kusan kowa bai runtsa ba , ya kamata ko sau dâaya ne su san halin da take ciki.â
Murmushi Alameen yayi yana jinjina masa kai â Ba matsala zasu iya shigowa su ganta, zan dâauki kasadar sabida baâa shigowa part dâin Moh , suna gama 10 minutes dâin su , they can all go out please.â
Kallan Mamy , Baffa yayi â Ya jikin nata ?â.
â Da sauâki sosai , Alhamdulillah.â A haka dai ta samu ta zauna a kan kujera .
Waya Baffa ya dâauka , ya kira Daddy , duka wayan seconni sukayi .
Baâa dâau mintuna 3 ba Aya ta budâe musu âkofa . Duk da Moh baya nan amma âkamshin turaransa yananan dan âkare a cikin part dâinsa.
If not halin da ake ciki , babu wanda bazai tsaya kallan falon Moh ba sabida yafi ga baki dâaya falukan gidan kyau, infact , duka âbangaran Moh ya fi na kowa yau da tsaruwa .
Sai dai kash babu wanda zai tsaya kallan falon yanzu Sabida Mimi.
Ameerah har yanzu akwai sauran âkwalla da take sharewa .
Zarah ma tayi kuka , sai dai me shigowa part dâin Moh da tayi akaran farko a rayuwarta taji duk damuwar rashin lafiyar Mimin ta soma tafiya .
Wani irin dadâi ta soma ji, wanda batasan ko na mene ne , a hankali take satar kallan wajan, tana imagining ganinta a ciki, a matsayin nata , kuma mallakinta na har abada.
A yanzu kam rashin lafiyar Mimi bata dâadâarata ba , daman asalin yadda kowa ya rudâe ne ya tayar mata da hankali har ya sata kuka ganin kowa yanayi amma yanzu kam komai ya warware , tana jin zuciyarta fari tass da ita .
Aya tana zaune a falo da su Momy, babu me umm babu me uhm uhm , yayın da Alameen da Mamy sukayi wa su Baffa jagowa zuwa duba Mimi.
Mazan basu shiga ba , Mamy ce ta shiga can kusa da ita , su daga bakın âkofa suka dubata kuma Ću kayi mata addua .
Suna dawowa Aya tayi wa su Ameerah tajora suka shiga inda Mimi take .
Ameerah tana ganin Mimi ta soma wani saban kukan , duk da tana âkoâkarin dannewa kar aji kukanta.
Zarah kuwa hannu ta sa tana ta faman goge fuska kamar da gaske kukan take itama , hakan yasa kowa ya tausaya musu suma sanin cewa tare suka taso.
Sunyiwa Mimi addua suma sosai, sannan suka fito daga dâakin, amma a haka Zarah waigowa take tana kallan Mimi, tana jin haushin cewa ta kwanta mata akan gadonta , wanda ko ita da take dashi bata hau kansa ba , hakan yasa wani tululun baâkin ciki ya shiga cikin zuciyarta, har yasa âkwalla saukowa a fuskarta, amma idan bakasan abunda yake zuciyarta ba , z kayi tunanin kukan rashin lafiyar Mimi take.
Su Baffa ne suka soma tafiya , suma su Mommy suka miâke dan ciki kuwa har da Mamy tunda baâasan hayaniya, amma Zarah ko âkoâkarin miâkewa batasan yi , ta wani lumshe akan gado sai kace nata.
Har sai da Ameerah ta dâan taâbo ta, tana fadâin â Ki tashi mana mu tafi, kamar baki da alamar tafiya fa.â
Cikin âkasa âkasa da murya Zarah ta furta â Wana irin mu tafi, mu da ya kamata mu zauna , tare da ita mu dinga kula da ita, ai in kowa zai tafi, banda mu , musamman ma ni.â
Zame hannunta Ameerah tayi tana bin bayan Mama( mahaifiyarta) bayan ta fadâawa Zarah cewa â Nidai babu ruwa na .â
Babu wanda yasan cewa Zarah bata taho ba . Tana zaune a falo tayi kalar tausayi sosai, idan ka ganta zaka rantse tana cikin tsananin damuwar Mimi ce .
Kallanta Alameen yayi , da wannan murmushin nasa mai wuyar shaâani â Kema ya kamata ki koma ko? Tunda kowa ya tafi, duk kuje ku huta .â
Hawaye Zarah ta soma yi , cikin shash sheâka â Gaskiya bazan iya tafiya na bar Mimi ba , zuciyana zafi yake sosai , taya zan tafi na bar Besty? Nidai ku bar ni anan .â
Aya tana tsaye daman tuntuni hannunta yana nannadâe a âkirji bata dai ce komai har lokacin, sai da idanuwanta ga baki dâaya Ćuna kan Zarah, ko kalle kallen da ta dinga yi dâazu duka akan idanuwan Aya tayi su, ta yi shiru ne kawai dan tasan idan ta tanka sai ta âballata a wajan.
Kallan Alameen yayi cikin nutsuwa ya furta â Karki damu , zamu kula da ita ni da Aya , idan ta warke ai zaku dinga ganin ta . Okay?â
Zarah kam taâki yadda , adole sai ta zauna , kuma bawai sabida Mimi take so ta zauna ba , No sabida ta kuma âkyalewa part dâin kallo ne , dan tana jinsa har âkasan zuciyarta ne .
â Ke tashi ki fita .â Cewar Aya , tana âkoâkarin nufota .
Cikin saurin Alameen ya shiga tsakiyar su, yana kuma cewa Zarah â Ki koma part dâin ku yanzu kinji?â.
Zarah ta tayi masa taurin ka yayi mata wani shegen kallo, kawai sai ya koma kan kujera . Da Aya ta funcikota sai da ta wuntsila âkasa, hannu Aya ta sa ta daddage ta tsinka mata mari, wani irin gigitaccen ihu Zarah ta saka sabida marin ya shige ta, Alameen yana zaune bece mata komai ba , haka Aya ta danâko kanta kamar wata gasashshiyar kaza, ko bari ta miâke tsaye ba tayi ba , haka ta jata a âkasa har zuwa âkofar part dâin mu, ta barta a âkasa a yatse, dan ma securities dâin sun San aikin su babu wanda ya kalli inda take ko yayi nuna akwai wata me kamar halittan ta a wajan.
Wani irin kuka Zarah ta sa me âkarfi tana nufar part dâin su .
Mommy da Daddy kawai gani sukai ta shigo falon kamar me taâbun hankali, ko sallama babu , ta wuce dâakin ta da yake sama.
Ga baki dâaya rudâe suka bi bayanta , duk a tunanin su ko wani abu ne ya samu Mimin.
A tsakar dâaki suka tarar da ita, tana faman rusar kuka, kamar wacce aka yanka .
Da iya âkarfin da Allah yayi mata take kukanta . Cikin sauri Mommy ta dâagata tana fadâin â Zarah me ya faru? Kike wannan uban kukan?.â
Ba tayi magana ba sai wani kukan da tasa, batasan Daddy ya shigo dâakin ba sai da ya daka mata tsawa yana tanbayarta , Meyasa meta, tukunna tayi saurin tsayar da kukan tana fadâin â Babu komai.â
âKaramun tsaki Daddy yayi kawai ya fita dâaga dâakin.
Lock Momy ta saka a âkofa tana dawowa wajan Zarahn.
â Wannan wana irin iskanci ne haka Zarah , zaki shigo ki dinga yi mana kuka, kamar wacce aka ce uwarta ta mutu? Gashi har kin âbata wa Dadyn ki rai.â
Cikin kuka Zarah ta soma fadâin âMommy yanzu mene ne laifi na dan na so Moh, kinga yadda waccan shegiyar tayi mun kuwa? Dan kawai nace zan zauna na kula da Mimi shine zata wanka mun mari har ta janyo ni waje kamar wata wulaâkantacciya, toh insha Allah Mimin ba zata tashi a nakash she zata âkare rayuwarta , shegiya har naji tsanarta a zuciya na .
Ta wani baibaye mun gadon miji kamar na ubanta ne ko hour 1 banyi a cikin part dâin bafa amma ita tanan a kwance waya sani ma ko na munafunci ne take yi , sabida kawai ta zauna a part dâin , Allah yasa ma karta farfado ga baki dâaya naji na tsaneta insha Allah kafin Uncle Moh dina ya dawo ta mutuâŠ..
_________________
To be continued⊠đ„
Aysha Galadima đ€đż
***
***