Chapter 25
by @umsar
WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
@umsarArewapen
Wattpad: Umma Mustapha
PAGE 25
Sannu a hankali, cikin wayo da dabara, Irfan yake ƙara kusantar Nihla, har ya kai ga cewa yanzu kusan kowace rana sai sun yi waya.
A makaranta ma, idan ba lecture, sau da yawa suna tare. Idan lecture ya zo, sai ya bar ta ya nufi ajinsa.
A hankali, sauran ɗalibai suka fara lura da irin kusancin da ke tsakaninsu.
Wasu suna kallonsu ne kawai, wasu kuma suna ɗan tsegumi a tsakaninsu. Amma Nihla ba ta damu da hakan ba.
Har yanzu Irfan bai taɓa furta mata cewa yana sonta ba.
Shi ma bai taɓa matsa mata da wata magana da za ta sa ta fara tunanin cewa abin da ke tsakaninsu ya wuce abota ba.
Amma duk da haka, akwai wasu alamomi masu ƙarfi da kullum yake nunawa ba tare da ta ankara ba.
A ɓangaren Nihla kuwa, tana kallon alakarsu ne a matsayin abota da kuma mutunci. Ko da yake a hankali ta fara jin wani irin abu a game da Irfan, amma sai ta ɗauki hakan a matsayin shakuwa kawai.
Ba ta taɓa sanin cewa Irfan yana da saurin fushi ba, balle ta san irin zafin kishin da ke tattare da shi.
Sai wannan ranar.
Bayan sun fito daga wani lecture, suna tafiya tare a harabar makarantar. Irfan kuwa Yana tsaye a jikin motarsa Yana jiransu.
Suna cikin tafiya ne sai wani ɗalibi, wanda yake Level 3, ya tare su.
"Don Allah Nihla, ina son magana da ke."
Kallo Daya NIHLA ta masa ta dauke kanta, ta fara kokarin zagaye shi ta wuce.
Shan gabanta yayi, yana ƙoƙarin bayyana mata abin da yake ji.
Amma ba ta saurare shi ba. Sai kawai ta kama hannun Fatima.
"Mu tafi."
juyawa suka yi suna ƙoƙarin wucewa.
Sai dai yaron bai haƙura ba.
Cikin sauri ya miƙa hannu ya riƙe mayafin Nihla, har yana haɗawa da gefen rigarta.
Nihla ta firgita.
"Ka sake ni!"
Ta fara ƙoƙarin ƙwace mayafin, amma yaron ya ƙara riƙewa, yana son lallai sai ta saurare shi.
Fatima ta juya da sauri.
"Ka sake ta mana! Wanne irin abu kake yi haka?"
Irfan na chan na jiran su.
Da ya lura sun daɗe ba su dawo ba, sai ya bi bayansu.
Amma yana zuwa, idanunsa suka gane masa abin da ke faruwa. Nan take fuskarsa ta sauya.
Hannun yaron da yake riƙe da mayafin Nihla yake kallo.
Wata irin wutar masifa ce take tashi a cikin zuciyarsa. So yake ya yi control ɗin ɓacin ransa, amma ya kasa.
Idonsa ya yi wani irin ja, lokaci guda fuskarsa ta sauya kamar bai taɓa dariya ba.
Bai jira komai ba ya isa wajen cikin ɓacin rai, kamar mayunwacin zaki da ya shekara bai ci abinci ba.
Kafin mutanen da suka taru a wajen su ankara, sai suka ji ihun yaron, yana dafe da hannunsa.
Nihla tana manne a jikin Fatima. Ganin abin da ya faru, jikinta sai rawa yake yi, duk ta bi ta firgita.
Sauran ɗalibai, 'yan uwansa, suka nufi yaron, suka kama hannunsa domin su duba shi. Kafin kace kwabo, hannu ya kumbura.
Jabir ne ya ƙaraso wajen a sukwane, sakamakon kiran da Fatima ta masa ta sanar da shi halin da ake ciki.
Yana zuwa bai jira komai ba, ya kama hannun Irfan.
"Irfan! Mu tafi."
Yana ƙoƙarin janye shi daga wurin.
Amma Irfan ko motsi bai yi ba.
Jikinsa yana tsuma saboda fushi, idanunsa suna yawo cikin taron ɗaliban, yana jiran wanda zai furta wata magana.
Jabir ya ƙara riƙe shi sosai.
"Don Allah ka nutsu. Mu tafi."
Daga Fatima har Nihla, a tsorace suke ganin abin da ya faru. Sabon abu ne a wajensu; ba su taɓa ganin irin wannan tashin hankalin ba.
Wani daga cikin ɗaliban ne ya fito ya fara faɗar maganganu, har yana haɗawa da zage-zage.
"Da uban wa yace su yi shigar da za ta ja hankalin maza zuwa kansu? Shegun yara, sai girman kan tsiya To wallahi, ba yadda za mu yi ba. Dole hukumar makaranta ta shiga cikin lamarin."
Yana maganar yana zaburowa Wasu daga cikin ɗaliban suka fara riƙe shi, ganin yana ƙoƙarin tinkarar Irfan.
Zagin da ya mata, da kuma alakanta ta da shigar banza, ya sa Irfan ya ƙwace hannunsa daga riƙon da Jabir ya masa, ya damƙi wuyan matashin yaron.
Hayaniya ta sake tashi.
Jabir da sauran mutane suka fara ƙoƙarin karɓar yaron daga hannun Irfan, amma suka kasa.
Ganin yana shirin kai yaron lahira, sai Nihla ta kasa jurewa.
Ba ta san lokacin da ta saki hannun Fatima ba.
Ta nufi Irfan da sauri, tana kuka.
"Irfan!"
Ya ɗan tsaya.
"Don Allah ka sake shi..."
Hawaye suna zuba mata.
"Don Allah ka sake shi. Kada ka janyo mana wata matsalar, don Allah."
Muryarta ta yi tasiri, har ya ɗan sassauta riƙon da ya yi wa yaron.
Juyowa ya yi ya kalleta.
"Don Allah ta sake faɗa."
A hankali ya saki matashin.
Yaron ya ja da baya yana tari, yayin da sauran abokansa suka riƙe shi.
Irfan ya tsugunna ya ɗauko mayafin Nihla wanda ya faɗi ƙasa a lokacin rikicin.
Miƙa mata mayafin ya yi, sannan ya kama hannunta suka bar wurin.
Ita kuwa ta kasa magana. Gaba ɗaya tsoronsa ta fara ji.
Bai tsaya ko'ina ba sai da suka je wajen mota. Ya buɗe ƙofar gaba ya tura ta ciki, sannan ya zagaya ya shiga mazaunin direba. Da mugun gudu ya ja motar, suka bar cikin makarantar.
Da kallo Jabir ya bi motar har ta ɓacewa ganinsa. Ya daɗe bai ga abokinsa a cikin irin wannan yanayin ba.
Numfashi ya sauke, ya shafa sumar kansa.
Dole su nemo mafita, domin ya san abokinsa ya riga ya yi abin da zai iya jefa su cikin matsala.
Kallonsa ya mayar kan Fatima. Duk wanda ya kalleta ya san ita ma a tsorace take. Addu'a take yi a cikin zuciyarta:
"Allah Ya sa kada wannan abin da ya faru ya zama silar korarsu ko a basu suspension."
Umsar ✍️
***