WA ZAI FUSKANCE NI??

Chapter 30

by @umsar

WA ZAI FUSKANCE NI??
BOOK 1
Umma Mustapha
@umsarArewapen
Wattpad: Umma Mustapha

PAGE 30

Washe gari da sassafe, Fatima ce take ta aikin shirya musu kayansu duk abin da zasu tafi da shi ta hada musu shi a waje daya.
Nihla tana zaune a gefen katifar, tana fama da tunani. Tun daren jiya, kalaman Irfan sun ƙi barin zuciyarta ta huta.
A duk lokacin da ta tuna yadda ya kalleta yana furta mata cewa yana sonta, sai zuciyarta ta yi wani irin bugawa ba ta San dalilin hakanba.
Ta girgiza kai, kamar tana son korar tunanin daga ranta.
"Me ya sa nake tunanin maganar nan haka? Me ya sa maganar ta tsaya min a zuciya?"
Ba ta da amsar tambayar da take wa kanta.
Ta ɗauko wayarta, ta shiga kan sunan Irfan. Ta daɗe tana kallon number ɗinsa, tana shawara da zuciyarta ta kira shi ko kuma ta bar shi.
Ya saba kiranta kowace rana da misalin ƙarfe takwas na safe domin su gaisa, amma yau har ƙarfe tara ta wuce, bai kira ba.
A hankali ta danna lambar wayarsa.
Kiran ya fara shiga, amma har ringing ɗin ya ƙare, ba a ɗauka ba.
Zuciyarta ta ƙara cika da damuwa. Ta ajiye wayar gefe, amma hankalinta bai bar kan lamarin ba.
A daidai lokacin ne Fatima ta fito daga kitchen, hannunta ɗauke da plate ɗin indomie. A gaban Nihla ta ajiye shi, sannan ta samu waje ta zauna.
Ta kunna rechargeable fan domin abincin ya samu iska ya huce da wuri.
Ta kalli Nihla, wadda har yanzu take cikin tunani.
"Tunanin me kike haka? Ko duk damuwar Irfan ɗin ce?"
Ta ƙarasa maganar tana ɗan murmushi.
Nihla ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta amsa:
"Kinga na kira wayarsa, bai ɗauka ba. Na ga ya saba kirana kullum da ƙarfe takwas, shi ya sa na gwada kiran na ji ko lafiya, amma bai ɗauka ba. Ko fushi yake da ni ne?"
murmushi Fatima ta yi.
"Ki kwantar da hankalinki. Irfan ba zai yi fushi da ke ba. Maybe ba ya jin daɗi, ko kuma ya yi nauyin barci."
Ta nuna abincin.
"Yanzu dai mu ci abinci, kar ya huce."
Da haka Fatima ta samu ta lallaba Nihla, suka fara cin abincin.
Bayan sun gama cin abincin, Nihla ta sake gwada number Irfan, amma har yanzu bai ɗauka ba.
Suna nan zaune wayar Aliyu ta shigo. Ya sanar da su cewa ya iso su fito.
Wannan karon shi kaɗai ya zo ɗaukarsu.
Suka fara fitar da kayansu, Aliyu yana ɗauka yana sakawa a cikin boot ɗin mota. Bayan ya gama jera musu kayansu, ya ce:
"Ku shiga mu tafi."
Gaba ɗaya suka shiga kujerar baya. Sai da Aliyu ya yi musu magana kafin Fatima ta koma gaba.
Nihla kuwa ta kwanta a kujerar baya, wayarta har yanzu tana hannunta. Ta sake gwada kiran Irfan, tana fatan wannan karon zai ɗaga, amma har yanzu bai ɗauka ba.
Damuwar da ta cika zuciyarta ta ƙaru.
Ta shiga messages, ta rubuta masa saƙon neman afuwa tare da sanar da shi cewa sun tafi.
Bayan ta aika, ta kalli screen ɗin wayar na ɗan lokaci, kamar tana jiran ganin wata alama daga gare shi.
Amma babu komai.
Ta lumshe idanunta, ta jingina kanta da kujerar motar, yayin da wata tambaya ta sake dawowa cikin zuciyarta:
"Me ya faru da Irfan?"
Bangaren Irfan kuwa, tun daren jiya da ya koma gida yake fama da ciwon ciki, ga kuma fargabar ko Nihla za ta karɓi soyayyarsa ko kuma za ta ƙi amincewa da ita.
Ciwon cikin ya ƙara tsananta masa, har ya kasa samun nutsuwa. Ganin halin da yake ciki ya sa Jabir ya haɗa musu kayansu domin su koma Kano, tunda wadda suke zaune a garin saboda ita, ita ma barin garin za ta yi.
Ya gama haɗa musu kayansu da duk abin da za su buƙata. Safiya tana yi, ƙarfe shida daidai, ya saka Irfan a mota suka ɗauki hanyar Kano.
Daga daren jiya zuwa wannan safiyar, gaba ɗaya Irfan ya jigata. Jabir kuwa gudu kawai yake shararawa, yana fatan su isa asibiti da wuri.
A dai-dai wani ƙauye mai suna Dabi, motar su Jabir ta yi faci. Gashi kuma sun yi nisa da ƙauyen, ba ya tunanin zai samu mai gyaran taya a wurin.
Ya fito daga motar yana duba tayar, sannan ya fara ƙoƙarin tsayar da motocin da ke wucewa domin neman taimako.
Amma bai samu ba.
Gaba ɗaya kansa ya fara ɗaukar zafi, musamman idan ya kalli halin da Irfan yake ciki.
Wata mota ce ta zo ta wucewa. Jabir ya yi ƙoƙarin daga mata hannu. Da farko kamar mai motar ba zai tsaya ba, amma sai ya rage gudu a hankali, ya fara ja da baya kaɗan-kaɗan, har ya zo daidai inda Jabir yake.
Sai ya leƙo ta window ɗin motar yana tambayar Jabir abin da ya faru.
Jabir ya tsallaka zuwa wajensa, sannan ya bayyana masa cewa motarsu ta yi faci. Ya roƙe shi da ya taimaka masa, idan ya isa ƙauyen da ke gabansa ya turo masa da mai gyaran taya.
Mai motar ya yi shiru na ɗan lokaci, sannan ya ce:
"Ka shigo mu ƙarasa ƙauyen. Idan ya so, sai ka taho da mai gyaran da kanka. Ina ganin kamar hakan zai fi."
Jabir ya girgiza kai.
"Ina tare da marar lafiya ne. Ba zan bar shi shi kaɗai a wurin nan ba."
Mutumin ya ɗan yi jim, sannan ya fito daga motarsa. Ya buɗe bayan motar, ya ɗauko spare tyre ya miƙa wa Jabir.
"Mu je na taimaka maka ka ɗaura."
Tare suka koma inda motar Jabir take. Mutumin ya taimaka masa, har suka samu suka ɗaura tayar.
Jabir ya yi masa godiya sosai, yana nuna Jin dadin irin taimakon da ya yi masa.
"Na gode sosai. Allah Ya saka maka da alheri."
"Karka damu. Ai yi wa kai ne. Ni ma ban san wanda zai taimake ni a gaba ba."
Jabir ya karɓi number ɗinsa.
"Idan Ka dawo Kano, zan kawo maka tayar har gida."
"Wane suna zan saka number ɗin?"
"Aliyu."
"Ni kuma Jabir."
Daga haka suka yi sallama. Aliyu ya ja motarsa ya tafi, JABIR ma ya shiga motarsu suka ci gaba da tafiya. 

Umsar ✍️ 
***