Asalin soyayyar mu ✨

CHAPTER ONE

by @hajeersulaiman803

CHAPTER ONE

Katsina state, kofar kaura.

karfe takwasa na dare ta tsayar da motarta ƙirar Hyundai Sonata fara a kofar wani madedecin gida, fitowa taya tana sanye da bakara abaya, bazaka kirata faraba kai tsaye amma fatarta tanada kyau da daukan hankali tanda matsakaici jiki 🫠 fuskarta kam anan aka gama halitta sai dai ace masha Allah danfa kyakkyawace, jiki a sake tashiga gidan kamar tasan abinda ke jiranta a ciki a hankali tabi tashin maganganun da take ji har bakin wani daki daidai lokacin da take addu'ar ba abinda take tunani bane yake faruwa tasa hannu tabode kofar da boɗeta yayi daidai da buɗe wani sabon shafin kaddarata dan jitayi wasu abubuwa sun rikito daga ƙwaƙwalwarta zuwa zuciyarta sai suka mata nawi a ƙirji ashi da gaskene da ake cewa da wani mugun ganin gwara mutuwa tabasa kazamtara da baka ganiba tsabtace toh taya akayi haka tafaru da ni shikara uku ina dakon soyayya duk ya tashi abanza kinan , halima! halima! daga nesa naji wata murya wada nasani tana kiran daga kai tayi tana kallanshi Ahmad ne rike da ita ashe faduwa kasa tayi, lokacine kuma ƙwaƙwalwarta taga yadace ta rabata da ruɗanin da take ciki idanunta suka bada goyon baya nan take suka rufe duhu ya mamaye ko ina, shekara uku baya.

four water! four water! kuzo ku sayi four water mai sanyi, Hajiya! Alhaji! yaro kuzo ko sayi ko kashe kishin ruwa.

header dan Allah kayi shuru ka ishemu da ihu! Toh kai idan ba'ayi tallaba tayi za'ayi mutane su sayi? sakin hannun kular ruwan nayi, header Ahmad da Umar duk suka tsaya, header shima ya saki hannun kular ta bangaranshi, dama kula dayace muke rike da ita ni da shi.

kunga nifa wallahi nagaji ku daya bamusayir ba nafada idon nacika da hawaye.

umar yawatsa min harara aikawa muka yi ido huɗu dashi.

Toh kai kuma uban mai kake kallona, dauke Kai yayi nikuma sanina Baze tankaba yasa nafashe da kukan daba hawaye.

lily dan Allah kiyi hakuri mukoma gida header yafada da sigar lallashi,

wallahi ba zamu kumaba, idan muka koma gida Abba ba saimin waya zeyi ba kuma gaskiya bazan bari Fatima tamin dariya ba da nayi abin kunya.

shi kenan mucigaba da yawo ku Allah ya sa musayar.

Ahmad dayake karma yace nagaji header muje inda muka zauna last week kinji Lilly dan Allah.

Toh muje nafada kamar ba nibace nake kuka, muka dauki kulolinmu wanda be wuce su dauki four water shabiyar ba ko wace ni da header muna rike da daya Ahmad da Umar suna rike da daya, a haka dai muka cigaba da tafiya header da Ahmad sai ihun four water mai sanyi suke Umar kam Kamar baya wajen sai wani cika yake yana batsewa a haka har muka iso wata rinfa muka zauna kuma ba lefi ansayar da ruwan dayawa toh dama beda yawa.

ganin Mun kusa sayarwa nafito da kudin daga pocket din wandona dama riga da wando sai baby hijab ne a jikiina ina dago kaina muka hada ido dashi yana tsaye da abokinshi a kofar wani shago tsaki naja ina murguda baki.

Mukhtar gah yarinyarka can yauma tadawo Yasir yafada yana nona halima da yatsa, kai Yasir rabani da wacan aljanar yarinyar nan ta taramin mutane wai saceta zanyi Allah ne kawai ya taimakeni Dubai yadda tasa Umar talla kamar ita ta haifishi.

haba Mukhtar wai tsaoran yarinyar nan kake toh bari kagani, yasir ya kashe sigar da yake busawa yanifo inda soke zaune.

karah cikume faska nayi ganin yayo inda muke yana isowa ya mikoman nera hamsin kalan shi nake ido cikin ido ganin bazai dauke hannunsa ba yasa nadawu ke idona, bana sayarwa da irin ku marmushi yayi yawuce yana sosa kai yatafi.

matsss header ruwa nawa ya rage? na kular Umar ne ba'a sayar ba, toh kutashi mutafi zamu shanye sauran a hanya kawai header yadora kular a kafaɗa Daman batada girma Umar ya dauki tasu suma muka kama hanyar gida a hanya inata ilga kudin kamar hakan zai sah sukaru har muka iso.