17.
by @zeeykumurya
*BARA A KUFAI*
*17.*
Mutsu-mutsu kawai Hasina take a bayan mota ita kaɗai saboda tsantsar nishaɗi ta kasa zama guri ɗaya, ji take kamar ta janyo lokaci ta ga komai ya kammala sai tafiyarta birnin tarayya kawai, murmushi ta saki ta latsa wayarta ta kunna data ta duba ko Farha ta tura mata hotunan da suka yi, amma sai ta ga ba ta tura ba, tun a lokacin ta so ta tura mata amma sai ta ce sai ta yi editing, ita kuma so take ta ɗora su su biyu a tare, ƙawayenta su gani su tabbatar da gaske ƴar'uwarta ce kamar yadda take faɗa idan ta saka hoton Farhan a status ɗinta.
Fatar Farha fara tas da take sheƙi da ɗaukar ido ta tuno, hannunta da yake dususu ta shafa, a fili ta furta. "Allah ka nuna mini ranar da ni ma zan ga fatata a haka."
***** *****
Misalin ƙarfe uku na rana, Juraij na kishingiɗe a bakin gado idanunsa a lumshe, Ramlah da ke mammatsa masa ƙafa ta dube shi ta ce. "Ka rame sosai My Man, ga jikinka da zafi alamar kana buƙatar ganin likita, ina daga nan amma ina jiyo bugun zuciyarka, don Allah ka dinga sassauta wa ranka, ina tsoron kar watarana a ga ka yanke jiki ka faɗi saboda tension, ko da ba ka furta ba duk wanda ya kalle ka ya san kana cikin damuwa, ka daina saka komai a ranka, ƙasar nan ta riga ta lalace, ba za ta taɓa gyaruwa ba, waɗannan burikan naka cika su tamkar shuka ne a cikin wuta, bana son na rasa ka, bana son ka yi abin da zai saka rayuwarka a cikin haɗari, don na san ka fi ni sanin me nake nufi, ka fi ni sanin abubuwan da suka faru a baya." Ta yi shiru tana sauke numfashi tare da matsowa ta kama hannunsa ta damƙe a cikin nata, kamar za ta yi kuka ta ce. "Please Mine ko don Daddy da buƙatar ka da yake fiye da kowa a cikin rayuwarsa ka yi haƙuri ka bar binciken abubuwan da kake yi." Idanunsa ya buɗe ya zuba mata, murya a sake ya ce. "Wa ya faɗa miki ina binciken wani abu na daban da ba wanda ya zama dole a aikina ba?" Rarraba ido ta yi na sakanni sannan ta saita kanta ta ce. "Babu kowa, amma na sani, saboda na san halinka, na san bin diddiginka akan abubuwan da aka ɓoye ko..."
"Dole kin sani Ramlah tunda kika furta." Ya yi maganar kai tsaye tare da miƙewa ya kwashi wayoyinsa ya fice daga ɗakin, ta bi shi da kallo gabanta na dukan tara-tara.
A ƙaramin parlour ya zauna ya latsa wayarsa ya bi bayan missed call ɗin Tahir da ya gani.
"AD."
"Ɗanzaki."
Numfashi Tahir ya fesar cikin damuwa ya ce. "Ɗazu na ci karo da wani tashin hankali Juraij, an je wani ƙauye an tashi garin, an kama matayensu, an kashe mazajen an ƙone musu dukiya an kaɗe musu dabbobi, abin ya firgita ni sosai, ina son na san ku kuna me har aka yi wannan ɗanyen aikin aka gama? Mene amfanin jami'an tsaron ƙasar nan? Gari guda fa aka tasa! Kuma aka yi video aka yaɗa"
Runtse ido Juraij ya yi yana hango wani lokaci a shekarun baya, wani lokaci da ya buɗe masa ido akan abubuwa da dama da suke faruwa a yankin ƙasashen nan, wani lokaci da ya tafi da wani ɓangare na rayuwarsa, wani lokaci da ya fara cin karo da abin da ya saka shi ɗaura ɗamarar gano wata ƙungiya da duk wanda yake cikinta, tare da shan alwashi iri-iri.
"Juraij..."
"Tahir maganar nan ba ta waya ba ce, ka bari zan fito anjima sai mu haɗu mu tattauna."
"Kana nufin ka san da faruwar abin da nake magana akai amma na ji muryarka a haka ba damuwar komai?"
"Ba kodayaushe bayyana damuwa yake nuna abu ya taɓa zuciya ba, musamman ma ga zuciyar da ta rayu a damuwar, kawai ka jira mu haɗun."
A sanyaye Tahir ya ce. "Ok sai ka zo."
Daga haka ya katse wayar yana ƙara jinjina abun a cikin ransa, wunin yau gabaɗaya ya kasa taɓuka komai, ko abinci ya kasa cin na kirki, don bai saba da irin wannan tashin hankalin ba, bai san haka yana faruwa ba, bai san rashin tsaron da ake fama da shi ya kai a tashi gari guda amma ba a kai musu ɗaukin komai ba har aka yi aka gama.
**** *****
Sai da aka caje su Saudat sannan aka bar su suka shiga cikin gidan, Atine tana gyara mata kayanta da aka hautsino bayan sun shiga farfajiyar gidan ta ce. "Tsari ne da gidan nan kamar a turai, sai kin lura da kyau kin haddace duk wasu dokokinsu idan kina son ku zauna lafiya."
Saudat dai ba ta ce komai ba sai bin ƙaton gidan da kallo kawai take, daga inda suke tana hango Apartments daban-daban, ga wata ƙatuwar runfa a gefe da aka jera motocin da ba ta san adadinsu ba a ciki. Tsaki Atine ta ja ta ce. "Wai da kurma nake tafe ban sani ba ko me? Tun ɗazu ina yi miki magana kin mun bakam kin bar ni da ɓaɓatu kamar taɓaɓɓiya."
"Ki yi haƙuri." Shi ne kawai abin da Saudat ta iya furta mata.
Mita mai haɗe da masifa ta ci gaba da yi har suka ƙarasa gaban wani babban part, ta danna wani abu a jikin gini sannan ta janyo Saudat tana faɗin. "Matso sosai, sai an gan mu sannan za a bari mu shiga." Saudat ta yi yadda ta ce, suka ji wata ƴar ƙara kafin ƙofar ta buɗe da kanta kamar ana zuge labule. Da sauri Atine ta yi gaba Saudat ta bi ta a baya tana ambaton sunan Allah a cikin ranta. Wata mace suka gani sanye da uniform, da hannu ta nuna musu ƙofar da za ta sada su da parlour, Atine ta yi mata godiya duk ta san ba ta jin Hausa.
Wani hamshaƙin parlour suka shiga, duk rashin damuwa da ƙyale-ƙyalen Saudat amma ba ta san ta shagala da kallon shi ba, a ƙasa suka zauna jikinta duk a sanyaye.
"Ki saki jikinki da fuskarki, wannan ɗari-ɗarin da kike yi ai sai su ƙi ɗaukar ki ma." Cewar Atine cikin kwantar da murya. Kai kawai Saudat ta gyaɗa mata, don komai ya dagule mata, wani iri daban take jin ta, ita ce a gidan wasu a matsayin ƴar aiki? Da gatanta da iliminta da komai?
Suna nan zaune jigum har tsahon wasu mintina kafin wata budurwa ta sauko daga sama da waya a hannunta tana latsawa, Gurfanewa Atine ta yi ta gaishe ta. A yatsine ta amsa tare da faɗin. "Mom ba ta nan ta je school, amma na kira ta ce ku jira ta." Daga haka ta juya ta koma inda ta fito ba tare da ta bi ta kan banbaɗancin da Atine take yi mata ba. Saudat ta bi ta da ido tana ƙare wa shigar jikinta kallo da ba ta yi kala da ta ƴaƴan musulmai ba, ga yanayin yadda ta yi wa Atine magana ba darajawa a matsayinta na wadda ta kusa yin jika da ita. Anya za ta iya rayuwa a cikin irin waɗannan mutanen kuwa? Ta tambayi kanta tare da rafka tagumi.
***** *****
Kamar wanda aka ɗaurewa zuciya haka Aliyu yake jin kansa, da ƙyar ya iya lallaɓawa ya ƙarasa hostel ya kwanta, yunwar da yake ji ma sai ya neme ta ya rasa, ya yi iya tunaninsa amma ya kasa gane abin da maganganun Dr. Dubiya suke nufi da abin da take nema a gurinsa, ya san dai ba zai wuce wani aikin ba ne a game da harkar school, amma duk da haka mamakin inda ta san shi da dalilin zaɓo shi a cikin dubunnan ɗalibai ya ƙi barin shi. Yana kwance yana ta saƙawa da kwancewa har su Auwal suka dawo, da mamaki suke duben shi, Auwal ya ce. "Da ma kana nan?" Ya gyada masa kai yana tashi zaune.
"Lafiya kuwa? Ya na gan ka wani iri?"
Buɗe baki ya yi zai labarta musu komai ko don su ba shi shawara amma sai ya ji kamar an saka masa wani abu ana jan harshensa zuwa maƙoshinsa, da sauri ya dafe wuyansa tari ya sarƙe masa, sannu suka shiga yi masa cikin tausayawa.
Musa ya ce. "Ko za mu je Clinic ne ƙwaro?" Girgiza masa kai ya yi, daidai lokacin wayarsa ta yi ƙara cikin sautin da Amma kawai ya saitawa shi, duk da halin da yake ciki amma sai da murmushi ya suɓce masa, ya zaro wayar daga aljihunsa ya ɗaga ya kara a kunne, abin mamaki ras suka yi magana suka gama, amma da ya ƙara yunƙurin ba wa su Auwal labarin abin da ya wanzu tsakaninsa da Dr. Dubiya sai ya ji irin abin ɗazu, dole ta saka ya haƙura suka shiga wata hirar.
Bayan sun yi sallar la'asar ya siya dafaffiyar masara ya ci ya sha ruwa sannan ya ce wa su Auwal zai je ya ɗan dawo, sai da ya fice daga makarantar gabaɗaya sannan ya ciro card ɗin daga Aljihun rigarsa ya jujjuya shi ya duba address ɗin jiki. A fili ya furta. "Allah ka sa mu ji alkhairi."
Abin hawa ya tara ya hau, bayan sun je unguwar ya yi tambaya aka nuna masa har numbern gurin da yake a jikin katin, zuciyarsa ɗaya ya taho, amma ganin gida ne ba guri na public mutane ba da ya yi tsammani ba sai ya ji zuciyarsa ta motsa, fargaba ta lulluɓe shi ya ji kamar ya juya ya koma, ga area ɗin ba jama'a duk manyan gidaje ne. Yana ƙoƙarin juyawa ya ga an buɗe ƙaramar ƙofar gidan, wani irin rawa zuciyarsa ta yi masa kamar ana kaɗa ta, babu walwala Dr. Dubiya da ke yi masa kallon tsaf ta ce. "Shigo." Kamar soko haka ya hau girgiza mata kai, murmushi ta saki ta ce. "Ba zan cutar da kai ba Haidara, haba Zakin Mamansa, karaya da tsoro ba su dace da kai ba kwata-kwata." Da wani irin shock ya dube ta jin sunan da ta kira shi, wanda Amma ce kaɗai take kiran shi da wannan sunan.
Murmushi ta saki tare da ba shi hanya ya wuce a ɗarare cike da tsoro kamar za a ce tak ya arce. Tana gaba yana bin ta a baya kamar raƙumi da akala har madaidaicin parlourn gidan. Ta nuna masa guri ya ɗofana kamar mai zaune akan wuta.
"Ka saki jikinka, bana son wannan ɗari-ɗarin." Ta faɗa tana zare mayafin abayar jikinta ta ajiye, sannan ta nufi wata ƙofa da ke cikin parlon. Da faranti shaƙe da kayan abinci ta dawo ta dire a gabansa, tana bin shi da wani mayen kallo ta ce. "Ka fara cin abinci sai mu yi magana." Aliyu da kansa ke ƙasa tun ɗazu ya ce. "Alhamdulillah na ƙoshi." A muryarsa ta ƙara fahimtar yanayin da yake ciki na tsantsar tsoro, hakan ya sa ta dawo gabansa ta tsaya, zip ɗin gaban rigarta ta ɗan yi ƙasa da shi kafin ta fara magana. "Ba zan matsa maka dole sai ka ci abinci ba, amma abin da na kira ka domin shi tilas ne ka yi shi, matuƙar kana son tsira da rayuwarka." Cikin rashin fahimta ya ɗago ya kalle ta, ɗage masa gira ta yi tana murmushin da yake ƙara saka shi a cikin tashin hankali. Saurin kawar da kansa ya yi gefe ganin kanta ba ɗankwali ga saman ƙirjinta a bayyane.
Taku ta fara a parkourn cikin ƙasaitarta, muryarta ɗauke da izza ta ce. "Tun ranar da na fara ganin ka nutsuwa ta yi ƙaura a rayuwata, zuciyata ta kwaɗaitu da kai, na so na yakice ka amma na kasa, shi ya sa na yanke shawarar kawai zan neme ka na bayyana maka ƙudurina, zuwan ka office ɗina na farko da haɗuwarka da mai delivery duk shirina ne, saboda ina son na gama tantance ka kafin na tunkare ka da abin da yake tafe da ni." Ta ja fasali tare da matsowa ta ranƙwafa daidai fuskarsa ta ce. "Ina son mu yi rayuwa ta jin daɗi da nishaɗi ni da kai, ka ɗebe mini kewar ƙishirwar namiji da take damu na, ni kuma zan ba ka ko nawa kake so, daga...."
A hargitse ya ɗago ya dube ta cikin rashin fahimta da alamun tambaya amma ya kasa furta komai, ido ta kanne masa sannan ta ci gaba da magana cikin wani irin salon.
"Rayuwa nake so mu yi da kai irin ta mata da miji, mai cike da farinciki, na mayar da maitata a kanka kai kuma ka samu tarin dukiya." Ta ƙarashe maganar tana ƙoƙarin kai hannu jikinsa.
"A'uzubillahi...! Ya faɗa a rikice tare da miƙewa ya ja baya jikinsa yana tsuma zuciyarsa na harbawa da sauri da sauri.
"Mene ne haka? Me kike faɗa ne? Don Allah ki dawo cikin hayyacinki, ɗalibinki ne fa a gabanki ba wani ba." Ya faɗa cikin rawar murya har lokacin jikinsa na ɓari.
Murmushi ta yi mai sauti ta ce. "Aliyu na san kai ba yaron da za ka kasa fahimtar abin da nake nufi ba ne, don haka kar ka wahalar da ni ka wahalar da kanka, ka amince kawai ka samu kuɗi, gida, mota waya mai tsada da ma duk wani abu na more rayuwa." Wani kallo ya wurga mata da idanunsa da suka sauya lauyi, gabaɗaya ya nemi kwarjininta da yake gani ya rasa, ƙimarta da girmanta suka zube a idonsa kamar faɗuwar gini, a ƙyamace ya ce. "Allah tsare ni da abin da kike nema a gurina, in sha Allah har na koma ga Allah ba zan taɓa aikata zina ba, bare..."
"Kai!" Ta daka masa tsawa tana zazzaro masa ido, wata irin muguwar faɗuwa gabansa ya yi, a gigice ya fara ambaton sunan Allah tare da neman ɗaukinsa."
"Na riga na kwaɗaita da kai, don haka dole ka yi abin da nake so, zan ƙyale ka yanzu, ka tafi saboda ina buƙatar nutsuwarka a duk lokacin da za mu kasance, amma ina so ka sani rayuwarka a tafin hannuna take, duk inda za ka je sai na nemo ka ko da birnin sin ne, saboda haka kar ma ka yi wani yunƙuri na guje mini don wahalar da kanka kawai za ka yi, zaka iya tafiya." Ta faɗa tana yin ƙasa da zip ɗin rigarta gabaɗaya. A hanzarce ya nufi ƙofa har yana ƙume kai da bango, ilahirin jikinsa ɓari kawai yake, bai san ya fito ƙofar gidan ba sai ya yi karo da wani dutse. A ƙasa ya zauna ya dafe kansa. A fili ya furta. "Mafarki nake, ba gaskiya ba ne, this is impossible!" Ya runtse idonsa yana fatan ya farka daga wannan mummunan baccin, amma da ya buɗe ido sai ya gan shi a zahiri, a wata unguwa da bai taɓa zuwa ba, sai da Malamarsu ta gayyace shi, Dr. Dubiya da ɗalibai ke mugun shakka, mace mai kamar maza, mai ɗaure fuska da rufe duk wata ƙofa da za a raina ta, kalamanta ne suka dawo masa, komai ya dawo masa kamar a lokacin yake faruwa.
"Da gaske ne, da gaske ni ne Aliyu, Why me? Me ya sa sai ni za ta nema da wannan ƙazamar rayuwar?" Ya faɗa kamar taɓaɓɓe yana ƙara bajewa a ƙasa, me ya sa ma ya zo? Me ya sa tun a fari bai yi tunanin wani mugun abun take ƙulla masa ba? Me ya sa ya kasa ba wa su Auwal labari? Ya san da za su ba shi shawarar kar ya zo. Haushin wani kare da ƙarfi ne ya sa ya yunƙura ya tashi, yana jinsa kamar a kan iska saboda jikinsa da ya yi masa sanyi laƙwas.
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un! Allah ban da kowa da komai sai kai Allah ka ƙare ni daga sharrin wannan matar."
Ya faɗa cikin imani da yaƙinin Ubangiji ne kaɗai zai shiga tsakaninsa da ita, don haka ya kai ƙarar ta wajensa, idan ta fi ƙarfin shi ba ta fi ƙarfin Ubangijin Musa da Harun ba.
Da wannan tunanin ya samu ƙwarin gwiwar jan ƙafa ya fita titi don samun abin hawa ya mayar da shi hostel.
Yadda su Musa suka gan shi ya sa suka yi Clinic ɗin makaranta da shi, don jikinsa sai rawa yake ga ƙafa yana ja kamar sabon gurgu, maganin ciwon kai aka ba shi suka dawo suka kwantar da shi a ɗaki yana sassauke numfashi.
"Sannu Aliyu, wai ina ka je ne? Me ya same ka?" Auwal ya tambaya cikin damuwa, bai iya ba shi amsa ba, sai idanunsa da ya lumshe yana fatan ya farka ya ga a cikin mafarki duk waɗannan abubuwan suka faru.
***** *****
Ƙarfe biyar da mintuna Dr. Dubiya ta ƙarasa gida, a hakimce ta fito daga mota ta nufi ciki, fuskarta babu walwala ko kaɗan.
"Welcome Ma." Wadda ta buɗe wa Su Saudat ƙofa ta faɗa cikin risinawa bayan ta buɗe mata ita ma. Kai kawai ta jinjina kaɗan ta shige main parkour cikin takun ƙasaita. Atine da har lokacin suna rakuɓe ba wanda ya ƙara bi ta kansu ta duƙa daga zaunen da take ta ce. "Sannu da zuwa Hajiya, barka da dawowa, da fatan kin dawo lafiya?"
"Yawwa." Kawai ta faɗa tana miƙa wa wata tsohuwa da ta fito daga wata ƙofa da sauri jin dawowar tata jakar hannunta, sannu da zuwa ta yi mata ta amsa kamar an yi mata dole tare da zama a kan kujera ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, tsohuwar kuma ta nufi saman benen da ke parlourn riƙe da jakar da aka ba ta.
"Hajjaju Makkatu ikon Allah, Ubangiji ya ja kwana ya ƙara sutura da wadata, Allah ya tsare gabanki da bayanki, ya yi...."
"Me ke tafe da ku ne Atine?" Ta katse ta da faɗin haka cikin ƙosawa.
Sai a lokacin Saudat ta ɗago kai ta dube ta, a hankali ta ce. "Ina yini?" Da hannu ta amsa mata idanunta a kan wayarta.
"Wata mai neman aiki ce na ƙara nemowa ko za a dace."
Ɗago kai Dr. Dubiya ta yi, ta yi wa Saudat kallon tsaf sannan ta ce. "Ita ce wannan?" Da sauri Atine ta gyaɗa kai ta ce. "E ita ce Ranki ya ɗade."
"Ke tashi tsaye." Ta faɗa cikin ba da umarni tana kallon Saudat.
Ba musu ta miƙe a hanzarce amma har lokacin kanta yana ƙasa, hawayen da ya cika mata ido take son mayarwa.
"Ɗaga tafin ƙafarki na gani."
Rarraba ido ta shiga yi don ba ta gane me take nufi ba, Atine ce ta zungure ta cikin gwaninta ta ce. "Hajiya ba ta maimaita magana, ki ɗaga tafin ƙafarki ki nuna mata ta gani." Numfashi Saudat ta sauke ta ɗaga ƙafar, sai ta yi taga-taga kamar za ta faɗi, hakan ya sa ta yi saurin dafa kujera, a haka ta nuna mata duka tafukanta, sai da ta ja sakanni kafin ta sake magana cikin izza. "Buɗe bakinki."
"Buɗe mata da kyau, haƙoran za ta gani." Cewar Atine tana wata dariya kamar shashasha.
Buɗewar Saudat ta yi a hankali, kyawawan haƙoranta farare ƙal suka bayyana.
"Sosai za ki wage shi fa."
Ji Saudat ta yi kamar ta mangare Atine saboda wannan neman sunan da take ya ishe ta, amma haka ta wangale bakin kamar mai tallan toothpaste.
"Good!" Dr. Dubiya ta faɗa tana jinjina kai.
"Sai yanzu kika kawo wadda za ta dace da zaɓin Son, duk da ba wai komai ya yi yadda yake so ba ne amma a yi maleji a haka."
Idanunta akan Saudat da ta gaji da tsayuwa ta yi maganar.
Godiya Atine ta shiga kwararawa tare da rattaɓo mata kirari da kanbabawa. Daidai lokacin aka buɗo ƙofar parlon aka shigo, yadda ya buga ta, ta koma ta rufu da ƙarfi ya sa dukan su kallon gurin.
"Son!" Dr Dubiya ta faɗa fuskarta ɗauke da murmushi.
Yana cika da batsewa kamar kodayaushe ya ce. "Mom."
"Welcome." Ta faɗa tare da tashi ta ƙarasa inda yake ta kama hannunsa ta yi masa side hug.
"Ka gaji da yawa daga gani, ka hau sama ka huta." Ta yi maganar tana shafa kansa.
Ƙara turɓene fuska ya yi ya ce. "Mom I'm very very tired, na gaji da aikin nan, yana takura rayuwata da yawa." Cikin rarrashi ta ce. "Ka yi haƙuri, ina nan ina lallaɓa Dad soon za a canza maka da wani."
"Ni aikin ne gabaɗaya bana so."
"Duk yadda kake so haka za a yi maka, ka je ka huta, ga sabuwar mai aikinka, za ta zo yanzu ta gyara maka part ɗinka."
Kallon raini ya yi wa Saudat ya ɗauke kai tare da jan tsaki, a wulaƙance ya ce. "Wannan sukutar za ta iya aikin kuma?"
"E son, za ta yi maka aiki irin yadda kake so, duk ta fi na baya da aka kawo qualities ɗin da kake so."
Baki ya taɓe ya nufi hanyar da za ta sada shi da part ɗinsa.
"Sannu da zuwa Yallaɓai, ina ta magana ba ka ji ba."
Wani banzan kallo ya watsa wa Atine da ta yi maganar ya ci gaba da tafiya.
Jingina da kujera Saudat ta yi jin jiri na neman kayar da ita, tana ta auna maganganun Hajiya don ta ƙara fahimta da kyau, wannan mai kamar basaraken za ta yi wa aiki ko yaya? Ta dai fahimci ɗan Hajiyar ne, abin da ba ta gane ba sabuwar mai aikinsa da ta ambata, mene ne haɗin aikinta a gidan da kuma Namiji?
"Ke bi bayan Son ya nuna miki inda za ki gyara masa, ke kuma Atine zan aiko a kawo miki saƙonki, amma ki koma daga waje ki jira." Dr. Dubiya ta faɗa tana nufar steps ɗin da ke parlourn.
"A sakko lafiya Hajiya." Cewar Atine baki a washe tana miƙewa tsaye, duban Saudat ta yi cikin raɗa ta ce. "Wannan da kika gani ya dawo yanzu shi kaɗai za ki dinga yi wa aiki, iya ɓangarensa kawai za ki na gyarawa kullum, shi kaɗai ne ɗan Hajiya namiji, yana da yayyi mata har biyar, wadda ta sakko ɗazu ita ce ƙaramar su, ita ce mai ɗan sauƙin kai a gidan." Ta ɗan yi waige-waige a parlourn sannan ta ƙara ƙasa da murya ta ce. "Ba ƙaramin ji da shi Hajiya take ba, don haka ki kiyaye ɓacin ransa idan kina so ku zauna lafiya, aiki akan kari ban da sanyin jiki da gaddama, sai kuma kin koyi buɗe baki kina yi musu gaisuwa ta ban girma, wannan dinkum-dinkum ɗin ajiye shi za ki yi gefe."
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un!" Saudat ta faɗa hawaye na sakko mata, murya a karye ta ce. "Gaskiya ba zan iya ba, na ɗauka aikin gida ne kawai zan dinga yi, amma aikin wani ƙato daga ni sai shi a ɓangare ɗaya ba zan iya ba gaskiya, ba zan zauna wani da ba mijina ko muharramina ya dinga juya ni ba."
Baki Atine ta hangame ta ce. "Ba a yi wa Hajiya haka ai, wasa da hankali? Taɓ! Ai tunda muka shigo gidan nan ta ɗauke ki to an yi an gama, gara ma ki haƙura, kuma mene abin damuwa a nan, aikinki fa kawai za ki yi ki baro part ɗin nasa, za a ba ki ɗaki a ɓangaren masu aiki, ni yanzu zan je na karɓi abinci a gurin su Asabe, tun ɗazu yunwa ke nuƙurƙusa ta."
Ido kawai Saudat ta runtse, idan ta tuna duk Mama ce ta janyo mata wannan tozarcin sai ta ji zuciyarta ta ƙara ƙuntata, komai ya duniyar ya fice mata a rai.
Wata mata ce da ba za ta wuce shekaru talatin da biyar ba ta shigo parlourn, suka gaisa da Atine sannan ta dubi Saudat ta ce. "Hajiya ta ce na zo na raka ki inda za ki zauna, ki ajiye kayanki sai na raka ki part ɗin Yallaɓai."
Sallama Atine ta yi mata ita kuma ta bi bayan wannan matar jikinta a matuƙar sanyaye.
Wani ƙaramin parlour suka ɓulla suka ƙara shiga wata ƙofar da ta sada su da wani corridor mai ɗauke da ɗakuna, ɗakin farko ta buɗe suka shiga, Saudat ta tsaya tana ƙare wa ɗakin da yake ɗauke da komai kallo. "Nan ne ɗakinki, ki ajiye kayanki na kai ki ɓangaren Yallaɓai." Kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki haka ta jingine box ɗin suka fito, ta ƙaramin parlourn suka ɓulla wata ƙofa again, gurin kamar parlour shi ma amma babu kujeru sai wasu decorations da suka ƙara ƙawata shi, a jikin wata ƙofa matar ta danna wani abu da yake baƙo a gurin Saudat, bayan wasu mintuna ƙofar ta buɗe kanta, matar ce ta fara shiga sannan Saudat ta bi bayanta.
"Ya ilahi!" Saudat ta furta cikin suɓutar baki don ta ɗauka a zuci ta yi maganar, saboda haɗuwa da tsayuwar parlourn, mamakin wannan wanne irin gida ne take, ta saba zuwa manyan gidaje na alfarma, don Familyn Abba da Mama duk da akwai masu kuɗi, amma ba ta taɓa zuwa wanda ya yi haɗuwar wannan ba.
"Barka da hutawa ranka ya daɗe." Matar ta faɗa cikin risinawa.
Sauban da ke tsaye daga shi sai singlet da dogon wando ya ɗaga mata hannu fuska ba walwala. Gabatar masa da Saudat ta yi sannan ta juya ta fita.
Rakuɓewa Saudat ta yi a bango tana jin kamar ta kurma ihu, ba ta taɓa kasancewa daga ita sai namiji a guri irin haka ba sai yau, Yaya Zubair ne kaɗai namiji a gidansu, shi ma kuma ba a nan garin ya yi karatu ba, shi ya sa suka tashi iya su mata a gida, ko office ɗin Malami ta je a makaranta sai ta ji duk ta takura, ba ta iya sakewa da maza kwata-kwata, hakan ya sa ta ji kamar an ɗauko dala da gauron dutse an ɗora mata akai saboda nauyin da kanta ya yi mata da girman abin da take gani, addu'oi kawai take yi a cikin ranta na neman ɗaukin Ubangiji.
Sauban bai bi ta kanta ba ya koma bedroom ɗinsa, har ta gaji da tsaiwa ta tsugunna bai sake fitowa ba, taimakon da Allah ya yi mata ma yau ba ta sallah, matsalar ɗaya ce tana buƙatar sauya pad, ga shi tsabar ruɗewa ba ta yo guzurinta daga gida ba.
Sai da aka kusa shafe awa sannan ya fito sanye da jallabiya yana latsa waya, satar kallon shi Saudat ta yi tana son tuno inda ta san shi don tun kallon farko da ta yi masa a ɗazu ta ga kamar ta taɓa ganin shi.
Wani ƙaramin towel ya cilla mata ya ce. "Ki goge ƙafarki sai ki shiga toilet ki wanke hannunki da kyau ki dawo." Ba ta ce komai ba ta ɗauka ta goge ƙafar, a gadarance cikin ba da umarni ya ce. "Malama sosai za ki goge fa, ko shafawa na ce ki yi da za ki wani goga ki tsaya?" Ranta ya sosu musamman da ta ga ƙaramin yaro da ba zai fi sa'anta ba ne yake yi mata haka, ta yi kamar yadda ya ce sannan ta ɗago da kalle shi da towel ɗin riƙe a hannunta.
"Wani hauka ne wannan, ki goge datti kuma sannan ki riƙe dustern da hannunki? Dalla Malama jefa ta can." Ya yi maganar a tsawace yana nuna mata wani guri, zuciyarta kamar za ta fashe haka ta je ta cilla a cikin wani abu da shi kaɗai ta gani a inda ya nuna mata da ba ta san mene ne ba, ta dawo ta tsaya a inda ta bari.
"Wai ke wacce irin daƙiƙiya ce? Ba cewa na yi ki je toilet ki wanko hannunki ba amma za ki zo ki mun tsaye a kai?"
Sosai ranta ya soso da wannan cin kashin, amma ta danne ta ce. "Ina ne toilet ɗin?" Sai da ya harare ta sannan ya nuna mata da hannu, ta tafi da sauri ta buɗe ta shiga, jingina ta yi da ƙofar ta saki kuka mara sauti, kalmar daƙiƙiyar da ya jefe ta da ita na yi mata kuwwa a kanta.
Anya za ta iya kuwa? Za ta jure wannan tozarcin? Haka masu aikin suke yi da ma? Duk da tana ganin yadda Mardiyya da Shamsiyya suke wulaƙanta masu yi musu aiki amma ba ta taɓa ganin sun yi musu irin haka ba, ba sa daraja su dai amma ba sa jifan su da irin wannan kalmomin na tozarci. Kuka sosai ta yi sannan ta share hawayenta ta je ta wanke hannun da sabulan da ta gani a toilet ɗin ta fito.
Yana ganin ta ya miƙe ya ce. "Mu ga hannun?" Cikin rashin fahimta ta dube shi da jajayen idanunta.
"Ware su mu gani idan sun fita." Ya faɗa cikin ɗaga murya da ƙosawa.
A ƙule ta haɗe su guri guda ta ɗago ta nuna masa, ya ƙare musu kallo sannan ya zagaye ta ya wuce ba tare da ya yi magana ba, bai jima ba ya fito ya cilla mata wata paper, ta ɗauka ta karanta, dokoki da tsarin ayyukan da za ta dinga yi masa ne a rubuce cikin harshen turanci, numfashi ta sauke tana jinjina azabar iyayi da tsari irin nasa, don ita a gurinta abun ya wuce ta kira shi tsafta sai dai gwalli da fi'ili, sai nanata wanke hannu kafin ta taɓa masa komai yake a cikin rubutun.
Abin da ba ta sani ba Sauban ƙyanƙyamin ta yake, ƙyanƙyamin duk wani talaka, aikin ma da yake yarda ake yi masa don babu yadda zai yi ne, shi ya sa mai aikinsa daban take da ragowar na gidan, ita kaɗai ce take zaune a cikin part ɗin masu gidan ba na ɓangaren masu aiki da aka ware musu ba, saboda a cewarsa ba zai yiwu tana taɓa masa kaya kuma tana cuɗanya da wasu ƙazamai ba, duk wani abu da yake wanke datti da ƙazanta a jikin mutum da kariya daga ɗaukar ciwo yana da su danƙar a cikin toilet ɗin parlournsa, a kullum kafin a fara yi masa shara da goge-goge sai mai aikin ta shiga ta wanke hannu da ƙafarta ta, bayan tsaftar da ta taho da ita a jikinta. A hakan ma wani lokacin yana jin ƙyaƙyamin, daurewa kawai yake yi. Inda a son ran Dr. Dubiya ne ta fi son ɗaukar masa masu aiki Christian don za su fi yi masa abin da yake so, amma saboda ba sa tsarki ya ce ba zai iya rayuwa suna taɓa masa abubuwa ba, musamman gyaran gadon da zai kwanta a kai, shi ya sa ta haƙura ake ɗaukar masa Hausawan, su kuma ba sa jimawa suke tafiya saboda ba sa jurewa yadda yake treating ɗinsu kamar wasu dabbobi, ga ƙyama ƙiri-ƙiri da yake nuna musu.
*#Zeey Kumurya*
*#****