1
Ba kowace mace mai HAIHUWA ba ce take gina al'umma. Amma kowace UWA ta gari tana gina ƙarni.
Kowa na iya amsa sunan MAHAIFIYA, amma ba lallai ne ta amsa sunan UWA ba. A yau, akwai yara da yawa masu MAHAIFIYA, amma ba su da UWA.
A zahiri, duk wadda ta ɗauki ciki, ta sha wahalar naƙuda, ta haifi ɗa, ta shayar da shi, ta raine shi, ita ce MAHAIFIYA. Wannan wata ni'ima ce da ALLAH ya ba ta. Amma UWA wani matsayi ne da ya fi haihuwa girma.
UWA ita ce wadda ke gina tarbiyya, tana shuka ɗabi'a, tana raya IMANI, tana koyar da TAUSAYI, GASKIYA da TSORON ALLAH.
Ba wai ga ɗanta kaɗai ba, har ga duk sauran ƳAƳAYEN AL'UMMA. Saboda haka, ba haihuwa kaɗai ke gina UWA ba. Tarbiyya ce ke ɗaga darajar MAHAIFIYA zuwa matsayin UWA.
Idan haka ne, ya ke 'yar uwata...
A matsayinki na mace, ki yi ƙoƙarin ki zama MAHAIFIYA UWA, ba MAHAIFIYA kawai ba. Ko da ALLAH bai ƙaddara miki haihuwa ba, har yanzu za ki iya zama UWA ta hanyar tarbiyya, kyakkyawan misali, nasiha, tausayi da riƙon amanar al'umma.
Sai dai akwai tambaya guda ɗaya da nake son mu tsaya mu yi wa kanmu...?
Me ya sa a yau kusan kowace mace tana iya zama MAHAIFIYA?, amma ba kowace ba ce take zama UWA?. Wataƙila amsar da zan bayar ba ita ce amsar da kika tanada a ranki ba. Ni ma ba na da'awar na mallaki cikakkiyar amsar. Ni ma kamar ke, ɗaliba ce ta makarantar rayuwa. Ina gani ne gwargwadon abin da ALLAH ya nuna mini. Ina fahimta ne gwargwadon ilimin da ya hore mini. Ina kuskure kamar yadda kowa yake kuskure.
Amma ina da yakinin cewa idan muka haɗa tunanina da naki, muka haɗa abin da na gani da abin da kika gani, muka kuma dubi kanmu da zuciya ta gaskiya ba da son zuciya ba. Da yardar ALLAH, za mu iya gyara wani abu a rayuwarmu. Domin babban haɗari ba yana shigowa gida da hayaniya bane. Wani lokaci yana shigowa ne cikin shiru ko sanɗar sirri da ba lallai kiji sautin a lokacin daya dace ba, har sai yayi gawurtar nuna kansa da kansa, zata iya yiwuwa kuma lokaci ya riga ya ƙure miki, an zo gaɓar da masu iya magana kance: BA'A ƁARI A KWASHE DAI-DAI.
Domin sakacinmu akan zama MAHAIFIYA-UWA a yau, yana fara kwasar tarbiyya. Yana kwashe mutunci. Yana kwashe tausayi. Yana kwashe zumunci. Har wata rana mu wayi gari muna kallon juna, amma bamu san ma ta inda muka rasa kanmu ba.
Shi SANTSI ba lallai ya kasance iska ba. Ba lallai ya kasance mutum ba. Ba lallai ma ya kasance abin da ido yake gani ba. Sai dai idan ya samu gurbi a rayuwa, yana iya kwasar mutum zuwa inda bai taɓa zato ba.
Wannan littafi ba ya da'awar cewa zai canja duniya. Ba kuma ya zo ne domin ya nuna cewa marubuciyarsa ta fi kowa sani ba. Ko tafi kowa iyawa, ko tafi kowa ganewa, ko ta fiku ganin abinda ku bakwa gani. Hasashe ne. Tunani ne. Darasi ne tare da hannunka mai sanda wajen samu mu farka a inda muka shagala ko muka manta, koma bamu sani ba.
Da fatan idan kika haɗa abin da kika sani da abin da za ki karanta a cikin wannan littafi. ALLAH yasa ya zama haske gare ni da ke. Ya tsare mu daga duk wani SANTSI da ke neman kwasar imaninmu, tarbiyarmu da rayuwarmu.
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا قُوا أَنفُسَكُمْ وَأَهْلِيكُمْ نَارًا وَقُودُهَا النَّاسُ وَالْحِجَارَةُ عَلَيْهَا مَلَائِكَةٌ غِلَاظٌ شِدَادٌ لَّا يَعْصُونَ اللَّهَ مَا أَمَرَهُمْ وَيَفْعَلُونَ مَا يُؤْمَرُونَ
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kãre wa kanku (da iyãlinku wata wuta makãmashinta mutãne da duwãtsu ne. A kanta akwai waɗansu malã'iku mãsu kauri, mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umurce su, kuma sunã aikata abin da ake umunin su.
(Suratut Taḥrīm: 6)
MANZON ALLAH ﷺ ya ce: “Dukkanku makiyaya ne, kuma dukkanku za a tambaye ku game da abin da aka ba ku amanarsa.”
(Bukhari da Muslim).
★______________★
««1992»»
NIGERIA
JIHAR-KATSINA.
Sosai sautin kukan yaron ya cika falon, har tamkar yana kaɗa bangon gidan. Yanda yake jan ajiyar zuciya kamar zai shiɗe dole ya baka tausayi. Ba kukan yaron bane abin mamaki, yanda mutanen dake cikin falon suka zuba masa ido kawai suna kallonsa tamkar kukan baya damunsu, shine mafi ban mamaki.
Gaba ɗaya yaron bai wuce shekara biyu ba a duniya. Duk wannan uban kuka da yake garzazawa yana riƙe a hannun wani matashi da bai wuce shekaru talatin da biyar ba ne. Ƙyaƙyƙyawa ne ƙwarai da gaske, fatar jikinsa da siffofinsa zai iya sa mutum ya ɗauka ba cikakken baƙin fata ba ne. Sai dai idan ka ƙara kallonsa sosai, zaka fahimci bayan wani launi yanki akwai ainihin jinin Hausawa da ke yawo a jikinsa.
Sosai yaron dake kuka yake kama da shi. Duk da ƙarancin shekarunsa, ko ba'a sanar maka ba zaka fahimci ɗansa ne. A gefen damansa wata dattijuwa ce zaune da kusan ya kwaso kamanninta, fuska a murtuke tamkar ba ta son ko kallonsa balle na yaron. Kusa da ita kuma wani dattijo ne mai cike da kamala, shi ma babu tambaya zaka gane mahaifinsa ne. Shi ma kallonsu kawai yake yi, ba tare da yace komai ba.
Sallamar shigowar wata tsohuwa da wata budurwa ke riƙe da hannunta ne ya katse yanayin falon. Sai dai banda kukan yaron da shi kam tamkar ƙara ƙarfi yake yi.
Iyayen biyu suka miƙe kusan lokaci guda suka tarbe ta cike da girmamawa. Fisha ta jinjina musu kai kawai, domin hankalinta gaba ɗaya yana kan matashin nan da yaron. Kallon da take masa kuwa cike yake da tsantsar ɓacin rai. Har tana ƙoƙarin zama ba dai-dai ba a kujera, sai da dattijon ya yi saurin zuwa gareta ya taimaka mata ta zauna da kyau.
A gabanta ya durƙusa tare da faɗin, “Sannu da zuwa Ammah. Fatan kuna lafiya?”.
“Ina fa zance ina lafiya, ina da jika irin ɗanka mai baƙin hali nan da rashin jin magana. Dan ALLAH yanzu wa gari ya waya Isma'ila? Ka duba wannan abin takaici da kaico. To yanzu wai ma daya ɗakko ɗan ya kawo mana waye anan bawansa da zai riƙe masa shi? Ko kece Ummu-Kulsoom?”.
Da sauri dattijuwar nan ta ce, “Ammah ni kam miya haɗani da riƙe masa ɗa? Kodai ya maidawa uwarsa idan ya girma ya amso, ko ya nemo mai riƙe masa. Ni ma tawa hidimar ta isheni. A lokacin da na nuna ban amince da aurensa ba ai nima nuna min yay ban isa ba.” Muryarta ta sarƙe alamar takaici..........✍🏼