FreeThe story
Synopsis
No synopsis yet.
Sample · 1
Ba kowace mace mai HAIHUWA ba ce take gina al'umma. Amma kowace UWA ta gari tana gina ƙarni.Kowa na iya amsa sunan MAHAIFIYA, amma ba lallai ne ta amsa sunan UWA ba. A yau, akwai yara da yawa masu MAHAIFIYA, amma ba su da UWA. A zahiri, duk wadda ta ɗauki ciki, ta sha wahalar naƙuda, ta haifi ɗa, ta shayar da shi, ta raine shi, ita ce MAHAIFIYA. Wannan wata ni'ima ce da ALLAH ya ba ta. Amma UWA wani matsayi ne da ya fi haihuwa girma. UWA ita ce wadda ke gina tarbiyya, tana shuka ɗabi'a, tana raya IMANI, tana koyar da TAUSAYI, GASKIYA da TSORON ALLAH. Ba wai ga ɗanta kaɗai ba, har ga duk sauran ƳAƳAYEN AL'UMMA. Saboda haka, ba haihuwa kaɗai ke gina UWA ba. Tarbiyya ce ke ɗaga darajar MAHAIFIYA zuwa matsayin UWA. Idan haka ne, ya ke 'yar uwata...A matsayinki na mace, ki yi...
Contents
Table of contents
Preview every chapter, see what is free, and continue reading when you join ArewaPen.