2
..........Caraf Ammah ta tareta da faɗin, “Karki sake ki zubda hawayenki a kansa. Yo bashi ya zaɓa ma kansa haka ba. Ai abinda kika faɗa shine dai-dai. Kodai ya maida yaron ga uwarsa, ko kuma ya nemo mai riƙe masa. Ko kuwa Mustapha?”.
“Haka shine dai-dai Ammah. Dan ni wallahi ma na ƙagara ya tashi ya koma inda ya fito ya bar min gida. Kukan ɗansa ya cika min kunne.” dattijon ya faɗa yana hararsa shi da yaron.
“Dan ALLAH ku yi haƙuri ku gafarceni iyayena.”
A karo na farko matashin ya yi magana. Hawaye suka gangaro masa.
Tamkar furucinsa ya yi musu tsawa, falon ya yi shiru lokaci guda. Shi ma yaron ya ajiye a ƙasa, sannan ya durƙusa bisa gwiwowinsa. Ya haɗa hannayensa biyu yana ci gaba da roƙo.
“Ni mai laifine a gareku na sani, na kuma tabbatar da fushinku kawai ya isa sakawa na ɗauki irin wannan sakamakon. Amma dan ALLAH kada ku hukunta yaron nan da laifin daba nashi ba. Yana buƙatar ku a matsayin AHALI, yana buƙatar irin tarbiyyar ku da kukai min a matsayina na mahaifinsa. Yau ne karo na farko ya iso duniyar ku, ku taimaka min Ammah kada ku koresa da laifin mahaifinsa, ku amshesa ni ku koreni da laifin dani na aikata muku iyayena. Ammah, Ummy, Abba dan ALLAH na tuba”.
Shiru kowa ya kasa magana. Da alama kalamansa sunyi matuƙar tasiri a zukatansu. Duk da Ummy harararsa take yi har yanzu. Tsawon wasu sakanni babu alamar wani zaiyi magana, hatta yaron ya langaɓe jikin kujera yana jan ajiyar zuciya alamar barci zaiyi.
Nannauyar ajiyar zuciyar Ammah ta katse yanayin, kafin ta buɗe baki ta kwala kiran sunan “Hussaina”.
Daga waje budurwar data shigo da ita ɗazun ta amsa tana shigowa. Cikin risinawa kanta a ƙasa ta ce, “Ammah gani”.
“Ɗauki yaron can ki goya”.
“To”.
Ta amsa da girmamawa tana ƙarasawa inda yaron yake kife a kujera. Har takai hannu zata ɗauke shi Ammah ta dakatar da ita.
“Kinga jira. Ummu-kulsoom bata zanen goyo”.
Babu jayayya tsakaninsu, dan haka Ummy ta miƙe, ɗakinta ta nufa, babu jimawa sai gata da zani na babbar atamfa dake fes yana ƙamshi, kai daga gani kasan nata ne. Hussaina ta risina ta amshi zanin. Tare da ɗaukar yaron da har ya fara barci ta saka a baya ta ɗaure, sannan ta fita a falon.
Amma ta sake sauke numfashi, sai kuma ta kalli matashin nan da tun shigowar Hussaina ya zauna a maimakon durƙuson da yake.
“Ja'iri mai kunnen ƙashi, dawo nan kusa da ni”.
Babu musu ya miƙe zuwa inda take, a ƙasa ya zauna kusa da ƙafafunta, caraf suka haɗa ido da Ummy dake jefa masa harara. Saurin duƙar da kansa ya sake yi.
Ummu-kulsoom sai haƙuri, harara bazata canja komai ba, sannan bazata magance komai ba. Tunda abinda aka gudar masa tun farko ya riga da ya faru sai kuma haƙuri ai. Kuskure dai yayi, ga kuma sakamakon nan ya amsa tun ba'aje ko ina ba. Isma'ila dama wannan shine abinda ake gudar maka tun farko bawai dan ana ƙinka ba. Amma idonka ya rufe giyar soyayya na ɗibarka da ƙuruciya, ka kasa ganewa. Maganar maimaita magana ma ɓacin rai ce dan haka a barta, yanzu sai ka shirya canjawa da fuskantar ainahin rayuwa. Mata dai babu irin kalar da bamu da su a yankinmu na Afirka. Anan ƙasarmu ta haihuwa ko ƙasar da mahaifiyarka ta fito, cikin dangi ko bare duk wanda ka kawo mu masu amsa ne da yarje maka, idan har mun gamsu da tarbiyya da addininta. Kama godema UBANGIJI da ta yarda ta baka ɗan ka kawo shi gida inda za'ai masa tarbiyya ta addininka. Dan gaskiya da ace bayan raba auren naku ta mallake ɗan nan to gaskiya ba lallai ni kaina na duba maka ba. Amma zan yafe maka saboda wannan yaron kawai daka nuna mazantakar karɓo mana.”
Sosai gaban Isma'il ya faɗi, zuciyarsa ta ƙara nauyi da jin kalaman Ammah. Dole ya haɗiye sauran bayanin daya dace ace ya musu bayan rabuwar aurensa da matarsa kenan. Dan idan yace zai ƙara da wani bayani bayan haka to akwai matsala. Gara ya daure su fara yafe masa komai ya dai-daita sai a sake sabon zama. Wannan tunani ya sashi haɗiye sauran zancensa ya kora shi ya dannesa da yawun bakinsa da tsiya-tsiya. Sai kalaman godiya daya sake jera ma Ammah dana sake neman gafara.
“Na gode sosai Ammah. In sha ALLAHU bazan sake ba. Wannan ɗin ma UBANGIJI ya ƙaddara hakan ne, sai kuma rabon wannan yaron. Ummy dan ALLAH kema ki yafe min ke da Abbah. Na tuba, na tuba”.
Shiru sunƙi suyi magana. Sai da Ammah ta ce, “Kuma ya kamata ku saki hakanan ai. Ku yafe masa ku saka masa albarka. Yaro kuma mu amsa mu riƙe ALLAH ya taya mu ruƙo. Dan ko aure ya sake ban yarda ku bashi ba balle matarsa. Gwara ya zauna a wajenku ku tarbiyancesa.”
Abbah ya jinjina kai cike da girmamawa. “Shi ke nan Amma yanda kikace haka za'ayi. Mun yafe masa ALLAH ya ƙara shirya mana su”.
“To Amin ya rabbi. Kefa Ummu-kulsoom”.
“Na yafe masa Ammah, ALLAH ya yafe mana baki ɗaya.”
“Haka nake son ji. Amin ya ALLAH. Kai Sama'ila miye sunansa?”.
Da lafiya lafiya ne cikin haushi zaice mata shi ba sunansa Sama'ila ba ta daina ɓata masa suna. Amma yanzu sai baiyi magana ba ya bata amsa da, “UMAR, muna masa alkunya da AHKAM!”.
“Munafuki, shi ne kasa sunan Babana ko?”. Abbah ya faɗa yana hararsa.
Murmurshi yayi mai yalwa yana shafa kansa, haka ma Ammah sai ta sanya dariya da faɗin, “Yo inama laifi. Shi ke nan ai ni Sama'ila ka sake wanke min zuciyata. Sunan Miji ai ba wasa ba. ALLAH ya raya shi ya albarkaci rayuwarku ku duka. ALLAH yasa ya gado mai asalin sunan da nawa mijin dan shima mutumin kirki ne”.
Karo na Farko Ummy ma tayi murmurshi. Hakan sai ya saka zuciyar Isma'il sake yin sanyi. Dan hakan na nufin Yaronsa ya samu ƙarɓuwa a cikin zuri'ar sa. Iyayensa kuma sun yafe masa. Sai dai kuma sauran matsalar bai san ta yanda zai fito da ita garesu su sake fahimta ba, dan kalaman Ammah sun tsorata shi, yana gudun ɓata goma biyar bata gyaru ba. Furta su tamkar taka SANTSI ne a zame. Komai kuwa zai iya ƁAREWA hatta da wannan yafiyar daya samu a yanzu a garesu. Hakan na nufin sai ya jinkirta, sai kuma ya sake neman dama...........✍🏼