017
by @oumfatima33
*MEERAH*
*017*
"Dama a binciken da na yi ne na gano cewar ɗaya daga cikin yaran da suka aikata abin ɗan gidan Honorable Ado Aaji Doguwa ne, abokin takarar shi Honorable Abbas Mamman Gwangwazo ɗin." Inspector Alim ya faɗa yana nuna masa file ɗin dake hannunsa.
Ɗago wa Commissioner Jibrin Yusuf ya yi ya kalli Inspector Alim yace.
"Are you serious Inspector?."
"Yes Sir, I'm very serious." Inspector Alim ya bashi amsa.
"Okay ka ɗan bani lokaci zan yi magana da Honorable Abbas ɗin, saboda na lura case ɗin zai iya sauya wa daga yanda muke kallon sa." Commissioner ya faɗa yana dafe goshinsa.
"Okay Sir." Inspector Alim ya faɗa yana ƙame wa haɗi da sara masa sannan ya fice a office ɗin baki ɗaya. Ajiyar zuciya Commissioner Jibrin Yusuf ya sauke bayan fitar Inspector Alim, wayarsa ya ɗauka ya saka kiran layin Hon. Abbas.
Bayan ya ɗauka da sallama suka yi gaisuwa irin ta aminai, Commissioner Jibrin Yusuf ne yace.
"Hon. Abbas a kan case ɗin daughter nake so mu yi magana."
"Okay ina jin ka, wani abu ya faru ne?." Hon. Abbas ya tambaya.
"Ƙwarai kuwa domin Inspector Alim ya tabbatar min da cewa ɗaya daga cikin yaran da suka yi yunƙurin ɗauke daughter yaron Hon. Ado Aaji Doguwa ne, shi yasa tunani na ya sauya daga yanda nake kallon al'amarin a da." Cewar Commissioner.
"Kenan dai zai iya zama shiryayyen abu ne, ma'ana da sanin Ado Aaji Doguwa yaronsa ya aikata hakan?." Hon. Abbas ya tambaya yana jin ɓacin rai.
"Ba zan iya iya cewa eh ko a'a ba, bincike ne zai tabbatar da hakan. Saboda haka na bayar da umarnin kamo yaran a gurfanar da su, na sanar da kai ne don ka san halin da ake ciki." Commissioner Jibrin Yusuf ya faɗa.
"Okay ba matsala case dai yana hannunka, ni dai abinda nake so shine a tabbatar da an hukunta yaran a kan abinda suka yi. Don babu wanda zai taɓa min Mamana na bar shi haka." Hon. Abbas ya faɗa.
"In sha Allah zamu yi abinda ya dace da tsarin doka." Cewar Commissioner daga haka suka yi sallama. da Hon. Akalar kiran ya mayar ga Inspector Alim ya bashi umarnin haɗa jami'ai aje a kamo su Nazzy.
_____________★
A ɓangaren Nawaz kuwa koda ya koma gida da dare ya samu Umma da Abba a kan maganar kuɗin daya samu, albarka suka saka masa tare da yi masa fatan alkairi. Gyara zamansa ya yi ya fuskanci su cike da nutsuwa yace.
"Abba dama nace tun da an samu waɗan nan kuɗin kuma suna da yawa babu laifi, shine nake ganin me zai hana a kai Umma asibiti mai kyau taga ƙwararren likita a kan matsalar ƙafafunta. Sannan abinda ya rage sai na biya kuɗin registration ɗina na wannan shekarar, ita ma Raihana sai a sama mata admission ta fara karatu da zarar result ɗin su ya fito."
"Hakan ma abu ne mai kyau Nawaz, Allah ya maku albarka kai da ƴan'uwanka baki ɗaya, ya ƙara buɗa maka kofofin samu na alkairi." Abba ya faɗa yana jin daɗin abinda Nawaz ɗin ta yi, domin shima duk fafutukar da yake yi a kan ganin ya samu ƴan kuɗin da za'a kai Umma babban asibiti ne a kan matsalar ƙafafunta.
Ita ma Umma albarka ta saka masa haɗi da yi masa godiya, daga haka ya miƙe ya fice daga gidan.
Koda ya tashi dawowa gidan biya wa ya yi ya yo musu siyayyar kayan abinci dai-dai misali, har da daƙwalen kaji ya sayo da kayan miya yace ayi miya.
Lokacin da ya kawo kayan addu'a sosai Iyayensa suka yi masa da fatan buɗin alkairi a rayuwarsa data ƴan'uwansa, ƙannensa kuwa murna suka riƙa yi da ganin kajin da ake dafawa a gidan nasu don ana jimawa ba'a yi hakan ba. Tun da Su Umma suka yi ritaya.
Kallon su yake cike da farin ciki, duk duniya bashi da wani burin da ya wuce Allah ya rufa masa asiri ya samu abinda zai kula da Iyayensa da ƴan'uwansa. Domin sune abu mafi muhimmanci a gare sa, haka kawai yana cikin wannan tunanin hoton fuskar Meerah ya hasko masa a cikin zuciyarsa.
Sai yake jin cewar tamkar ita ma a yanzu ta shiga cikin mutanen da suke da muhimmanci a gare sa, a hankali ya riƙa jin burinsa na ƙaruwa fiye da na baya. Don tun daga lokacin da ya fara ɗora ido a kanta, babu abinda zai yi ba tare da ta faɗo cikin tunaninsa da lissafinsa ba.
Hannu ya saka cikin aljihun rigarsa ya zaro ribbom ɗinta da ya ɗauka a asibiti, idanu ya tsira masa yana kallonsa yayin da zuciyarsa ke nuna masa shagwaɓɓiyar fuskarta.
Tashi ya yi ya buɗe drawer ajiye kayan sakawarsa ya ajiye ribbom ɗin a wuri na musamman yana sauke ajiyar zuciya.
Ficewa ya yi daga ɗakin yana ƙoƙarin kore tunaninta daga ransa, don ya ga abin na neman wuce gona da iri. Saboda haka yazo ya zauna cikin ƙanensa suna hira cike da farin ciki da shaƙuwar dake tsakaninsu.
Ɗaya bayan ɗaya yake bibiyar karatun ko wanne daga cikinsu don ganin yanda suke mayar da hankali, da kula da inda suke da rauni tare da gyara musu inda suka yi kuskure.
¢¢¢¢¢¢¢¢¢¢¢¢¢
A ɓangaren Inspector Alim kuwa sun kamo Nazzy da Shamos a wani Club da suke zuwa, bisa umarnin da aka bashi na arrest warrant. Cikin ƙan-ƙanen lokaci maganar kamun ta watsu a social media sakamakon gardama da su Nazzy suka yi yayin tafiya da su.
Wanda hakan ya janyo hankalin mutanen dake wurin suka fara ɗauka a wayoyinsu dan da nan suka fara watsa wa, don neman engaging a shafukan su na sada zumunta.
Da dare ne aka yi kamun amma zuwa safiya maganar ta fara watsuwa a duniya, sai dai har yanzu ba'a san ainahin dalilin da ya saka aka yi kamun ba.
Hakan yasa mutane keta yin canki in canka wurin lalubo dalilin da yasa aka kama su, duk da cewar a bayyane take kowa ya san cewar su Nazzy ɗin basa jin magana ko kaɗan. Amma hakan bai hana wasu cewar kama su na da alaƙa da siyasa ba, an yi ne don a ɓata mahaifinsa tunda zaɓe ya taho.
A ɓangaren Hon. Ado Aaji Doguwa kuwa hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba lokacin da ya samu labarin an kama masa yaro, domin kuwa yana matuƙar son yaronsa kasancewar shi kaɗai Allah ya bashi. Wannan ne dalilin da ya sa ma ya sakar masa yake yin yanda yaga dama.
Bai tsaya ɓata lokaci ba ya nufi Police Head quarter da aka kai su cikin ɓacin rai, kai tsaye Commissioner ya nemi gani. Shine ya haɗa sa da Inspector Alim wanda case ɗin ke hannunsa ya yi musu bayanin abinda ake zargin yaran da aikata wa.
Kai tsaye yace bai yarda ba ƙarya ake yiwa ɗansa, kuma hakan ba abin mamaki bane tunda kowa ya san Hon. Abbas Mamman Gwangwazo abokin takararsa ne a siyasa.
Dady aka kira domin Hon. Ado Aaji Doguwa ya nemi a bashi belin yaran, kuma hakan ba zai yiwu ba dole sai an kira Dady ɗin don shi ya shigar da ƙaran. Ba zai yu a bayar da Berlin ba da saninsa ba.
Sai dai lokacin da aka kira sa ɗin tafiyar gaggawa ta kama shi zuwa Abuja. Don haka Ya Ajmal da Ya Sultan suka je suka wakilci sa. A ɓangaren Ajmal dama hakan yake so don ya yi alƙawarin babu ɗaga ƙafa sai an hukunta yaran nan koda waye Ubansa a ƙasar nan.
Lokacin da suka iso Hon. Ado Doguwa so ya yi ya nuna musu isa da iko, sai dai abinda bai sani ba shine Ajmal ya fi Dady kafiya da zafin zuciya. Don kai tsaye yace basu amince a bada belin yaran ba, sannan yace kawai a tura case ɗin kotu ba tare da ɓata lokaci ba.
Rai ɓace Hon. Ado Aaji Doguwa ya bar Police Head quarter tare da lauyansa, inda suka fara shirin yanda zasu tunkari shari'ar. Don ya lura da zafin kan yaron nan Ajmal da ya kalli tsakiyar idanunsa ya tabbatar masa cewar bai isa ya kare ɗansa daga hukuncin laifin da ya aikata ba, matuƙar yana raye sai an hukunta sa.
***** A ɓangaren su Ajmal shima suna komawa gida ya kira Dady ya sanar da shi halin da ake ciki, ya kuma tabbatar masa cewa a halin yanzu an miƙa case ɗin Kotu. Don haka yana buƙatar zama da lauyoyinsu domin tattaunawa a kan shari'ar.
Hakan kuwa aka yi lauyoyin sun zo kamar yanda ya buƙata, sun kuma zama dasu sun gabatar musu da dukkanin hujjojin da suke dasu. Saboda haka duka ɓangaren biyu a shirye suke tsaf don shiga kotun.
******* A ɓangare ɗaya kuma fitar maganar da zargin da ake yiwa su Nazzy ya zama wani topic ɗin da ban, domin tuni ƴan bani na iya suka amshe batun suka yi ta ciccira shi a social media. Inda magoya bayan Hon. Ado Aaji Doguwa suka juya maganar da cewa shiryayyen abu ne Hon. Abbas ya shirya don bɓata masa siyasa.
A ɓangaren magoya bayan Hon Abbas suma cewa suke da sanin Ado Doguwa ɗansa ya aikata hakan, don yaci zarafin Hon. Abbas ɗin. Haka dai magan-ganu suka yi ta yawo, kowa na tofa albarkacin bakinsa a kai.
****** Hon. Mamman Basiru Gwangwazo, Mahaifi a wurin su Hon. Abbas Mamman Gwangwazo yaji batun shiga kotun da ya fito fili da irin ƙananan magan-ganun dake yawo game da zuri'arsa.
kiran Dady ya yi a waya suka tattauna sosai a kan case ɗin. Kuma shi da kansa ya shiga maganar saboda batu ake na taɓa mutuncin ahalinsa
Wanda idan ba'a ɗauki mataki a kai ba, gobe wani da ban zai iya yunƙurin aikata hakan wa zuri'arsa. Saboda haka ya basu goyon baya ɗari bisa ɗari a kan hukunta yaran, don babu wanda ya isa ya taɓa zuri'arsa ya zauna lafiya.
Wannan kenan.
€€€€€€€€€€€€
Yau ta kama saura kwana ɗaya a fara shari'ar, don haka tako wane ɓangare sun kammala shirinsu. Inda a ɓangaren lauyan Hon. Ado Doguwa ya samu gana wa da su Nazzy ya yi musu tambayoyi kan yanda abin ya faru.
Kai tsaye Nazzy ya tabbatar masa ya aikata, kuma ko gobe ya samu dama a kan yarinyar sai ya dama, don ba kalar wacce za'a gani a ƙyale bace.
Lokacin da ya yi wannan furucin cikin bushewar ido da rashin kunya sai da mamaki ya kusan halaka barrister dake masa tambayar, duka duka Nazzy ɗin ba zai fi 18 years ba idan ma ya cika kenan. Amma tsananin gata da sakaci da tarbiyyar yaran mu da muke fama da ita a yanzu ya jefa rayuwarsa a irin mummunar hanyar, har yake irin wannan furucin ba tare da tsoro ko shakka ba.
A waɗan nan shekarun nasa kamata ya yi ace ya mayar da hankali ne wurin karatu da gina gobensa. Amma saɓanin haka tsananin gata da ya samu wurin iyaye, haɗi da rashin kwaɓa. Uwa Uba kuma kuɗi da aka sakar masa yake yin yanda ya ga dama da su, sun taimaka wurin lalata masa rayuwa, wanda iyayensa ke ɗaukar hakan a matsayin gata da samun ƴanci.
Ajiyar zuciya Barrister ya sauke lokacin da yazo nan a tunaninsa, kasancewar aiki aka ɗauke sa kuma aka biya sa manyan kuɗaɗe ya saka shi manta wa da komai ya shiga tsara wa Nazzy da abokinsa abinda zasu faɗa a kotu. Yana gama abinda ya kai shi ya fice don ƙara kimtsa wa shari'ar.
*Ajmal....*
Zaune yake a study table ɗin sa yana duba tsarin lectures ɗinsu da zasu fara sati mai zuwa, wanda a ƙa'ida yau saura kwana uku su wuce London kamar yanda aka tsara.
Sai dai wannan case ɗin ya sa suka ɗaga tafiyar zuwa satin gaba, domin ya yi wa kansa alƙawarin ba zai tafi ba sai an ƙar-ƙare ta. Saboda ya nuna wa Ado Aaji Doguwa cewar Dady ba sa'an wasan sa bane shi kaɗai ma ya ishe sa, domin kuwa shine tsaye a kan shari'ar.
Ƙaran da wayarsa ta yi ne ya saka shi dakata wa daga sarrafa key board ɗin laptop ɗinsa da yake yi cike da ƙwarewa tamkar wanda ya hardace ko wani madannin da harafin dake ɗauke a kai.
Hakan ya saka yake typing ɗin cikin sauri da zafin nama abin sha'awa, da wani irin salo ya juya ƙwayar idanunsa zuwa saman screen ɗin wayar don ganin mai kiran nasa.
*Mamynah....* shine sunan da ya gani yana kaɗawa a saman screen ɗin, wanda ya saka shi kumshe ido don ya tabbatar wani rikicin ne zata zo da shi.........
*Oum Fatima*
***
Barkanmu da dare.