Washegari aka tashi da wani irin sanyi mai ratsa kashi, gajimare ya rufe sararin samaniya yayin da jama'a ke ta kaiwa da kawowa wajen gudanar da harkokin na yauda kullum."
"Ƙarfe tara na safe, motoci guda uku kalar baƙi ƙirin masu kirar Range Rover Autobiography da Mercedes-Benz S-Class suka tsaya a gaban helkwatar Bin Ali Holdings. Masu tsaro sanye da baƙaƙen suit suka yi saurin ƙarasawa tare da buɗe ƙofar motar tsakiya."
"Bin Ali ya fito cikin takunsa na izza da ƙwarjini. Sanye yake da dakakkiyar shadda da akayiwa dinkin kaftan ta alfarma kalar light grey data sha ɗinkin sarauta, haɗe da agogon Patek Philippe da ke daure a tsintsiyar hannunsa."
"Fuskarsa bata nuna fushi, Ko alamar fargaba a tare da shi, duk da sanin cewa taron mambobin board na yau shi ne zai ƙayyade makomar shugabancinsa a kamfanin."
"Taufeeq ya mara masa baya da sauri yana dauke da takardun gudanarwa. Yayin da suke tafiya ta hanyar corridor zuwa babbar VIP conference room, Taufeeq ya rage muryarsa kasa: 'Aliyu, Hajiya Halima has already arrived with her lawyers.
She’s been talking to the major shareholders since 8:30 AM. She’s confident she has the numbers to pass a vote of no confidence if you don't present a solid succession plan.'"
Bin Ali bai ko kalle shi ba, illa É—aga girarsa guda É—aya da ya yi tare da saita É—aurin agogonsa. "Let her talk, Taufeeq. Noise doesn't win battles; strategy does."
Da shigar sa cikin babban wajen da ake taron, duk maganganun da ke tashi a cikin É—akin suka tsaya cak. Idanun kowa suka dawo kansa.
A tsakiyar dogon teburin gilashin dake dakin taron, Hajiya Halima tana zaune cikin shigar alfarma sanye take da wani lace mai matuƙar tsada daya amshi jikinta, idanunta sun na ɗauke da cikar nasara da ƙiyayya. A gefenta kuwa, saurayin yarta ne zaune sanye da suit, mai kyau da tsada shima.
"Bin Ali ya isa babbar kujerar data fi sauran girma (Chairman’s seat) ya zauna cikin ƙasaita, sannan ya buɗe taron ba tare da ɓata lokaci ba."
"Good morning, members of the board," Bin Ali ya faÉ—a cikin murya mai kwarjini da sanyi. "I believe we are all here to discuss the future and stability of Bin Ali Holdings."
Hajiya Halima ta gyara zamanta, ta yi saurin katse shi tun kafin yayi nisa. "Yes, Aliyu.
And the future of this company relies on stability. A company worth billions cannot be left in the hands of a leader who has no long-term personal stability—no wife, no child, no heir. If anything happens to you today, the stock value drops to zero. We need a co-chairman who has a family structure to secure our investments."
Mambobin board É—in suka fara haÉ—a baki suna gyada kai alamar goyon bayan abinda Hajiya Halima ta fada.
Bin Ali ya yi murmushin mugunta wanda bai kai ga zuciyarsa ba. Ya jingina da kujerarsa, ya haÉ—e yatsun hannayensa guda biyu yana kallon su daya bayan daya.
"Is that all you have, Hajiya Halima?" Bin Ali ya faɗa yana bin kowa da kallo ɗaya bayan ɗaya cikin sanyi mai firgitarwa. "You are running a multi-billion naira conglomerate, yet you are consumed by my marital status? Bin Ali Holdings operates on market dominance, strategic acquisitions, and ironclad legal governance—not on my bed space."
Ya miƙe tsaye cikin takunsa na izza, ya gyara agogonsa na hannu.
"In the last quarter alone, under my leadership, our share value rose by twenty-four percent. If any board member here feels my personal life threatens their investment, you are free to sign the buy-back paperwork today and step down. But as long as I remain Executive Chairman, no one dictates my private choices."
Kowa dake dakin taron yayi shiru saboda kwarjini da kalaman nasa suka haifar. Hajiya Halima ta kafe shi da ido, fuskarta ta sauya saboda haushin yadda ya taka mata burki a gaban kowa.
Bin Ali ya kalli Taufeeq. "Meeting adjourned." Ya juya ya fice daga É—akin taron cikin takama, yana barin É—akin cike da shiru da ikon da ya nuna.
Taufeeq ya bi bayansa cikin sauri har suka shiga penthouse office ɗinsa. Taifee ya kulle ƙofar yana yana kallon Bin Ali.
Bin Ali ya zauna a kujerar dake gaban teburinsa, ya kalli Taifeeq. "That is why you are here, Taufeeq. Call Dr. Farooq now. I want the surrogate candidate shortlisted by tomorrow."
AFEEFA..
Da safe misalin karfe takwas, Afeefa ta fito daga gidan nasu sanye da doguwar rigar atamfa ta dogon hijabi kalar sararin samaniya.
Zuciyarta sai tsalle take yi saboda fargaba. Saura kwana biyu kacal ranar Litinin ta yi ranar da ake buƙatar ₦750,000 don aikin ƙodar ƙanwarta Rahma.
Ta bazama cikin unguwanni da titunan unguwanin masu kudi dake nan Abuja domin neman kowace irin sana'a ko aiki domin samun damar fara hada kudin tigatar Rahma."
Ta shiga shagunan abinci (Restaurant), manyan gidajen wankin tufafi (laundries), har ma da kanana gidajen mai, amma duk inda ta shiga amsar ɗaya ce: "Babu aiki," ko kuma a ba ta aikin da albashinsa bai wuce ₦20,000 a wata ba—kuɗin da ba su isa ko sayen maganin Rahma na mako ɗaya ba.
Misalin ƙarfe uku na rana, zafi da gajiyar tafiya da ƙafa sun sa ƙafafunta fara zafi. Ta isa wani babban asibiti mai zaman kansa na City Care Hospital dake tsakiyar unguwar Asokoro, inda take fatan watakila za su buƙaci ma'aikaciyar shara ko wankin toilets.
"Tana tsaye a harabar asibitin, tana ƙoƙarin saita numfashinta yayin da kwallan takaici suka cika idanunta.“
"Mama Asabe, tsohuwar ungozomar da ke aiki a asibitin kuma ta san Afeefa tun tana ƙarama, ta hango ta tsaye a harabar asibitin tana kuka a hankali."
Mama Asabe ta ƙaraso kusa da ita cikin sauri. "Afeefa? Ke ce a nan? Lafiya kike kuka haka, me ya faru?"
Afeefa ta yi saurin goge idanunta, muryarta tana rawa. "Mama Asabe... Rahma ce.
Tana buƙatar ₦750,000 kafin ranar litinin don yi mata aikin ƙoda, idan ba haka ba... idan ba haka ba mutuwa za ta yi Mama! Na zagaya garin nan ko ina neman aiki ko wane irin ne amma ban samu ba.
Don Allah Mama ko akwai aikin da zan iya yi a nan in samu ko da rabin kuÉ—in ne?"
Mama Asabe ta sake baki da mamaki da tausayi. "Dubu É—ari bakwai da hamsin a tsawon kwana biyu? Afeefa wannan wace irin musiba ce?"
"A daidai wannan lokacin, Taufeeq dake sakkowa da ga doron benen farko na asibitin bayan ya kammala magana da Dr. Farooq. Yana shirin saukowa, ya hango Afeefa da Mama Asabe tsaye suna magana a ƙasa.
Kyawun fuskarta, yanayin shigar ta, da kuma tsananin kukan da damuwa da fuskarta ta nuna suka ja hankalinsa nan take zuwa gareta."
Taufeeq ya tsaya yana kallonta ta tsakiyar gilashin benen, sannan ya kira Dr. Farooq a waya cikin sauri.
"Dr. Farooq," Taufeeq ya faɗa yana nuna ƙasa. "Come to the window. Look at that young lady in the blue hijab crying near the pharmacy. I need you to find out who she is and why she is in distress. She fits the exact profile Bin Ali wants for the surrogate background—innocent, young, and respectable."
Dr. Farooq ya ƙaraso ya kalleta. "That’s Afeefa. Her younger sister is facing end-stage kidney failure, and they need ₦750,000 for surgery by Monday. They are extremely poor but very honorable people."
Taufeeq ya yi murmushin samun nasara. A hankali ya gyara agogonsa tare da fada a rarsa: This is not just a coincidence; this is fate.
Tariq ya kalli Dr. Farooq. "Arrange a private meeting with her right now in your office. I have an offer that will save her sister's life today—if she is willing to sign Bin Ali’s contract."