ƊAURIN ZUCI

Chapter 7

by @maryamstar248

***

𝐃𝐀𝐔𝐑𝐈𝐍 𝐙𝐔𝐂𝐈
         𝐁𝐘
𝐌𝐀𝐑𝐘𝐀𝐌 𝐒𝐓𝐀𝐑

💪𝗝𝗔𝗝𝗜𝗥𝗧𝗔𝗧𝗧𝗨 𝗪𝗥𝗜𝗧𝗘𝗥'𝗦 𝗔𝗦𝗦𝗢𝗖𝗜𝗔𝗧𝗜𝗢𝗡💪✍🏻

𝗙𝗥𝗘𝗘 𝗕𝗢𝗢𝗞
Chapter 7
Hasalima shi ne ke yawon nemo mutanen da zasu fake a inuwar su, su gudanar da zalunci son rai ba tare da angane da hanunsu ba.
Kamar dai yanzun da Me girman shugaban ƙasa Alhaji Abubakar ke zaune a gabansu, yana sharce gumin tashin hankali.
     Tsohone sosai da ganin shi ya kwana biyu a duniya, domin kuwa hatta da gashin kan shi ya nuna jimawar shi a duniya, gaba ɗaya kalar gashin ta tashi daga baƙi zuwa fari sol, sannan kuma ya rage yawa da cika ya zama ɗan kaɗan irin sili-sili yanda suman tsofaffin da ke samun hutu yanda ya kamata ke komawa, fari ne tas dogo da dukan alamu a yarintar shi yayi jiki sai de kuma yanzu da tsufa ya riske shi wannan ƙibar du ta zuganye, amma kalo ɗaya zaka yiwa fatar shi ka gane lallai yana samun kula diye da yanda ya dace, Alhaji Mansur Ashiru kenan, mataimakin Mafaka kuma jagoran shi a harkokinsa na sarari dana ɓoye.

A karo na babu adadi Saminaka ya kalli farar fuskar Alhaji Mansur wacce ta rikiɗe a idon shi zuwa baƙa ƙirin, duda ya tsoro ya bayyana muraratan a fuskar shi bama iya tsoronba harda kaɗuwa da razana akan gaskiyar da suka soma buɗe ma shi a yau hakan bai hana ya kalle su ɗaya bayan ɗaya ba, sannan ya ce cikin ƙarfin hali.
    "Idan da kun san da zan yi muku kafiya da taurin kai mi yasa tun farko kuka zaɓe ni, miyasa baku faɗa min ainahin gaskiyar ku ba sai yanzu da tafiya ta miƙa, mi yasa zaku kawo min wannan zancen alhalin kun san idan har ina cikin hayyacina ba zan taɓa aminta da shi ba."  ya faɗi lokacinda zuciyar shi ke karyewa a ƙirjin shi.

    Mafaka ne ya soma magana cikin buɗaɗɗiyar muryar shi wacce a yanzun sautin ta ke sake kaɗa hanjin cijin Saminaka.
    "Mune muka saka mutane suka zaɓe ka, ba wai iya cancantarka bane, siyasarma gaba ɗaya mune muka saka ka, sannan munbaka dama irin wacce bamu taɓa bawa wani ba, to kuma yanzu anzo gaɓar da muke jiran azo lokacin da zaka biya mu ya zo, don haka dolenka ne ka yi abin da muke da muradi, daga yanzu zuwa ko yaushe muna son ikon sarrafa mulki ya dawo hannunmu tunda dama mulkin ai namu ne kawai muna aza wasu ne don su kafa mana gwamnati daga baya kuma mu ture su mu muzauna muyi yanda mukaga dama."
   Mafaka ya faɗi hankalin shi a kwance sam babu damuwa ko tausayin yanayin da ya jefa mutum me karamci da kima.

  Girgiza kai Saminaka ya soma yi yana jin rashin aminta da abin da suke shirin saka shi ya aikata.
    Ƙwaro ne ya soma tashi tsaye bayan ya dogara sandar da ke taimaka ma shi wajen tsayuwa da kuma tafiya, ya soma zagaye kujerar da Saminaka ke zaune yana faɗin.
     "Kaje ka yi du tunanin da kake son yi daga yau zuwa gobe muna jiran amsarka ammafa karka manta da batu akan jini,  muna buƙatar ganin wannan jar kalar na malala a kan ƙasa, muna da muradin jiyo sautin ihun jama'a da kukansu, idan da halima muna buƙatar jin takun gudunsu na jijjiga ƙasar da muke takawa." 
    Sai ya duƙa tare da aza fuskar shi akan kafaɗar Saminaka muryar shi can ƙasa sosai ya ce.
   "Muna kuma buƙatar jin kukan jinjirai sababin haihuwa a cikin gidajenmu."...



Ba iya zuciya ba hatta da gangar jikin Saminaka sai da ta tafi dogon hutu saboda tsabar razana.
Awanin sa suka biyo baya sun shuɗe ne da wani yanayin wanda sam ba zai iya kwatantawaba.
   Kallon shimfiɗaɗɗiyar kwaltar da lafiyayyun motocinsa ke gudu akai ya ke, yana ƙirgen adadin awannin da aka ɗibar ma shi domin soma ƙaddamar da baƙin zalunci.
      Ko da aka isa da shi tangamemen gidan shi bai iya ya kalli kowa ba, hasalima baya so kowa ya ganshi domin kuwa yana jin yanda dattin zunibin da ake shirin aikatawa a jikin shi.
    Kuma ko da yayi nasarar shiga wawakeken sashen shi kai tsaye ya shige toilet ya soma zubawa kanshi ruwa masu tsananin sanyi ko zai samu yaji wannan zafin da tururin da jikin shi ya ɗauka na raguwa, sai de a mau akon hakan du saukar da ruwan zai yi a jikin shi yana jin tsananin zafi fiye da misali,sai da ya ɗaga idanuwansa da suka birkice zuwa kalar kaɗuwa da tsananin tashin hankali ya kalli ruwan sannan ya tuna da wani abu, wani abu wanda ya tilasta ma shi zabura ya fita daga cikin haɗaɗɗen jakuzin babu shiri ya saɓi babban towel ya suturta jikin shi, sai de kuma kwatankwacin abin da yaji a ruwan shi yaji a jikin wannan towel ɗin da sauri tunanin shi ya harso ma shi dalilin faruwar hakan.
    Tun usul shi mutum ne kamili me tsananin tsoron Ubangiju da gudun haram, a yanzun da yake amfani da kayan da bana halal ba shiyasaka yake jin wucin wutar azabar da ke jiran shi a sanda yabar wannan duniyar ya fuskanci Ubangijin shi da yayi ma shi gargaɗi da gudun haramun.

Tuna hakan da yayi ne ya saka shi sake ɗimaucewa ya fice a sittin bakin shi na ambaton almar istigifari don neman gafarar Allah.

Bai samu nutsuwa ba, kamar yanda ya kasa zama ya dinga zagaye shi ɗaya a wawakeken room ɗin shi, har sai da shida kan shi ya kira wayar wanda ke wakiltar shi a sabgogin kasuwanci wanda yake mallakin shi tun usul.
   Bai damu da mamakin da ya tsinkayo a muryar Muktar Manager ba,  a lokacin da ya gama lissafa ma shi abubuwan da yake buƙata, ya yanke wayar yana sauke ajiyar zuciya.

Gaba ɗaya kwanyar kan shi a hargitse ta ke akan lamarin da ya kunno kai a rayuwar shi, babbar damuwar shi bai wuce sanin tsayin lokacin da suka binne suna shirya wannan ta'asar ba....


Tsaf ya fito cikin shiga ta alfarma, kalo ɗaya zaka yiwa kamulalliyar fuskar shi ka ganne tabbas akwai damuwar da yake son ɓoyewa ta ƙarfin tsiya.
    Wani abu ne me kama da mashi ya soke shi a zuci sanda ya isa dining room inda iyalanshi ke zazzaune suna cin abinci a nitse, cikin nauyin jiki ya isa wajen bai samu damar amsar gaisuwar kowa ba illa ɗaga musu hannh da yayi....

"Ina so ku ɗauki abubuwan da kuke so amma masu muhimmanci, cikin satinan zamu bar gidan nan."
    Ya faɗa lokacin da ya kora lumar data tsaya mashi a wuya ta gagara wucewa.

     Hamshaƙiyar matar da ke a zaune tana danna wayar ce ta ɗago da mamaki shimfiɗe akan fuskarta ta ce.

"Barin gida kuma, duka yaushe muka tare ina yau shatinmu biyu kenan."
  Ta yi maganar mamaki shimfiɗe akan fuskarta.

   Sai de kamar yanda ya faɗa tun usul bai sake tankawa ba saima tashi da yayi yabar wajen.
    Da kallo iyanlan nashi suka bishi inda wani matashi da ba wai rufe shrkaru ashirin zuwa da biyu ba ya ce.
   "Kai Dad ko problem, komi yaa kawo maganar tashi ana zaune ƙalau?.
   Anyway banda case da hakan because gobe zan bar ƙasar gaba ɗaya."
   Yana gama faɗin hakan ya tashi tare da ɗaukar wayar shi ya saka head phone ya fice daga dinning room ɗin.....

*****


Yau kwana Zunaina da Muhammad biyu a gidan Malam, kuma sosai take jin daɗin zamanta da Huwaila saboda macece me mutunci da karamci, babbar damuwar Zunaina bai wuce Muhammad ba, domin abin nashi kullum ƙara ta'azzara yake yi babu wani sauƙi a ciki, yanzu kam ta ɗaukewa kanta kallon idanuwan shi dan sosai suka zama abin tsoro saboda yanda kullum suke ƙara turewa da launin ja.

A ɓangaren Muhammad kuwa yana rayuwa ne a yanda tazo ma shi, bai damu da kowa da komi ba, sai de sallah akan lokaci bata wuce shi, babban abin ɗaure kai da yanzu ya daina magana kwata-kwata baya umm baya ummumm ko abinci baya ci, da farko Zunaina ta tayarda hankalinta amma daga baya Malam yace ta daina damuwa hakan ma wata alama ce ta jira shi na ƴan kwanaki kwaɗan zai warware.
   Ita kanta Zunainar akwai wani gagarumin kamari daya fara bayyana a rayuwarta, sai de bata sanar ba ta bar abin a ranta, ba tare da saninta ta ta ɓoye lamarin da zai girgiza duniyarta a nan gaba, ta bawa ƙaddararta damar kusantar ta ba tare da ta shirya karɓarta ba.

Yauma kamar kullum a firgice ta farka daga barcin da take yi ƙirjinta na hawa da sauka, idanuwanta suka firfito alamar tsoro da razani, a kiɗime ta soma lalubar kofin da take cikawa da ruwa tana ajewa kusa da ita du dare saboda farkawa.

    Kasancewar Kofin farine ya saka ta iya ganin sauyawar kalar abin da ke ciki, har ta gumtsa a bakinta sai tayi saurin janyo kofi tare da ƙura idonta tana kallon ciki, kasancewar bata gani da kyau ya saka ta haɗiye na bakinta ta kuma kai kofin baki tana, ta ɗan sha babu laifi, a sanda take cire kofin daga bakinta a sannan ne  aka kawo wutar nepa.
Wata iriyar hautsinawa hanjin cikinta suka yi lokacin da hasken jan ƙwan ya haske mata ruwan cikin kofin wanda suka sauya launi zuwa ja.
   Hannunta na ƙyarma ta saka yatsa ta dangwalo danshin kan leɓenta, a sannan ne tsananin firgice da razana suka baibayeta bata san sanda tayi fatali da kofin ba ta miƙe tsaye a hanzarce ta nufi wajen Muhammad tare da cakumarsa tana hakin tashin hankali.
    Bata lura da yanayin da yake ciki ba sam dan gaba ɗaya ta soma fita a hayyacinta.

Malam ne daga can waje yake kallo du abin da ke faruwa, makirin murmushi ya saki tare da ɗaukar wayarshi ya tura saƙo, bayan ƴan sakanni ta kawo haskw alamar shigowar massage, sai da yaɗanyi jimm kaɗan kamar yana tunani sai ya kuma ya yi reply.

   Ɗakin Huwaila ya nufa tare da tasota, sai gasu sun fito cikin baƙar shiga daga shi har ita, ita ta nufi wajen napep ɗin shi ta kunna, sannan ta nufi wani waje da aka loda kaya ta soma tattare kayan wajen, sai ga wata ƙofa da ke rufe ta bayyana, nan ta buɗe ƙofar sannan ta dawo.

      Cike da dabara Malam ke nitsa ƙarfen a saitin ƙirjin Zunaina yana kanainaye ta da daɗin baki ta hanyar tambayarta, bai dakata ba sai da ya tabbatar da ya nitse a naman ƙirjinta saman zuciya sannan ya kira Huwaila suka kama ta zuwa lokacin ta gama ficewa a hayyacinta suka saka a napep.

   Shima Muhammad haka suka yi mashi, sai de shi ya riga da ya fice a hayyacinsa   ba kamar Zunaina ba.

Ta ɓogayyun hanyoyi suka soma tsala gudu da Napep ɗin suna keta cikin gonaki, sai da suka yi nisa sosai sannan suka isa mararrabar hanya a kuma nan ne wata dalleliyar mota ke tsaye tana jiran isarsu.
  Malam ne ya soma fitowa ya saɓo Muhammad yayinda Huwaila ta janyo Zunaina suka kama mata aka saka su a cikin motar.

    Kamar  masu ruku'i haka suka duƙawa mutumin da ba'a iya ganin komi nashi sabida ya rufe ruf, wanu abu ya miƙa musu sannan ya shige cikin motar ya bata wuta, ganin haka suma su Malam suka nausa ta hanyar da suka zo suka koma gida.....✍🏻

TOFA GA WATA DAMALMALALLAR CAKWAKIYAR TA ƁULLO KAI🥺

Shin mike shirin faruwa da rayukan Zunaina da Muhammad🤔.

Domin jin amsar wannan tambayar ku kasance tare da ni.

#Daurin zuci
#Maryam Star.

MARYAM STAR CE