Sirrinmu

CHAPTERS 4–10 — SIRRIN DA YA GIRMA DA MU

by @113817622749984015388

CHAPTERS 4–10

NANA TA SHIGO

Washegari da safe, gidan Alhaji Musa ya cika da hayaniyar Halima.

“Ummaaa! Ina uniform ɗina?”

Hajiya Hauwa da ke zaune a tsakar gida tana gyara wasu kayan miya ta ɗaga kai.

“Kin sake manta inda kika ajiye shi?”

“Ban manta ba. Kawai dai ban san inda na ajiye shi ba.”

Hajiya Hauwa ta girgiza kai.

“Halima, duk rana haka za ki yi? Ki koma ɗakin ki duba sosai.”

Halima ta koma ɗaki tana magana ita kaɗai.

“Uniform ɗin nan ma yana da wahala. Jiya yana nan, yau ya ɓace.”

Bayan ɗan lokaci sai ta fito tana riƙe da uniform ɗin.

“Ga shi!”

Hajiya Hauwa ta kalle ta.

“Ina kika same shi?”

“Kan kujerata.”

“Kin ce ba ki san inda kika ajiye shi ba?”

Halima ta yi murmushi.

“Shi kansa bai gaya min ba.”

Hajiya Hauwa ta yi dariya.

“Je ki shirya kafin ki makara.”

Halima ta ɗauki jakarta ta nufi ƙofa, amma sai ta tsaya.

“Umma…”

“Me kuma?”

“Akwai kosai?”

Hajiya Hauwa ta kalle ta da mamaki.

“Da safe kenan?”

“Eh mana.”

“Ba ki koshi da abincin jiya ba?”

“Na koshi. Amma yau sabon yunwa ce.”

Hajiya Hauwa ta girgiza kai.

“Allah Ya shirya ki.”

Halima ta yi dariya ta fita.

A hanya zuwa makaranta, ta haɗu da Maryam da Raliya.

Raliya ta kalle ta sosai.

“Yau kin yi wanka kuwa?”

Halima ta tsaya.

“Me ya sa kullum sai kin tambaye ni wannan?”

“Saboda amsar tana da muhimmanci.”

Maryam ta yi dariya.

“Raliya, ki bar ta mana.”

Halima ta gyara jakarta.

“Ni dai na zo makaranta ne. Ba na zo domin ku binciki jikina ba.”

Raliya ta ce:

“To me ya sa kike gudun amsa?”

Halima ta kalle ta.

“Saboda ba ruwanki.”

Duk suka yi dariya.

Suna cikin tafiya sai Maryam ta tsaya.

“Ku tsaya. Ga Nana.”

Wata yarinya ce ta zo kusa da su. Ta kasance mai nutsuwa, tana riƙe da ƙaramin jaka a kafadarta.

Maryam ta ce:

“Nana ta dawo jiya daga garin da suke zama.”

Raliya ta kalli Nana daga sama zuwa ƙasa.

“To ita ce sabuwar mutum ɗin?”

Nana ta yi dariya.

“Sabuwar mutum kuma?”

“Eh. Ni Raliya ce. Wannan Maryam ce. Wannan kuma…” Ta kalli Halima. “Ita ce matsalar wannan ƙungiyar.”

Halima ta buɗe baki.

“Raliya!”

Nana ta fashe da dariya.

Maryam ta ce:

“Kar ki damu da ita. Tana son magana sosai.”

Halima ta kalli Nana.

“Ke ma kina son magana?”

Nana ta amsa cikin nutsuwa.

“Idan akwai abin faɗa.”

Halima ta yi murmushi.

“To shikenan. Za mu iya zama abokai.”

Raliya ta yi sauri ta ce:

“Kin riga kin yanke hukunci?”

“Eh.”

“Ba ta ce za ta zama ƙawarki ba fa.”

Nana ta yi murmushi.

“Ni ban ce ba, amma ban ce a’a ba.”

Halima ta kalle ta na ɗan lokaci sannan ta yi dariya.

Daga wannan rana, Nana ta fara kasancewa tare da su.

A lokacin hutun makaranta, su huɗun suka zauna a ƙarƙashin wata bishiya.

Raliya ta tambayi Nana:

“Ke kina son kosai?”

“Eh.”

Halima ta yi sauri ta ce:

“To kin shiga ƙungiyarmu.”

Maryam ta yi dariya.

“Wannan ne sharadin?”

Halima ta gyada kai.

“Eh. Wanda ba ya son kosai ba zai iya zama cikakkiyar ƙawata ba.”

Nana ta ce:

“To na samu matsayi kenan?”

“Kin samu.”

Duk suka yi dariya.

A hankali, Nana ta fara saba da su.

Ba ta da hayaniyar Raliya, kuma ba ta da saurin fushi irin na Halima. Tana yawan sauraro kafin ta yi magana.

Amma abin da Halima ta fi so a tare da ita shi ne, Nana ba ta yawan hukunta mutum idan ya yi kuskure.

A wannan shekarun, abinda ya fi muhimmanci a gare su shi ne makaranta, wasa, dariya, kosai da yawo tare.

Ba su san cewa shekarun nan na ƙuruciya za su zama wani ɓangare na tarihin rayuwarsu da ba za su taɓa mantawa da shi ba.

---

RANAR AIKI

Alhamis ce.

Tun da safe, Halima ta lura cewa malamai suna yawan fita da shiga suna ba ɗalibai umarni.

Raliya ta matso kusa da ita.

“Me ke faruwa yau?”

Maryam ta amsa:

“Ai yau ranar tsaftace makaranta ce.”

Halima ta tsaya cak.

“Me?”

“An ce kowa zai yi aiki.”

Halima ta kalli ajinsu.

“Ni ma?”

Raliya ta fara dariya.

“Ke ɗin fa?”

“Ni ban shirya irin wannan ba.”

Maryam ta ce:

“Babu wanda ya shirya.”

Sai wani malami ya fito.

“Dukkan ku ku ɗauki kayan aiki. Kowa ya shiga aikin tsaftace makaranta.”

Halima ta kalli tsintsiya da aka ba ta.

“Wannan fa?”

Raliya ta ce:

“Tsintsiya ce.”

“Na sani.”

“To me kika tambaya?”

“Ban san me zan yi da ita ba.”

Raliya ta fashe da dariya.

“Share mana!”

Halima ta fara sharewa.

Bayan mintuna kaɗan, sai ta jingina da bango.

Maryam ta kalle ta.

“Halima, me kike yi?”

“Na ɗan huta.”

“Kin fara minti biyu da suka wuce!”

“Ni mutum ce. Ba inji ba.”

Raliya ta fara dariya.

“Idan malamin nan ya gan ki fa?”

“Ba zai gan ni ba.”

A dai-dai lokacin sai muryar malamin ta zo daga bayanta.

“Halima!”

Ta rufe ido.

“Na’am sir.”

“Na ce ki ci gaba da aiki.”

“Eh sir.”

Ta sake ɗaukar tsintsiya.

Wannan karon ta yi aiki da gaske.

Ta share ajinsu, ta tattara tarkace, sannan ta taimaka wa wasu ɗalibai wajen gyara wajen ƙofar aji.

Da aka gama, malamin ya zo ya duba.

“Halima.”

Ta ɗaga kai.

“Sir?”

“Yau kin yi aiki sosai.”

Fuskarta ta haskaka.

“Na gode sir.”

Raliya ta rada mata:

“Yau kin zama mutum.”

Halima ta juya.

“Me kika ce?”

“Babu komai.”

“Na ji.”

Raliya ta gudu tana dariya.

Halima ta bi ta.

“Ki tsaya!”

Maryam da Nana suka fashe da dariya.

Bayan an gama makaranta, su huɗun suka zauna a ƙarƙashin bishiya.

Nana ta ce:

“Yau na ga wani sabon Halima.”

Halima ta kalle ta.

“Wane?”

“Halima mai aiki.”

Raliya ta ƙara:

“Kar ku saba da wannan. Gobe za ta koma tsohuwar Halima.”

Halima ta ce:

“Tabbas.”

Duk suka yi dariya.

A wannan ranar Halima ta fahimci cewa ba kowane aiki ake so ba, amma wani lokaci dole mutum ya yi abin da aka sa shi.

Ko da yake ita kanta ba ta shirya yarda da hakan gaba ɗaya ba.

---

 BAƘON DA YA ZO

Da yamma, Halima tana zaune ƙarƙashin bishiyar mangwaro tana ƙoƙarin cin mangwaro ɗaya ba tare da Hajiya Hauwa ta gan ta ba.

Sai ta ji muryar Umma.

“Halima!”

Ta ɓoye mangwaron a bayanta.

“Na’am Umma?”

“Zo ki taimaka min.”

Ta ajiye mangwaron ta shiga gida.

Da ta shiga, sai ta ga wani dattijo zaune tare da wata mata.

Dattijon ya kalle ta na ɗan lokaci.

“Wannan Halima ce?”

Hajiya Hauwa ta amsa:

“Eh, ita ce.”

Dattijon ya yi murmushi.

“Subhanallah. Kin girma sosai.”

Halima ta yi murmushi cikin kunya.

“Na gode.”

Matar da ke tare da shi ta kalle ta.

“Har yanzu kina da wannan halin?”

Halima ta ɗan daure fuska.

“Wane hali?”

Matar ta yi dariya.

“Kin manta?”

Halima ta girgiza kai.

“Ban sani ba.”

Dattijon ya yi dariya.

“Ba za ki iya tuna mu ba. Kin yi ƙanana sosai lokacin da muka san ki.”

Halima ta kalli Hajiya Hauwa.

“Umma, su waye?”

Hajiya Hauwa ta amsa:

“Mutanen da muka daɗe muna sani ne.”

Halima ta zauna gefe tana sauraron hirarsu.

Ba ta fahimci duk abin da suke magana a kai ba.

Bayan ɗan lokaci, baƙin suka tashi.

Kafin su fita, matar ta taɓa kafadar Halima.

“Ki ci gaba da karatu sosai.”

Halima ta gyada kai.

“Insha Allah.”

Bayan sun tafi, Halima ta koma wurin Hajiya Hauwa.

“Umma.”

“Me?”

“Su waye?”

“Na gaya miki. Mutanen da muka sani tun da dadewa.”

“Amma me ya sa suka san ni?”

“Saboda sun gan ki tun kina ƙarama.”

“Ni ban tuna su ba.”

“Ba abin mamaki ba ne.”

Halima ta yi shiru.

“Sun ce ina da wani hali.”

Hajiya Hauwa ta yi dariya.

“Sun san ki sosai kenan.”

Alhaji Musa, wanda ke zaune a kusa da su, ya yi murmushi.

“Halima, ba duk mutanen da suka san ka ne dole kai ma ka tuna su ba.”

Halima ta kalle shi.

“Amma ni ina son sanin komai.”

Alhaji Musa ya yi murmushi.

“Mun sani.”

Halima ta koma ƙarƙashin bishiyar mangwaro.

A zuciyarta kuwa, wata ƙaramar tambaya ta fara tasowa.

Me ya sa wasu mutane suke ganin kamar sun san ta fiye da yadda ita ta san su?

---

 RANAR KASUWA

Ranar kasuwa ce.

Tun da safe Halima ta fara roƙon Hajiya Hauwa.

“Umma, yau kasuwa zan je.”

Hajiya Hauwa ta kalle ta.

“Me za ki je yi?”

“Abubuwa.”

“Wane abubuwa?”

Halima ta fara lissafi.

“Zan sayi kosai.”

Hajiya Hauwa ta yi murmushi.

“Abin da kika fi so kenan.”

A lokacin Maryam da Raliya suka bayyana a ƙofar gidan.

“Halima!”

Halima ta fita.

Nana ma tana tare da su.

Raliya ta ce:

“Mu je kasuwa.”

Halima ta juya wurin Umma.

“Kin ji.”

Hajiya Hauwa ta ce:

“Ku je, amma ku dawo da wuri.”

“Za mu dawo.”

A hanya, Raliya ta ce:

“Ni zan sayi alewa.”

Maryam ta ce:

“Ni zan sayi ribbon.”

Nana ta ce:

“Ni zan sayi littafi.”

Halima ta ce:

“Ni kuma zan sayi kosai.”

Raliya ta kalle ta.

“Abin da kika fi so kenan?”

“Eh.”

“Ko kina da wani abu a rayuwarki?”

Halima ta yi dariya.

“Da yawa.”

Da suka isa kasuwa, hayaniya ta cika kunnuwansu.

Masu sayar da kayan miya, kayan marmari, kayan sawa da abinci suna ta kira.

Halima ta tsaya wajen mai kosai.

“Anti, ki ba ni guda uku.”

Raliya ta kalle ta.

“Guda uku?”

“Eh.”

“Za ki iya ci?”

Halima ta kalle ta.

“Me ya sa ba zan iya ba?”

Maryam ta yi dariya.

Suna cikin kasuwa sai wata tsohuwa ta kalli Halima sosai.

“Ke…”

Halima ta juya.

“Ni?”

Tsohuwar ta yi murmushi.

“Halima ce?”

Halima ta gyada kai.

“Eh.”

Tsohuwar ta ɗaga hannunta tana yi mata addu'a.

“Allah Ya raya ki. Allah Ya ba ki albarka.”

Halima ta ce:

“Amin.”

Tsohuwar ta ci gaba da tafiya.

Raliya ta kalli Halima.

“Kin san ta?”

“Ban sani ba.”

Nana ta ce:

“Wataƙila ta san iyayenki.”

Halima ta ɗan yi shiru.

Amma kafin ta yi tunani sosai, Raliya ta ja hannunta.

“Zo! Na ga wani abu.”

“Me?”

“Alewa.”

Halima ta yi dariya.

Daga baya suka dawo gida da kaya fiye da yadda suka shirya saya.

Hajiya Hauwa ta kalle su.

“Wannan duk me ne?”

Raliya ta ce:

“Abubuwa ne.”

Hajiya Hauwa ta kalli Halima.

“Ke kuma?”

Halima ta nuna jakarta.

“Kosai.”

Hajiya Hauwa ta girgiza kai tana dariya.

“Ni na san haka za ki ce.”

Da dare, Halima ta kwanta tana tunanin kasuwar.

A cikin kwanaki kaɗan, mutane daban-daban sun gane ta.

Ta tambayi kanta:

Me ya sa mutane da yawa suke kamar sun san ni?

Amma ba ta da amsa.

---

 MAGANAR ALHAJI MUSA

Da dare, gidan ya yi shiru.

Hajiya Hauwa tana cikin ɗaki, yayin da Alhaji Musa yake zaune a ƙarƙashin hasken fitila.

Halima ta fito domin ta ɗauki ruwa.

“Baba.”

Alhaji Musa ya ɗaga kai.

“Zo.”

Ta zauna kusa da shi.

“Kin yi karatu?”

“Eh.”

“Kin rubuta aikin da aka ba ku?”

Halima ta yi shiru.

Alhaji Musa ya kalle ta.

“Halima.”

“Zan rubuta.”

“Yaushe?”

“Yau.”

“Yau yaushe?”

Halima ta yi murmushi.

“Bayan na gama hutawa.”

Alhaji Musa ya girgiza kai yana dariya.

“Ki kula da karatu. Ilimi zai taimaka miki sosai a rayuwa.”

Halima ta gyada kai.

“Baba…”

“Me?”

“Zan tambaye ka abu.”

“Tambaya.”

“Yaya Baba Ibrahim yake?”

Alhaji Musa ya yi shiru na ɗan lokaci.

“Me ya sa kika tambaya?”

“Saboda ina son saninsa.”

Alhaji Musa ya yi murmushi.

“Baban ki mutum ne mai kirki. Yana da fara'a, kuma yana son mutane.”

Halima ta yi murmushi.

“Shi ma yana da taurin kai?”

Alhaji Musa ya yi dariya.

“Ɗan kaɗan.”

Halima ta nuna kanta.

“To shi nake bi.”

“Kin fi shi.”

Halima ta yi dariya.

Sai ta sake tambaya:

“Baba, wasu mutane suna kallona kamar sun san ni. Me ya sa?”

Alhaji Musa ya yi shiru na ɗan lokaci.

“Wataƙila saboda kina kama da babanki.”

“Da gaske?”

“Eh.”

Halima ta taɓa fuskarta.

“To idan na kama da shi, ya sa na zama kyakkyawa?”

Alhaji Musa ya yi dariya.

“Ke da kanki kin san kina da kyau.”

Halima ta yi dariya.

Bayan ɗan lokaci ta tashi.

“Baba, zan tafi.”

“Ki kwanta da wuri.”

“Na ji.”

Ta shiga ɗaki.

Alhaji Musa ya kalli inda ta tafi.

Fuskarsa ta nuna irin kallon da iyaye suke yi wa yaro wanda suke ƙauna sosai.

Halima kuwa ba ta san komai ba.

A wannan daren, ta fara son sanin abubuwa da yawa game da iyayenta.

Amma har yanzu akwai tambayoyi da yawa waɗanda ba ta san amsarsu ba.

---

WASIKAR

Washegari da rana, Halima tana waje tana wasa da Raliya da Maryam lokacin da wani mutum ya zo gidan.

Ya tsaya a ƙofar.

“Alhaji Musa yana nan?”

Halima ta amsa:

“Eh. Shiga.”

Mutumin ya shiga.

Bayan ɗan lokaci, Halima ta ga ya miƙa wa Alhaji Musa wata ƙaramar wasika.

Alhaji Musa ya karɓa.

Da zarar ya buɗe, fuskarsa ta canza.

Halima da ke kallonsa ta lura.

Ta kalli Maryam.

“Kin ga?”

Maryam ta ce:

“Me?”

“Baba ya canza.”

Raliya ta ce:

“Ko wasiƙar ta sa shi dariya?”

“Ba ya dariya.”

Mutumin ya tafi.

Halima ta shiga gida.

“Baba.”

Alhaji Musa ya ɗaga kai.

“Me?”

“Wace wasiƙa ce?”

“Ba komai.”

“Daga ina ta zo?”

“Ba komai ba ne, Halima.”

“Amma…”

“Ki tafi ki yi wasa.”

Ta fita.

Amma ba ta manta ba.

Da dare, Halima ta farka saboda jin muryoyin Alhaji Musa da Hajiya Hauwa.

Ba ta fita daga ɗakinta ba. Ta saurara kawai.

“Lokaci ya yi,” Alhaji Musa ya ce.

Hajiya Hauwa ta amsa cikin sanyin murya:

“Amma har yanzu yarinyar ƙarama ce.”

Alhaji Musa ya yi shiru.

“Mun san haka.”

Halima ta buɗe idanunta sosai.

Lokaci ya yi na me?

Ta kasa fahimta.

Sai ta ji Hajiya Hauwa ta ce:

“Mu jira.”

Alhaji Musa ya amsa:

“Eh. Mu jira.”

Halima ta kwanta tana kallon rufin ɗakinta.

“Me suke ɓoye min?”

Ta juya gefe guda.

Ta sake tunani.

“Lokaci ya yi na me?”

A karo na farko, Halima ta fara jin cewa akwai wasu abubuwa da manya suke magana a kai waɗanda ita ba ta sani ba.

Kuma Halima ba ta son a ɓoye mata abu.

Amma wannan karon, tambayar ba ta da amsa.

---

 KUNGIYAR ƘAWAYE

Washegari, Halima ta kasance cikin nutsuwa fiye da yadda aka saba.

Da ta isa makaranta, Maryam ta lura.

“Halima, me ya same ki?”

“Babu komai.”

Raliya ta kalle ta.

“Kin yi shiru.”

“Shiru ba laifi ba ne.”

Nana ta ce:

“Amma ke ba kya yin shiru haka.”

Halima ta yi murmushi.

“Ni ma zan iya yin shiru.”

Raliya ta ce:

“Wannan sabon abu ne.”

Halima ta kalle ta.

“Raliya…”

“Na daina.”

Duk suka yi dariya.

Bayan darasi, suka zauna a ƙarƙashin wata bishiya.

Nana ta ce:

“Idan akwai abin da yake damunki, ba dole ki faɗa mana yanzu ba.”

Halima ta kalle ta.

“Me ya sa kika ce haka?”

“Saboda kina tunani.”

Halima ta yi shiru.

Maryam ta riƙe hannunta.

“Duk abin da yake damunki, mu muna nan.”

Halima ta yi murmushi.

“Na sani.”

Raliya ta tashi.

“To idan babu wanda zai yi magana, mu yi gasar hawa bishiya.”

Halima ta kalle ta.

“Gasar me?”

“Hawa bishiya.”

“Kin san ba za ki iya ba.”

“Ke ce ba za ki iya ba!”

Halima ta tashi nan take.

“Ni?”

Nana ta fara dariya.

“Kun fara.”

Su huɗun suka nufi wata bishiya.

Raliya ta fara hawa.

Halima ta biyo ta.

Maryam ta ce:

“Ku kula!”

Halima ta hau sama tana dariya.

“Na fi ki!”

Raliya ta ce:

“Ba ki fi ni ba!”

A lokacin da Halima ta matsa ƙafarta zuwa wani reshe, sai ƙafarta ta zame.

“Halima!”

Ta kama wani reshe da sauri.

Maryam da Nana suka firgita.

“Ki riƙe!”

Raliya ta sauko tana taimaka mata.

Bayan sun sauke ta, Halima ta zauna tana dariya.

Raliya ta kalle ta.

“Me kike dariya?”

“Na ji tsoro.”

“Idan kin ji tsoro me ya sa kike dariya?”

“Ban sani ba.”

Duk suka fara dariya.

A ƙarshe suka koma gida.

Rayuwar Halima a wannan lokacin har yanzu tana da sauƙi.

Makaranta.

Ƙawayenta.

Rigima ƙanana.

Dariya.

Mangwaro.

Kosai.

Da sauran ƙananan abubuwan da suke sa yara su ji cewa duniya ba ta da wata matsala.

Amma a gidansu, manya suna da abubuwan da suke tattaunawa a hankali.

Akwai abubuwan da Halima ba ta sani ba.

Kuma ba ta san cewa rayuwarta za ta fara canzawa a hankali ba.

A gare ta, gobe za ta kasance kamar yau.

Amma rayuwa ba ta taɓa gaya wa mutum abin da take shiryawa ba.