Soyayya bayan sirri

BABI NA UKKU

by @aishora

SOYAYYA BAYAN SIRRI

BABI NA UKU — SAƘON DA BA A SAN MAI AIKO BA

Amina ta kasa barci a wannan daren.

Saƙon da ta samu yana ta yawo a cikin zuciyarta.

“Ki daina binciken abin da ya faru a baya, idan kina son ki zauna lafiya.”

Ta sake buɗe wayarta ta duba lambar.

Ba ta san mai ita ba.

Ta yi tunanin kiran Maryam, amma sai ta tuna cewa Maryam ma tana ɓoye mata wani abu.

Amina ta ajiye wayar kusa da kanta.

“Me ya sa kowa yake ɓoye min gaskiya?” ta furta a hankali.

Da safe, ta tashi da wuri.

Lokacin da ta fito daga ɗakinta, ta tarar da Maryam a falo.

Maryam ta kalle ta.

“Kin yi barci?”

Amina ta girgiza kai.

“A’a.”

“Me ya faru?”

Amina ba ta ce komai ba. Sai ta miƙa mata wayarta.

Maryam ta karanta saƙon.

Nan take fuskarta ta sauya.

“Ya Allah…”

Amina ta lura.

“Kin san wanda ya aika?”

“A’a.”

“Kina tabbatarwa?”

“Eh.”

Amina ta zauna kusa da ita.

“Maryam, ina roƙonki. Kada ki sake ɓoye min komai.”

Maryam ta yi shiru.

“Akwai wata yarinya,” ta ce a ƙarshe.

“Wace yarinya?”

“Ta taɓa zama a gidan Fahad.”

Amina ta daure fuska.

“Yar uwarsa ce?”

“A’a.”

“To wacece ita?”

Maryam ta sauke kai.

“Ba wanda ya san inda take yanzu.”

Kafin Amina ta iya sake tambaya, sai aka ji murya daga bayan su.

“Wane ne ba ku san inda yake ba?”

Dukansu suka juya.

Fahad ne.

Amina ta riƙe wayarta.

Fahad ya kalle su.

“Me kuke magana a kai?”

Amina ta miƙa masa wayar.

“Wannan.”

Fahad ya karanta saƙon.

Fuskarsa ta canza.

Amina ta lura.

“Ka san wanda ya aika?”

Fahad ya yi shiru.

“Fahad?”

Ya ɗaga ido.

“Ki manta da wannan saƙon.”

“Me ya sa?”

“Saboda ba abin da ya kamata ki shiga ba ne.”

Amina ta fusata.

“Amma ya shafe ni!”

Fahad ya yi shiru.

“Me kuke ɓoye min?” Amina ta tambaya.

Fahad ya kalleta na ɗan lokaci.

“Ba yanzu ba.”

“Har yaushe?”

Ya juya.

“Har sai lokacin da ya dace.”

Amina ta kalle shi yana tafiya.

A wannan lokacin, ta yanke shawara.

Za ta gano gaskiyar da kanta.