RU'UYAA (The dreams we never lived)

17. ... matsaloli...🖊️

by @autum17

               




Yau weekend,wurin ƙarfe goma Asma'u na zaune saman lilo ita kaɗai ba kamar sauran ranaku ba da mutane ke tururuwa yau daban ne ... saye da wandon jeans da riga sai hijabi peach color fuskarta fayau amma kyaunta bai ɓoyu ba..a hankali take shilla lilon tayi nisa cikin tunanin Khalil tana tsara an impossible future with him murmushi tayi tana lumshe ido ta fara shilla lilon da ƙarfi da nishaɗi tana sama da ƙasa ko tsoro bataji

Da sassarfa yake tafiya hannunshi riƙe da baƙar leda,kayan jikinshi yadi baƙi yasha ruwa ya gaji takalmin ƙafarshi ma sun siɗe bai ankara da mutum a saman lilon ba...GBAM!! Ƙafafun Asma'u suka sauka a fuskar shi da ƙarfi har Saida yayi baya baya ya faɗi baƙar ledar hannun shi ta faɗi duk abubuwan dake ciki suka zube ya dafe gefen idonshi daya fashe yana zubar jini... Asma'u ta ƙanƙame lilon that was spiralling out of control a mugun tsorace ..sai jujjuyawa yake da ita yana haɗa tada bishiyar ta bugu ba kaɗan ba ihu kawai take...


'' kamar Asma'u ce ke ihu ko?" Cewar inna sarai data fito daga ɗaki a gaggauce hannunta riƙe da hijabi, Anaam ma ta fito saye da gyale suka fita daga gidan a tare...nidai ina kwance a ɗakin mu..yau ranar tazo min a wani irin yanayin ƙunci da har bana son ko motsawa,kamar inyita kwanciya kada in tashi...bawai dan na mutu ba... jan bargo nayi na lulluɓe har zuwa kaina...

Da ƙyar Mama sarai ta tsayar da lilon daga juyawa Asma'u ta ƙanƙame ta kamar tana gudun idan ta saki zata faɗi idonta a matuƙar firgice tana numfashi sama sama tambayar ta inna sarai take Meya faru amma ta kasa Magana sai juyawa tayi inda mutumin nan yake zaune..gaban rigar shi ya ɓaci da jini hannun shi ɗaya rufe da idonshi..su Inna sarai suka kalli inda take kallo 


'' Innalillahi wa inna ilaihi raji'una meya faru?" Anaam ta kafe gayen da ido inna sarai take sallallami,wurin shi suka isa Anaam ta duƙa tana tattaro mashi abubuwan shi.. Asma'u ta duƙa gaban shi fuskar ta ɗauke da rashin jin daɗi.. batare da tunanin komai ba ta kai hannun ta,ta cire nashi dake rufe da idon...har wurin ya kunbura idon ma yayi ja

 '' laahaula wala ƙuwwata illa billa...wai Meya faru ne?'' 

Murya na rawa Asma'u tace '' buge shi nayi ban san yana zuwa ba kayi haƙuri dan Allah...'' naɗan lokaci baice komai ba sai ƙoƙarin buɗe idon yake amma ya kasa..da sanyayyar murya yace

 '' ba komai...'' hakan yasa Asma'u ta ƙara jin bata kyauta ba..she felt guilty..'' tunda kina da fes ait bos ki kular mashi da ciwon mana...'' da sauri ya girgiza kanshi '' ki bar shi kawai sauri nake..''

'' A'a bawan Allah tunda ita tayi maka wannan ta'asar kabari ta gyara dama nos (nurse)take so ta zama...'' 

bai sake cewa komai ba cire hannun ta Asma'u tayi daga fuskarshi ya miƙe da ƙyar suka nufi cikin gidan sai da suka fara shiga sannan ya bisu..kujera Anaam ta ɗauko daga kitchen ta ajiye mashi a tsakar gida.. Asma'u ta shiga ɗaki ta ɗauko first aid box a gaggauce ta fara wanke mashi ciwon bayan ta share jinin da auduga kamar yanda aka koya musu a practical.. sannu Inna sarai da Anaam suke mashi every now and then

Daga cikin ɗakin ina jin yanda suke ta yi mashi sannu suna ƙara bashi haƙuri harda Mama amma ban fita ba na cigaba da kwanciya ta...zuciya ta a ƙuntace na rasa inda zan sa kaina ji nake kamar in aske fatar jikina in sauya zuciya ta da komai nawa ko zan samu sauƙin abinda ke damu na...yaushe zan samu abin da na roƙa? Yaushe rayuwa ta zata sauya? Wayyo Allah na! siririn hawaye ne ya sauka daga idona nayi saurin share shi jin an ɗaga labule

 '' wai Abeedah yau lafiya kuwa?" Inna sarai ce take tambayar yi nayi kamar ina bacci ban tanka taba...a can tsakar gida Asma'u ta gama addressing ciwon ta manna mashi auduga da plaster with expertise...ta sauke ajiyar zuciya tana kallon fuskar shi,samu tayi shima ita yake kallo ta ɗauke idon ta tareda miƙewa ta kwashe abubuwan da tayi amfani dasu tana faɗin 

'' kabi a hankali kada ruwa ya taɓa wurin kaji...'' sai kawai ya gyaɗa kanshi ya nemi tafiya..inna sarai da Mama suka hanashi wai ya ɗan jira kaɗan..bai so yayi musu kawai sai ya zauna ɗin...Anaam ta jawo kujera ta zauna kusa dashi ta fara zuba kamar pamfo...shidai daga uhm sai uh uhm da murmushi a fuskar shi



Daga lokaci zuwa lokaci idonshi ke kaiwa gefen da Asma'u take duk tayi sanyi..bayan wani lokaci ya miƙe cike da girmamawa yayi ma su Mama sallama..sosai suka ƙara bashi haƙuri akan abinda ya faru yace ba komai ya ɗauki ledar magungunan shi ya ƙara kallon Asma'u one last time da murmushi kafin ya fice...

'' kamar in bishi...''

'' daga ganin mutum kamar ki bishi to ki bishi ɗin...'' turo baki Anaam tayi da abinda inna sarai ta faɗa...

Ji nayi fuskata ta fara ƙaiƙayi ban wani damu ba na cigaba da kwanciya ta amma ƙaiƙayin ya cigaba...tashi zaune nayi na fara sosawa ƙaiƙayin ya ɗan rage na ƙara yin kwance ina kallon ceiling...nan bacci ya kwashe ni...

'' Innalillahi Asma'u zoki ga fuskar Abeedah sama sama nake jiyo hayaniyar su hakan yasa na buɗe idona'' 

'' taɓ ɗi jam...'' Asma'u ta rufe baki tana jinjina kai faɗuwa gabana yayi da sauri na tafi gaban madubi take zuciyata ta tsuke kamar ana matse min ita da ƙarfi ƙirjina ya fara sama da ƙasa na kasa kuka sai raɗaɗin da zuciya ta take yi wasu manya manyan pimples ne suka ƙara fito min da yawa kamar an watso su a ƙarƙashin haɓa da goshi da hanci...


'' wani abu kika sha hala?" Anaam ta tambaya tana duba ni nan da can. lumshe idona nayi hawaye suka fara silala kafin jikina ya fara rawa kuka na ya fara fita da sauri ...sukayi tsaye suna kallo na babu wanda ya lallashe ni

 '' wai Meye nake jin tashin kuka?" Inna sarai ta shigo cikin ɗakin..nuna mata ni Anaam tayi

 '' ƙuraje ne suka fito mata a fuska shine take kuka...'' inda nake inna sarai ta iso

'' na gani...'' itama ta shiga duba fuskata daga gefe da gefe

'' ƙila wani abu tasha ko ta shafa..'' ina ji suna cinke cinken abinda nayi dayasa fuskata ta lalace har haka ban buɗe idona ba ƙuncin dake raina baya misaltuwa meyasa ni kaɗaice ta daban? Meyasa kowa yana rayuwa cikin sauƙi da jin daɗi banda ni? 

Ƙara rushewa da kuka nayi inna Sarai take lallashina har da cewa zata taya ni tafiyar dasu hakan yaɗan rage min wani abu kaɗan ba mai yawa ba Asma'u da Anaam kallo kawai suka bini dashi

'' ke baga jiki ba ke baga kyau ba..oh ni tuwo..wannan abu haka? gaki da shegen tsawo mutum tsaf zai ɗauka ke namiji ne..'' 

cewar Anaam, bayan tafiyar inna sarai Asma'u tayi wata yar iskar dariya mai ƙular da mutum ...ina jinsu amma ban tanka ba..toh mema zance? Da gaskiyar ta ai..nidai bani da Sa'a...
Maganganun Jay d akan zama pozitif (positive) suka faɗo raina...wani siririn hawaye ya sulalo min..taya zan zama pozitif bayan abinda yake faruwa ba hasashen shi nake ba...da gaske ne? Taya zan mayar da duk wannan a bayan ƙwaƙwalwa ta in cigaba da rayuwa kamar babu abinda ke damuna? taya zanyi farin ciki bayan abinda zai sani farin cikin banda shi? Fita su Asma'u sukayi ya rage ni kaɗai cikin ɗakin... 


miƙewa nayi da jajayen idona na isa gaban madubi naja doguwar riga ta baya ina kallon ƙirjina kamar ƙara shafewa yake a kowace rana... cikina ma ƙato sannan ƙuguna da bayana duka a shafe..meyasa? Fuskata kam bana son kallo ba ƙaramin ɗacin rai hakan ke sani ba...gashin gira ta yanzu a ɗan kwai shi amma bai da yawa...gashin idona har yanzu baida tsawo..sai dogon wuya duk ƙasusuwa da nake fama dashi...niɗin dai mummuna ce ta ƙarshe ma...

sakin rigar nayi ina tunani..akwai abinda nake ba daidai bane? Ko banda yaƙini ne kamar yanda ake cewa mutum yayi addu'a da yaƙini... ko akwai wani zunubin da nake aikatawa wanda yake hana addu'oi na karɓuwa? Wannan tambayoyin sun zama wani sashe na rayuwata..wanda har yanzu na kasa samun amsar su...

Cike da baƙin ciki na baro gaban madubin nazo na zauna saman katifar mu..Anaam ta shigo tana magana da kanta ƙasa ƙasa ban ma san abinda take faɗa ba wurin kayanta ta nufa tana neman wani abu..bin bayanta nayi da kallo..tana da faffaɗan ƙugu mazaunan ta manya...juyowar data yi yabani damar ganin yanda ƙirjinta ya ƙara girma cikin yan kwanakin da sukayi a tare damu...da bahaka suke ba,ƙanana ne ko ganin su ba'ayi amma yanzu har sunyi wannan girman ban taɓa lura ba sai yanzu...ƙasa nayi da kaina zuciya tana barazanar tarwatse wa...murya na rawa nace

 ''...n..i..ta dabance?'' na rasa inda zan sa kaina gaba ɗaya duniyar tayi min faɗi ban san inda zan kama ba...


Magana ta fara yimin da ba'a tana dariya...a ƙufule nace

 '' abinda kike min dariyar akai..yanda nake bani nayi kaina ba kuma bani na zaɓi zama hakan ba ki dena bana so bani nayi kaina ba bani na zaɓi hakan ba''

murya ta tafito kamar raɗa hawayen da nake ta riƙewa suna rige rigen wanke fuskata kamar an ɗaura min wani abu a maƙoshi na kasa numfashi da kyau...jikinta ne yayi sanyi...nadama bayyane a fuskar ta bata ce komai ba ta fita ta barni ni kaɗai...

Washegari bayan mun gama kari inna sarai ta kawo wani abu da bansan Meye shiba ta kirani a tsakar gida Mama na zaune daga baranda tana kallo..shafa min shi ta fara yi tana faɗin zai tafiyar da pimples ɗin sosai naji daɗi amma daɗin da sauri ya gushe...idan fa baiyi aiki ba? 

Su Asma'u daga gefe suna kallo wurin awa ɗaya abin yayi a fuskata koda aka wanke na duba madubi babu abinda ya ragu...kuma nasa rai koda za'a wanke inga fuska ta ta dawo lafiya lau ashe dai ni wawuya ce dana yi tunanin hakan.... Aloe vera ta ƙara shafamin bayan minti shabiyar ta wanke..ina jin Asma'u na faɗin wannan abin ba aiki zai yi ba...ban bi takansu ba...

Bayan lokaci itama aloe vera'r aka wanke ban damu kaina da duba madubi ba dan dai Nasan labarin gizo baya wuce ƙoƙi...


Ranar haka ta wuce zuciya ta ɗauke da nauyin daya kasa sauka...na ƙuntata nake ji kamar duk nauyin duniyar ne a kafaɗu na babu abinda ke min daɗi...abun ya ƙara tsanani da washe gari aka tashi rana bata fito ba ko ina yayi shiru yaran dake taruwa a gaban gida yau ma basu fito ba,da kosu mutum ya gani ƙila yaji sanyi a ranshi Da ƙarfe goma na fita sayen pad duk a takure nake hannu na gaban hijabi,iska na kaɗawa a hankali faɗuwa gaba na yayi dana ga hanyar da zanbi in wuce akwai dandazon maza da yawa na taka burki ina ji kamar in koma amma ina matuƙar buƙatar pad ɗin...dogon numfashi naja zuciya tana dukan tara tara na cigaba da tafiya 

'' a'a kaga wata yar silandiyon nan tafe...'' wani daga cikin mazan ya nuna ni

'' doguwa yar shafal shafal...inama zata saki hijabin sai mu auna....'' wani ya faɗa yana tsareni da shegun idonshi da suke ja


Nidai cikin raina sai addu'a nake jikina duk yayi sanyi tsoro ya shige ni ta shi wani daga cikinsu yayi ina kawo wa daidai wurin su ya jera dani muna tafiya Innalillahi ji nayi kamar in zura da gudu..abokanshi sai shaƙiyanci suke mana...hankalina yayi mummunan tashi

'' yan mata ya yau...'' Muryar shi kamar irin na riƙaƙƙun yan shaye shaye,ban amsa ba nayi sauri nayi gaba yana biye dani a baya iska yake kwashe min hijabi naji kamar inyi kuka ban ƙara shiga yanayi ba sai dana isa shagon naga nan ma akwai maza da yawa zaune a wurin...taya zance a bani pad yanzu?

Allah yasa akwai mutane da yawa kafin ni...sai binmu suke da kallo...

'' kaga wata mai idon mage...'' wani ya taɓa abokinshi yana nuna mashi ni.. ƙin kallon sashen su nayi babban burina a wannan lokacin shine inga na isa gida

 '' yan mata mai za'a baki?" Mai shagon ya tambaya da murmushi a fuskar shi...numfashina na riƙe ina tunanin abinda zan faɗa mashi batareda wa'yannan sunji ba biro idona ya hango min sai na ɗauka na rubuta saman kuɗin ' Pad'na miƙa mashi...karantawa yayi a ranshi cike da fahimta ya juya ya ɗauko yasa cikin baƙar leda...

'' na gode...'' na faɗa da sassauci a raina.

.'' yauwa...'' na ƙara gyara hijabina sannan na juya Zan fita

 '' kalla kalla idonta wallahi kamar na mage...'' wani daban yayi maganar da hanzari nabar wurin

Wannan gayen da ya biyo ni yana nan tsaye muna haɗa ido ya sakar min wani murmushin dayasa naji cikina ya bada ƙuuu..gaba ɗaya zubin shi bai yi kama dana mutanen arziƙi ba...

Wuce shi nayi ina tafiya da sauri...yana biye dani babu abinda nake faɗa sai Lailaha illa anta subhanak inni kuntu minazzalimeen

'' yan mata ji mana..'' ya sha gabana saura kaɗan jikin mu ya haɗu.. nayi saurin ja baya

 '' Innalillahi wa inna ilaihi raji'una...'' na furta hawaye na ƙwace min wasu biyu daga cikin ƙawayen nashi suka zagaye ni suna maganganu ba daɗin saurare

 '' ni yanzu wa zai taimake ni?" Nayi ma kaina tambayar cikin raina..ina kallon su da idona da sukayi ja ash ɗin ya ƙara duhu

'' ku kalli ƙwayar idonta kamar ruwan toka...''

'' eh lallai ba shakka hakane...''

'' daɗin ta na daban ne da alamu...'' suka kwashe da dariya ni kuwa babu abinda jiki na keyi banda rawa...na zama kamar tunkiya a tsakiyar kuraye..ban ƙara ruɗewa ba sai da naji ana jan hijabina daga baya...

Na fashe da kuka '' wallahi ƙwayar idonta da shape ɗinsu ƙara tsumani suke.. ''


Na shiga tashin hankali na tsorata sosai..fara matsoni suka yi dukan su babu mai kyau'n gani sai jajayen idanu...

wani daga cikin su ya riƙe hannu na dana damƙe hijabina dashi..ihu na kurma gaba ɗaya na fice hayyacina na shiga wani irin yanayi da nima ban fahimta ba sakina yayi suka dafe kunnuwansu kafin kuma suka fara tserewa sakamakon ihun da nayi ya jawo hankalin wani mutum dake wucewa ...da sassarfa ya ƙaraso inda nake nikam na rufe idona sai ihu nake...

'' baiwar Allah...'' mutumin ya kira da ƙarfi fuskarshi da damuwa..buɗe idona da suke rufe nayi...suka sauka akan fuskar shi...ido guda manne da plaster ɗayan kuma lafiya lau..''.kina lafiya?" Ya tambaye ni

Girgiza mashi kaina nayi...duƙawa yayi ya ɗaukar min ledar pad ɗina data faɗi

 '' mu tafi in raka ki...'' ban Musa ba nayi gaba yana biye dani duk a ruɗe nake... babu abinda nake banda hawaye ina tafiya da sassarfa kamar zan kife..yana faɗin inbi a hankali...

Jikin Mama na faɗa na rushe da kuka tana tambaya ta mai ya faru...inna sarai kuma ta fita zuwa ƙofar gida saboda sallamar da mutumin keyi...na tafi na barshi da pad...

Anaam ma tazo ta zauna daga gefe haka ma Asma'u...hankalin Mama ya tashi.. sassauta kukan nayi na faɗa mata abinda ya faru...ta rungume ni tana shafa baya na...'' Allah yasa bawan Allah'n nan da Asma'u ta jiwa ciwo yana kusa shine ya ceceta..gashi har yanzu bamusan sunan Shiba...''.inna sarai ta faɗa da alhini...

Anaam da Asma'u suke taywy Mama lallashina a haka har bacci ya ɗauke ni.... gaba ɗaya babu wanda yaji daɗin abinda ya faru...

Ranar Monday da wuri muka isa makaranta har ma muka samu assembly kuma Diyaam da Jay D suma har sun iso...hakan yayi min daɗi '' uniform ɗin sunyi maki kyau..'' Murmushi Anaam tayi da jin Diyaam ta yabe ta '' na gode...'' 

'' Attention..'' Assembly pirifet ta ɗaga murya..hakan yasa yan SS 1 da 2 sun yi ƙasa da surutun da suke..kowa ya shiga layi..nice a baya gaba ɗaya dan wurin gyaran layi mun rabu sannan dama nafi son kasacewa a ƙarshe bana son kowa yana goga min jikin shi a baya bayan anyi addu'oi, national anthem da national pledge principal ta hawo saman dakalin ta fara magana akan jarabawar dake ƙaratowa... Tayi mana nasiha da kuma ƙarfafa mana guiwa da muyi karatu sosai

Bayan tagama ezzam master (exam master) shima ya hawo bayan ya gama cika mu da surutu yake faɗin kuɗin waec da neco dubu saba'in da biyar...'' hmmm!!" Wurin ya ɗauka da surutu wasu kamar zasu dake shi jin uwayen kuɗin daya ambato ya ƙara da faɗin wani sati za'a fara mock exam ɗin...naji gabana ya faɗi...idan fa banci jarabawar ba? Idan fa na faɗi? 

Ƙasa nayi da idona na ɗaura hannu na a gaban goshi na saboda ranar data fito...gashi ko kuɗin wannan term ɗin bamu biya ba...kuma mu uku ne..kenan kusan dubu ɗari biyu da wani abu zamu biya...BALA'I!! Ji nayi zufa tana wanke ni daga ko wacce kusurwa ta jikina..jini ya janye daga fuska ta...

Sai da suka gama yi mana gargaɗi akan mu da ake bi bashi muyi sauri mu biya idan ba haka ba,bamu ba rubuta jarabawa.. sannan aka sallame mu...

Koda muka shiga aji sai alhini suke wasu suna faɗin baza su rubuta jarabawar ba dasu biya dubu saba'in da biyar Gara sun kama sana'a...ni kuwa nawa tunanin shine dole in ƙara ƙoƙari wurin neman aiki zama nayi ina cigaba da tunani naji wasu daga gefe na suna faɗin '' wai fa ba'a haɗa da kuɗin lesson ba...in an haɗa dasu dubu tamanin da biyu ne...'' da ƙarfi na juyo

Wacce ke shan ruwa kusa da wacce tayi maganar ta fesar da ruwan ta window ido zare '' dubu tamanin da biyu? Kam bala'i da yake dai Allah yasa ba lesson ɗin nake ba...'' wacce ta fara magana da farko ta sheƙe da dariya '' dey play..yarinya ko kinyi lesson ɗin ko bakiyi ba dole sai kin biya...''


Ajin ya kacame da surutu kowa yana ƙorafin kuɗin sunyi yawa...ina zan sama mana kusan dubu ɗari biyu da arba'in da wani abu? ɗauke kaina nayi na koma kallon window..ina hango bishiyoyin da ganyayyakin su suke Kore shar...hasken rana na ƙarama kalar su haske,ga yara can ƙila yan SS 1 da 2 suna kai kawo wasu na shiga aji wasu na fita babu ruwansu da abinda ya shafe mu..mu yan SS 3...haka zalika babu wanda yasan abinda ke raina babu wanda yasan matsalolin dake damuna... Bana tunanin akwai abinda za'a faɗa idan dai ba kuɗin za'a kawo ba da zai canja min yanda nake ji a raina...oh Allah ni Abeedahtu tako wace fuska ina da matsala...


'' Bee...'' Jay d ta jijjigani tana yaƙune fuska ta kasa fahimtar me nake tunani da har banji taba...'' me kike tunani haka?" Matsa mata nayi ta shiga ta zauna ƙamshin turaren ta yaɗan sa naji yar ƙaramar nutsuwa.. Diyaam ma ta zauna a nata gefen sai lokacin naga ashe Itama tasa uniform sosai tayi kyau farar fatar ta ko mutum bai taɓa ba zai san tana da laushi 

'' lesson ɗin da akace wai ko mutum bai yiba zai biya sannan ni ban san cewa ana biya ba wallahi..'' na faɗi rabin gaskiyar abinda nake tunani...juya idonta Jay d tayi '' dama suna abu kyautane?" Na girgiza kaina...na juyo gefen Diyaam 

'' Ma sha Allah Sofia Diyaam tayi kyau'' tayi murmushi batace komai ba... Daga nan malamin literature ya shigo ajin.. mayarda hankali mukayi akan abinda yake koyarwa musamman ni..a da bantaɓa jin ina buƙatar in mayarda hankali ba domin in fahimci karatu ba saboda na riga da na yarda cewa bazan gane ba..amma yau daban ne,ina so in fahimci abinda ake koyar damu...kuma ƙwaƙwalwa ta taƙi bani haɗin kai..amma na tilasta kaina..bayan ya tafi nasa Jay d da Diyaam suka ƙara yimin bayani...


''.you know what? Idan an tashi ki biyo ni gida mu dinga study session akan English da math.. kin ji?" Jay d tayi maganar tana kallo na...'' idan na biki,wazai nema min aiki?" Dogon numfashi taja.. Diyaam tabi mu da ido...'' zamu iya duk lokaci guda...ina nufin,idan mun fara mock,wasu ranaku zamu tafi gida da wuri sannan jarabawar Bama dole bace.. idan mun gama study session sai ki tafi neman aikin...'' gyaɗa kaina nayi da gamsuwa da abinda ta faɗa....

'' zamu iya farawa yau?idan an tashi tara'' 

'' idan kina so...'' murmushin jin daɗi nayi...daga nan muka cigaba da hira.. Diyaam ta bamu wani cakulet da muka tambaya ina ta samu saboda daɗin cakulet ɗin 


'' hamma na ya kawo Mani daya tafi ƙasar su...'' kallon ta mukayi dan bamu fahimci abinda take nufi da 'ƙasar su'' ba amma bamu yawaita tambaya ba Anaam itama ta shigo cikin hirar...bayan an tashi tara bamu fita ba,maka Jay d ta ɗauka tayi rubutu a gaban allo..sannan ta juyo ga sauran dake cikin ajin tace 

'' ina bada study session kyauta ga duk mai so zai iya shigowa... subjects ɗin da nake koyarwa math da English da literature..'' rabi da kwatan yan aji duk sukace suna so yan kaɗan kawai ne suka tafi wasa...Jay d ta tsaya gaban allo tana mana bayani da ƙwarewa da kuma haƙuri...yanda take bayanin ko wani malamin albarka.... Kuma ina fahimta dama tun farko matsalata ba rashin fahimta bane sai na fahimta na gane sosai amma kuma nan da ƙanƙanin lokaci sai in daburce idan an tambaye ni...


Bayan an tashi makaranta mu yan SS 3 muka tsaya domin lesson ɗin....sai ƙarfe huɗu muka gama.. sallah muka fara yi sannan kowa ya kama gabanshi...yan ajin mu sai godiya suke ma Jay d..nida kaina naji ina alfahari da ita...

Wurin famfo muka tsaya mu biyar ɗin,muna wanke ƙafafun mu da suka ɓaci da ƙasa..nake kallon ranar data zama ja ta fara tafiya gida sai kuma makarantar mu data zama empty ba mutane da yawa duk sun fita...ajujuwan mu da wasu tagogi suke buɗe...ƙaraurawar dake maƙale da bishiya bata da mai bugata...da yan tsiraran mutane da suka rage...wasu suna wasa a hanyar su ta fita..wasu suna da yawa..wasu su kaɗai suke tafiya..ba kowa tare dasu...


Wasu da murna da farin ciki a fuskokinsu wasu kuma... fuskokinsu ba walwala naji abu ya tsaya min a ƙasan ciki..kamar kada mu tafi...kamar mu koma aji...bana so in rabu dasu..na gode Allah daya sa bani kaɗai ce zanbi hanya ba da irin fanƙon (emptiness) da zanji sai ya ninka wanda nake ji a yanzu...

'' mu tafi...'' Diyaam data gama wanke fuskarta ta faɗa...a tare muka jero muna tafiya suna hira nidai nayi shiru ina sauraren su... A bakin gate muka samu motocin su Jay d da Diyaam sun iso kafin muyi wata tafiya mai nisa... dolen mu muka yi musu bankwana suka shige motocin su,mu kuma muka cigaba da tafiya a ƙasa... Na juyo ina kallon wa'yanda ke bin hanyar nan da mutane da yawa ke bi...rana ta haska bayan su,mu kuma muna fuskantar ranar...ina cikin yanayi...ban san abinda kemin daɗi ba...har ji nake kamar in jawo gobe... Jay d..da Diyaam..su nake kewa duk da bamu daɗe da rabuwa ba...sai kuma damuwar data maƙale min a zuciya kamar baƙar tsutsa... (leech)

Da muka koma gida babu wanda yayi maganar kuɗin makaranta...kawai muka yi wanka muka ci abinci..na fito bakin ƙofar gidan mu domin wasa da sauran dake wurin..abubuwa suna tafiya dai dai da farko su Asma'u ma suka fito suma..bada daɗewa ba mutane suka soma taruwa...

Ina tsaka da lilo naji wata mai suna A'e tana faɗin '' fuskar ki Abeedah kamar anyi ƙunar baƙin wake...duk ta gwalje ta lalace...'' wa'yanda ke kewaye damu suka fashe da dariya...lilon dake shilla wa da ƙarfi... Ya rage tashi kamar farko...naji kamar an soki zuciyata da mashin da aka ɗosana cikin wuta.... 

'' wallahi kuwa da gaskiyar ki..da nice da irin fuskarta,da bana tunanin zan iya fitowa cikin mutane...'' inji Sumayya...sauka nayi daga lilon... Wata yarinya ta hawo..na ƙaraso inda suke 

'' cin fuska har a gabana baxaku iya bari in bar wurin ba?" Nayi maganar da ɗacin rai...da farko zaune suke sai suka miƙe '' wasa muke fa..ke baki iya ɗaukar wasa bane?" Haleema ɗaya daga cikinsu take min kallon rainin wayo...

Haɗiye abinda ya tsaya min a wuya nayi...na kalli A'e '' Fuskata bata gwalje ta lalace ba A'e,ƙila rashin idon ne yasa kike ganin haka...ina nufin,mutum mai ido biyu yafi mai ido ɗaya...ki kalli kanki a madubi A'e...ƙila shima ɗayan idon naki ya fara samun matsala...'' sakin baki A'e tayi tana kallona suma sauran sukayi shiru Anaam ta matso kusa tana hararar su, wurin yayi tsit da wani iska mai nauyi na juyo na kalli Sumayya

 '' da yake ni bana kunyar fitowa da yanda fuskata take..ba sai nayi kwalliya mai yawa ba don ɓoye Fuskata da yake Allah ya rabani da yawo da fuskar da gefe guda fari gefe guda baƙi kamar anyi gobara tsabar bleaching...'' Sumayya ta zaro ido...da alamu mamaki take ya akayi na sani...

'' haba Abeedah akan me zaki dinga zaginsu har haka ke baki san wasa ba..?" Aliya da batayi magana ba tuni ta furta..ganin yanda suka yi shiru kamar ruwa ya cinye su... dariyar da bata kai zuci ba nayi..ina danne baƙin ciki na...'' wasa?"

 na ɗago idona ina kallon su duka

 '' lokacin da suke wasar sun yi tunanin yanda zanji? Sunyi tunanin wani irin yanayi hakan zai jefa Ni? Sunyi tunanin wane irin tasiri hakan zai haifar a zuciya ta da rayuwa ta?..."

Na dakata ina share hawayen da suka sauko min dukan su jikinsu yayi sanyi na cigaba da faɗin 

'' mafiyawancin mutane suna faɗin abinda yazo kansu ne batareda tunanin yanda wanda aka faɗawa maganar zaiji ba...a wurin su wasa ne..abin ayi dariya...amma wanda aka faɗa mawa? Baya mantawa! Wasu har su mutu wannan maganar tana kasancewa dasu ta rayu dasu....wasu maganar tana gina su wasu kuma ta rusa su... Akan mai zasuyi wasa da abinda bani na ɗaurawa kaina ba? Ita A'e da take da ido ɗaya,ita ta halicce kanta a haka? Meyasa bazatayi tunanin yanda zata jiba idan wani ya faɗi magana akan yanayin halittar ta? Bana son irin wannan wasannin!" 

Na ƙarashe maganar da gargaɗi ban jira cewar kowa ba na wuce ciki...kallo ya koma akan su A'e..da yawan su sun gamsu da abinda na faɗa...ai babu wanda zaice ba'a taɓa faɗa mashi wata maganar data tsaya mashi a rai ba ko?

'' ku iya bakin ku idan ba haka ba wata rana zai saku a matsala...'' cewar Asma'u kafin ta wuce ciki...da nadama a muryarta A'e tace '' dan Allah Anaam ki bawa Abeedah haƙuri...'' suma sauran abinda suka faɗawa Anaam kenan....