BOOK ONE CHAPTER ONE
*CHAPTER ONE*
*ZAINAB*
Falon ya yi shiru.
Shirun da ke cike da ƙamshin turare na biki, da ƙamshin bakin ciki da ba a faɗi ba.
Zaune take a tsakiyar kujera. Kujerar da take zama akai shekaru goma sha biyar tana kiran wannan gida “gida na”.
Yau, kujerar ta yi mata nauyi. Kamar ba ta san shi ba.
Kofin shayin hannunta ya yi sanyi.
Zuciyarta na huro wani irin zafi mai ƙuna.
Yau ce ranar farko da amaryar mijinta za ta shigo gidan.
Tun da yagaya mata bikin take jin wannan zafin aƙirjinta har yau da ta uni tana murmushin yaƙe ga danginsa da maƙotan da suka taru.
Tai kwalliya badon tanada muradin tai kyauba, taita murmushi na ƙarya domin taɓoye sirrin ranta kamar yanda aminiyarta Zaliha tabata shawara.
Kuma tayi iya ƙoƙarin ta wajen yin hakan duk da ƙawar tata batanan tayi tafiya zuwa garin su tun ana biki saura kwanaki bakwai.
Unin yauma gaba ɗaya basui maganaba saboda taron jama'a.
Miƙewa tayi da kasdin ɗauko wayar ta adaki takirata,
Ƙofar falo ta yi ƙara.
Dayike dama haka kofar take indai an taɓata seta bada sauti.
"Assalamu alaikum"
Muryar mijinta tai sallama cikin tattau sar muryanshi datake matuƙar so.
Ahmed ya shigo a gaba. Hannunsa a bayan sa. Fuskan sa ɗau keda wani irin yanayi data kasa fahimta.
A bayansa, amarya na shigowa a hankali. Kan ta a ƙasa. Jikinta a lulluɓe da doguwar mayafi fari.
Tajuyo gare su sosai, wani mul mule-len abu mai ɗaci yatokare mata maƙoshi, daƙyar ta iya haɗiyeshi ta buɗe bakinta da niyyar cewa
"Maraba da zuwa ƙanwata...."
Amma bakinta ya maƙale, muryarta na ɓoyewa awani wuri da batasan da zamanshi ajikin taba.
Idanuwanta kafe akan matan dake tsaye a gefen mijinta.
Zaliha....
Ƙwaƙwalwarta ta wassafo sunan zuciyarta na dokawa.
Idan har ba makanta tafaraba tabbass wannan Zaliha ce a tsaye.
Kawarta ta.
Aminiyarta.
Matar da ta bama sirrin gidan ta, da raunin zuciyarta, da farin cikinta da baƙin cikinta, na shekaru goma sha biyar.
Duniya ta tsaya.
Kofin shayin da ke hannuta ya zame.
Ƙara ya bazu a falon kamar wani abu mai rai da ke mutuwa.
“Ke ce?”
Muryarta ba ta fito daga bakin ta ba. Ta fito daga wani wuri mai zurfi a cikin ta. Wuri da ta ƙi yarda yana nan.
Zaliha ba ta ɗaga kai ba.
Amma murmushin da ke gefen bakinta ya isa ya gaya mata komai.
Murmushin mace da ta ci nasara. Murmushin mace da ta sayar da amana ta saya gadon abokiyarta.
Ahmed ya matso kusa da ita.
“Zainab,” yakira da ƙaramar muryansa da tai sanyi amma mai kauri kamar duwatsu biyu da aka ɗaura a makogwaro.
“Kiya haƙuri. Kada kitina komai da yafaru abaya, zaifi mu soma daganan.... inanufin mafari....domin makomar gidan mu”
Makomar gidan!!!
Maganar ta buge ta kamar guduma.
Domin a wannan lokaci ne ta fahimta:
Ba Zaliha kaɗai ba ce ta ci amanarta.
Mijin ta ma ya ci amanar ta.
Mutumin da ta bashi linzamin rayuwar ta, da yardan zuciyarta, da shekaru na mafi kyau… amma ayau ya zabi kawarta akanta.
Ta kalli Zaliha.
Ta tuna yadda ta riƙe hannun ta ranar da ta gaya mata tana tsoron mijinta zai ƙara aure.
Kalaman ta a wan can lokacin na dawo mata : “Zainab ki kwantar da hankalin ki mijinki yana son ki na tabbata babu wata mace da zata sauya zuciyarshi daga wannan ƙaunan....ba fata na keba amma idan wani abu yafaru a tsakanin ku to ni zan tsaya miki.”
Ƙwallan da suka ciko idanun tane suka sanya zuciyarta dakatawa anan.
Da nauyi mai girma taɗago idanunta tasauke su akan Zaliha dake tsaye amma ba a gaban taba a gefen mijinta.
Ta kalli Ahmed. Ta tuna yadda yayi rantsuwa ranar da ta haifi ƴarta na fari.
“Daga yau duk abin da zan yi arayuwa, zan yi ne domin ke da ƴaƴanki.”
Yau, duk abin da ya yi, ya yi ne domin ya kashe ta da ranta.
Saboda ayan zunnan da take tsaye ƙirjin ta zafi yake mata. Zafi mai kaifi kamar wuka.
So take yi ta yi ihu.ihun da sautin shi zai fasa gidan gabaɗaya yanda kuwwa ze fahimci abinda takeji.
Ƙafafunta da sukai sanyi ƙalau taja tazauna jirinda ke ɗibarta na niman kifadda ita atsakiyar falon.
Ta kalli Zaliha. Ta kalli mijin ta. Ta girgiza kanta daye mata nauyi kamar an dora mata nauyin duniya da abinda ke cikinta gabaɗaya.
Akan idanunta Ahmed yabude bakinshi yasoma maganarda sautinshi baya kaiwa cikin kunnuwanta balle tajishi.
Bayan yagama itama Zaliha tasoma nata.
Da tagama suka miƙe hannuwansu cikin najuna suka bar mata ɗakinta.
Batasan tsawon lokacin data ɗauka a zaune ba tukun ta mike ahankali.
Ta soma tafiya kafafun ta na rawa. Amma zuciyarta ta ƙi faduwa.
Ta ce wa kan taa: “Zainab, ki tafi ɗakinki. Gobe za ki tashi. Gobe za ki yi yaƙi.”
Tana isa ɗakin ta.
Ta rufe ƙofa.
Ta zauna a gefen gado.
Numfashi take fizgowa daƙyar, zuciyarta ciwo take mata, kuka takeso tayi , kuka da zai fitar da duk abin da ke matse mata rai.
Amma zuciyar ta ta ƙi bata haɗin kai.
Kamar ta ce: “Ba yanzu ba. Idan ki kayi kuka yanzu, za su ce sun karya ki. Ki rike hawayenki bayan zuba.....”
Don haka ta kwanta.
Idanuwanta a rufe.
Amma bacci bai zo ba.
Dare ya yi tsayi. Kowane minti kamar shekara. Da duk numfashin da zata shaƙa da yanda ciwon abinda yafaru ke ƙara zama a zuciyarta.
*ALIYA*
Kuka ne kawai ya rage mata a wannan dare.Ba kukan da ta saba yi domin a ji ta ba.
Kukan da mutum yake yi ne idan zuciyarsa ta cika da abubuwan da harshensa ya kasa furtawa.
Zaune take a tsakiyar gadon da aka ajiye ta, sautin ajiyar zuciya tareda numfashinta na maƙalewa a sararin ɗakin.
Mayafin kanta tazare zuciyarta karye na huro wani irin zafi dayake ratsawa ko wani kafa na jikinta.
Cikeda rashin ƙwarin jiki tazame ta kwanta, kanta daye mata nauyi kamar an mata gammo da duniya da abinda ke cikinta gabaɗaya na sauka asaman tattausan pillown da inga acikin hayyacinta take da ba abinda zehanata yin santinshi tareda son sanin dame aka yi shi.
Ƙamshin turaren da aka shafa mata yana yawo a ɗakin, amma ita ko kaɗan ba ta jin daɗinsa.
Saboda tunaninta yana wani wuri dabam.
A wajen mutumin da yanzu aka ce mijinta ne.
Ta ɗago kai a hankali ta kalli ƙofar ɗakin.
Har yanzu tana jin muryoyin mata a waje. Wasu suna dariya, wasu suna taya ta murna, wasu kuma suna ta bata shawarwari tare da sharhi akan wannan auren.
“Ki kasance mai biyayya.”
“Ki girmama mijinki.”
“Ki yi haƙuri.”
“Ki daina yawan magana.”
“Ki tuna kin bar gidan ubanki.”
Kalmomi ne da aka jefa mata tun safe har dare.
Amma babu wanda ya tambaye ta kalma ɗaya:
“Tayaya zaki rayu da Malamin ki, Yayan ki kuma mijin yarki abaya?”
Ta runtse idanu.Hawayenta suka zubo.
Ba wai tana ƙin auren ba ne. Abin da ya fi tsoratar da ita shi ne matsayin wanda ta aura awurin ta.
Ba bu soyayyar aure a zuciyarta kamar yadda ta kwana da sanin babu soyayyar ta tafannin aure a zuciyarsa.
An shirya komai ne saboda wanke ciwon zuciya wanda son zuciya ya haifar.
Da dukkan zuciyarta ta amshi aurennan saboda farin cikin mahaifin ta.
Amma a cikin zuciyarta akwai wata ƙaramar murya da ta ci gaba da cewa:
“Idan har yanzu Ustaz mijinki ne, shin dole ne ku kasance baƙi har ƙarshen rayuwarku?”
Ta goge hawaye.
A'a.
Ba ta son hakan.
Ba ta son ta rayu a gidan da ita da mijinta suke kallon juna kamar baƙi.
Ba ta son kowace matsala ta koma wurin mahaifinta.
Wani abu mai kamada baccine taji yakawo mata ziyara, tajuya kafaɗar ta da kyau tana ƙara sakin ajiyar zuciya akaro na ba adadi.
Bayan kwanaki talatin ciph da hijirar bacci agareta ayanzu yazo gare ta da ƙarfinshi.
Ruma batai gardamaba ta amsheshi da hannu bibbiyu hakan yasa komai nitsewa acikin kanta, shiru da duhu suka mamaye komai amma banda makomar auren ta.
❇️USTAZ RAYYAN ❇️
Ledan hannunshi dake ɗaukeda abubuwan da inza'a yankashi bai san ko meye acikiba yasaka a fridge.
Roƙonda Zaid ya dinga mai akan yasaki ransa na cika mai kai, wai yau shi Rayyan shine da mata.
Wata mace daban ba Jamila ba, inda ƙaddara da rayuwa basu garashi sun matseshi har numfashinshi ya gaza fita daga huhunshiba dase yace ƙarya ne.
Amma ayanzu komai na duniya ya daina bashi mamaki ko tsoro, a shekaru biyu kacal ya ɗauki darussan da ba'a koya maiba a makarantun da yayi tun daga matakin nursery har degree ba.
Ƙaddara ce______anya kuwa beyi son zuciya ba idan yakira abinda yasameshi da ƙaddara ba.
Kamar yanda kuwwa zefaɗi shima yasan son zuciya ne data maƙale a inuwar zaɓi.
Ita kuma Aliya bai san yadda zai rayu da itaba matsayin matarsa, yaɗan ɗaga lumsassun idanunshi dake bayyanar da gajiya da sarewa akan ƙofar ɗakinta.
"Ya kamata inshiga....?"
Wata karamar murya tafaɗi acikin kansa.
Da ze iya daba abinda ze hanashi takawa yaje____sedai bayada zuciyar da ze'iya haɗa ido da Aliya a matsayin matarshi.
Tun farko ma shiyasa yace da su Abba baya buƙatar aure ayanzu..
Gaza fahimtar shi da sukayi shine matsala, shidai yasani ɓangaren zuciyarshi dake ɗaukeda soyayya ta mutu tun aranar da Jamila tasaki hannunshi takama na waninshi daban.
JAMILA.....
Ƙwa-ƙwalwarshi ta wassafo sunan, zuciyarshi na dokawa kuma kamar wannan damar zuciyar tashi take jira taɗibeshi ta watsa shi wasu shekaru can baya.