MIJIN AMAL

Chapter 4

by @reza12

*MIJIN AMAL

Chapter 4
Ta ce "A'a wallahi babu ruwansa ma Mama, shi yama kwanta tuntuni yayi barci abunsa, kiyi hakuri kizo ɗin". Ta faɗa a ƙoƙarin ta na kare shi. "To mai nene ma a cikin gidan naku idan ba fatara da talauci ba. Wannan yaron da gani ko kuɗin ma yayi wallahi ba zaiyi imani da taimako ba". Daga haka dai suka gama wayar, ta dafe kai tana kiran sunan Allah a fili. Ta leƙo ta hango shi ya sake kunna Laptop ɗin yana kallo. A hankali ta ce "Allah ya bar min kai mijina, Ubangiji ya cigaba da ƙara maka sona da tausayi na, ya kuma rufa mana asiri mufi ƙarfin bukatunmu". Ta na karasawa gurin ya ce "Na fara jin barci ke nake ta jira". Ta zagaya ta bayan kujerar, ta cusa kanta a wuyan sa, ta zagayo da hannunta tana kallon Film ɗin da yake Daulodin da sai yanzu ma yayi rabi ta Telegram. Ta ce "Tom ai gani kusa da kai kayi duk yadda kaga dama". "Tom bari Film ɗin ya ƙarasa muje mu kwanta gobe sai mu kalla". "Tom ranka shi dade duk yanda kace haka za'ayi". Yayi murmushi yana ci gaba da yin wani abu ita kuma idonta na kan laptop din. Ta saka hannunta a cikin rigarsa tana wasa da ƙirjinsa. Ta ce "Film ɗin waye haka ƙauna biyu?" Ta faɗa tana karanta sunan Film ɗin a fili. "Alu Arjun ne, ina ta neman Film ɗin fassarar algaita sai yanzu wani ya bani wannan number wai nai masa magana a Telegram shine fa ya Turo min. Ta ce "Tab ashe gobe muna da kallon babbar jarumin mu Sarkin soyayya". "Hahhh ke dai bari, badan ina jin barci ba ai da yanzu zamu fara, kuma kinsan dole aci dariya saboda Rangila na ciki". "Kai ashe madara da siga aka haɗa ga Alu Arjun ga Rangila master. Ya sauke ajiyar zuciya saboda abubuwan da take masa sun fara sauya masa yanayi. Kuma daidai lokacin Film ɗin ya gama sauƙa. Ya miƙe tsaye yasa ta a chaji ya kashe wutar palon ya kulle palon ya ɗauketa tana dariya suka shiga cikin ɗaki. Ya kwantar da ita yay mata rumfa yana mata magana da muryar da ta san gejinta. "Kin kuna ni, dan haka kiyi saurin ƙarasa aikin ki". Ta ce "Addu'ar kwanciya barci". "Ai ba barcin za'ayi ba, bari mu fara yin wasa". Ya faɗa yana cire jallabiyar jikinsa. Ta sakar masa murmushi tana kanne masa ido ɗaya. Ya murgina da ita ta dawo sama, ya fara cire mata riga tana bashi hadin kai. Ya jawo bargo ya rufe su gaba ɗaya. Bayan minti ashirin yana zaune a bakin gado ta fito daga toilet daure da tawul tana goge gashin kanta. Ya ce "Kefa nake jira barci nake ji". Jin haka yasa ta saki tawul ɗin ta dauko rigar barci ta saka. Ta ƙaraso kan gadon, suka fara karanta addu'ar kwanciya barci a fili. Suna gamawa ya kashe wutar ɗakin ya kwanta. Itama ta tashi ta saka hula a kanta, ta zo ta kwanta a jikinsa.

Misalin ƙarfe takwas bayan sun gama karyawa. Ya ce "Bari naje na buɗe masa shago na dawo yau ina gida". Ya faɗa yana gyara hular kansa. Ta ce "Ko nazo muje sai mu dawo tare?" Ta faɗa da sigar wasa. "Idan kika ga na fita dake anguwa to Tabbas mota ce dani, amma dai ba akan mashin kowa na kllon ki ba". Ta buɗe baki zatayi magana suka ji ana buga ƙofa. Take ta shiga damuwa domin tasan Mama ce, kuma bata so su haɗu da shi, tunda bai san ma zata basu kuɗin ba. Ya ce "Shiga ciki kisa hijjabi". Ya faɗa yana nufar Kofar ya buɗe. Ido biyu sukayi da Ali, wanda kafin ma yayi magana ya shigo cikin gidan. Ali yayi masa wani kallo yana kawar da kai. Ya samu guri ya zauna yana tambayar ina Madam. "Kaga tashi muje sai muyi magana a waje dan Allah?" Ya faɗa yana jin ransa na ɓaci. Ali ya ce "Bayan ka mayar dani mutumin banza ko?" "To da kai mutumin meye?" Ya katse shi da sauri. Suna haka Amal ta fito jin murya Ali. Bayan sun gaisa ta kawo masa ruwa. Ya ɗauka ya sha ya ce "Kece kika hana shi ɗaga min waya tun jiya ko? Shi yasa na zo da kaina naji dalilin hakan?" Ya faɗa yana murmushi. Amal ta ce "Ni kuma, a'a ba ruwana, yanzu ma fa yake cewa zai je gurin ka". "Wato dai zaki goyi bayansa". Tayi ɗan dariya. Yasir ya ce "Dan Allah muje muyi magana a hanya rana tana yi". Ali ya tashi ya kalleta ya ce "Tom sai anjima Madam".  Ta amsa. Yasir ya dawo da baya ya zo har kusa da ita ya mata kiss yana cewa sai ya dawo. Tai masa addu'a suka fita.

"Dan Allah ajiye mashin ɗin nan mu tafi a Mota, idan zaka dawo ka faɗa min na dawo da kai". "Kai kasan wanda zai hau motar ka ai, amma dai ba ni ba". Ali da ya cire makullim mashin ɗin ya ce "Gya dan Allah ka waye mana, mutanen nan fa sun ƙara kuɗin ya kai 6ml fa wallahi, kuma bro iya fa auran ne ba wani abun da zai faru. Kawai dai asan dai tayi wani auran ne". Yasir ya ce "Ali bani kina dan ubanka, Allah zan maka wulaƙanci, to kai ka karɓi kuɗin ka aureta mana ɗan iska kawai". "Da hakan zai faru ai da ban tsaya ina binka da arziki kana min wulaƙanci ba. Kai da wannan ra'ayin naka tsaf zaka cuci kanka wallahi, na faɗa maka cewar babu wanda zai sani naka. Kawai zakuyi hoton aure ne da kuma ziyartar gidan iyayenta da dai sauransu. Ana daurawa sati ɗaya sai saki kaci 6m ɗin ka, amma ka tsaya wasa. Wallahi ba wanda zai sani harda ita Madam ɗin da kake tsoro kamar wata uwarka". Ya ƙarasa yana sake dawowa Serious. Yasir ya kalli mashigar Palon sa, yayi shiru. Ya ce "Ali bani makulli na dan Allah?" "Ka yarda za'ayi?" Ya ce "Ban yarda ba, dan Allah kaje ka nemo wani, wai ana dole ne?" Ya ce "Ina sonka da arziki ne Yasir. Idan ka samu kuɗin nan, zaka iya sayan Mota ko ta 3m ce, sannan ka haɗa solar da kake ta waƙar kana so, har ma wasu abubuwan rayuwa da kake so, kuma zaka ƙara jari, dubi shagonka ba wasu kayan kirki a ciki, dan Allah kayi tunani. Kuma wannan auran ba wai zaka kwanta da ita bane, suma sunce babu haka a tsarinsu, kawai auran ne". Ya ƙarasa yana marairaicewa. Yasir ya sake yin shiru ya kafe ƙofar gidan sa da kallo. Ya buɗe baki zaiyi magana sai ga Mama ta shigo cikin gidan kamar ana turo ta. Ya sauƙo daga kan mashin ɗin yana gaidata har ƙasa. Ta amsa a gantale tana binsa da wani irin kallon kiyayya. Ta ce "Mota ka saya ne, koda  yake kamar ga mai ita anan fa ko?" Ta faɗa tana sake bin Ali da kallo. Ali ya gaidata ta washe baki tana amsawa. Ta ce "Ita dubu biyar ɗin da ka bayar dai ba abun da ake nema bane, ita ce da shegen iyayi tace dubu biyar, to wallahi bayin allan nan dubu ashirin ne kuɗin kwasar da suka yi, dama ina ta sauri na sameka ko goma a samu". Ta faɗa tana kallonsa. Yasir ya ce "Ban gane ba Mama wani gyaran masai?" Ta ce "Wanda Amal ta faɗa maka ka bata dubu biyar mana, idan banda abunka mai dubu biyar zatayi idan ma banda abu na babu". Yasir yayi shiru, Ali ya sa hannu ya ciro dubu goma ya ce "To gasu Mama, ayi amfani da su ba yawa". Ta sunkuya hannu bibbiyu tana godiya. Tana ta zubo magana har ta shige cikin gidan. Ali ya shiga mota ya kunna. Yasir ya bishi da kallo ya rasa abun cewa. Haka dole ya shiga motar suka nufi shagon Yasir ɗin maganar Mama na tai masa yawo a kai. Kafin su ƙarasa an kira Ali kusan sau biyar. Yana jin yadda yake ta waya da manyan mutane yana tabbatar musu da cewa za'a kawo musu a kan lokaci. Shi kam ya faɗa tunanin da bai san yana yi ba. Bayan ya buɗewa yaron shagon ya kalli shagon da Kyu, rabon da ya saro kaya ya dade, komai a ciki yake yi, shagon ya rame sosai. Yana ciki wasu ƴan mata suka shigo sayan hijjabi, sai dai babu kalan da suke so, kuma da yawa zasu saya. Ya ce "Ku bari zuwa jibi za'a kawo". Da yake dama costormars ɗin sa ne, take suka tura masa kuɗin guda dozin da alƙawarin jibin zasu zo su amsa. Har zai tafi wasu ma suka zo sayan atamfofi na anko. Suma suka nuna masa amma bashi da irinsu. Suma suka ce ranar asabar zasu zo su ɗauka, suka bada kuɗin rabi. Har lokacin dai Ali na cikin Mota yana jiransa. Bayan ya rubuta komai. Ya ƙarasa gurin Ali, sai dai yana shiga motar yaji ana gaida shi. Koda ya juyo wasu kyakkyawan yan mata guda biyu ya gani sun sha kwalliya. Ya amsa yana kallon Ali. Yayi murmushi ya ce "Anan zamu ajiye su Kinss Hotel". Bai sake cewa komai ba, har suka iso hotel ɗin ya na jin yadda Ali yake jaddada musu cewar suna fitowa su tabbatar sun tura masa kasonsa idan ba haka ba sun kashe gaba. Ya kira mutanen da ya kawowa yaran ya faɗa musu ga sunan shigowa. Yaja Mota yana kama hanya. Ya ce "Ali kaini gida kawai dan Allah?" Ali yace "Gida dai, ai kawai kwantar da hankali ina so ne na kaika gurin mutumin nan kuyi ido huɗu domin ka tabbatar". "Ya ce "Ali ba zan iya ba, wallahi ba zan yi ba, dan Allah ka kai ni gida ko kuma ka sauke ni anan". Ya faɗa da karfi. Ali ya sha kwanar gurin da zasu je ya na faɗin "Ai wallahi ko dan ka ci mutuncin wannan surukar taka dole ka dage kayi kuɗi, haba ace baka da mutunci ko ɗaya a idanun suruka alhalin kuma kasan dalili. Kaga nifa wallahi wannan abun da na gani yasa raina ya ƙara ɓaci, ko baka so sai anyi wannan auran. Samun 6ml a sati an faɗa maka wasa ne, ko muma sai idan kamar mun kamo babban kifi muke iya haɗa wannan kuɗin a wata". Ya faɗa yana fakawa a wani ƙaton gurin wanda Yasir ɗin bai ma taɓa zuwa gurin ba. Ya kan ɗan wuce dai lokaci zuwa lokaci. Ali ya ciro waya ya kira. Ya ce "Gani tare da shi Alhaji, zamu shigo". Ya masa da tom". Yana faɗa ya kashe wayar yana sawa a aljihu. "Dan Allah Yasir kar ka bada mu, ka natsu ka kwashi arziki ka bar shi, Please be a man dan Allah". Ya faɗa yana buɗe masa motar ya fito. Suka jera gaban Yasir sai faduwa yake, har lokacin bai jin zai iya aikata hakan,  idan ya tuno da Amal sai yaji kamar bai kyauta Mata ba, haka idan ya tuno da burinsa na bata gata da jin dad'i, sai yaji kamar ya yarda. Sannan gefe ɗaya kuma ga maganar babu abun da zai shiga tsakaninsu, kuma babu wanda zai sani a cikin danginsa. Har suka shiga ciki yana ta tunani. Ali dai na ta tafiya suka shiga linta tayi sama da su. Har lokacin baiyi magana ba. Wani ofis ya tura da sallama, wata mace ta amsa. Kafin ma su sake cewa komai ta ce "Kaine Ali ko?" Ya amsa da murmushi. "Oga ya ce ka shiga yana ciki". Ta faɗa tana nuna musu hanyar cikin ofis ɗin. Yana gaba yana binsa har ciki.

Wayar Hafiza ce ta hau ƙara hakan yasa ta tsaya da karatun tana kallon number da ake kiranta da shi. A yadda labarin nan ya ɗauko dad'i badan shine yake kira ba da bazata ɗaga ba. Tayi murmushi ta ɗaga da sallama. "Ina ta buƙa ƙofa ne naji shiru, shine na kira ki?". Ai da sauri ta tashi ta nufi ƙofar tana mamakin ya aka yi bata ji ba. Tana buɗewa kuwa sai gashi tsaye. Ya ce "Kin fara barcin yamma ne?" Ya faɗa da sakin fuska. Ta ce "A'a ina toilet ne ban jika ba". Ta ɗora da cewa yaya Hajiyan take?" "Tana lafiya alhamdu lillah!". Bayan ya zauna ta kawo masa ruwa. Ya amsa ya ajiye a gefe ya ce "Hafiza ji nake kamar wasa wallahi wai na samu aiki?" "Ba maganar wasa, haka Allah yake ikonsa". Daga haka suka cigaba da hira har lokacin salla tayi. Har lokacin hankalinta naga cigaban karatun littafin nan. Amma dai haka ta haƙura ta kula da mijinta wanda yanzu sai ta fara masa kallon Yasir. Ta fara tunanin to kenan shi Yasir ɗin ya yarda ne da har ya biyo shi zuwa gurin mutumin. Tambayoyi da furjik akanta har washegari. Da safe kuwa tayi amfani da abun da ta karanta a cikin littafin wanda Amal takewa Yasir ita kuma batayi wato wanka. Shi kansa Hafza yayi mamakin ganin yadda itace take ta shirya shi. Da zai fita ta ce "Duk wani abokin da zai baka shawara mara kyau Allah kar ya haɗa ka da shi. Kuma dan Allah Komai zakayi ka dinga tunawa dani a gida. Kuma bana so ka ɓoye min komai na daga cikin abun da ya faru daga fitar ka har dawowa". Hafiz ya ce "Ikon Allah, yau kuma?" Ta ce "Da gaske fa nake. Dan Allah kar ka kalli kowa". Daga haka ya fita yana dariya. Bata bar gurin ba sai da ta tabbatar ya tafi. Ta dawo ciki da sauri ta kwashe kayan da suka ɓata kaman dai yadda taga Amal nayi idan zatayi abu sai ta tabbatar da ta gama gyara komai na gidan ta. Ta dawo Palo ta zauna tana murmushi ita ɗaya. A fili tace ashe dai karatun novel akwai dad'i kuma ana ƙaruwa da wasu abubuwan. Ta buɗe daidai gurin da ta tsaya taci gaba da karatu.

Wani mutum fari tass zaune a cikin ƙaton ofis ɗin, shima ba wani babba bane, daga gani kam babu tambaya ya tada kai da masu gidan rana. Bayan ya basu iznin zama ya ce "Ali ai har na fara tunanin gara mu samu wani, domin maza da yawa sun fara kai mata hari, kuma iyayenta ma suna ta matsa mata, bana son ɓata lokaci". Ya kalli Yasir ya ce "Yasir ko? Kana da aure ne?" Ali ya ce "No bashi da mata, tukunna dai". Yasir ya ce "Eh ina da Mata". Mutumin ya kalli Ali ya kuma kalli Yasir. Sai ya kawar da wannan tambayar ya ce "Tom ka amince da komai ko na ƙara faɗa maka abun da muke so?" Ali yace "Ya alhaj tun da ka ganmu anan ai kasan ya amince, dama munzo ne saboda muji ranar da za'a ɗaura auren da kuma sauransu". Ya ce "To ma sha Allah, za'a ɗaura ranar juma'a mai zuwa. Kai Ali zaka nemo masa masu karɓa masa auran. Yanzu kuma bani wayarka na saka maka number ita matar, yau da daddare zaka je gurinta hira, gobe da yamma ma zaka je, anan ne zata nunawa iyayenta cewar kai take so. Zasuyi bincike a kanka amma ita ba zata bari ayi hakn ba. Zata nemi a daure ran juma'a, sai aje da mutanen da aka samo. Zakuyi hoton Aure za'a sa a socel media saboda asan ta yi wani auren dalili kuwa kowa yasan bata da aure yanzu. Za'ayi duk wannan ne saboda ita ɗin yar babban gida ce akwai idan al'umma a kanta". Basu bar ofishin ba sai da dubu ɗari-dari kash wai su saka mai a mota. Har ƙofar gida ya kawo shi bayan dogon jawabin da Ali ya ke ta masa. Ya haɗa masa gaba ɗaya ɗari biyun ya bashi. Ya dade a ƙofar gidan ya kasa shiga domin ji yake yana shiga Amal zata gane abun dake faruwa. Ya kalli number matar da aka ce ya kira an rubuta sunanta Hajiya Suhailat. 

Bangaren Amal kuwa, tun da suka fita ta haɗa kayan da suka ɓata ta kai kiching. Ta ɗauki ƴanfinta ta kunna waka, tana wanke-wanke tana bin waƙar. Waƙar a bar wa rai take yi tana bin baita ceke da shauƙi kamar ita da M Sharif ɗin suka rera ta. Kaine mai bayar da sahihen labarina, kuma kaine zaka zamu cikonnin tarihine, ba wani bayanka, dukka mazaje kai musu rata. A bar wa rai abun da yake so shi yafi daidai in za'a bani kai ɗai zan dauka a cikin yan gayu". Sai taji kamar ana buga mata ƙofa. Hakan yasa ta goge hannunta ta sa stop ta nufo gurin tana tambayar waye?. Tana budewa taga Mama tsaye tana ta kallon gurin da motar Ali ta fita yanzu. Bayan Mama ta shiga ta leƙa taga mashin ɗin sa a gurin, ta ɗan bi mashin ɗin da kallo a karon farko kenan da taga ya shiga motar Ali ɗin. Bayan sun gaisa ta ce "Waye wancen mai motar, a ina kuka samo shi?" "Abokin Yasir ne, sunansa Ali". Ta faɗa tana yin hanyar ɗaki domin ta dauko mata kuɗin. Har ta shiga ta fito Mama tana magana akan Ali wanda ita dai bata ma gane mai take cewa ba, sai da ta bata kuɗin tace "Irin waɗancan mazan sune surukan fita kunya, ta ciro kuɗin da ya bata ta ce "Kalla, ban haɗa komai da shi ba, ban bashi ƴa ya aura ba, daga gaisuwa ya bani dubu goma, to ina ga shi ne yake auranki, kai ni wallahi ina ma shi kika aura ba wannan mai ƙashin tsiyar ba". "Amal ta ce "Yanzu mama dan Allah shima sai da kika tambaye shi kenan, wai Mama dan Allah meye duk wannan abun, kina ganin da wani mijin ne zai juri duk wannan abun?" Ta faɗa wani irin ɗacin abun da take yi ɗin na dukanta. "To kar ya jura mana dan uwarsa, idan ya gaji dani ya sake ki ko yace na daina zuwa gidan naki, wallahi da nafi kowa murna, ga maza nan a gari masu arziki, wallahi ko yau ya sake ki a gobe sai kinga an fara miki layi". Amal ta tsayar da kukan ta ce "Saki fa Mama! Ke da bakinki keke min fatan saki?" "To meye a ciki, idan ya sake ki ba wani ne, meye shi a cikin kayan miya aikin banza, har wani Abu ne da matsiyaci ya sake ki". Amal ta ce "Wallahi Mama babu irin Yasir a cikin Maza, shin Mama ke baki duba irin farin cikin da nake ciki da kwanciyar hankali ne, haba mana Mama". Ai take Mama ta faɗi kalmar da sai da Amal tayi da ta sanin faɗin haka, take wata irin kunya da nadama suka kamata, ai kuwa tayi shiru har Mama ta gama ta fita bata sake cewa komai ba, domin lamarin Mama ya wuce minsharrin wasswassul kan nass. Mama ta ce "Ai dama Maza irin su matsyata Indai jaraba ce sun kware a bangaren, dole kice a cikin maza ba kamar shi saboda abun da suka fi iyawa kenan kwanciya da Mace". Ina ma ƙasa ta tsage Amal ta shige ciki, lamarin mama ya girmi tunaninta....📝


S-Reza