MIJIN AMAL

Chapter 6

by @reza12

Chapter 6
A hankali ta raɗa masa cewar ya saki jikinsa dan Allah kar ya bata matsala a gaban yan gidan su. Hakan yasa Yasir ya saki jiki harda murmushin dole, ya koma kamar wani robot sai yadda aka yi da shi. Ya ji wata yarinya tana faɗin "Anrty wallahi yanzu ne ma zakiyi auren so, kin samo kyakkyawa kuma ɗan daidai ba irin wancen mai zuciyar tsiyar ba". Wata ma ta ɗora da cewar "Ga kuma sunansa mai daɗi". Suhailait ta ce "To ya isa haka ku barshi ya huta". Ta faɗa cike da nuna farin ciki. Hannunsu cikin na juna har suka zauna a ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun falon da suke ta ɗaukar hankalin sa tun ɗazu. Wata babbar mata da yake tunanin ita ce uwar ta su ta ce "Maraba da zuwa Yasir". Ta faɗa cike da fara'a tana karasowa idanunta a kansa har ta zauna. Hakan yasa ya sauƙo ƙasa da sauri yana gaida da ta. Tayi saurin faɗin "No no pls me haka? Tashi ka zauna bana son wannan ƙauyancin, wannan ai halin yan ƙauye ne, gashi kai kuma ba kayi kama da su ba". Yasir ya tashi ya koma kan kujera yana jin yadda take ta ƙara mannewa a jikinsa. Duk tana kokarin ɗaga masa hankali. Uwar ta ce "Halisa kuje ku faɗawa yaran nan su fito da abincin bakon ya iso". Ta faɗa tana fito da wayar ta da ta fara neman akaji. Wacce aka kira da Halisa ta tashi da sauri. "Eh yana nan yanzu haka muna tare da shi, kuma baka ganshi ba, kyakkyawa da shi kuma saurayi". Sai tayi dariya tana sake faɗin "To Allah ya kawo ku lafiya, munyi kewarka". Har zata kashe wayar ɗaya daga cikin yaran tazo da gudu ta ce "Daddy Daddy I love you!" Ta faɗa tana amsar wayar da har Hajiya ta kashe. Daga haka aka fara fitowa da Yasir abinci kala-kala. Har lokacin bai ko samu damar magana ba. Haka suka haɗu gaba ɗaya harda yaran aka fara cin abinci. Ana ci ana hira akan tsohon mijin Sihalait ɗin da ya saketa ko wata uku basu yi da aure ba, hakan yasa kaba ɗaya yan gidan suka tsaneshi. Ta ce "Baby gara ka saki jiki fa kaci abinci ka daina kunya, mu gidan nan ba'a irin wannan". Ta faɗa tana masa wani irin kallon soyayya. Ya ce "Wallahi na koshi ne shi yasa". Ya faɗa yana shafa cikinsa. Hajiya ta ce "Ai lokacin da motar ka ta lalace da ka ka kira Suhailait ɗin sai a tura maka direba yazo da kai, da baka sha wahalar hawa mashin ba". Ya dago ya kalleta cike da mamaki. Har zaiyi magana tayi saurin faɗin "Ai ya kira ni, kafin na faɗa masa hakan ne yace min wai mashin ɗin abokinsa ne". Hajiya ta girgiza kai. Ta sake faɗin "Dan Allah kar ka bamu kunya, ka riƙe mana ita amana, tunda har Allah yasa ta cire soyayyar wancen ɗan iskan a ranta ta saka naka to mun san ba ƙaramin so take maka ba. Dan Allah ka share mata hawaye ta manta da shi gaba ɗaya". Hajiya ta ƙarasa maganar cikin Muryar tausayi. Ya ce "In sha Allah Hajiya ba zan baku kunya ba". Suka haɗa ido da ita ta daka masa wata shegiyar hararar da sai da ya kusa kwarewa. Haka suka gama cin abincin sannan aka tashi aka barsu su biyu. Kowa na fita ta haɗe fuska tamkar bata taɓa dariya ba. A fusace ta ce "Kai wani irin wawa mara hankali ne, mai zai sa kazo da mashin bayan kuma an faɗa maka irin gidan da zaka zo. Yanzu badan Allah yasa nayi dabara ba ai da tun yanzu ka tona mana asiri". Ta ƙarasa tana jin Kamar ta ɗauke shi da mari tsabar takaici. Dama tunda taji cewa da mashin yazo ranta ya ɓaci, shi yasa ta saka mai gadi ya dinga duba mata. Ya kalleata ceke da jin zafin furincin da tai masa ya ce "Karki ƙara kirana da wawa ko mara hankali, idan ba haka ba zan shayar dake mamaki. Kuma karki kuskura ki sake taɓa ni ko da kuwa a gaban su ne". Ya faɗa shima yana tashi tsaye. Ta ce "An faɗa maka wawa ɗin ko ba shi bane?" Tana rufe baki aka turo kofar aka shigo hakan yasa ta faɗa jikinsa tana dariya haɗi da faɗin "Please honey kar ka tafi ban gama ganinka ba, ni idan ma tani ne ka kwana anan". Yasir da hakan yazo masa a bazata sai ya tsaya yana kallonta. Maimakon yaji haushi sai yaji jikinsa ya mutu. Ya kalli wanda ya shigo yaga wata yarinya ce kamar mai aiki. Kuma tana ganin haka ta juya ba tare da tace komai ba. Ta ɗago daga jikinsa ta ce "Gobe zaka zo ku haɗu da dadyy, kuma kar ka zo min da mashin na faɗa maka". Ta faɗa tana sake haɗe rai. Ya kama hanya zai fita ta ce "Kai Malam ban gama magana ba". Ta karoso har gabansa ta ce "A haka zaka fita rai a ɓace?" "Ya ce "Eh! Sannan kuma bari na faɗa miki mashin nake da shi, kuma da shi nake zuwa ko ina". Ya faɗa zai fita ta jawo hannunsa ta ce "Kai wasa nake maka fa, I'm sorry da nace maka wawa, duk cikin gwaji ne. Sannan ko zuwa da mashin ɗin ma wasa nake maka. Kawai dai goben kazo da wuri dan Allah. Kuma ko yanzu ma tare zamu tafi har bakin get". Ta ƙarasa tana murmushin nan nata da ya kasa gane dalilin sa. Ta ce "Dan Allah ka saki fuska kuma kayi mun murmushi". Haka ta riƙe masa hannu har bakin get mai gadi ya buɗe masa ya fita tana ɗaga masa hannu. Yana fita a fili ta ce "Wawa ƙazami ɗan ƙauye kawai, badan ma da dalili ba kai har ka isa na kalleka bare na haɗa jiki da kai". Ta koma ciki tana tofar da yawu.

Ya kai minti biyar a gurin kafin ya hau mashin ɗin sa ya kama hanyar gida. Shi kansa ƙamshin turaren jikinta ya dame shi bare kuma yaje gida da rigar. Hakan yasa ya biya ta gidan Ali. Ya faɗa masa duk abin da ya faru. Ali ya dinga dariya yana tsokanarsa da cewa ashe ya sha love a gidan yan gayu. Bayan yayi wanka ya saka kayan Ali ɗin ƙanana ya nufi gida yana shirya karyar da zai mata domin dai ya san zai sha tambaya. Bugawa ɗaya kuwa ta buɗe tana masa barka da dawowa cike da nuna kewarsa. Ta ce "Amma sai da nace dan Allah kar kayi dare fa". Ta ƙarasa tana tsayar da kallonsa a kayan jikinsa. "Ina kayan da ka fita dasu kuma?" "Au wai kaya na, ai faɗuwa mukayi a kwata shi yasa muka bi ta gidan Ali nayi wanka da yake yafi kusa". "Ayya sorry, dama dai baka ji ciwo ba ko?" Ta faɗa tana duba jikinsa hankalinta a tashe. "No ba wanda yaji ciwo, kawai kayan ne suka ɓaci". "To Allah ya sake kiyayewa". Tana jikinsa har suka zauna. Ta ce "Tunda kayi wanka bari na kawo mana abinci?" "Wai kina nufin baki ci abinci ba?" "Eh mana Kai nake jira, ta yaya zanci abinci baka nan". Tana faɗa ta shege kicin ta barshi zaune yana bin bayanta da kallo. Ta fito riƙe da kular abinci tana faɗin "Ya hakuri rasuwar, Allah yaji kan wanda suka mutu, idan tamu tazo yasa mu cika da imani". Ya amsa da amin yana faɗin "Nifa a ƙoshe nake munci abinci a gidan". Ya faɗa yana riƙe mata hannu ganin tana dubawa da yawa. Sai ta haɗe rai ta ce "To nima na koshi". Ta faɗa tana tura baki tana kawar da kai gefe ɗaya. Ya ce "I'm serious fa, dole a kayi mana sai da kowa yaci ya koshi a gidan". "To ni nace maka dole sai kaci nawa ne". Ya ce "Tom kinga bari naci ko kaɗan ne". Haka dole ya zauna suka ci tare. Bayan sun gama ta kai komai kicin ta fito ta same shi yana kashe kayan wuta. Bayan sun gama shiryawa cikin kayan barci suka karanta addu'ar kwanciya barci a tare kafin kowa ya kwanta. Jin shiru bai fara bata kabari Kamar yadda ya saba bane yasa ta ce "Hi". 

Ya amsa yana faɗin "hi".

 Ta ce kamar wani abu na damun ka ko?" Ta faɗa da cool voice nata. 

 "Mai kika gani?"

 "Tun jiya na lura da hakan. Kuma ina tunanin akan Mama ne, kawai kaƙi faɗa min ne dan kar raina ya ɓaci ko?"

 "No ba haka bane, nace ki daina tunanin abun da Mama take min yana bata min rai, wallahi ko ɗaya, yadda na ɗauki uwar da ta haife ni haka na ɗauki mama". Ya faɗa yana shafa kanta. Ta ce

 "To me yake damun ka, dan Allah ka faɗa min Please?" 

"Amal kin fi kowa sanin da akwai wani abu da na faɗa miki, kawai dai ina tunanin rashin samun wannan aikin ne". Ta sauke hajiyar zuciya tana jin yadda yake wasa da hannunsa a jikinta, kuma hakan na neman hargitsa mata lissafi ta ce "Ahamm, kar ka manta fa ina of". Ta faɗa tana ɗorawa da magana. Shima maganar da tayi ce ta tuna masa.

"Dan Allah na roki wata Alfarma a gurinka?"

"Ina jiki?" 

"Kamin alkawarin zaka min?"

"Muddin zan iya zan miki Amal". 

"Amma kasan ba zan rokeka abun da nasan ba zaka iya ba ko?"

"Tom ina jinki".

"Alkawari zaka ɗauka akan zaka min?"

Ya sauke ajiyar zuciya.

Ta ce "Dan Allah kace kayi alƙawari".

Ya ce "Nayi alkawari".

"Tom dan Allah ina so ka je ka amshi aikin da Yaya ya samo maka, kaga shikenan sai ka fita a wannan damuwr. Wallahi bana so na ganka a cikin damuwa, zuciyata zafi take min, duk sai na kasa samun natsuwa. Dan Allah kamin wannan alfarmar muddin ina da ita a gurinka". Ta ƙarasa harda kukan shagwaɓa. Yayi shiru yana tunanin abubuwa da dama ciki harda shi aikin da take magana. Amma kuma har cikin ransa baya son aiki ta karkashin Yaya. Sannan bai san lokacin da yaji son wannan 6ml ɗin ta shige shi ba. Ya ce "Ya isa kiyi shiru, zan je na same shi muyi magana". Take ta tsayar da kukan ta ɗago ta ce "Da gaske dan Allah?" Ya ce "Eh sabo da ke". Ai kuwa sai gata tana dariya cikin daren nan. Ta ce "Bari nai maka dabara irin tamu shine tukuicin wannan alfarmar". Daga haka kuwa ta shiga faranta masa cike da dabara ɗin har ya samu natsuwa. 

Washegari ma ta tashi da farin ciki. Lokacin da ya shirya zai fita kuwa babu irin addu'ar da ba tai masa ba akan Ubangiji ya bashi Sa'a da nasara. Ta rungume shi ta sake rungume shi tana cewa idan yaje duk yadda suka yi ya kirata, kuma kar ya dawo gidan nan sai da aiki. Bayan ya fita ta gyara komai kaman yadda ta saba. Ta ɗauki waya ta kunna data. Kamar kuwa ita ake jira sai ga kiran Hafsah video call. Kawai sai wannan misalin na Yasir yayi mata kwanaki ya fado mata, hakan yasa ta ƙi ɗagwa har kira uku. Ta kashe datar ta tashi ta shiga daki domin dako laptop tayi kallo. Tana ta farin ciki abunta yau zasu samu aikin yi, kuma za suyi kuɗi mama ta daina ci musu mutunci. Har ta ɗauko laptop ɗin ta fito ta tuna da chajar ta, saboda akwai wuta sai ta jona a chaji tana yi tana kallo. Ta buɗe gurin da yake ajiye chajar ɗin ta dauko. Sai taga wani abu a daure a bakar leda, kuma bata san da shi ba. Har ta rufe zata tafi sai kuma ta dawo ta ɗauka tana kauncewa a ranta tana tunanin ko menene wannan. Kuɗaɗe ne dauri biyu suka fado sabbi. Hakan yasa ta tsorata har laptop ɗin hannunta na ƙwacewa tare da wayarta. Da sauri ta ɗaga laptop ɗin taga ta fashe. Take kuwa gabanta ya sake faduwa ganin taki kawowa. Ta kalli kuɗin ta sake kallonsu ta rasa irin tunanin da zata yi saboda tsoron da ya cikata. Ga ganin wannan kuɗin ga fashewar laptop. Sai kawai kuka yazo mata mai karfi tana yi tana toshe baki jikinta har rawa yake yi. Ta mayar da kuɗin gurin da suke ba tare da tasa a leda ba, ta tattaro laptop ɗin itama tayi hanyar waje.

"Assalamu alaikum" Hafiza taji an faɗa a bayanta. Hakan yasa ta firgita domin sai taji Kamar ta cikin littafin ne a kayi Salama saboda yadda take a tsorace. Har wayarta na faduwa a ƙasa. Ta dauko da sauri tana dubawa ƙirjinta na hauwa da sauƙa na tsoro. Sai taga batayi komai ba. Ta amsa sallamr tana kallonsa yadda ya shigo jikinsa a Mace kuma ya kafe ta da ido kamar mai tuhumar ta. Da farko ma kenan dama a buɗe ta bar Kofar gidan ko yaya!. Kaman kuwa yasan tunanin da take yi kenan Hafiz ya ce "Ina ta sallama shiru, shine na zagayo ta kichin". Ta ce "im sorry"? Ta faɗa tana haɗe hannu. Ya ce "Wai me kikeyi ne kwana biyu da waya Hafiza, sai ayi ta magana baki ji duk kin bata hanhalinki gaba ɗaya?" "Ta ce "Kayi hakuri ba zan sake ba". "Ya wuce". Ya faɗa fuskar nan tasa ceke da damuwa. Ta ce "Yaya gurin aikin, komai ya tafi daidai sun baka aikin ko?" Ta faɗa daidai ta ajiye masa ruwa. Ya ce "Akwai matsala ne Hafiza". Ta ce "innalillahi wa innalillahi rajiun!. Ta faɗa tana dawowa kusa da shi ta ajiye wayar a gefe. "Mai ya faru?" 

"Ba dan Allah zasu bani aikin nan ba, sai na amince da wani abu kafin a bani, ni Kuma ba zan iya ba". Take gaban Hafiza ya bada wani irin sauti tana tuno da labarin mijin Amal, mai yake shirin faruwa ne. Ta ce "Mai suke so kayi musu har haka?" Ta faɗa a rarrabe tana addu'ar Allah yasa ba abun da take tunani bane. Ya ce "Abar wannan maganar, ba zan iya bane kawai, abun ma ba mai daɗin ji bane, muddin ba zasu bani saboda Allah ba, ko saboda chanchanta ba to na hakura". Hafiza ta kafe shi da ido. A ranta tace yau karatun novel zaiyi amfani. Bari ta gwada irin na Amal ko zata dace.

Ta ce "Na roki wata Alfarma a gurinka?"

"Eh ki roki ko wacce irin alfarma amma Banda wannan maganar dan Allah". Ya faɗa yana katseta.

Sai ta fashe da kuka tana faɗin "Kenan bani da alfarmar da zan iya jin damuwar ka. Kasan irin yadda nake ji idan na ganka a damuwa, wallahi ji na nake na rasa natsuwa ta, dan Allah ka faɗa min ko zan san yadda zan iya baka gudun mawa ta bangare na". Ta faɗa tana kwantar da kanta a kafadar sa, tana ta gayyato kuka. Ya ce "Jin bashi da amfani a gurinki domin ba..." "Ni dai idan ina da alfarma a gurinka to ka faɗa min ko menene?" Ta katse shi da sauri. Ya ce "To Hafiza ƴarsa yake so na aura shi mai kamfanin". Take kukan shagwaɓar ya tsaya chak. Ta ɗago daga jikinsa fuskarta ko ɗugon hawaye babu. Ya ce "Abun da yace min kenan da naje. Yace muddin na yarda zai bani babban matsayi, wai tun ranar farko da nazo yar tasa ta ganni tace tana so...📝


Wato idan kana karanta littafi mai kama da rayuwar ka, abun akwai daure kai! To Hafiza dai ta faɗa one hon. Amal kuma ta shiga tara.