Chapter 8
by @reza12
Chapter 8
Anty na barin gurin Yaya ya ce "Mai ke tafe da kai ɗan Samari?" Yasir ya kalleshi kallo ɗaya sai kawai yake hango lokacin da ya kama shi yana bin bayan wani ƙaramin yaro. Take yaji wani tsanar abun da kuma tsanar Yayan nasa gaba ɗaya. Wallahi akan dai ya yarda ya samar masa aikin yi ta alfarmarsa gara yaje yayi aikin 6ml ɗin nan ya fi masa alkairi. Ya ce "Nazo ne akan batun aikin nan da ka tura Anty gida ta samu Amal. Nace maka bana son aiki ta ɓangaren ka, dan Allah kar ka ƙara min wannan maganar, idan kuma ba so kake kowa yasan dalilin da yasa bana son kaɓar aikin ba". Ya ƙarasa ransa a jagule. Shi wallahi kallon ƙazami ma yake wa yayan nasa, domin dai idan ba ƙazami ba waye zai dinga bin maza yan uwansa. Yaya Ya saki wata bahaguwar dariya mai ban haushi yana tashi tsaye. Ya ce "Jira ni ina zuwa". Ya shige ciki yana ta wannan dariyar tasa da ya saba yin irinta. Kusan minti uku ya dawo ya zauna ya ce "Maimaita abun da kace ɗazu?" Yasir ya kalleshi ya kalli kuɗin da ya ajiye a ƙasan kapet ɗin ɗakin ɗauri guda. Ya ɗora da faɗin "Wannan da kake gani sune mutum a wannan zamanin namu. Idan har kana da su, to ba wannan ba, ko mutum ka yanka a gaban mutne ba wanda zai ce ya gani muddin ka rufe musu ido da wannan. Ko Mata da kake gani sai da wannan ake iya rayuwar farin ciki da su a ciki kuwa harda matar wannan gidan da kake ciki. Hatta yan uwa da abokai idan har kana da wannan to kai Ubangiji ne a gurinsu. Kai ma nasan matarka ce ta ce kazo ka samu aikin saboda tana son kuɗi ko?. Amma da yake kai zuciyar kafurai gareka ba zaka iya ba. A duniyar nan akwai masu aikata laifuka masu muni fiye da namu. Kama daga kan masu satan yara suna kashewa, da masu satan haƙkin mutane, da fashi da mamaki, da bokaye, harda ma bin matan mutane. Duk wannan bai dame ka ba sai sana'ar mu?. Idan zaka kawar da komai ka samu aiki to ka kawar, idan kuma wannan shirmen zaka tsaya yi to ga ka ga mutane ka faɗa musu abun da kaga dama". Ya ƙarasa yana cigaba da dariyar tasa. Yasir ya ce "Tur da mutum irinka, Allah ya wadaran wannan sana'ar da babu komai a cikinta sai zub da mutunci da wulaƙanta da..." "Dakuma rufin asiri ba". Ya faɗa yana tashi tsaye. Ya ce "Saboda kai kanina ne har yasa nake lallaɓa, kuma har ka san sirrina kuma na barka, to amma daga yau ina mai ka maka kunne akan kar ka sake maimaita wannan maganar". Ya faɗa yana haɗe rai kamar ba shi ba.
Yasir ya ce "Naji duk abun da kace, to dan Allah kaima bana so ka sake zuwa gida na ko ka tura matarka muddin akan wannan batun ne. Bana so bana bukatar komai daga gareka, kaje kaci kuɗin ka". Daga haka ya tashi fuuu ya bar gidan ransa na masa ƙuna. Yana jiyo shi yana cewa yazo ya ɗauki kuɗin. Wato shi har gadara ma yake yi da wannan ƙazamin aikin nasa. Shi a tunanin sa duk abun da ya lissafo ɗin nan sunfi nasa muni a gurin Allah kenan. Har ya dawo shago yana tunanin abubuwan da suka tattauna. Sai kawai yaji ba abun da yake son gani sai matarsa, kuma yana ayyana Amal a matsayin da Yaya ya faɗa. A ransa yana jin Amal ba kamar sauran Mata bace da sai yana da kuɗi zata zauna da shi. Ko bashi da ko sisi zasu rayuwa tare saboda ita ɗin yar aljanna ce.
Ganin ƙofar gidan nasa a buɗe ya bashi mamaki. Domin yasan bata taɓa barin ƙofa a buɗe. Ya je zai shiga sai ga Nana ta fito daga ciki. Tai masa kallon gefe ɗaya ta wuce abunta. Idan ya gani daidai ma harda harara tai masa. Ya tsaya yana kallonta yana mamakin sauyin nata, ko itama Mama ta shawo kanta ne. Domin dai yasan Nana idan har suka haɗu sai ta gai da shi ko a ina ne. Duk da bata jin magana amma tana girmama shi.
Ya shiga gidan da sallama idonsa akan gurin daga suke saka Kayan chajinsum. Ganin komai a kan chaji ne yasa ya sauke ajiyar zuciya yana sake kiran sunanta cike da marmarin ganinta. Dama yau suna da wasa na dare karfe takwas. Ta fito daga kicin tana ƙoƙarin boye halin da take ciki. Sai dai kallo ɗaya yayi mata ya fahimci abun da yake zargi. Ta ce "Ka dawo da wuri, kuma baka kira ba". Ta faɗa da muryar da itama tasan ba da ita take masa magana ba. Ya karaso kusa da ita, ya kai hannu ya kama haɓarta ya ɗagota suka haɗa ido sai ta faɗa jikinsa ta saki kuka a hankali. Ya sauke ajiyar zuciya yana sauraron kukan nata tun daga ƙasan ransa. "Ta ce "I'm sorry, ka yafe min, ba da sanina bane, dan Allah kar kaji haushi, idan ma dukana zakayi to ka dake ni amma kar kaji haushi, kar ka ɓata rai, kar kayi fushi dani dan Allah?" Ta ƙarasa tana sake rungume shi, kuma tana ta kukan da ya fara bashi mamaki. Ya riƙe dantsen hannunta biyu ya yagota daga jikinsa yana so su haɗa ido amma taƙi. Ya ce "Wai mai ya faru, mai kika min haka, amma ai kin san bana yin fushi dake ko? Ko mai zaki min sai dai nai miki faɗa ba dai fushi ba Amal". Ta ce "Na sani, amma wannan babban abu ne, dan Allah kar ka sauya min fuska. Kawai idan na gama faɗa maka ka dake ni sai kayi dariya kaji?" Sai abun ya bashi dariya yana mamakin ikon Allah. Ya ce "Tom naji faɗa min". Ta fara kame-kame. Har dai ta fadi abun da ya faru. Tana rufe baki kuwa ya kalli gurin. Da sauri ya sakar mata hannu ya ƙarasa gurin da ta juna laptop ɗin a chaji ya shiga dannawa. Ta tsaya daga gurin tana kallonsa ganin ransa ya ɓaci. Ta sake tsorata tayi narai-narai da ido duk taji ta tsani kanta akan wannan laifin. Ya ciro laptop ɗin daga wuta ya dawo kan kujera ya shiga kunnawa yana mamaki. Sai lokacin ya kalleta ganin tana kuka a gurin da ya barota, ya ce "Zo nan na zane ki". Ya faɗa da murmushi. Sai kuwa ta ƙarasa gurin. Ta koma ta ciro chajar laptop ɗin ta mika masa. Ya amsa ya ninka ta gida biyu. Ya ɗaga ya zuba ma kujerar kusa da ita yana dariya. Amal da har ta rantse ido ta buɗe ta ce "Dan Allah ka dake ni muddin zaka huce". Ya ce "Saboda laptop ɗin ko? Abar da zamu iya sayan wata ko a gobe ma". Da sauri ta ce "Kana da kuɗi ne?" Ya ce "Kin manta da aikin da zan fara?" Tayi shiru tana so tayi magana amma ta rasa ta yaya zata fara, domin ta lura bai shirya faɗa mata komai game da batun kuɗin ba. Ya jawota jikinsa yana share mata hawaye yana faɗin "Wai mai Nana tazo ta faɗa miki ne?" Sai ta ɗan yi dariya kawai tana jin wani irin farin ciki da ta samu Yasir a matsayin miji. Mutun mai fahimta da kuma soyayya domin Allah, babu abun da za tai ta biya shi sai biyayya da sosai da zama da shi cikin aminci da bashi farin ciki a koda yaushe. Ya ce "Ina jinki, naga tana min wani gani-gani ne kamar na mata laifi ne". Ta ce "Kishi take taya ni fa, kasan Nana da ɗaukar abu Serious, bata san kuma kai ɗin ba haka kake ba". "Ban fahimta ba?" Ya tambaya da mamaki. "Wai ta ganka da Hafsa a tsaye kuna chanjen number, shine tace wai aure zakayi, tace na hana Hafsa zuwa gida na". Ta faɗa tana kallonsa kuma tana dariya. Ya kalleta yana jin wani abu kaman dai sako take tura masa. Ya ce "To mai yasa da nazo baki fara min maganar ba sai wancen laifin?" Ta ce "Ai na san mijina ciki da waje. Da an faɗa min abu akan ka, nakan gane gaskiya da karya. Idan da hakan ne kafin ta gani ko taji zan sani domin babu haka a tsakanina da kai, baka boye min komai naka". Take yaji yawun bakinsa ya ƙafe ƙaf!. Ya ce "Am dama fa, dama batun nan ne na Ali, shine kawai na bata number tasa, naje taje ta same shi babu ruwana". "Nima abun da ya faru zuwar min rai kenan da take faɗa min. Na ce mata mijin Amal na Amal ɗin ne, ta kwantar da hankalinta". Yasir ya sauke ajiyar zuciya yana kallon laptop ɗin yana kallon ta. Wallahi bai san adadin son da yake wa Amal ba, a kullum ƙara jin sonta yake a ransa, kuma yasan abun da yake tabbatar da hakan shine biyayyar da take masa. A ransa yace anya ba zai hakura da batun 6ml ɗin nan ba kuwa kar a damu matsala. Sai kuma ya tuno da cewar ai saboda ita zai aikata hakan.
Ta katse tunanin nasa da faɗin "Yauwa ya ya kukayi da Yaya, an samu aikin?"
"Eh zuwa gobe dai yace na koma mu karƙare magana". Ya faɗa yana ajiye laptop ɗin ya shige ciki. Domin baya son a sake Jan maganar.
Ta daga murya da karfi ta ce "Allah ya tabbatar da alkairi, yasa a fara a sa'a, Allah yasa alkairi ne a cikin rayuwarmu". Ya juyo ya amsa da fasali yana murmushi.
Gurin kuɗin ya fara nufa ya buɗe yana kallonsu a bayyane ba acikin leda ba. Ya ciro su yana dubawa ita Kuma ta karaso cikin ɗakin tana faɗin "Kasan irin farin cikin da nake ciki kuwa da ka samu wanan ai.." ta tsaya daga nesa tana kallonsa yayin da shima yake kallonta. Maganar tata ta maƙale a haka. Kusan minti biyar ba wanda ya iya magana sai shine ya ce "Amal". Ya faɗa yana nufo gurin ta yana kuma kallonta riƙe da kuɗin a hannunsa.
Ta ce "Kuɗin waye wannan? Su na gani ɗazu lokacin laptop na hannuna shi ta fadi, na tsorata da ganinsu ne"
"Nawa ne" ya bata amsa yana kallon kuɗin. Kafin tayi magana ya ɗora da faɗin. "Zan sayo laptop da su gobe".
"Amma a ina ka samo su ban sani ba, kuma baka taɓa faɗa min ba?".
"Kaya ake so a gurina shine na amso aro a gurin Ali zan je na sayo, idan aka gama biya zan bashi".
"Yaushe ka fara karɓar bashi ban sani ba?" Ta sake katse shi.
"Wannan na bashi bane aro ne. Ina sayar da kayan zan bashi. Nayi haka ne dan kar kasuwar ya wuce ni. Sannan koda bana cin bashi zan iya ci saboda ke".
"No kar kaci saboda Ni, bana son kaomi a tare da kai sai kai ɗin. Ni a haka nake sonka, idan baka da shi muci gaba da rayuwa a yadda mukeyi komai lokaci ne, dan Allah saboda ni kar ka ci bashin kowa, ko wannan ma dan ka riga da ka karɓo ne, kuma shima dan a kasuwa za'a suba ne da an mayar masa".
Yazo da sauri yana rugumeta. Wallahi bai san lokacin da hawaye ya zubo masa ba. Ya ce "Na gode Amal, na gode da samuwarki a cikin rayuwata. Na gode gode".
Har yamma yana bitar maganar Amal domin yaji dad'i sosai. A ransa yana jin kamar ya faɗa mata abun da yake shirin yi domin yaji mai zata ce. Yasan idan taji ba zata amince ba, amma kuma saboda ita zaiyi hakan. Yasan itama zata so jin daɗi da sauyin rayuwa mai kyau.
Kaman yadda kuwa suka tsara hakan ne ya faru. Mahaifin Suhailait yayi masa tambayoyi sosai kuma ya bashi amsa kamar yadda suka shirya. Ya kirata gata gashi ga gaba ɗaya yan gidan akan cewar da gaske tana sonsa, ta amsa da Eh. Shima Yasir aka tambaye shi, ya daga kai yajin faɗuwar gaba. Daga nan yaje da kansa gurin iyayensa na karya. Sannan shi kansa saurayin Suhailait ɗin ya sake kiran Yasir ya masa alkawarin wani kuɗin idan komai ya tafi daidai. Haka aka bari akan gobe juma'a za'a ɗaura auren kaman yadda dama suka shirya. Yana hanyar gida yana tunanin maganganun da mahaifin Suhailait yayi masa wanda sun kashe maza jiki. Tabbas shi ɗin uban arziki ne, duk da ɗan Boko ne, amma yasan mai yake yi. Wallahi bai taɓa tunanin za'a samu iyaye yan boko irinsa ba. Hakan yasa jikinsa ya mutu da batun auren nan. Dai kuma yana tuno da 6ml zai ji zai iya.
A daren bayan magriba ya dawo gida ya samu tana ta shirye-shirye, da gyare-gyare. Sai farin ciki take abinda har hakan ya bashi mamaki. Tana ganinsa ta tsayar da abun da yake yi tana masa barka da dawowa. Gaba ɗaya ta sauya wa kujerun falon zama, labulaye ma ta cire ta sa wasu. Hatta hotonsu na bangon dakin ta sauya masa gurin zama. Haka gurin da suke ajiye littattafai shima ta sauya masa muhalli. Ya tsaya yana kallon ikon Allah, hadi da mamaki da kuma fargaba duk lokaci ɗaya.
"Meye yake faruwa a gidan ne?" Ya faɗa kamar tashin hankali na son danne komai. Domin abun da yake yi yayi kama da uwar gida na shirin tarɓar amarya.
Ta ce "Alkairi ne yake faruwa mana yallaɓai".
"A'a fa, wannan farin cikin da kike ciki tabbas akwai ƙarin wani abu bayan wannan. Kuma irin wannan gyara falon shima dai akwai dalili".
"Tabbas a kwai dalili mai girma ma kuwa". Ta faɗa tana shiga kichin da sauri. Sai ya biyota yana dariyar dole. Ya ce "Ban fa gane miki ba hajiyta". Yana shiga ya tsaya turus yana kallon abun da ya sake bashi gorubar mamaki mai taurin gaske. Ta ce "Gobe juma'a muke cika shekaru biyu da aure, shi yasa na shirya mana komai, ina so mu dawo kamar goben za'a daura mana aure, hatta gidan da komai ya dawo sabo". Ta ƙarasa tana buɗe wani kwali. Sai ga rigar Da yasa ranar. Da wanda itama ta saka harda takallamnsu duk an goge an ajiye su. Gefe guda kuma ga wani dan ƙaramin ceke. Yayi shiru yana kallonta. Kaman haɗin baki kuma sai ga kira ya shigo waayarsa. Ya kalli wayar yaga number Suhailait ce. Sai ya saci kallon Amal yaga ba ma shi yake kallo ba tana ta farin ciki abunta. Sai ya koma da baya ya daga wayar...📝
S-Reza