Chapter 1
by @fulani2
'Yan mata biyu ne kyawawa da ba za su haura shekara 20 zuwa 22 ba, kansu ɗaya. Idan ka gan su kai tsaye, ba za ka iya bambanta su da 'yan biyu ba. Suna sanye da kayan makaranta na boko, ɗayar na tafiya haɗe da 'yan tsalle-tsalle, ɗayar kuma tafiya kawai take, fuskarta ɗauke da murmushi.
Mai yin tsalle-tsalle ta ce, "Zhara, yau sosai nake jin kaina cikin farin ciki, gaskiya dole ne yau na haɗa 'yar ƙwarya-ƙwaryar party."
Ta dire gaban Zhara, dukan su suka tsaya kafin ta ci gaba da faɗin, "Ya kika ga fuskar Uncle Munir a gaban shugaban makaranta?"
Zhara ta tuntsire da dariya. "Wallahi Halima, baki da dama, wallahi tausayi ya bani. Ya yi wani tsuru-tsuru da shi, ga uban gumi kamar an ciro shi daga cikin tafkin ruwa."
"Ya ma daina baki tausayi wallahi. Mutum duk ya bi ya uzurawa rayuwar mu, abu na laifi da ba na laifi ba ya hau duka da zaginmu. Shi ya sa kawai na je na masa sharri, yana neman mata a gun shugaban makaranta. Kinga gobe ai ba zai ƙara ba. Ni fa so na yi ma a kore shi."
Suna mai ci gaba da tafiya, Zhara ta ce, "Kai, Halima, kora fa! Kin san adadin nauyin da yake kansa kuwa? Ki dinga jin tausayi a ranki, Halima. Sannan ai kai tsaye wannan ba zai sa a kore shi ba, tunda karo na farko ne da aka kama shi da hakan. Kawai dai ki kiyaye kar a zo a gano gaskiya, allura ta tono garma."
"Hmm, ni ban damu ba. Don an koreshi, koma miye, ai shi ya janyowa kansa."
Suna tafe suna zancen har suka samu adaidaita suka hau. Ana zuwa unguwar su, layin farko aka sauke Zhara, suka yi sallama akan sai da yamma idan za su Islamiya. Tafiya kaɗan aka ƙarasa gidan su Halima. Ta sauka ta biya shi kuɗi, sannan ta shiga cikin gidan su tana waƙe-waƙenta. Ta samu Hajiyar su tana shanya tufafin da ta gama wanki. Kallonta Hajiya ta yi tana faɗin, "Allah ya shirye ki, Halima. Naga sanda za ki yi hankali. Sallama wannan ba za ki yi ba, sai dai ki shigo gida da waƙoƙin banza."
Ta ɗan turo baki a shagwaɓe ta ce, "Oh Hajiyar mu, shikenan, daga shigowa ta kuma har an fara tarbana da faɗa, ko kewata ma ba ki yi ba."
Tana sharce zane ta ce, "Rigimar taki ce zan yi wa kewa? Ni dai je ki ki cire kayan makaranta ki zo ki yi sallah."
Cikin shagwaɓa ta ce, "To, amma fa yunwa nake ji, Hajiyar mu, kuma dama an ce ci na gaba da sallah, kar na je ina sallah ina tunanin ɗa'ami."
Hajiya ta gyaɗa kanta tana faɗin, "Ni dai je ki, kar ki cika min dodon kunne da surutun ki."
Ta nufi ɗakinta. Hajiya ta ce, "Ki saki jiki ki zo ki yi sallah, sannan ki ci abincin."
Ta riƙe kai, a ranta ta ce, 'Idan har ba sallar nan na yi ba, Hajiyarmu ba barina za ta yi ba.'
Da yamma Halima ta biya ta gidan su Zhara. Ko da ta shiga, har ta shirya, ta ɗauki jakar ta da Ƙur'ani, za su fito. Halima ta ce, "Wai ya na ji gidan shiru ne? Ina Mama da 'yan biyu?"
"Kin manta na faɗa miki? Yau za su tafi Kano, bikin murnar dawowar babban ɗan Daddyn Kano daga Australia."
"Oh, na manta. Yaya Hafiz da ya kammala karatunsa ko?"
"Shi fa."
Ta faɗa tana rufe gidan da key. Ta je ta kai wa maƙociyar su, Aunty Sumayya ajiya. Bayan sun fito suna tafiya a hanya, Halima ta ce, "Su 'ya'yan masu kuɗi sun ji daɗin su wallahi."
"Mu kuma 'ya'yan talakawa fa."
"To, sai dai mu ce Alhamdulillah kawai. Ki duba ki ga yanda karatun gaba da Sakandare, Jami'a, yake neman ya fi ƙarfin ɗan talaka. Sun rufe makarantu, da masu shekarar ƙarshe da masu shekarar farko da farawa, komai ya tsaya cak! Su masu kuɗin da shugabanni masu faɗa a ji sun ja baki sun yi shiru, ko a jikinsu, tunda su nasu 'ya'yan sun kai su ƙasashen waje suna shan romon ilimi, ko a jikinsu."
Cikin ajiyar zuciya Zhara ta ce, "Hakan ne, Halima. Ai ƙasar tamu ce, sai addu'a. Da yawa ina jin mutane suna kukan matsalar yajin aikin nan da aka shiga, da yanzu sun gama sun fara fafutukar aiki bayan kammala NYSC."
"Ki duba ko Yaya Mahmuod ya tattara duk wani buri nasa a kan karatun nan da kuma aikin gwamnati, amma komai ya sauya sanadin yajin aikin. Dole ya koma kasuwa tare da Baba."
"Allah dai ya kyauta kawai."
"Amin, don Alfarmar Annabi (S.A.W). Ni har fargaba nake ji, anya burinmu na zama lauya zai cika?"
"Da yardar Allah zai cika. Ki dai ci gaba da addu'a, muna fatan sauyi ga ƙasar mu."
"Allah ya sa."
"Amin. Kin iya hardar ki kuwa?" Zhara ta mata tambayar tana kallonta.
"A'a wallahi, cikin sumunu uku ɗaya kawai na iya."
"Tab, ashe kuwa yau ke da Malam Isa mai raba ki da shi sai Allah."
"Hahaha, idan ban iya ba ko? Kafin a fara biyawa sauran a kaina. Dama gyara ne ya mun, saura rashin mutumcin nasa na yau, sai dai ya yi wa wata, ba dai Halima ba."
Tun bayan dawowar su Mama daga Kano, Zhara ta fahimci Mama tana cikin damuwa, sam ba ta da kuzari kamar koyaushe. Hakan sai ya jefata a damuwa. Bayan ta ƙarasa wanke-wanke, ta ɗora girkin dare, kasancewar yau Alhamis babu Islamiya. Ɗaki ta shiga, ta samu Mama tana zaune a kan kujera ta yi tagumi. Zama ta yi kusa da Mama, ta dafa kafaɗarta.
"Mama."
Cikin ajiyar zuciya Mama ta juyo da kallonta kan Zhara ta ce, "Na'am, Maman manya, har kin gama aikin ne?"
"Eh, na ma ɗora tuwon."
Gyara zamanta Zhara ta yi kafin ta ce, "Mama, wani abu ya faru ne bayan tafiyar ku Kano?"
"Me ya sa kika mun wannan tambayar?"
"Mama, naga tun bayan dawowar kike cikin damuwa. Da kin zauna ke kaɗai sai naga kina tunani. Don Allah Mama, me ya faru? Ko matar Daddyn Kano ce ta miki wani abu kamar yanda ta saba?"
Cikin ajiyar zuciya ta ce, "Zhara, ban taɓa ɗaukar matsalar Hajiya Turai matsala ba, bare har na sa ta a raina. Ke ma kin sani kuma."
"Haka ne Mama, to faɗa min me ke damun ki?"
Ba ta so ace ta ji ba har sai taga abin da ya ture wa buzu naɗi, sai dai ba ta da wani zaɓi da ya wuce ta faɗa mata ɗin kamar yanda Baban su ya umurce ta. Dama ko ba ta tambaye ta ba, tana da niyyar kiran nata.
"Zhara, ba komai ne ya saka ni cikin damuwa ba, ke ce Zhara."
Da sauri ta kalle Mama tana fito da idanu ta ce, "Ni kuma Mama?"
"Eh, Zhara. Lokacin da muka je Kano, bayan gama biki, da dare Mahaifinki da Daddyn Kano sun yi magana a kanki da kuma Hafiz."
Mama ta yi shiru. Zhara zuciyarta ta dinga bugawa da ƙarfi, ta shiga fargaban jin abin da yake bakin Mama. Mama ta numfasa kafin ta ce, "Sun yi shawara a tsakanin ku, za su haɗa ki aure da Hafiz. Zhara, abu biyu ne suka jefani cikin damuwa. Na farko, ko ba kya so, na tabbata mahaifinki ba zai dubi illar auren dole ba, zai ce zai miki ko da ba kya so. Sannan kuma ina duba matsalar mahaifiyar sa, Hajiya Turai. Ta tsane ni, na tabbata ba za ta taɓa son abin da yake tsatsona ba. Sann..."
"Sannan me kuma? Wato ke da na ce kawai ki faɗa mata maganar tsayar mata da miji sai ki kawo wani zance can da zai sa ta bijire min ko?"
Baba, da tun ɗazun yake tsaye bakin ƙofa, wanda sam ba su ji shigowar sa ba, ya yi maganar ransa a ɓace. Ƙarasa shigowa ya yi ya zauna gefen Zhara, suka sa ta a tsakiya. Mama ta ce, "Ka yi haƙuri, Baban Zhara, wallahi ba nufina kenan ba."
Ko ta kanta bai bi ba, ya riƙo hannayen Zhara ya sa cikin nasa. Ta yi ƙasa da idanunta domin a tsorace take. Ji take yi kamar ace mafarki take, domin ba ta son abin da zai rushe mata dukkan muradanta da take da su.
"Fatima Zhara, na sani ke ɗin yarinyar kirki ce mai biyayya. Ba za ki taɓa bani kunya ba. Yayana ya nemi haɗa ki aure da babban ɗansa Hafiz domin ƙara ƙarfafa zumuncinmu. Ni kuma ba zan iya ce masa A'a ba. Anan take na amince masa. Don haka ina roƙon ki da kada ki ba Babanki kunya, da yake da matuƙar yarda a kanki."
Ya zuba mata idanu yana kallonta. Gumi ne yake tsattsafo mata cikin jikinta. Har ga Allah babu zancen aure a tsarinta a wannan lokacin dai. Babban burinta ta yi hardar Alƙur'ani da wasu littafai, sannan ta zama lauya domin ƙwato haƙƙin 'yan'uwanta mata. Bayan wannan sannan ta yi aure, amma ba za ta iya ɓata yardar da Babanta yake da ita a kanta ba.
Cikin sanyin murya ta ce, "Tunda har ka amince Baba, nima ba ni da wani zaɓi da ya wuce naka zaɓin."
Cikin farin ciki ya ce, "Allah ya yi miki Albarka, Mamana. Na sani ke yarinya ce mai biyayya, ba za ki taɓa ba Babanki kunya ba."
Kallonsa ta yi da murmushi a fuskarta ta ce, "Amin, Baba."
Mama dai kallo kawai ta bisu da shi. Ta sani Zhara ta amsa ne kawai don ba za ta iya musa masa ba. Addu'a kawai za ta mata, don ba ta isa ta yi komai ba, amma tana ji mata tsoron zama da Hajiya Turai.
Bayan Magarib Zhara ta je gidan su Halima. Ta samu tana zaune a kan darduma, idanunta a rufe tana karatun Ƙur'ani. Hajiya na lazumi. Gaban Hajiya ta ƙarasa ta gaishe ta cikin ladabi. Cikin fara'a Hajiya ta amsa mata gaisuwar tana tambayar ta mutanen gidan.
"Suna lafiya, Mama ta ce na gaishe ki."
"Ina amsawa. Kwana biyu ai haɗuwa ta yi wahala. Insha Allah zan shiga gidan naku gobe ko jibi."
"Allah ya nuna mana."
Halima ta ƙarasa kai aya ta juyo tana faɗin, "Kin san Allah karatun nan nake, amma gaba ɗaya zuciyata tana wajanki."
"Tunanin me ki ke a kaina to?"
"Oho, ni kawai dai tunanin ki nake."
Riƙo hannunta Zhara ta yi ta tashi, suka shiga ɗakin Halima. Zama suka yi a kan katifa. Zhara ta ɗora kanta jikin Halima, ta sa kuka mai ƙarfi, wanda tun da dama tun ɗazun yake ciyo ta tana dannewa, don ba ta son ko kaɗan ta nunawa Mama damuwarta, bare har ita ma ta damu.
Cikin tashin hankali Halima ta ce, "Me ne ne Zhara? Ba ki da lafiya ne, ko wani ne ya mutu?"
Zhara ta kasa cewa da ita komai sai kukan da take. Halima ita ma ta sa kuka. Hajiya ta shigo tana faɗin, "Subhanalillah! Kai, me ya faru, kuke kuka haka?"
Cikin kuka Zhara ta ce, "Nima ban sani ba, kawai Zhara ce ta zo tana kuka."
Tsaki Hajiya ta yi kafin ta ce, "Shi ne kuma don shashanci! Maimakon ki lallashe ta ta faɗa miki abin da ke damunta, sai ke ma ki fara kukan?"
Zama ta yi kusa da Zhara tana lallashin ta, "'Ya ta Zhara, yi shiru, ki daina kuka. Ki faɗa min abin da yake damunki."
Cikin kuka ta faɗa wa Hajiya komai. Ihun kuka Halima ta sa, Hajiya ta kai mata duka tana faɗin, "Ba na son shashanci, Halima. Za ki yi min shiru ko sai na ɓaɓɓallaki?"
Gefe ta koma tana ci gaba da kukanta, sai dai ta rage sautin murya.
Cikin tausayi ta ce, "Kin yi albarka Zhara, da har ba ki yi tunanin bijirewa mahaifinki ba. Insha Allah, tunda har kika yi biyayya, za ki ga sakamako mai kyau, za kuma ki yi farin ciki. Ki daina wannan kukan, ki ƙara ƙarfafa zuciyarki, ki yi ta addu'a a kan Allah ya sa hakan ya zama Alkhairi ga rayuwarki. Nima zan taya ki da addu'a, Insha Allah."
Sosai ta lallashe ta da nasiha har ta yi shiru. Ta fita ta barsu su biyu.
Hajiya na fita, Halima ta matso tana faɗin, "Yanzu shikenan, burinmu na mu yi karatu tare, mu zama lauyoyi, mu yi aikin nemawa mata 'yanci a tare, duk ya rushe?"
Cikin muryar kuka ta ce, "Nima tunanin da ya fi komai ɗaga min hankali kenan, ga hardata ma tsayawa za ta yi."
"Ba komai Zhara. Mu yi ta addu'a, Insha Allah burinmu zai cika. Na tabbata zai barki ki yi karatu, tunda ai shi ma wayayyen mutum ne mai ilimi, ya san amfanin ilimi. Dole zai barki, na tabbatar da hakan. Ki ma ji daɗin ki, kin samu damar karatun ki a ƙasar waje. Da wannan maganar ta samu ƙwarin guiwa, domin ita ba auren take ji ba, muradanta ne ba za ta so ta rasa su ba. Na kuma san za ki so shi, duk da rabona da shi tun muna yara. Na tabbata yanzu ya zama ɗan gayu, ya ƙara kyau da girma."
Cewar Halima.
Zhara ta ce, "Hmm, nima dai ai ba zan iya kawo shi a yanzu ba, don na jima ban gan shi ba, tun dai muna yara. Ban sani ba ko zan so shi ko shi ma zai so ni, za mu yi wa juna ko kuma A'a?"
"Insha Allah ma za ku yi wa juna, Zharana. Ai son kowa, ƙin wanda ya rasa ce."
Dukan wasa ta kai mata, suka yi dariya a tare. Hajiya da take ƙofar ɗaki tana jinsu, ta yi murmushi. A ranta tana jinjina ƙauna irin ta su. Su yi kuka tare, su yi dariya tare, komai nasu iri ɗaya ne. Tana musu addu'a Allah ya sa zumuncin su ya ɗore har 'ya'yansu.
Yau tun safe Baba ya je ya yi cefane, ya kawo za a yi wa su Hafiz girki. Zai zo tare da abokinsa. Suka zage, ita da Halima, suka shiga kitchen suna girki. Hakan ya sa Mama farin ciki, ganin 'yarta ba ta cikin damuwa. Fargabarta ɗaya, mahaifiyar Hafiz.
Zhara ciki take da tunanin ya za ta ga Hafiz. Shin zuciyoyin su za su karɓi juna ko kuma dai dukkansu biyayya za su yi wa iyayensu?
Ko da goma ta yi, sun gama girki, sun gyara gidan, suka yi wanka, suka shirya cikin riga da siket na atamfa. Kayan iri ɗaya, hatta ɗinkin iri ɗaya suka yi, suka fito kamar 'yan biyu.
Suna zaune suna firar yanda za su gan shi, haɗaɗɗi ne kamar yanda suke hasashe shi, ko kuma akasin hakan. Suka ji tsayuwar mota. Jim kaɗan suka ji 'yan biyu, Hassan da Hussain, sun shigo suna ihun, "Ga Yaya Hafiz nan ya zo!"
Zhara ta riƙe hannun Halima da ƙarfi har sai da hannunta ya yi ƙara.
"Kai, za ki ɓallani."
"Halima, a tsorace nake, ban san me ya sa nake jin faɗowar gaba ba."
"Kinga, ki ƙarfafa zuciyarki, kar ki zama matsoraciya. Faɗuwar gaba ba komai ba ne, don wannan ne karo na farko da za ki tsaya da wuni taɗi."
Komawa ta yi ta kwanta tare da rufe idanunta. Zuciyarta na ta saƙe-saƙe iri-iri, ba tare da ta iya cewa da Halima komai ba.
Fulani