11
*BAYA TA HAIHU*
11
https://www.arewapen.com/book?id=6a9287eff3eaa6dc8f153f72
Ummu Maher (Mrs green)🍀
*AREWA WRITTER'S ASSOCIATION*
Habibu ya tashi da sauri, me gadi ya ce"Hajiya da ma wata baƙuwa ki ka yi amma sanin bakya son baƙi yasa na ce bakya nan".
Hafsah ta yi hamdala sannan ta ce"ok to je ka".
Baba ne gadi ya fita yana tunanin wannan wani irin baƙo ne haka tamkar dai balarabe? Duk a ɗazu ya gan shi sai ya ƙara masa kyau yanzu.
Sanyin A/c falon ne ya soma ratsa shi, ya furzar da iska da kuma gumin da ya fara tun ma kafin a fara karatun kenan?.
A ranar dai Hafsah an cika mata burinta, ta dinga sanya wa Habibu albarka saboda shima Habibun shaiɗan ya gina masa saƙa ya faɗa, sannan akwai maganin da Billy ta ba ta tace ta hura masa a fuskarsa in har ta yi masa haka ba zai dinga ganin kowa a gabansa ba, sannan zai ga tamkar dai ke ɗin muharramarsa ce.
Sai daga baya ne hankalinsa ya fara dawowa jikinsa, ya tashi da sauri yana istigfari Hafsah kuwa sai kallonsa take da murmushi ta janyo wani akwati na kusa da ita, ta miƙa masa bandir ɗin kuɗaɗe ta ƙara janyo wani ɗan ƙaramin aƙwati ta bashi ga mi da ce wa"karɓi ka sanya kuɗaɗen a cikin nan".
Ya ji tamkar ya tsinewa kansa saboda girman zunubin da ya aikata ya isa haka, yayar matarsa ya kusanta uwa ɗaya uba ɗaya? An ya kuwa zai yafewa kansa? Yanzu me zai cewa Mero?.
Tambayoyin da ya dinga yiwa kansa kenan kuma babu wanda zai basa amsar su.
Hafsah kuwa tana gefe sai smilling take yau cikar muradinta na kuntatawa ƴar uwarta yanzu dai ita da ƙanwarta matsayinsu ɗaya ne babu wani abin da za ta nuna mata.
Ta faɗa a zuciyarta, Mero ke kika buɗe min sirrinki kika faɗa min irin mijinki irin namijin da na ke so saboda shi ne ya yi dai-dai dani.
Da ƙer ya dinga haɗa hanya har dai Allah ya kawo shi gida lafiya.
Ya dinga kallona tamkar dai wadda aka canza masa, ɗan ƙaramin akwatin da ya ciro a ciki ƴar jakar bakko yasa na ce"Hammah wannan akwatin fa? Sannan kuma ka samu kuɗin?.
Tura min akwatin ya yi, na buɗe a hankali ina kallon ikon Allah, to shi kuwa a ina ne ya samu waɗannan kudaɗan da ko a tv ban taɓa ganinsu ba, gabana ya yi wani irin faɗuwa da sauri na ɗago ina kallon ƙwayar idonsa wacce na ga ta yi jajur kamar jini sai kuma na hango wata tarin ƙwalla a idonsa.
Cike da tausayinsa na ce "duk da ina mamakin wannan kuɗin amma mamakin kuɗin bai kai na hawayenka ba, don girman Allah ka faɗa min abin da yasa ka kuka idan ba haka ba ka ga nima zan yi kukan". Na faɗi hakan udanuwana sun yi rau-rau. Na tsinkayo maganarsa yana cewa "Mero ki yafe mun don Allah, bana so na mutu da haƙƙinki a kaina tabbas na aikata kuskure babba".
Ya faɗi hakan yana ruwan hawaye tamkar dai an buɗe famfo.
Da sauri na riƙe hannayensa duka biyu na fashe da kuka, saboda jikina ya gama yin sanyi akan sato wannan kuɗaɗen ya yi to idan ba haka ba a ina ya samo su?.
Tun kafin na tambaye shi ya ce"tabbas na samu matsala babba, ki yi min addu'ah amma ba zan faɗa miki ba sai lokacin da aka ɗakko Baba domin yanzu ma kiransu zan yi na ji ta inda zamu haɗu na basu kuɗin..."
Tun kafin ya rufe bakinsa ya jiyo ana ce wa"Baba ya dawo! Baba ya dawo!!".
Da mugun gudu muka fito daga cikin ɗaki mu dukkanmu murna ta sa kayan barci ne ma a jikina na fita da gudu ina murna.
Ai kuwa Ba ɗin ne, muna cikin murnar suka kira wo Habibu a waya. Ya ɗaga sai kuwa ya ji Muryar wanda ya kira sa rannan ya ce"to matalauta da mun san ba ku da kuɗi da ma bamu ɗauke shi ba, to ga shi nan mun dawo da shi a cigaba da ga shi". Ƙit aka kashe wayar, sai duk jikin mu ya yi sanyi ga murna ga kuma tuna babban zunubin da Habibu ya aikata, ya faɗa a zuciyarsa wallahi da yasan zasu dawo da shi da bai akaita abin da ya aikata ba, saboda haka ya zamar masa dolensa ya mayar mata da kuɗinta sannan ya yi mata mummunan kashe di akansa domin in har bai yi haka ba ya zama BAYA TA HAIHU kenan.
Tun da aka kama Baba har aka sako shi Ammi ba ta zo ba, ba ta yi saƙo ba sai anan ne na ji tabbas Ammi ta fara sare min a zuciya domin duk ƙin da take mun ai hakki ne a kanta idan wani abun ya faru dasu tazo ta yi musu Allah ya kiyaye amma shiru kamar malam ya ci shirwa, duk abin da take mun ban taɓa damuwa har inji haushinta ba sai akan wannan abin da ta yi mun. Bana kuwa sai biyu yana zuwa domin ya ji a inda aka kwana, yanzu ma da yaji Baba ya dawo har gida ya zo ya daɗe sosai suna ta hira da Baba yana ba shi labarin mutanen, nan dai Baffanmu ya ba shi addu'o'i sosai na neman tsari da kuma kariya.
Tun da safe na nemi Hammah Habibu na rasa, sosai na yi mamakin hakan saboda a ganina ai ya kamata ya zauna ayi murnar dawowar Baba da shi, Anty Baraka tun safe ta zo har yanzu da yake yamma ba ta tafi ba, ita da take ma a gidan wani amma shi tun safe ya fita babu busa ba ɗaga hannu.
Na yi ta gwada lambar wayarsa amma abu ɗaya baturiyar take faɗa min shi ne, switch off nan da nan raina ya so su sosai sai kuma na fara tunanin Allah yasa dai lafiya, domin nasan yana sane hakan ba zai taɓa yiwuwa ba.
***
Hafsah da Billy suka tafa, Billy ta ce "uhum ai kowa yaci tuwo da mu miya ya sha saboda haka wallahi tallahi yanzu ma aka fara wasan".
Hafsah ta yi dariya, ta miƙawa Billy dubu ɗari biyu cash, Billy ta hanyar buɗa tana ce wa "sai uwar ɗakina, gaskiya wannan aikin na ki yana kyau ina son aikin da na yi za a bani dambu wato kuɗi kina irin wannan harkar manyan ai dole ne ayi miki abin da kike so, waccan dubu ɗari da hamsin ɗin da kika bani ma na ji daɗinta sosai wallahi don da ita na canja kayan kwalliya, domin waccan ɗan iskan da nake bi yanzu babu abin da yake min sai dai yaje ya yi shaye-shayensa ya dawo".
Hafsah ta murmusa sannan ta ce "uhum ai duk abin da na yi miki duk a cikin tukwici ne, kin san ance yaba kyauta tukwici tun da ke kika ƙara nuna min hanyar wannan harkar kin ga kuwa dole ne a dinga miki alheri..."
Cikin ƙara ji suka tsinkayo muryar Habibi yana ce wa "Allah ya tsine muku albarka, makirai masu sharri iyayen ahaiɗan in sha Allah ba za ku gama da duniya lafiya ba".
Hafsah ta yi wani murmushi wanda ake cewa yafi kuka ciwo, saboda ta ji haushin waɗan nan maganganun da ya faɗa, tabbas tasan ta can-can ci ya faɗi duk abin da yake so amma ita a yanzu ta fi ƙarfin ko wani mutum y buɗe tsattsamin bakinsa ya ce zai kawo mata wargi, duk da tana son Habibu ya zamar mata dolenta nuna masa tabbas tana da matsayi a wajensa tun da ko ba komi za ta cire sa daga ƙangin talauci. Ba ta ankara ba kwai ta ga ya buɗe akwatin ya watso mata kuɗin akan fuskarta, ya wurgu akwatin ma ya faɗi akan tayal ya ba da wani irin kauuuuuuu.
Zuciyar Hafsah ta tunzura sosai, ta ji tamkar dai ba ita bace sai kuma ta ga gwara ta nuna masa ita ma mace ce, sannan nan da nan ta ji kishin ƙanwarta ta ɗarsu a cikin zuciyarta, tabbas tasan Habibi bai saba da kowacce mace ba idan ba Mero ba, ba ya ganin kowacce mace a gabansa idan ba ita ba to ya zamar mata dole ta yi yaƙi da ƙanwarta sannan ta raba ta da mijin ta ga yadda za ta yi.
Ta ƙarasa har inda yake a tsaye yana huci, ta fara karkaɗa hannu yana ba da saurin ƙas.ƙas.ƙas sannan ta ce"Malam Habibu ka ke kowa? Idan kaya ya gaji gammo ya ɗauka tabbas Hausawa sun yi gaskiya da wannan karin maganar sannan wannan karin maganar ta yi aiki akanka, ada kana neman kuɗi ido rufe yanzu kuma saboda mahaifinka ya dawo shi ne ka dawo min da kuɗi ai duk na ji wannan labarin, saboda haka wallahi tallahi baka isa ba idan ka shirya bari na ni ɗin ban shirya ba, sannan yanzu ne dana ɗan ɗana zumar son ka sa ƙaunarka na ji ba zan iya rabuwa..."
Kau!kau!!kau!!!
Hafsah ta hango wasu taurari akan fuskarta, cike da tashin hankali take kallonsa da kuma mamaki amma saboda tsinkewar zuciya ga abin da take so, sai ta fara ƙelƙela wata irin mahaukaciyar dariya.
Habibu ya yi mata wani irin ba zan kallo saboda har ga Allah ya tsani Hafsah tsana mafi muni.
"Habibu ka da ka yi tunanin za ka tsere min amma wallahi tallahi ina sonka zan faɗa kuma ba zan fasa faɗa ba".
Billy ta miƙe sannan ta ce" abu ɗaya ne idan ka yi ƙoƙarin guduwa ko kuma tona mata asiri dole za ta bayyana wannan bidiyon".
Billy ta buɗe wayar Hafsah sai ga fuskar Habibu ta bayyana ba ki ɗaya. Ai da sauri ya miƙo hannunsa zai karɓi wayar ga wani irin jiri da hajijiyar da suka cika mashi kwanyar kai. Billy ta ce"ai wannan bidiyon idan ba ka yarda ka zama abokin sirrinta ba zamu yaɗa sa duniya ta gani tasan cewa kai waye, sannan ka ga babu wanda zai yi tunanin komi, tun da ka ga babu fuskar ƙawata a jikin bidiyon ka ga wasa tare ci banban".
A ranar dai dolen Habibu ya haƙura, ya yarda da abin da suke so ɗin tun da sun dabaibaye sa kuma babu yadda zai yi.
***
_*Mero*_
Ranar na ga tashin hankali, domin kuwa Hammah Habibu bai dawo ba sai ƙarfe sha biyu na dare. Ai kuwa ko da ya dawo na sha kuka na ƙoshi udanuwana sun yi luhu-luhu kana ganinsa ba sai an faɗa maka ba kasan ina cikin wani yana yi.
Jikinsa a sanyaye ya ƙara sa ya hau gado a hankali, saboda yadda kunya ta lilluɓe sa bai san d wani ido zai kalle ta ba.
Ina jinsa na tashi, na fashe da kuka ina cewa "Hammah ina kaje tun safe, wallahi ina cikin tashin hankali zuciyata baki ɗaya bugawa take".
Haƙuri ya fara bani sannan ya ce"yi haƙuri kwanta da safe zan miki baya ni saboda kin ga dare ya yi yanzu". Ba don na so ba na haƙura, sai me kuma? Muna kwanciya wayarsa ta fara ruri ya kasa tashi ya ɗaga ban sani ba ko ba ya son ɗagawa ne oho.
Ni dai na kai hannu a hankali na ɗauka, so dai sunan da na gani a kai ne ya sanya ni firgici sosai.
Mrsgreen ce.