Chapter-03 (A Deal With Destiny)✨
by @eshamuhd
Wata sanyayyiyar iska ce ke kadawa a filin asibitin City Care. Afeefa na jingine jikin bango tana share ƙwallar idonta da gefen hijabinta, yayin da Mama Asabe ke ta faman lallashita.
Daidai lokacin, wata ma'aikaciyar asibiti (nurse) ta fito daga office din Dr. Farooq ta gansu, ta ƙaraso da sauri. "Mama Asabe, Dr. Farooq yana kiran wannan yarinyar a ofishinsa yanzu nan."
Mama Asabe ta kalli Afeefa da sauri. "Afeefa, ki duba ki gani... Allah Ya kawo mafita! Maza goge hawayenki ki bi ta zuwa ofishin Dr. Farooq, ƙila akwai wani taimako da zai iya yi muku." Mama Asabe ta fada sanin cewa Dr. Farooq ya saba da taimako duk sanda yaga mai bukatar hakan.
Afeefa ta goge idanunta da sauri, zuciyarta tana tsalle saboda fargaba. Ta kalli Mama Asabe. "Mama Asabe... ko dai akwai wani aikin da zan iya yi a asibitin nan na samun kuɗin? Ko wankin kwanoni ko shara ne..."
"Je ki ji abin da likitan zai faɗa da farko, Afeefa. Maza ki bita."
"Suna hawa benen farko, yanayin asibitin ya mata baki ɗaya, ko ina tsaf da shi kalar fari ƙal, tare da sanyin na'urar daidaita yanayi (air conditioner) da ke kaɗawa a hankali.
A hankali Afeefa ke tafiya tamkar ƙafafunta ba za su iya ɗaukar ta ba, tana jinta kamar kowa na karanta ƙuncin da ke zuciyarta.
Suna isa gaban ƙofar ofishin Dr. Farooq, nurse din ta ƙwanƙwasa a hankali.
"Come in," muryar Dr. Farooq ta fito daga ciki.
Nurse din ta tura kofar tana yiwa Afeefa alama da hannu da tashiga tana ita kuma ta juya ta koma inda ta fito .
Tsakiyar ofishin mai faɗi da teburin gilas, Dr. Farooq yana zaune a kan kujerarsa. Amma abin da ya fi jan hankalinta shi ne mutumin da ke zaune a kujerar dake fuskantar likitan Taufeeq.
Taufeeq yana sanye da kwat (suit) kalar baƙi da agogon azurfa mai ɗaukar ido. Yana riƙe da wata leather folder kalar ruwan ƙasa.
Yanayinsa kawai yana bayyana cewar shi ɗan gayu ne, mai ilimi da matsayi na musamman.
"Assalam’alaikum," Afeefa ta faɗa cikin muryarta mai rawa da natsuwa, tare da rusunawa kaɗan ta tsaya a bakin ƙofa, idanunta na kallon ƙasa.
Dr. Farooq ya yi murmushi cikin sanyi. "Afeefa, shigo ciki ki zauna. Wannan shi ne Barrister Taufeeq, lauya ne mai zaman kansa."
Afeefa ta taka a hankali ta zauna a gefen kujera, ta na matse yatsun hannayenta da juna saboda fargaba. Ba ta ko ɗaga kai ta kalli Taufeeq ba.
Taufeeq ya gyara zamansa, ya zuba mata ido yana nazarinta daki-daki: Natsuwa, mutunci, kyawun fuska na halitta, da tsantsar bukatar taimako. Ba tare da bata lokaci ba, ya gane cewa wannan ita ce ainihin macen da za ta dace da sharudɗan da Bin Ali ya gindaya.
"Afeefa," Taufeeq ya kira sunanta cikin muryarsa ta lauyoyi—mai natsuwa da dadin saurare a kunne. "Dr. Farooq ya bayyana min halin da ƙanwarki Rahma ke ciki.
Na samu labarin cewa kuna buƙatar ₦750,000 kafin ranar litinin domin yi mata aikin fiɗar ƙoda, idan ba haka ba rayuwarta tana cikin haɗari."
Afeefa ta ji gabanta ya faɗi. Ta ɗaga kanta da sauri, idanunta cike da mamaki. "Yallabai... haka ne. Rahma tana cikin wani hali, kuma ba mu da kowa sai Allah..."
Taufeeq ya ɗaga hannunsa a hankali don katse kukan data somayi. "I have a solution for you, Afeefa.
A solution that will not only cover the ₦750,000 for Rahma’s surgery today, but will also set you and your mother up comfortably for the rest of your lives."
Afeefa ta buɗe baki saboda tsantsar mamaki. Abin ya mata kama da mafarki. "Taimako Yallabai? Wace irin mafita ce wannan da za ta iya biya musu wannan tarin kuɗin?"
Taufeeq ya ajiye takardun hannunsa a kan teburi, ya jingina da kujerar da yake kai kaɗan. Muryarsa ta fito a hankali.
"I represent a client a very wealthy, powerful, and private businessman. He needs a surrogate mother (mace da za ta ɗauki cikinsa). Medical process ne na IVF. Dr. Farooq za su dasa embryo ɗinsa a mahaifarki.
You will carry the pregnancy for nine months, give birth to the child, and hand him over to my client."
Taufeeq ya ɗan dakata kafin ya ci gaba da bayani dalla-dalla: "In return, he will pay for Rahma’s ₦750,000 surgery immediately today. Additionally, he will pay you ₦50 Million as compensation upon delivery, and buy a house for your family."
Kamar an soketa da allura, Afeefa dake zaune a kujera ta muskuta a kujerar. Muryarta a sarƙe, ta kalli Taufeeq sannan ta kalli Dr.
Farooq cikin firgici da rashin yarda.
"Ɗaukar ciki? Ba tare da aure ba?" Muryar Afeefa ta fito tana rawa saboda tsantsar firgita. "Yallabai... ni mace ce mai mutunci da tarbiyyar musulunci. Wani irin zance kake yi min? Wannan ai... wannan ai da zina ba ta da bambanci, tamkar sayar da mutunci da amanar iyaye na ne!"
Taufeeq bai ji mamakin abinda ta fada ba. "No, Afeefa. It is NOT zina. It is a strictly medical procedure (IVF).
Non-physical contact. Babu wani abu da zai shiga tsakaninki da shi. Out of respect for your dignity and religious values, this is purely a legal and medical agreement. Dr. Farooq is here, he can explain the medical and ethical parts to you."
Dr. Farooq ya gyara zamansa. "Afeefa, a fannin likitanci, ba za a haɗa shimfiɗa da ke ba. Jininsa ne da kwayayensa kawai za a dasa a mahaifarki. Amma dai... yarjejeniya ce ta doka dole saida yardar ki komai zai faru."
Afeefa ta miƙe tsaye da sauri, hawaye masu zafi suna wanke fuskarta. "A'a! Wallahi ba zan iya ba! Mahaifiyata ta koyar dani cewa mutuncinmu shi ne kaɗai abin da muka mallaka! Ta yaya zan ɗauki cikin namijin da ban sani ba, ba miji na ba, domin kuɗi? Me zan faɗawa Allah? Me zan faɗawa mutane idan cikin ya fito?"
"Taufeeq shi ma miƙewa ya yi tsaye, ya buɗe takardun dake hannun shi ya nuna mata ainihin adadin kuɗin da ke rubuce da zasu bata bayan biyan kudin aikin kanwarta..."
Monday morning is the deadline for Rahma's surgery. If you walk out of this door without signing this contract, where will you get ₦750,000 in less than 48 hours? Are you going to let your 18-year-old sister die because of pride?"
Wannan kalmar ta ƙarshe—"Are you going to let your sister die?"—ta daki zuciyar Afeefa kamar saukar aradu.
Tayi shiru kanta a kasa tana tunani, tana sauke numfashi mai nauyi. Wani gefe na zuciyarta yana hango fuskar ummun su da ta ƙanwarta Rahma a kwance a asibiti tana numfashi ta inji, yayin da wani gefen ke hango mutuncinta, tarbiyyarta, da fushin Allah.
Taufeeq ya tura mata pen zuwa gabanta a kan teburin.
"Sign the contract, Afeefa. The bank transfer of ₦750,000 will be made directly to this hospital within five minutes, and Rahma's surgery will be scheduled for tomorrow morning."
Afeefa ta kalli alƙalamin dake kan teburi, ta kalli hannayenta da ke rawa...