25
💕 NUFIN ALLAH 💕
By
Anisa Muhammad yahaya
Page 2️⃣5️⃣
A shawarma king yatsaya ya siyar musu sanan suka cigaba da tafiya
A karkasara gidan Anty yake, basu suka isa ba sai after magriba daman ba da wuri suka fito ba kuma sunyi tsaye tsaye
A kofar gidan yayi parking be shigar da motar shi ba, Ahmad yayi parking a bayan shi
Fitowa sukai har ya Ahmad ɗin, itama Jalila fita tayi, ta bude motar zata fita ne yayi saurin sa lock
Kallon shi tayi taga ya wani maze kamar bashi ya saka ba
"Yahh ban fita ba fah" tayi maganar a ɗan shagwaɓe tana kallon shi
"Baki bani card ɗina ba" shima ya juyo yana kallon ta
Kai ta kawar ta dauko card ɗin nashi a jakar ta ta miƙa mishi dan ita tama manta
Kara yunkurin buɗe handle ɗin tayi yace
"Hanky" gefen ta ta duba ta gan shi ta dauko shima ta miƙa mai
Hannun nata ya kalla sai kuma ya amsa still ita yake kallo, Amman itama ta ɗan haɗe rai, saboda jinta take wani iri a gurin Barin ma yanda ya kafe ta da idanu
Ajiyar zuciya ya ɗan sauke yace
"Ki ɗauka ledan dake ƙasan kafanki ki tafi da shi naki ne, ɗayan Kuma ki basu Ashraf" ya faɗa yana cire lock ya taɗa motar alamun yana jiran ta fita
Mamaki ne ya kamata tunda taga sanda ya ba Jalila ledan shawarman sai tace
"Ni kuma"
"Eh" ya faɗa yana ƙara haɗe rai dan karma ta ƙara tambayar shi
Itama ganin haka yasa tayi mai godiya ta ɗauka tayi waje dan bata ga face ɗin cewa bazata amsa ba
"Ah ah inasu baban nawa, maisa basu shigo ba, ko batare kuke ba" Anty dake zaune a parlour tana kallo tayi maganar
Gaisheta sukayi fareedah tana cewa
"Yah Ahmad yace wai a kawai wani abu da zaije yi a office in suka shigo yasan baza su fito da wuri ba gashi dare yayi Amman wai zasu zo musamman"
"Okay nifa ince dan Amma tace su zasu kawo ku"
"Addahhh!!!" ashraf dake zaune kusa da anty ganin su ya taso da gudu yana rungume fareedah
"Na daɗe banganki ba Adda nayi missing dinki"
"Nima haka boy, yakake, ina ya majeed"
"Ina lapiya, yana sama bara in kira miki shi" ya faɗa yana ƙoƙarin fara gudu yaje sama ya kira majeed, Anisa tace
"Ni ai bakayi missing dina ba ka manta dani ko ashuu nah??" tana ɗan kwaɓe fuska kamar gaske
"Laaa addah ai banganki ba addah reedah kawai na fara gani shi yasa"
"Daman ina zaka ganmu ga favorite sis ta zo" nabila tayi maganar tana aika mai hararar wasa
"Kaii adda dagaske ita na gani fah kawai sai yanzu na ganku"
"Kaidai kasani kira mun mutumi na nima tunda kai baka ganmu ba sai yanzu" Jalila ta faɗa tana zama kusa Anty
"Wai ina kuka je ne naga kun daɗe baku iso ba dan amma tace tun kukayi laasar kuka fito Amman se yanzu nake ganin ku, ina nan ina medile''
"Mun ɗan tsaya a ShopRite ne fah anty su yahh sun mana siyayya" fareedah ta faɗa tana ɗaga ma Anty ledan hannun ta
"Aikam sun kyauta,sai kutashi kuje saman ku ajje kayan"
Toh suka ce Anisa ta miƙa mata na ɗayan hannun ta tace '' ya Faruq yace abasu majeed'' suna miƙewa sukayi sama
Da kallo ta bisu tana fatan Allah cigaba da ɗaurar da zumuncin nan haka, daba dan ma anty shaheeda da addah abida suna neman raba kan yaran ba ai da ba haka ba
Tunda sun nuna su baso suke yaransu na zuwan musu ba, su kuma da suke barin nasu yaran suna zuwa ba suce karsu zo ba Amman sai su ringa musu kora da hali
Shi yasa suma suka kyale tunda ba'a dole tunda ba sa so sai su kyale su, ko da iya haka ne zumuncin ya isa tunda su basa so ayi da nasu yaran
"Wai ke wanan extra ledan fah tun muka shigo na ganshi a hannun ki" fadin Jalila tana janyo ledan kusa da Anisa
"Yahh ne fah ya bani"
"Wani yayan??" suka faɗa kusan tare suna zare ido dan sun san dai a motar ya Faruq ta zauna, Amman basa tunanin dai shi, saboda ya Faruq fah ya Faruq ne
"Shiya bani da zan fito yace wai nawa ne"
Budewa suka fara yi kamar waɗanda aka aike su
Perfumes,skin care products,hair products da sweets, biscuits, chocolate da ice cream
"Keee wallahi zato na yanzu dai yazama hundred percent sure, bara kuga" Jalila ta faɗa tana janyo wayar ta dake kusa da nabila
"Yauwa zancen zan miki na ɗazu daman yana raina sister" fareedah ta faɗa tana washe baki kamar gonar auduga
Videon da ta musu ɗazun ta nuna musu
"Awwwwn!!!" Nabila da fareedah suka faɗa
"Wallahi You two make the perfect couple, ke Black beauty shi ɗan fari" faɗin fareedah
"To mukuma fah, bamuyi making perfect match ba ni Black shi Black" faɗin nabila tana wani juya ido cike da shauƙi
"Ke fah bakida kunya nifah yanzu in law dinki ce Amman kike wannan rashin kunyar a gabana" fadin Jalila
"Tabb waya ga ai abinda yafi haka ma zanyi a gabanki, kunyar ki na me zan ji" faɗin nabila
"Su in law manya, muga me kuke gani" Anisa ta faɗa tana kwace wayar hannun fareedah
"Kutty see ayaushe kika yi wannan taasar" tayi maganar tana riƙe baki
Dan idan ka kalli videon sai kai tunanin wasu love birds ne barin ma yanda take wani shagwaɓa yana wani mata magana da taushashen murya ya miƙa mata hanky
_____________________
By
Anisa Muhammad yahaya 🌺