BOOK ONE CHAPTER TWO
Ƙwa-ƙwalwarshi ta wassafo sunan, zuciyarshi na dokawa kuma kamar wannan damar zuciyar tashi take jira taɗibeshi ta watsa shi wasu shekaru can baya.
*
Tsaye take a gaban shi, jikinta sanye da suturar da sukafi kowanne burge shi a duniya wato ƙananun kaya.
Wata ƴar ƙaramar gownce ajikinta pink color mai hannun vest daya siyo mata zuciyarshi na hasko mai ita acikin rigar.
Amma ayanzu data sanya rigar, take tsaye daph dashi, ƙamshin tiraren ta mai nutsadda zuciya na dukanshi, uwa uba kuma tsayayyun idanunta.
Idanunta sune abu nafarko da suka soma jan hankalinshi alokacinda yasoma ganinta a lulluɓin jarirai.
Kuma sune ayanzu suke fizgarshi zuwa gareta, murmushin da takeyi nasanya zuciyarshi dokawa.
Space ɗin dake tsakaninsu yamatse, yahaɗe goshinshi da nata yana sauke numfashi mai nauyin gaske.
"Inasonki...."
Kalmar tafito cikin ƙaramar murya amma daga ƙarƙashin zuciyar masoyin dake cikin kogin ƙauna.
*
Damshin hawayen da suka sauko samar fuskanshi su suka sanya zuciyarshi dakatawa anan.
Da nauyi mai girma yaɗaga ƙafafunshi yasoma takawa zuwa ƙofar ɗakinshi.
Kayan jikinshi yasoma cirewa, yaɗaura towel a ƙugunshi ya shiga bathroom ye wanka da alwallan da yaɗau keshi mintoci sha biyar.
Yafito yana goge kanshi zuwa fuskar shi da ƙaramar towel ɗin dake hannunshi.
Pyjamas yasanya sky blue, yafesa tirare mai sanyi, yasanya haƙar ƙarinshi a katifa yana lumshe idanunshi.
Yarigada ya rufe babin ƙin bacci saboda tinanin Jamila, akwai dai tarin mafar kanta acikin baccin nasa.
Tun asalin da yana rufe idanunshi yakejin bacci, ayanzun ma dai baccine yaɗau keshi cikeda mafar kanta.
*JAMILA*
Dakin ya yi shiru.
Shiru irin wanda ba ya nufin babu sauti, sai dai zuciyar mutum ce ta cika da abubuwan da suka fi ƙarfin harshe ya faɗa.
A tsakiyar wani katafaren bedroom da aka kawata shi da kayan alatu na zamani, amaryar tana zaune gefen gadonta.
Komai na ɗakin yana bayyana arziƙi. Babban gadon....., labule masu nauyin gaske, fitilun ado masu haske a hankali, carpet mai laushi, kayan kwalliya da aka tsara cikin tsari, har ma da ƙamshin turaren da ya cika sararin ɗakin.
Wannan shi ne gidan da take mafarkin samu. Gida mai girma. Gida mai cike da kuɗi. Gida da babu abin da za'a ce ba za'a iya saya ba.
Sai dai duk da irin wannan ni'ima da ke kewaye da ita, akwai wani abu guda da yake dan ƙare akasar zuciyar ta wanda tarasa ko menene sedai kila yanada alaƙa da abinda ya faru ayau dinnan.
Ta ɗaga kai tana kallon ɗakin. Sai ta yi murmushi. Amma murmushin bai kai zuciyarta ba.
“Da gaske na samu abin da nake so...” ta furta a hankali.
Ta miƙe daga kan gadon. A hankali ta fara zagayawa cikin ɗakin, tana leƙa kowane lungu kamar wadda aka ba ta wani sabon duniya.
Ta taɓa labulen. Ta kalli madubin da ke jikin bango. Ta duba kayan kwalliyarta. Ta koma taga tana kallon harabar gidan da ke ƙasa.
Babban gida ne, mai faɗin fili, motoci masu tsada suna ajiye a harabar sa.
A lokacin ne ta ji wani irin farin ciki ya taso mata. Ta tuna da rayuwar da ta bari a baya.
Rayuwar da ta yi imanin ba za ta taɓa kai ta ga wannan matsayi ba.
Ta tuna Ustaz Rayyan. Ta tuna gidan da yake da shi.
Gidan da ba shi da irin wannan ɗaukakar. Ba shi da tarin kayan alatu. Ba shi da motoci masu tsada. Ba shi da rayuwar da ta gani yanzu.
Sai dai yana da abu guda... Zuciya!.
Zuciyar da ta taɓa ɗaukar ta a matsayin abin da ya fi komai daraja.
Amma ita ta zaɓi wani abu daban. Ta zaɓi duniya. Ta zaɓi kuɗi. Ta zaɓi jin daɗin da ido ke gani, maimakon farin cikin da zuciya ke ji.
Ta girgiza kai kamar tana ƙoƙarin kore tunanin.
“Na yi abin da ya dace,” ta faɗa wa kanta.
“Rayuwa ba soyayya ce kaɗai ba.”
Sai ta koma gefen gadon ta zauna.
A dai-dai lokacin ne wayarta ta yi ƙara.
TING!
Ta zauna a gefen gadon, wayar a hannunta, amma idanunta na hasko mata abinda ke rubuce a kan screen.
"Bazan samu damar shigowa ba ayanzu haka ina Abuja tafiya ta kamani zuwa Mexico zanyi 6 month before na dawo"
A hankali ta koma ta zauna. Sai kuma wayarta ta yi ƙara.
Kiran mijinta ne. Ta kalli sunan da ke screen.
Ta share hawayen da batasan sadda suka ciko idanunta har suka zubo ba, ta goge su da sauri kafin ta ɗaga.
“Hello.”
Muryarsa ta fito daga ɗayan ɓangaren.
“Kin karanta saƙona?”
“Eh.”
“Na shirya komai. Gobe da safe zan tafi.”
Ta yi shiru.
“Kin ji?”
“Na ji!"
“Ki kula da gidan. Zan bar miki komai. Idan kina buƙatar wani abu, ki sanar da manager.”
Ta haɗiye wani abu a makogwaronta.
“Ba za ka daɗe ba ko?”
Ta tsinci kanta da jefa mai wannan tambayar asanda kanta yagama kullewa da tarin wasu abubuwa da bazata iya kayyade wa ba.
Ya yi ɗan shiru.
“Na gaya miki, kusan watanni shida. Amma idan komai ya tafi yadda aka tsara, zan iya dawowa kafin lokacin.”
Ta lumshe ido. Watanni shida. A da, watanni shida ba su kasance komai a gare ta ba. Amma yanzu sun yi mata nisa acikin kanta kamar shekaru dari shida bawai watanni shida ba.
“Okay.”
“Me ya same ki?”
Ta yi saurin amsawa.
“Babu komai.”
“Kin yi kuka?”
Ta yi shiru.
Sai ya sake tambaya:
“Kin yi kuka ne?”
“Ba komai ba ne.”
Ya sauke numfashi.
“Ki huta. Gobe zan kira ki kafin na tafi.”
“Okay.”
Kiran ya katse.
Ta kalli wayar.
Sai wani sabon tunani ya shigo zuciyarta.
“Shin Rayyan ma ya taɓa barinta ko na kwana guda?”
Ta yi saurin girgiza kai.
“Kar ki fara.”
Amma zuciyarta ta riga ta fara.
Marar ta ta kulle, gaban ta yashiga tsukku yana motsawa da kansa saboda magungunan da tasha don raya wannan daren da take ma ɗauki da tarin mafarkai masu kyau amma yanzu komai yarushe.
Ta takure a tsakiyar gadon tana hade jikinta tare da matse cinyoyin ta, wasu hawaye masu zafin gaske suka sauko mata.
A da, irin wannan gida shi ne burinta. Ta yi tunanin idan ta samu irin wannan rayuwa, babu abin da zai sake ɓata mata rai.
Amma yanzu ta fahimci cewa mutum na iya zama a cikin katafaren gida... amma zuciyarsa ta zauna a wani wuri dabam.
Ta miƙe daƙyar, Ta taka zuwa taga. Ta buɗe labulen. Iskar dare ta shigo.
Ta ɗaga kai tana kallon sararin sama. A cikin duhun dare, wata daya ne kawai ke haskakawa.
Sai ta tuna wata magana da Rayyan ya taɓa faɗa mata.
“Wani lokaci Allah kan rufe maka wata ƙofa ne saboda kana ganin abin da ke bayan wata ƙofar ya fi kyau. Amma kai ba ka san abin da ke jiran ka a can ba.”
A lokacin ta yi dariya.
Ta ce:
“Ni dai ina son abin da ido na ke gani.”
Yanzu ta tuna. Sai hawaye yasake zubo mata akaro na ba adadi.
“Na yi kuskure...”
Kalmar ta fito daga bakinta ba tare da shiri ba.
Ta rufe bakinta da tafin hannunta dayasha jan lalli.
Ta ji tsoron kanta.
Domin wannan shi ne karo na farko da ta furta abin da ta daɗe tana ƙin amincewa da shi.
Ta yi kuskure.
Amma shin kuskuren yana da gyara? Ko kuwa wasu ƙofofin idan an rufe su...
Allah ne kaɗai ya san ko za su sake buɗewa?
Ta koma a hankali ta kwanta tana sake rushewa da kuka mai sauti jikinta na kyarma yanayin da take ciki na tsananin bukatar mijinta na kara rikita ilahirin jikinta da ruhin ta.
Wannan chapter din shine ya kasance shimfida na wannan labarin, da fatan zaku bini sannu a hankali na feɗe muku biri har wutsiyar sa.