SULTANIM

Chapter 38

by @msssamher590

SULTANIM
      Na
Mss Samher

Instagram mss_samher
Tiktok mss_samher
Wattpad mss_samher


Page38


Rarraba ido ta farayi kamar wadda ta yiwa sarki ƙarya, gaba ɗaya ta ruɗe, Faruq so yake ya ja mata abin kunya, haka kawai Mami ta raba musu ɗaki ta gansu kuma tare

“Nidai please ka tashi, babu kyau fa”

“Me kenan?”

“Shiga ɗakin mutane babu izini mana” tayi maganar tana turo baki kamar yana kallonta.


“Ko shekera zakiyi nidai ina nan zan jiraki yammata”

Ta ɗauki tsawon lokaci a banɗakin nan, na ƙarshe data leƙa saita hango shi ya gyara kwanciyar tasa zuwa rub da ciki bata da wata mafita dan haka ta buɗe banɗakin a hankali ta fito


Batayi aune ba taji Faruq ya jawota ta faɗo jikinsa, lallausan murmushi ya saki abun daya ƙarawa fuskansa kyau, towel ɗin ta riƙe jin yana neman kwancewa 

“Ka sakeni na saka kaya sai nazo ka tambayeni tunda kace shiya kawoka” ta faɗa idanunta cike da kwalla.

“Idan hawayen nan suka zubo kema kinsan mai zai biyo baya ko”

Da kanshi ya tashi ya ɗauko mata kayan, normal riga da wando ne amma marasa nauyi saboda zafin da akeyi a gari, ɓanɗakin taso shiga ta saka kayan yace sam bai yarda ba shikam, sai baya ya juya mata ta sanya, batama gabama ya juyo ba ƙaramin kyau kuwa tayi ba, zagayata ya dingayi yana ƙare mata kallo kafin daga bisani ya jata cikin jikinsa yana shaƙar ƙamshinta, sun jima a haka ba tare  daya kuma cewa komai ba, ita kuwa ta ɓangaran Nadrah har ta fara sabawa da wannan sabon salon da Faruq ya tsira dan lafewa tayi sosai a jikinsa tana sauraran bugun zuciyarsa.

“Ke kin amince da wannan shirin na Mami?  Tukunna ma wani irin shirye shirye ne haka da ba’a iya miki shi a naki ɗakin ba” ɗagowa tayi tana kallonsa, idan da ce mata akace Faruq zaiyi magana da ita mai tsawon wannan bazata yar ba, ta kasa daina mamaki 

Idanuwanta ya hure, dan kura masa ido tayi wanda batama san tayi ba 

“Madam irin wannan kallo haka, relax don’t fall for me yet” wata irin kunya ce ta kamata saida ta rintsa idanun tanaji kamar ƙasa ta buɗe da shige, wani shirme ta aikata haka? gani take Faruq so yake ya rabata da tunaninta gaba ɗaya.


“Dare yayi ka tashi ka tafi please” ta ƙarasa tana me janye jikinta daga nashi.

“Alright, good night” lafiyyan kiss ya sakar mata a goshi kafin ya miƙe ya sauka a gadon tana kallonshi ya murza key ya buɗe ɗakin lallai har ma wani key ya saka mata a daki kamar nashi, bata tanka masa ba har ya fice, hasken ɗakin ta kashe ta kwanta fuskanta ɗauke da ƙayataccen murmushi, idan da ace mafarki takeyi ai kuwa baza taso tashi daga wannan baccin ba.


Ta makara sosai gun tashi kuma Mami bata tayar da ita ba,  gashi ko hayaniyar su Zahra bataji ba, bakinta ta wanke da fuskarta ta fito falon bata samu kowa ba sai Abu tana ta gyara kitchen, nan ta tsaya suna gaisawa har mamin ta sauko, tayi adonta cikin dogowar riga mai zubin buba saidai ready to wear ce wannan, bayan sun gaisa mamin ta gaya mata ta shirya mai gyaran jiki na zuwa anjima zata fara mata gyaran jiki, ita gaba ɗaya kunya ma kamata take duk da ta sani Mami bata dauketa suruka ba amma akwai kunya tsakani, ta amsa mata da to sannan ta koma daki ta ɗaura towel ta shiga wanka.
 


                Cikin kwanakin nan gyara sosai Nadrah kesha wanda ko bazawara aka yiwa hakan sai ta tsere ma sa'a, itadai Nadrah nata ido, wannan ƙauna da Mami kewa Faruq ba kaɗan bace.


Itakanta ko ba'a gaya mata ba tasan ta canza, wani santsi da ƙamshi fatarta ke fitarwa na musamman, wani lokaci har shinshina kanta takeyi kota tsaya kallon kanta a madubi, magani masu kyau mamin ke bata na ainihin ƴaƴan itatuwa, tana jin nauyinta da kunyarta haka zata karba ta sha tana rufe ido, Mamin takanyi mmurmushi tace

“Babu kunya tsakaninmu Nadrah ɗiyata ce ke kamar Zahra da Zaina, namiji kuwa ɗan son gyara ne bashi da kunya ta wanann ɓangaren.”

An ɗauki tsawon kwanaki batasa Faruq a idanunta ba sai dai ta kanji muryanshi ɗaga falon, dan ko falon idan ba dole ba Mami ta hanata fitowa abinci ma saidai a kai mata ɗaki, shima kuma bai sake nemanta ba.


Kwana goma kenan Mami bata bari an dakatar da gyaran da ake mata ba, tamkar ana shirin canza mata fata ita kanta mai gyara ta yaba yadda gyaran ya karbi jikin Nadrah din sosai da sosai, Abu kuwa zama take kawai tana kallon Nadrah 

“Gaskiya Nadrah anya ba canza miki fata hajiyar nan me gyaran jiki take ba?” duk sanda ta fadi hakan dariya take basu ita da Mami.

Ƴan biyun Mami kuwa duk yadda sukaso a haɗa dasu Mami bata yarda ba ace warta su jira nasu lokacin tukunna.


***********

Ƙarfe biyar na yammacin ranan juma’a, Nadrah ne kawai a gidan sai Abu wanda itama tana can baya inda ɗakinta yake,  Zahrah da Zaina sun fita ita kuma Mami tana gidan Hajiyar Hisham zasu kai lefe, dan haka tayi zamanta a ɗaki ko bayan firarsu bata fito ba.


Ta shirya cikin atamfa doguwar riga simple ɗinki babu wani hayaniya, tayi little makeup kana ta feshe jikinta da turaruka masu daɗi, ta ɗaura ɗankwalinta ta gyara gashinta ta haɗeshi da ribbom madaidaici, haka nan ta tsinci kanta da yin kwalliyar


Tun tana waya da Abba taji shigowar mota amma harta gama bataji alamun an shigo ba, sai ta miƙe ta isa gaban window ta leƙa, Faruq ne tsaye shi da ɗaya daga cikin security ɗin gidan suna magana


Maimakon ta saki labulen ta koma kamar yadda take so saita kasa, ta aza idanunta akansa tana ƙare masa kallo kamar yadda yake mata, ko ta ina Faruq cikakken namiji ne da samun irinsa sai an tona, kyau zubi da tsarinsa kaɗai ya isheshi ya godewa ubangijin daya ƙageshi, sanye yake da wasu lafiyayyun yadi light blue kaftan, gashinsa a kwance kamar ko da yaushe baƙi sidik, kana duban fuskarsa zakasan ba ma'abocin fara'a bane.

 Kamar wanda aka yiwa cunenta ya ɗaga kansa zuwa sama yana saukesu a bakin window ɗin, cikin jikinsa yaji kamar ana kallonsa, cikin hanzari ta saki labulen taja da baya ta faɗa saman gadon gabanta yana faduwa, idanunta ta waro

"Allah yasa bai ganni ba" ta faɗa tana dafe goshinta, idan ya ganta aita tafka abun kunya.
Sauke idanunsa yayi daga kallon wajen yaga labule ya motsa alamun an koma da baya.



                    A hankali taji ana taɓa ƙofar sanna aka turota, cikin sakanni tattausan ƙamshinsa ya buwayi hancinta, kallo ɗaya ta masa ta sauke idanunta ƙasa, kunya takeji sosai, ga wani maganaɗisu dake fisgarta cikin idanunshi, wani kyau na musamman taga kamar an ƙara masa, nauyin hada ido take da shi yayi kyau sosai


Fuskarsa cike da murmushi mai bayyana sirrin kyansa, hannayansa ya buɗe yana faɗin

“Can i get a hug please?” Yayi maganar yana karyar da wuyansa alamar roƙo.
“Please” ya maimaita a hankali.


Sannu a hankali ta ƙaraso ta shige faffaɗan ƙirjinsa, ajiyar zuciya ta saki jin wata natsuwa na saukar mata, ta sauke ajiyar zuciya tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa, dukkanninsu sukayi shiru kowanne bugun zuciyarsa na daduwa.

Kanta ta ɗauke daga ƙirjinsa saboda yadda ƙamshinsa ke kashe mata kowacce gaɓa ta jikinta yana kuma haifar mata da wani irin yanayi, ta zame a hankali, sai ya sauke hannayensa wanda ya zagaye bayanta dasu, saidai idanunsa dake kallon fuskarta.


Hannunta yaja zuwa bakin gado, ya zauna tare da zaunar da ita saman cinyarsa, cikin kamilalliyar muryansa yace

“Ɗago idanunki ki kalleni”

Babu musu ta ɗaga kanta idanunsu suka mannu da juna, kallon juna suka shigayi babu ƙaƙƙauta tamkar zasu haɗiye junansu

“Madam kinsan yadda nakeji game dake cikin zuciyata kuwa?” Yayi tambayar yana tura tattausan hannayan cikin ƙirjinsa bayan ya balle maɓallan rigansa, tafin hannunta ya mannu da fatar ƙirjinsa

“Kina iya jiyo bugun zuciyata?”
Kanta ta gyaɗa masa tana murmushi ɗan tana jin yadda zuciyar tasa ke bugawa da saurin gaske.

Ya ɗanyi ajiyar zuciya sannan yace
“Abinda kikeji yanzu baikai kaso ɗaya cikin ɗari na yadda nakeji cikin zuciyata game dake baaaa……..