KUSKUREN WAYE?

Chapter 2

by @fulani2

Halima ta sa ta gaba da dariya tana mata tsiya, “Yarinyar nan, matsalata da ke tsoro wallahi, kamar wata farar kura.”

Zhara ta harare Halima ta gefen ido tana faɗin, “Tsoro dai ai halal ne ko, ya fi mai neman rigima da kuɗinsa.”

“Ni kin san in dai rigima ce, ba ni da ita sai idan an taɓo ne. Dama kuma Annabi ya ce idan har aka maka laifi, ka rama daidai yadda aka maka. Don haka ni rigima ta ba na yin ta sai da dalili.”

“Iskancin banza! Amma kafin a ce ki rama daidai da yadda aka yi miki, me Annabi (S.A.W) ya faɗa? Ka yi haƙuri ka yafe. Idan ba za ka iya yafewa ba, an ce ka rama daidai da yadda aka maka, aka ƙara da cewa an fi so ka yi haƙuri.”

“Na dai ji ɗin. Sai a tashi a gyara fuska kafin a ce ki fito,” tana hararar Halima ta ce, “Ba wata kwalliyar da zan yi. Gara ya gan ni a hakan. Idan zai so ni, ya so ni a zahirin Zhara, shi ne so na gaskiya.”

Ta tashi ta zauna ta riƙo duka hannayen Aysha tana faɗin, “Kin san me?”

Tana girgiza kai ta ce, “A’a, sai kin faɗa.”

“Tunanin da nake yanzu, idan har na gan shi bai yi min ba, shi kenan ban isa na musa ba, dole hakan zan yi biyayya wa mahaifina? To shi, idan ban masa ba, me zai faru?”

“Wannan tambayar daga ni har ke ai ba mu da amsarta. Zhara, kawai mu yi fatan idan har da alkhairi Allah ya tabbatar, idan kuma babu, to Allah ya rusa maganar cikin sauƙi ba tare da ran kowa ya ɓace ba.”

“Uhm, Amin Halima.”

Bayan su, Yaya Hafiz sun kammala cin abinci, duk da ba sosai suka ci ba. Ka san cewa a ƙoshi suke suka shigo cikin gidan, suka gaisa da Mama a mutunci. Ta tambaye su mutanen gidan.

“Suna lafiya,” Momy ta ce.

“A gaishe ki,” tana murmushi ta ce, “Ina amsawa.”

A ranta ta san Hajiya Turai ba za ta taɓa aiko mata saƙon gaisuwa ba. Bayan sun gaisa suka koma falon Baban Zhara suka zauna.

Yaya Hafiz ya kalle abokinsa Anwar ya ce, “Ba laifi, yaran da mahaifiyar duk suna da natsuwa, sai dai ita ɗin ko a ya take, oho.”

Anwar ya ce, “Shi ne matsalar rashin zumunci. Ai ƙanwar ka da Babanta da Baban ka uwa ɗaya, uba ɗaya, ya wuce wasa fa! Amma a ce ba ku san juna ba, gaskiya ka ji kunya.”

Yana harararsa ya ce, “Amma ka fi kowa sanin ai ba a ƙasar nan ki a zaune ba. To, ta yaya zan santa? Kawai dai idan har bata sauya a yadda na santa tana ƙarama ba, tabbas a ko ina zan iya gane ta.”

“Uzurin ka kenan? Ba ka ƙasar, amma ni ba zai wani gamsar da ni ba. Kar ka manta kana zuwa hutu. Me ya sa ba za ka dinga shigowa kana gaishe su ba?”

“Muna haɗuwa da Baban su a Kano, shi ya sa.”

“Yawwa, kaga dai maganata dai ta fito. Zumuncin ne ba ka so, tunda ba ka damu da zuwa har gida ka gaishe shi ba.”

“Mtsw! Sarki mai ta! Ni ba wannan ne damuwata ba. Ina tsoron na ganta na ji bata min ba, kuma a yadda na fahimci Daddy a kan maganar nan, za mu iya samun matsala matuƙar rashin amincewarta ta fito daga wajena.”

Gyara zaman sa Anwar ya yi yana faɗin, “Ba na ma tunanin za ta ƙi yi maka ba. Kawai ka sa a ranka za ta yi ma. Dama wani lokacin mu muke sakawa kanmu a bu.”

“Uhm!” Ya numfasa yana mai yin shiru, yana tunani a ransa. Tabbbas baya son mace wacce ta yi zurfi a boko, amma kuma baya son kidahumar mace marar wayewa. Ya fi son wayayyar mace ‘yar gayu da ƙwalisa, wacce ba zai ji kunyar nuna ta a ko ina ba.

“Wai da gaske ki ke ba za ki yi kwalliyar ba?”

“Halima, kin fi kowa sanin halina. Tunda har na ce ba zan yi ba, dama alƙawari ne duk mijin da zan aura, a zahirin Zhara ta zan fito masa. Ina so na samu miji wanda zai so ni domin Allah, ba don wani ƙyale-ƙyale ba.”

“Na san da wannan, amma dai da kin shafa ko fauda da kwalli haka. Ba dole sai kin yi kwalliya sosai ba.”

“Aifa, sai ki yi,” cikin jin haushi ta ce, “Matsalata da ke kafiya. Ka da Allah ya sa ki yi!”

Rungumeta Zhara ta yi tana dariya ta ce, “Haba rabin ran, ba dai fushi ba ko?”

Daga waje Mama ta ƙwalla musu kira, “Wai Halima, Zhara, me kuke yi ne har yanzu ba ku fito ba? Kun bar su suna jiran ku.”

“Gamu nan fitowa, Mama!”

Halima ta yi maganar tana mai ture Zhara daga jikinta ta fito. Zhara ta biyu bayan ta. Suka fito suka jira a tare. Tufafi iri ɗaya suka saka, har da ɗinkin. Halima ta sa mayafi, amma ya rufe ko ina na jikinta. Zhara ta sa hijab mai hannu har ƙasa.

Halima ta sa ƙafa ɗaya daga cikin falon, kira ya shigo wayarta. Ta yi baya. Zhara ta dube ta. Halima ta yi ƙasa da muryarta ta ce, “Ki shiga, ina zuwa.”

Ta yi maganar tana mai tura Zhara ciki. Ba yadda Zhara ta iya, dole ta ƙarasa shiga. Halima ta koma daga baya, kanta a ƙasa ta ƙarasa shiga falon, ta zauna a kan kafet daga ɗan nisa da su kaɗan. Cikin jin kunya da tausasa murya ta gaishe su.

Anwar ya karɓa da fara’a ya ce, “Barka da fitowa, Sarauniyar mata. Ya gida? Ya karatu?”

“Alhamdulillah!”

“Ma sha Allah, hakan ake so.”

Ya dinga janta da zance da zolayar ta, sai dai ta yi murmushi ta kasa cewa da shi uffan. Yaya Hafiz ya zuba mata idanu, so yake ya mata kallon tsab, amma sam ta ƙi bada damar hakan.

Dukansu suka yi shiru. Anwar ya ɗauke wayarsa ya miƙe yana faɗin, “Shi kenan, bari na baku wuri. Tunda na zama sirikin ku, kun bar ni ina ta zuba kamar ‘ya’yan kanya.”

Ƙasa ta yi da kanta tana murmushi, haushin Halima ne fal a ranta. Ta je ta yi zamanta ta bar ta ita kaɗai, kunya na shirin ɗauke mata numfashi.

Kusan a tare suka ɗago suka kalle junansu. Saurin yin ƙasa da kanta ta yi. A ransa ya ce, ‘Ba laifi, tana da kyau. Sannan kamanninta na yarinta bai sauya ba, sai dai kawai ɗan abin da ba a rasa ba da girma zuwa wasu sauyi-sauyi.’

Cikin sakin fuska ya ce, “Ni dai ƙawata da na sani a da, mai yawan surutu ce ga kuma ƙiriniya. Amma wannan gaba ɗaya naga magana ma wahala take mata, kamar mai ciwon baki. Ko dai an sauya min ita ne?”

Ya yi maganar idanunsa na a kanta. Sake sunkuyar da kai ta yi tana dariya marar sauti. Duk yadda ya so ta sake jikinta da shi su yi magana, ta kasa. Zhara mace ce marar saurin sabo, tana da kunya sosai.

A jiyar zuciya ya yi kafin ya ce, “Na san tun kafin zuwana Baba ya miki bayanin komai. Ni dai ta wajena babu matsala. Duk abin da Daddy ya yanke a wajena, banda ja, na kan karɓe shi hannu bibbiyu. Sai dai a wajen ki ne ban san ya kika ɗauke al’amarin ba.”

“Nima a wajena babu matsala,” ta ƙarasa maganar tana mai ɓoye kanta cikin hijab.

Murmushi ya yi. Duk yadda ya so ya ja ta da fira don ta saki jikinta da shi, amma kunyarta ta hana hakan. Wannan ya sa bai wani ɗauke dogon lokaci ba ya mata sallama. Bayan ta shiga gida ya je ya yi sallama da Mama. Suka fito tare da su Hussain. Ya ba su saƙon Zhara da tsarabar su. Anwar ya ja mota suka bar garin.

Tana fitowa falon ta samu Mama na aiki. Ta tambaye ta Halima. Mama ta faɗa mata Halima tun ɗazun ta tafi. Ɗaki ta shiga, sai bayan tafiyarsu ta fito zuwa gidan su Halima.

Tana zuwa ta samu Halima tana aiki kitchen. Shiga kitchen ɗin ta yi. Halima ta duƙa tana zuba albasa a kan naman kaji. Zhara ta kai mata duka a baya har sai da Halima ta gantsara tana ihu ta juyo. Ganin Zhara ce a tsaye tana harararta, ta yi ajiyar zuciya.

“Wayyo! Wai dama ke ce? Gaskiya kin ɗau alhakina, Allah! Dukan ya shigeni.”

Cikin harara ta ce, “Babu ‘yar wulaƙanci da rainin wayo irin ki wallahi. Kawai sai ki yi tahuwar ki ki bar ni.”

“Wayyo, yi haƙuri, jinin jikina. Wallahi ni kaina ba hakan na so ba. Ban ji daɗin rashin ganin Yaya Hafiz ba. Yaya Mahamod ne ya kirani wai ya kawo aiki, Hajiya bata nan. Idan ina kusa na zo na gyara masa. Zai yi baƙi ne. Na fara kawo masa uzuri tun kafin na ƙarasa, ya hau masifa. Kin san halinsa. Hakan ya sa dole na dawo, amma ni kaina ban so hakan ba. Ki yi haƙuri.”

“Mtsw! Gaskiya Yaya Mahamod bai kyauta min ba. Kinga yadda na zama kamar a ce ar na arci na kare.”

Dariya Halima ta yi ta rufe tukunya. Suka fito waje suka zauna a kan kujerar roba.

“Bani labari, ya haɗu? Ya yanayinsa yake? Yana da fara’a? Ya kuma yi miki ma’ana? Kina son shi?”

Tagumi ta yi tana kallon Halima har ta gama zuba. Sai ta janye tagumin tana dariya ta ce, “To, ni wannan tambayoyi haka kamar a gidan jarida! Wanne zan amsa, wanne zan bari?”

Halima ta kai mata duka a kan cinyarta tana faɗin, “Malama, duka nake so ki bani amsa. Faɗa min, don Allah. Duk na zaƙu na ji. Aiki fa nake, amma hankalina na wajen ku. Na ji kamar na kama Yaya da suka ɗan haushi.”

Murmushi Zhara ta yi kafin ta ce, “Gaskiya ya haɗu. In gaya miki a fakaice, na ƙare masa kallo. Kinga kyakkyawa ne kamar dai yadda kika ga Babanmu da Daddyn su suna kama, to shi ma ɗinsu ya ɗauko. Sai dai kawai kinga shi akwai yarinta da kuma yanayin inda ya taso. Komai na sa har ya fi na su kyau. Ga shi yana da sajin fuska, kamar dai irin na Salman Khan. Ke, har ya fi na Salman Khan kyau fa.”

Ta yi shiru tana lumshi idanunta. Halima ta tintsire da dariya tana faɗin, “Yarinya kawai, dai ki ce kin faɗa Yaya Hafiz ya cire tuta.”

Ta buɗe idanunta tana ɗaga mata gira ta ce, “Yes, faɗi da babban murya.”

Ta gyara zamanta tare da magana cikin natsuwa da nuna ba wasa ta ce, “Magana ta gaskiya na faɗa. Ba ƙaramin faɗawa na yi a ƙoramar son shi ba, har ina jin fargaban kar ya ce ban masa ba.”

Halima ta dafa kafaɗar Zhara tana faɗin, “Ki ma daina sa wannan tunanin a ranki. Ina da tabbacin zai ji fiye da abin da kika ji. Domin ke ɗin kina daga cikin irin matan da ba ko wane irin namiji ne zai iya gani ba, zuciyarsa ba ta buga ba har ya ji ina ma zai same damar ɗaukar wannan gwal mai ƙyalli da kawalwainiya.”

“Allah ya shirye ki, Halima. Tunda ni taki ce, ai dole ki kurantani hakan. Amma rigar da ta yi wa wani, to ba lallai ne ta yi wa wani ba. Abincin wani aka ce gubar wani. Ke dai kawai na bar wa Allah. Duk abin da ya yi daidai ne.”

“Gaskiya ne. Allah ya tabbatar mana da alkhairi.”

“Amin.”

Ta tashi suka yi. Zhara ta kama mata aikin. Suna aiki suna ci gaba da zancen Yaya Hafiz. A maganar da suke, da Zhara Halima ta fahimci Zhara ta faɗa so ba da wasa ba.


A mota suna tafe, dukansu sun yi shiru sai waƙar D.Y. da ke tashi a motar. Anwar ne ya gaji da shirun. Ya rage murya ya ɗan kalle gefen da Hafiz yake, kujerar mai zaman banza. Yana dannar waya, ya mayar da hankalinsa a kan tuƙin da yake kafin daga bisani ya ce, “Kuna kama da ita sosai, kuma yarinyar ta burge ni. Tana da kunya da natsuwa. Ina fatan dai ta maka, don na san halinka. Ba ƙaramin aikin ka ba ne ka ce ba ta maka ba.”

Murmushi Hafiz ya yi kafin daga bisani ya ce, “Ko ba ta min ba, ai ban isa na ce a’a ba. Ka kuwa san yadda Daddy ya ɗauke lamarin auren nan?”

Ya ja numfashi ya furzar kafin ya ci gaba da magana, “Ni fa ban mata kallon tsab ba. Gaba ɗaya ta duƙunƙuni guri ɗaya. Kunyarta ta yi yawa.”

“Ba wani yawa da kunyarta ta yi, Malam. Kawai al’adar masu jajayen kunne ka ɗauko rayuwar wayewa. Amma ni ban ga matsalar kunyarta ba fa. Hakan mace dama ya kamata a ce ta kasance. Ko ba ka san kunya tana daga cikin adon mace ba? Kuma ko a addinance ana son mace ta kasance mai kunya. Tana daga cikin alamomin mace tagari.”

“Malam, duk na san wannan karatun, amma fa na ta yi yawa. To, ta yaya zan san ainihin wace ce zan aura?”

“A she, to ƙarya kake da kake cewa ba ka son wacce ta yi zurfin karatu. Ni dai a sanina, mafi a kasarin ƙanana yara masu ƙarancin shekaru irin Zhara, da wahala ka same su da irin wayewar da kai kake so. Don sai ka je can jami’a ka ɗauke wayayyar mace. Babu kalar da ba za ka samu ba sai wacce ka so ɗauka. Amma fa bance a jami’ar babu masu kunyar ba. Akwai, amma kuma a can za ka sami irin kalar da kake so.”

Harararsa Hafiz ya yi kafin ya ce, “Kai, iskancinka yawa ne da shi. So kake Daddy ya yankani ya yi tsire da ni don tashi hankali. Sannan ni na ce maka bata min ba? Kawai dai yanayin da nake son matar da zan aura ne bata kai ba. Amma ba komai, tunda bana jin ƙinta, zan iya aurenta a hakan.”

“Kada Allah ya sa maka aure ta ɗin!”

Dariya marar sauti Hafiz ya yi, ya ɗauke wayarsa ya ci gaba da dannawa. Ya san abokinsa ya shaƙa, dama Anwar akwai saurin fushi.


Hajiya Turai tana zaune cikin babban falonta. Ta yi shiga ta alfarma, tana riƙe da remote a hannunta. Ta miƙe ƙafafunta tana daga saman kujera. ‘Yar aikinta Dije tana zaune a gabanta tana mata tausa.

Hafiz ya shigo falon yana waya, yana sanye da wando jins ɗin iya gwaiwa, sai riga mai ƙaramin hannu.

“Anwar, tashina kenan fa. Ka bari kawai, anjima za mu yi magana.”

Yana gama faɗa ya tsinke kiran. Ya ƙara saƙa cikin falon ya zauna a kusa da Hajiya Turai yana faɗin, “Momy, me aka dafa mana ne? Yunwa nake ji.”

“Abin da ka fi so na saka aka ma.”

Cikin farin ciki ya ce, “Momy, sinasin aka yi?”

Ta gyaɗa masa kai tana murmushi ta ce, “Har da farfesun da ka fi so, farfesun kayan ciki.”

Cikin farin ciki ya nufi ɗakin ya zauna yana ci suna fira. Bayan ya gama ya dawo cikin falon ya zauna. Ta dubi Dije ta ce, “Maza, ki bar nan.”

Da sauri Dije ta tashi ta fita. Ta dawo da hankalinta kan Hafiz, fuskarta babu annuri ta ce, “Tun bayan dawowarka Jigawa ba ka ce da ni komai ba. Kaga yarinyar ta maka?”

Shafa sajin fuskarsa ya yi yana murmushi ya ce, “Ba laifi, Momy, ta yi.”

Ta ɗauke fuska kafin ta ce, “To, idan har kai ta yi maka, ni ba ta min ba, ba kuma zan taɓa barin wannan auren ya yiwu ba.”

Gyara zaman sa ya yi ya riƙo hannayenta cikin tausasa murya ya ce, “Momy, don Allah ki yi haƙuri. Kar ki nunawa Daddy ba kya son zaɓin shi. Ba na so wata matsalar ta taso a sanadin wannan auren. Ki yi haƙuri, Momy. Komai ya wuce abin da yake tsakanin ki da Maman yarinyar nan daban, ita ma yarinyar daban.”

Fizgi hannunta ta yi kafin ta ce, “Ba fa zan yarda ba, Hafiz. Dole ka bi umurnina. Ka je ka faɗawa mahaifinka ka je yarinyar bata maka ba. Ya yi haƙuri, za ka fito da wata. Idan ya so, ka je cikin ‘yan’uwana ko ‘ya’yan ƙawayena ka duba. Na tabbata ba za ka rasa wacce za ta maka ba a cikinsu.”

Cikin damuwa ya ce, “Momy, ta yaya zan iya tunkarar Daddy da wannan zancen? Sanin kanki ne, ba zai taɓa yarda ba. Faɗar hakan ma zai iya janyo matsalar da daga ni har ke ba za ta mana daɗi ba.”

Ya gyara zamansa yana kallonta cikin marairacewa da kwantar da kai ya ce, “Don Allah, Momy, k…”

Ta ɗaga masa hannu.

“Na gama magana. Hafiz, ba na son haɗa zuri’a da mugun iri, irin Mayu. Don haka umurni na ke baka. Ka faɗa masa kamar yadda na faɗa maka.”

Tana gama faɗa ta tashi ta haura sama ta bar shi zaune a wajen kamar mutum-mutumi.

Hafiz mutum ne mai gudun zuciya. Yana matuƙar son iyayensa, yana da biyayya da gudun zuciyarsu. Gaba ɗaya ya shiga ruɗani har ya rasa wani irin tunani zai yi. Haka ya tashi jiki ba ƙwari ya koma sashinsa ya kwanta rigingine a kan gado, idanunsa a rufe ya faɗa duniyar tunani.

Idan har ya ƙi bin umurnin Momy, shi kenan ya taro wa kansa rigima. Sannan ranta zai ɓace, za ta yi fushi da shi. Haka uwa Uba Daddy, idan har ya yi gigin faɗa masa hakan, komai ma zai iya faruwa.