AASIYAH

1

by @mamuhgee

Aasiyah

By

Mamuhgee

1

DEDICATED to the sole owner of the name (Asiyah Ahmad Bala Gummi) A gift for you on your 30th.

They say 30 is a milestone.

And somehow on this milestone I get to give you something that carries your name AASIYAH,

Thank you for every push,every encouragement,every conversation,every reassurance, and every moment you reminded me not to give up.

So when I thought about what I could possibly give you on your 30th birthday,I realized that perhaps the most beautiful gift I could give you is something that will carry your name long after this moment has passed.

This is my 30th gift to you🤍

A story born from my heart, carrying the name of someone who has held a very special place in it.

Happy 30th birthday, my AASIYAH🤍

May Allah bless your new decade with everything your heart quietly prays for, and may He reward you for every way you have been a light in my life

AASIYAH for you, with love💋

********

BismillahirRahmannir Raheem

Allah ya bamu ikon gamawa lafiya kaman yanda zamu fara lafiya da ikonsa.

RF Prison Bilen

Tuesday 01 sept 2026

1:34 am

Kaman yanda agogon Nigeria ya nuna karfe daya da mintina talatin da hudu na tsakar daren daidai wannan lokacin koina yayi tsit kowace hayaniya ta lafa babu sautin komai,

Wata black BMW X5 ce wadda batada kowace hayaniyar tafiya da sautin engine sbd kudin da suka amsa kudi ne suka siyeta wadda kalar black dinta yake wani sheqi daban a cikin duhun daren ta iso bakin babban makeken gate din prison din wanda yakeda tsaro sosai da hasken lantarki ta koina tareda security cameras.

Tin kafin motar ta iso daf da asalin main gate din na farko kenan security cameras suka nunawa shugaban gurin motar wadda ta sakasa miqewa tsaye a natse daga kan lafiyayyar kujeran office dinsa dayake zaune yana waya yayi sallama da wanda yake wayar a tsanake yana nufar kofa ya fito kai tsaye yana nufar kofar daya san nan motar zata iso ta paka.

Su kuwa securities din gate din tin bata qaraso ba aka kashe kowace camera dake hanyar dukkanin gate din tin daga na farko harna karshe da duk hanyar da motar zatabi aka tsayar da komai tareda wangale gate din sbd motar bata tsayawa koina ko slow a koina saita isa inda zata tsaya a ciki,

Motar kuwa na isowa haka ta wuce da wata irin nutsuwa da kwanciyan hankalin mai tuqata babu abinda ake gani a motar bayan sheqinta dan kuwa kaf securities din dake wannan aikin na bude gate ga koma wanene a cikin motar babu wanda ya taba ganinsa koda kuwa inuwarsa ce abu daya ne kawai suka sani shine ranakun zuwan koma waye a prison din kuma a daidai wannan lokacin da babu kowane dan adam dazai taba samun dace da saar ganinsa.

Ratsa cikin gate din motar tayi wanda haka tsananin hasken dake ratse da hanyar da motar ke tafiya yake ragewa ahankali cikin wani irin tsarin da babu kuskure a cikinsa ko daya.

Motar na shigewa aka rife kowace gate data wuce ruf babu kowace emergency da zata saka gate din kuma budewa a wannan lokacin sai lokacinda motar ta fice.

Bata tsayaba sai data isa har bakin hanyar kofar da iya manyan prison din na kololuwa ne kadai suke da iko da damar kai motocinsu a gurin ta dakata daidai nan shugaban gurin da kansa dayake tsaye yana jiran isowan motar ya qaraso yana tsayawa a natse da kwanciyan hankali a fuskansa.

Kofar gaban motar ce bangaren seat din driver aka bude tareda ziro kafafu tukuna ya fito gabaki daya kallo daya Sir IB ya masa ya saki fuska a hankali da nutsuwa da wata irin zallan ilimi yana amsa gaisuwan daya bude baki da wata nustuwa ya masa suka zagayo gabaki dayansu a natse zuwa dayar kofar wadda tin kafin su qarasa zagayowa wanda yake ciki ya budeta da hannunsa daya wanda shine ya fara bayyana sanye da wani black Audemars piguet agogo wanda yake daure a hannunsa dayake fari tas fatarsa na bayyanarda dukkanin hutu da lafiya tareda wata irin tayar da tsigar jiki kafin ya fiddo kansa ahankali da wani irin slow da nutsuwa da kamewan datake bayyana a kowace motsi da fitar numfashinsa da ya fito gabaki daya yana bayyana sanyeda Balenciaga sweatsets black da fcap din NiKe black wadda ta hana fuskansa bayyana sosai wadda kwarjinta yakewa Sir IB yawan da baya iya kallansa yanda ya kamata.

Kamshinsa ne na tsadadden bolt lightening ya sauya niimar gurin wanda ya ratso daga cikin motar ya biyosa ya dago idanuwansa da sukai wani iri tareda tsananin haske da wata izza da zafin wuta a cikinsu wadda a kallonsa kadai zaka iya jin zafinta jikinka batareda fitowan kalma ko daya daga bakinsa sbd sune iya zafin da zai baka mai kona fata da jini kafin fitowan kalamai daga bakinsa da hakan shine matakin da xaka san anje babban mataki.

Hannu ya daga ya miqawa Sir Ib tareda dago kansa da idanuwansa ya sauke akansa batareda y iya furta kowace kalma ko daya ba sai sallamar data fito bakinsa ahankali.

Cikin nutsuwa da kulawa Sir ib ya amsa sallaman yana bude baki da kulawa da rashin wata bata lokaci da hayaniya ya juya yana bin hanyar da zasu bi wadda a tsanake shima ya daga kafafunsa cikin tafiyar cikakken lafiyayyan maji karfin namiji wanda babu abinda rayuwarsa ta rasa sai abubuwa kalilan.

A natse da wata irin girmamawa da asalin kulawa wanda ya tuqo motar ya tako yana binsa a gefensa yana daga wayarsa ya bude ya saukar da idanuwansa akan jerin footages din da wayar take dauko masa a jere kusan guda biyar wainda yake monitoring daga nan inda yake din na gida dana hatta dakin Ubangidan nasa.

Mayar da wayar yayi yana kallan kofar da suka iso wanda tini aka bude ubangidan nasa dayake gabansa aka janye gefe ana basa hanyar shigewa wanda ya saka kansa kai tsaye da wani irin nutsuwa da kamewa take dukansu suka je gefe suka tsaya daga bakin kofar suna tsayawa cak kaman wasu soldiers.

A daidai wannan lokacin motsi ya fito daga wata hanyar datake asalin hanyar shiga can kurya inda asalin prisoners suke bangaren mata,

Mata biyu ne masu karfin gaske da uniform dinsu a jikinsu suka riqo wata prisoner wadda take sanye da uniform dinta na prison da numbernta baro baro a jikin kayanta wato Number 6.

Kokarin kwacewa takeyi tana wani irin fusgewa da tirjiya tana kokarin bude baki tayi ihun data saba tana yakushinsu da kokarin cizo,

Hannuwanta da kafafuwanta duka sanye suke da sarkar da aka daureta dasu harsun kwanta sosai a jikinta amma bata damuba sbd dukkanin alamunta suna nuna ba iya prisoner bace tanada tabin hankali mai karfi maana akwai hauka a tareda ita mai karfin gaske data sauya kamanninta da komai nata fiyeda yanda zaa ganeta kai tsaye duk da babu kazanta atare da ita sam tana samun kulawa sosai da tsaftacewa.

Sake kokarin kwacewa takeyi tana fixgewa tana neman su saketa amma sanin idan ansaketa wani gurin zata iya guduwa batareda damuwa da daurin sarkar dayake kaffunta ba gudu takeyi tana faduwa tana raunata kanta wanda yake sake tabbatarda haukarta tuburan.

Kofar dakin suka iso da ita wanda ya saka Tajj sauke kansa ahankali qasa batareda da ya kuma dago su ba Sir IB kuwa bude kofar yayi da kansa tareda musu alaman su saketa da hannunsa,

Sakinta sukai tareda Juyawa suma suka kama hanyar da suka fito suka dan nesa da kofar dan su jira koda kuwa jiran zai kai asuba ne wannan aikine da bana hukumar prison dinba aikine na musamman da babu wanda ya sani kaf duniya sai iya Sir Ib daya daukesu ya basu tsawon shekaru na kulawa da matar batareda sanin kowa ba kaf prison din hakama camera bata bata dauko hakan ba sbd tsari da tsaro tareda tsaftar aikin wanda dukkaninsu sun zabi rasa ransu akan kuskuren ga wannan aikin dayake baida banbanci da rasa ran idan har aka samu kuskuren bayyanarsa ga kowace hukuma ta sharia da tsaron Prison din.

Prisoner din suna sakinta cak ta tsaya a gurin kaman ba ita ba kafin dakanta ta saka kafafunta kofar ta shige wadda take Sir IB ya rife kofar a natse da juyawa yabar gurin yana komawa office dinsa dan sake bawa yanayin da lokacin dukkanin tsaro.

Ana rufe kofar ta tsaya cak daga inda take tareda dago idanuwanta da sukai wani irin rami da duhu ta saukesu akan bayansa.

Bai juyoba saidai motsawa yayi ahankali tareda rufe idanuwansa da sukai wani irin jan da suke wani irin radadin dayake ratsa kowace jijiyar jikinsa yana ratsa jininsa dayake kona kowace drop ta jininsa kafin ya budesu ahankali tareda juyowa da asalin kwarjininsa dayake hade da wata wuta mai tsananin zafi da radadi ya sauke idanuwansa da suka saka kowace gabar jikinta sakewa da wani irin radadi take kafafunta suka sare mata ta xame ahankali zata zauna ya bude bakinsa da muryansa da kaurinta yake tayar da tsigar jiki dan kaifinta yace,

"Mammah"

#MAMUH

#AASIYAH

#BEST LOVE/REVENGE STORY

#SECRECY

#CHECKMATE

#THE TRAP

CRAZIEST LOVE/ROMANCE

#SWEETHEARTS

1K REGULAR

5K VIP

***

***