❤️‍🔥LOVE LEET HEATE ❤️‍🔥 Where Love Meets Revenge Two Hearts, One Secret Between Love and Hate A Dangerous Love Story When Hearts Collide Love Was Never the Plan From Hatred to Forever 🥹❤️

❤️‍🔥LOVE LEET HATE ❤️‍🔥

by @angelbossauthor

❤️‍🔥LOVE LEET HATE ❤️‍🔥

By Maryam sulaiman 

miss Nasir ♥️ ✍️ 

[27_9_2026_ 9:00pm]

Chapter 13&14


Ya kafa hula da agogon sa na azurfa ya manna son glasses dinsa Wanda ke Kara fito masa da kyawun sa na ainihi Sai baza kamshi yake ga black shoes dinsa Sai kyalkyali yake.
Kaga Yadda kafiya kuwa Man wllh so nice 👍 yafada Yana masa alama da hannun sa banza yayi masa ya fito daga dakin shima ya biyoshi a Baya 

A cikin masalacin unguwar za a daura auren idan an idar da sallah jama'a 

DANA 
Tunda garin Allah ya waye take kuka taki saunawa Saida hajiya kaka tazo tamata fata fata kamin ta zauna aka Mata ja da bakin lallen a hannunta a kafa kuma aka Mata shima ja da bakin Dan Zane ga kwalta tayi dodar😂

Bayan angama Sidra ta wanke Mata kanta da mayukan wanke Kai masu kamshin tayi Mata gyaran Kai saboda shine Sana'ar ta 
Nantake bakin sitik din sumar ta wacce har tsakiyar bayanta ta fito tai kyau Sai kamshin take aka hada Mata ruwan turare take tayi wanka.

Duk fa wannan abin da akeyi tana kuka akeyi bayan tayi wanka a kazo makeup 
Nanfa ta tara jama’a a kanta saboda Sam hawaye yaki tsayawa a idonta haka Sai simple makeup akayi Mata 

Lasce ta sanya maroon colour yasha dinki na alfarma SE walwali yake alama ta dauri mai Kyau Nanda Dana tafito amarya sak aka Lulubeta da lafaya mai mai tsawo Sai hutuna Ake Mata Amma fa hawaye sunki tsayowar😂

Masallacin

Sanar WA aka farayi Andaura Auren
MUNAWWARA MU’AZU DA MAHABUB SULAIMAN akan sadaki Naira dubu Dari biyar 500,000….

Masu karatu Andaura fa hhhhhh Akwai showwww wllh😂💃💃🤸🤸

Bayan daurin auren angwaye suka tafi gaisuwar surukai duk Yadda mahabub yaso yazame Mu'allim yaki bashi dama haka babu Yadda ya iya suka tafi tare 
Da Hajiya suka fara yin Karo kallon take bin mahabub dashi daga Sama har Kasa sannan ta tabe baki 
Wllh anji kunya mahabubu Saida aka daura auren za aga idannun ka saboda rashin ta Ido Kai ga Ango kana Jiran Kai maka yar cikin Ka haikemata ko 
Ya ya furta Yana sukuyar dakai Kai wllh kama dena sukuyar da Kai kamar na Allah kanan sumi sumi dakai kamar na Allah Sai shegiyar jaraba to wllh kafita idona nadanna kiraka awaya zance Kadan turamin kudi nakar da na hannuna Zan Dan siya wasu Abubuwa saboda Kar kajita lami kace ai laifin mune, kama ki dauka saboda ga sa’ar Ka takiraka ko.

Ina Kasa take Mahabub ya nutse jiya ke duk duniya Bai taba Jin kunya ba Irin na ya'u abokan sa kuwa inbanda dariya babu abinda suke sunajin dirima tsakanin jika da kaka, kallon su Hajiya tayi tace kude ringa masa fada ya rage bakar zuchiyar. Tafada tana wucewa abita ko a gyalenta

Kai Dan iskan muje, kayi wani poster ko kulasu Bai ba yawuce Sai iya shege su kemar har dakin mummy suka je suka gaisheta sannan suka fito aka nufi wajen walimar da Mu'allim ya hada, tun suna hanya mahabub ke jifan Mu'allim da mugun kallo saboda yasan duk Shirin sane Bai kulashi ba har suka karasa wajen walimar Daya cika da mutane Mata da Maza kowa bangaren Shi daban ne.
Ga amarya ansha lilibi sosai manyan kalamai suka fadakar suka bayyana hakkin Mata akan mijinta shima shima hikkinsa akanta sosai Kan Dana ya kulle Jin wai Yana da hakkin akanta tsaki tayi a kasan ranta tana cewa wllh inde zanga hakkinan to ko zai mutu bazan bashi na

Karfe 6:00 aka tashi daga walimar kasancewar ba yaune amarya Zara tare ba yasa suka kaita gidan Abbun ta 
Hajiya kaka na parlourn taga shigowa Sidra da Dana suna tafe suna na kuka 😭 
Kai nifa bana son Iskanci nakece gida Daya zaku ba wannan gabjejen yayan naki zata aura bane to wllh Kar nakarajin anamim kuka a gida saboda ba mutuwa a kayi sunnar ma’aiki muka hada, karmaji Kar nagani ato tafada sake gyara zaman glass dinta.

Mahabub Dan Allan kayi hakuri kaje wajen dinner friends Dinka zasu tafi da maganar auren dole aka yi maka, so what? Su fada mana ai dama auren dolen akamin idan ba auren dole na Mai zanyi da wannan yar jinjirar yarinyar wacce idan nayi aure da wuri inada yar like ita so Dan anfada ma, I don't care yafa Yana daga kafada kafa alamar bai damuba,
Please Man karamin haka badan niba kodan darajar iyayen da suka hada.

Jikinsa yayi sanyi Jin abinda Mu'allim yace saboda yasan darajar iyayen sa so komai sukace yayi insha'Allah zaiyi inde Bai kauce wa Shari'a na, okay zanje 
Ooh my friend! are you sure, yeah I'm sure okay thanks Bari naje mugama Lauren shirye shiryen kafin indawo Ka tabbatar kagama abinda zaki okay 
Ko kallon sa baiyiba ya wuce bedroom din sa Zama yayi Yana mai daukan laptop dinshi yafada daga Yadda ya dakata.

Haba jama'a nifa kunga banason tashin hankali banason gutsiri tsoma Sai mainene Dan Mata kunshin gargajiya Ku Yan zamani bakusan amfanin shiba to insha'Allah Sai munawwara tazo tana gode mini shine akazo aka kafani ana yankar namana to Maza kowa yatashi yatafi gidan ubansa dama mi bamu gayyaci kowa, Sidra ce tamike tafara bawa hajiya hakuri, please hajiya kiyi hakuri mana bafa gulmar ki ake ba, Keeee mai sunan aljanu ki kiyayeni anfada Miki ni kurmiyane zakice ba gulma ta ake ba to Maza Maza hada Kansu su barmin gida.

Wai ni hajiya da kike tacewa abar Miki gidan ki tayaya yazama gidanki ba gidan uncle bane gsky mukum babu Yadda zamuje, lailahaillahu Muhammada Dan Abdullahi Dan Abdul mudallabi Dan hashimu ni ni Mai sunan aljanu zaki dinga zagi? Nifa wllh ba zagin kinaiba kawai nace baza mubar gida ba saboda ai ba gidan kibane, ehy Annabin yayi gaskiya to Bari uban naki ya Shigo ya'u a gidan koni ko Shi idanma wannan tsomo logon mijin naki ke hure maki kunne ko uwar take zasuzu simin bayani tafita tana kaza jajanta zancen.

8:30 kowa yayi Shirin tafiya wajen dinner yayinda amarya Dana ke zaune ana yayyarfa Mata makeup Amma abinnata Bana Kare bane domi kuka fa yaki karewa 
Saida mummy tayi da gaske kafin ta tsaida hawayenta shirye take cikin wedding dress white colour masu sheki ga gashinna nata yasha gyara Sai kelli yake gashi ammasa stely mekyau an rabashi
3 stely ansanya gel an kwantar dashi idan kaga amarya kamar Ka saceta a hip's dinnane kamar su fito suyi magana a haka motocin daukan amarya suka karaso.

Fita da ita akayi ana sanya ta a wata haddiyar mota wacce ta lashe kudade da yawa iya ita tashiga kawaye suka Shiga sauran motocin aka dauki hanyar holl dinda za a gudanar da biki
Sani sassanyan kamshine mai tada hankali abokin tarayya ya daki hanci sa a razane ya dago ya sunan ta Jin Yadda tsikar jikin sa ta mike lokaci guda ga wani irin sanyi da yafara ji one time.

Keee yakira sunan ta! A gigice ta juyo saboda ita bata taba tinanin Akwai wata halittar bayan itaba idanuwan sane suka sauka a cikin Mata babu shiri ta sukuyar da Kai. Wai akace tashin senses to ya'u fa mahabub ya Shiga tashin senses Wanda ba’a samasa date domin kuwa ba karamin kasara masa gabban jiki kamshin turaren ta keyi ba ga wani yanayi da Bai taba riskar kanshi a ciki ba Yana Neman samun Matso guni a jikinsa..

end of free page 

to be continued..

MISS NASIR ♥️ ✍️