Chapter 3
by @fulani2
Kira ya shigo wayarsa. Mirginawa ya yi tare da miƙa hannunsa gefen da wayar take, ya janyo wayar. Sunan Nabila ya gani. Ya yi tsaki tare da ajiye wayar. Ya sauko daga kan gado, banɗaki ya shiga ya yi wanka. Ya fito yana shafe kansa da ƙaramin tawul. Aka sake kira. Ya matsa wajen gadon yana dubawa, Nabila ce dai. Tsaki ya sake yi a karo na biyu yana faɗin,
“Idan har ba ɗagawa na yi ba, yarinyar nan ba za ta bar ni na huta ba.”
Gab da kiran zai tsinke ya ɗaga kiran tare da danna amon muryar wayar. Ya ajiye a kan madubi ya buɗe man shafawarsa yana shafawa. Cikin raunanniyar murya ta ce,
“Me ya sa ko yaushe kake son wahalar da zuciyar da ba ta san komai ba bayan soyayyar ka? Uhm! Yaya Hafiz, laifi ne don ina son ka da har na zama abar wufantarwa a wajen ka?”
Lumshe idanunsa ya yi ya ja numfashi tare da furzarwa a hankali. Cikin sassanyar muryarsa ya ce, “Nabila, ya kamata ki fahimce ni. Ba wai ina wufantar da buƙatarki ba ne domin hakan ya zama wulaƙanci. Kin sani ni mutum ne da ba na son ɓata lokaci a kan abin da ba zai zama tabbataccen abu a rayuwata ba.”
Ya ɗan yi shiru kafin ya ci gaba da faɗin, “Don me zan yaudare ki da abin da babu shi a zuciyata? Ke ɗin ƙanwata ce saboda ƙanwar abokina ce. Don haka ki yi haƙuri ki tsaya a wannan matsayin, ba wancan matsayin da babu shi a raina ba. Yaudara ba halina ba ne, ba kuma zan fara a kan ki ba. Don haka ki yi haƙuri, ina miki fatan alkhairi.”
“Ya…”
Tsinke kiran ya yi yana faɗin, “Kanana da ku tun kafin ku tafasa kuke son ku ƙona. Banda fitsara irin ta wasu matan yanzu, mace ce take buɗe baki ta fara taran namiji da kalmar so. Mtsw! Allah ya kyauta!”
Nabila ta ji ɗib. Janye wayar ta yi daga kunninta tana kallon wayar. Hawaye masu zafi suka zubo a kan fuskarta. Zama ta yi gefen gado ta fashe da kuka.
‘Wace irin ƙaddara ce wannan? Zuciyarta sam ba ta mata adalci ba, da har ta rasa wanda za ta so sai wanda sam bai san darajar so ba, wanda bai san darajar zuciyar masoyi ba. Mutumin da kansa kawai ya sani, bai damu da damuwar wani ba.’
Ƙaninta Fa’iz ya shigo ɗakin da gudu yana faɗin, “Aunty Nila, Yaya na neman ki.”
Ya yi turus ganinta zaune tana kuka. Juyawa ya yi da sauri ya samu Safwan zaune a kan kujera yana ƙoƙarin sauya tasha.
“Yaya, Aunty Nila kuka take?”
“Kuka?” Safwan ya maimaita kalmar kukan cikin mamaki. Tashi ya yi ya nufi ɗakin Nabila. Ya samu har yanzu tana zaune tana kuka. Zama ya yi gefenta tare da kai hannunsa ya dafa kafaɗarta. A tsorace ta juyo. Ganin yayanta ya sa ta yi ajiyar zuciya tare da kwantar da kanta a kan kafaɗarsa.
Cikin damuwa ya ce, “Me ya faru? Me yake damun ki?”
Cikin shisshiƙan kukan ta ce, “Yaya, Yaya Hafiz ne.”
Cikin tsoro ya ce, “Wani Hafiz ɗin?”
“Abokin ka.”
Ɗago ta ya yi daga jikinsa yana kallonta ido cikin ido ya ce, “Me ya miki? Kenan ba ki ji maganata ba ko?”
Ƙasa ta yi da idanunta. Cikin rauni ta ce, “Ka gafarce ni, Yaya Safwan. Na kasa tanƙwarar zuciyata ne kamar yadda ka umurce ni, har sai da na faɗa masa sirrin da yake ƙasan raina. Sai dai tun da na faɗa masa, gaba ɗaya ya sauya min. Na rasa ta yadda zan shawo kansa. Zuciyarsa, yadda ka san zuciyar ɗanƙo, hakan take da wuyar tanƙwaruwa.”
Cikin jin haushi ya ce, “Me ya sa ba ki jin magana, Nabila? Ai shi kenan, kin je kin zubar da mutuncinki kin yi farin ciki ko?”
Ya miƙe tsaye yana ci gaba da harararta ya ce, “Bari ki ji, yanzu haka an tsayar masa da mata, ‘yar’uwarsa. Don haka sai ki natsu ki kama kanki, ki kuma fidda rai da abin da yake gaibu ne a gare ki.”
Yana gama faɗa ya fita daga ɗakin, cike da haushin ƙanwar tasa.
Tunda zancen tsayar da matar ya faɗa kunnenta, bugun zuciyarta ya ƙaru tamkar zuciyar za ta fasa ƙirjinta ta fito. Wani irin sanyi da ba ta taɓa ji ba ya ziyarto jikinta, sai karkarwa take. Kwanciya ta yi a kan gado ta janyo bargo ta lulluɓe jikinta. Hawayen idanunta suka tsaya cak, sai zugin yaji da take ji suna mata. Wani irin so take wa Hafiz da har take ji a ranta, idan ta rasa shi za ta iya mutuwa. Shi ɗin tamkar ma’aunin rayuwarta ne.
Da dare suna zaune suna ɗan hira a falon Daddy bayan sun idar. Daddy ya ɗauke ruwan gora ya kafa a bakinsa ya sha. Bayan ya sha ya ajiye yana kallon Hafiz ya ce, “Hafiz, me ya yi saura a kammala asibitin naka?”
Ajiye cokalin hannunsa ya yi yana faɗin, “Daddy, dama maganar da nake so na maka kenan. Komai ya kammalu har kayan aiki. Duk abin da aka yi odar yau za su ƙarasu In sha Allah. gobe za mu ƙarasa shirya komai, In Sha Allah.”
“Ma Sha Allah. To Allah ya sa albarka a ciki. Ina ga to a saka ranar bikin buɗe asibitin watan biyu ko?”
“Hakan ya yi, Daddy. Allah ya nuna mana.”
Khadija, ƙanwar Hafiz da ba za ta haura shekara sha shida ba, ta ce, “Yaya, nima idan na gama karatuna a asibitin ka zan yi aiki, sai ka dinga biyana albashi mai tsoka.”
Dariya ya yi marar sauti yana faɗin, “Ai bakinki ne mai tsoka. Da wannan ƙwaƙwalwar taki ta kife ne za ki iya karatun likita?”
Ta turo baki cikin shagwaɓa ta ce, “Kin ji shi ko, Momy? Ni ce mai ƙwaƙwalwar kife, ni da nake yin ta biyar.”
“Ƙyaleshi, Khadin Momy ba kya ma son asibitin ta sa ke ma ta ki za a buɗe miki wacce ma ta fi ta shi komai da komai.”
Cikin farin ciki ta ce, “Yawwa, Mommyna. Hakan ya mun, kowa ma ya ji da na shi.”
“Yanzu ta biyar ɗin ne har ki ke wani faɗa irin da ji da kan nan kamar kin yi wani ƙoƙari? Ni tun da na fara karatu, daga na ɗaya sai na biyu nake yi. Don haka ki ƙara ƙoƙari idan har kina so ki zama likita. Karatun likitanci ba na marasa ƙoƙari ba ne, na masu ƙwaƙwalwa ne.”
“Uhm, Yaya, zan baka mamaki kuwa. Na tabbata ko matar nan taka ‘yar ƙauye ba za ta fini ƙoƙari ba.”
Cikin faɗa Daddy ya ce, “Idan na sake ji kin ce da ‘yar’uwarki ‘yar ƙauye, sai ranki ya ɓaci. Kin ji ko?”
Gyaɗa kanta kawai ta yi ba tare da ta sake cewa komai ba. Hajiya Turai ta ɗaure fuska. Har a cikin ranta ta ji haushin Daddy. A kan me zai yi wa ‘yarta faɗa a kan bagidajiyar yarinyar nan?
Kallon Hafiz Daddy ya yi kafin ya ce, “Ka fara shirin aurenka, don ba na so a ɗauki dogon lokaci. Wata biyu ko uku da fara aikin ka sai a yi bikin.”
Hafiz ya kai dubansa wajen da Hajiya Turai take a zaune. Ai kuwa ta sake ɗaure fuska. Daddy ya kula da yanayin Hajiya Turai. Hakan ya sa ya miƙe tsaye.
Hafiz ya ɗaga kai ya kalleshi zai yi magana. Daddy ya ɗaga masa hannu yana faɗin, “Ni zan fita. Ka kasance cikin shiri. Wata biyu masu zuwa, In Sha Allah, za a yi bikin naku.”
Ta shi ya yi ya bi bayan Daddy yana amsawa, “Daddy.”
Bayan fitar su, Hajiya Turai ta ja numfashi ta furzar da ƙarfi.
“Lallai, wato Alhaji so yake ta ƙarfi sai an yi auren nan. Shi kenan, a yi auren wallahi. Daga ita har uwar ta, sai sun yi dana-sanin auren.”
“Momy, ina bayan ki. Kina ganin yadda tun kafin yarinyar ta zo Daddy yake yi min faɗa kamar zai dakeni. Ni wallahi har na ji na tsane ta tun kafin ta zo. Wannan ai inaga idan ta zo raba mu da Daddy za ta yi, kamar ma ya fi sonta da mu wallahi.”
Cikin takaici ta ce, “Barni da su, Khadija. Ai uwarta ta san wace ce Turai. Da ni da uwarta kar ta san kar ne. Na tabbata ba za ta yi gigin kawo ‘yarta gidana a matsayin sirika ba. Idan har kuma ta yi wannan gangancin, tabbas ta san abin da ta yi!”
Gyaɗa kai Khadija ta yi cike da gamsuwa da kuma jin daɗi. Dama tun suna yara ba shiri take da Zhara ba. Ta tsane ta, haushinta take ji, yadda gaba ɗaya ta fi ta kama da Daddyn ta. Lokacin idan ta zo hutu gidan, kowa ya ganta cewa ya ke sak Daddy. Shi kuma Daddy rasa ina zai sa ta yake, kawai don tana da sunan Maman su Daddy. Ta ƙudurci a ranta, matuƙar Zhara ta auri Yayanta, sai ta ɗanɗani kuɗanta a wajenta.
A ranta tana jin son Hafiz fiye da tunanin mai tunani, sai dai kuma kunyarsa take ji. Gayan hakan ya sa take kasa sakin jikinta da shi. Idan ya kira waya, daga “eh” sai “a’a”, hakan zai ƙara ta surutunsa ya gaji su yi sallama. Idan ya zo, ba ta wani sakewa da shi. Sai dai duk zuwan da yake, suna samun saɓanin haɗuwa da Halima. Hakan ya sa har yanzu ba su ga juna ba. Koyaushe ba ta da labarin da ya fiye yi mata daɗi irin zancen Hafiz. Wani irin so take masa da ba za ta iya kwatanta irin sa ba.
Tafe suke a kan hanyarsu ta dawowa bikin ƙawarsu Zainab. Zhara ta ce, “Shi kenan, kamar yadda Zainab ta rasa damarta ta karatu ta yi aure, hakan za ta kasance da ni.”
“Waye ya faɗa miki hakan? Ai ba za ki haɗa kanki da Zainab ba. Dama ita kin sani, tun a makaranta ta sha faɗa aure ne babban burinta, ba karatu ne a gabanta ba. Ke kuma kina da burin karatu. Na tabbata daga Yaya Hafiz har shi kansa Daddy, ba wanda zai hana ki karatu. Dukkansu ma su tsaya miki tsayin daka ne wajen ganin burinki ya cika.”
“Uhm! Allah ya sa. Kin san me? Ina son karatuna sosai, amma kuma son da nake wa Yaya Hafiz, idan har ya ce ba ya da ra’ayin na yi karatu, tabbas zan iya haƙura da burin karatuna, na ajiye shi a gefe.”
Halima ta jinjina kai tana faɗin, “Na sani ai wallahi. Ki dinga kama kanki, Zhara, wannan lokacin da muke ciki, ba a yi wa namiji irin wannan son, domin su ɗin ba tabbas ne da su ba.”
“Na yarda maza ba su da tabbas, amma ba duka aka taro aka zama ɗaya ba. Ina da kyakkyawan zato da yaƙini a kan ɗan’uwana Hafiz.”
Dariya Halima ta yi kafin ta ce, “Uhm! Ke dai ki dinga sassauta zuciyarki, kar ki yi zurfin da ba za ki iya yin iyo ba, da za ki fitar da kanki. Shi kenan, tunda har kina musu a kan Yaya Hafiz, zo ki ji…”
Halima ta tsaya gaban Zhara tana murmushi ta ce, “Ba za ki iya ba.”
“Zan iya mana. Ai da ba zan iya ba, da ba zan faɗa ba.”
Gyaɗa kai Halima ta yi. Suka ci gaba da tafiya suna ci gaba da firar Hafiz.
Maman Zhara sosai ta shiga damuwa. Ta rasa ta wace hanyar za ta bi don ta rusa maganar auren nan. Ba ta isa ta nunawa Baban Zhara ba ta so ba, ta tabbatar ko auren ta za ta iya rasawa a kan maganar. Ta kuma fuskanci Zhara na son Hafiz duk da ƙoƙarin ɓoyewa da take. Sai dai shi so abu ne da ko ka so ɓoyewa, ba zai ɓoyu ba. Dama Hausawa su kan ce a tambayi fuska labarin zuciya. Don haka fuskarta da yanayinta ba za su ɓoye abin da yake zuciyarta ba, duk da ƙoƙarin hakan da take.
Ba ta da wata mafita da ta wuce ta dage da addu’a, domin Allah kaɗai ne zai kawo mata mafita. Amma har cikin ranta tana jiyewa Zhara tsoron zama da Hajiya Turai.
Da yamma bayan ya fito daga asibiti a gajiye, ya je liƙis. Don yau C.S uku ya shiga ga marasa lafiya da ya duba sosai. Ya so ya wuce gida ya samu ya huta, sai dai ba yadda zai yi. Dole ya biya ta gidan su Safwan ya duba mahaifiyar Safwan da ba ta jin daɗi. Hakan ya sa ya karya kan motarsa zuwa Fage, gidan su Safwan.
A ƙofar gidan ya yi parking. Ya fito. Motar Safwan ta fito cikin gidan. Ganin Hafiz ya sa ya yi parking gefen motar Hafiz. Ya fito yana murmushi ya ce, “Fitowar nan da na yi, Allah asibiti zan je wajen ka.”
“Lallai kuwa da ka dake garwa. Daga can na fito, na ce bari na zo na duba jikin Mama.”
“Ok, mu ƙarasa ciki. Mama ta ji sauƙi. Ka san asma, lokacin ruwan sama ya fi matsa mata.”
Suna tafiya ya ce, “Hakan ne. Allah ya ba ta lafiya. Akwai wata allura, In Sha Allah, idan har aka dace za ta samu sauƙi sosai. Ciwon sai dai ya zama tarihi.”
“Gaskiya da na ji daɗi wallahi. Ciwon yana matsa mata. Kaga jiya babu wanda ya yi tsammanin za ta waye gari, irin yadda numfashinta ya dinga kai da kawo.”
Suka ƙarasa cikin babban falon da sallama a bakinsu. Rufaida da take zaune a kan kafet tana gyaran farcen hannunta ta amsa sallamar cikin fara’a ta ce, “Sannu da zuwa, Yaya Hafiz. Ina wuni?”
“Lafiya lau. Rufaida, ya gida? Ya karatu?”
“Alhamdulillah, Yaya.”
Zama suka yi a kan kujera. Safwan ya ce, “Je ki kira Mama.”
“To,” ta faɗa tare da miƙewa tsaye.
Bayan ta kira Mama ta tafi ɗakinsu da sauri. Ta samu Nabila tana kwance a kan gado tana kallon hotunan Hafiz a wayarta. Fatima tana zaune, ‘yar Rufaida tana zaune a kan kafet tana karatu.
Rufaida ta kai wa Nabila duka tana faɗin, “Albishirinki!”
Nabila ta harare ta tana faɗin, “Shi ne kuma don za ki yi min albishir sai kin dakeni? Yarinyar nan, ba ƙaramin raini ne ya shiga tsakanina da ke ba wallahi.”
“Aunty, masifa! Aunty, son girma kamar gyanmbo. Duka shekara ɗaya da ‘yan kai ne fa tsakanina da ke. Babu dole ma na kira ki da Aunty, kawai dai don Yaya Safwan ya tilastani ne. Ke ma kin san da ba ki kai na kira ki da Aunty ba.”
Tashi ta yi da sauri za ta kai mata duka. Rufaida ta kaucewa dukan. Cikin faɗa Nabila ta ce, “Daɗin abin dai ko da kwana ɗaya ne, na riga wata shan iskan duniya. Ki riƙi Aunty, ban so marar kunyar banza kawai!”
“Shi kenan. Dama abin da kike so na zo na faɗa miki. Tunda kika min masifa, na fasa faɗa miki sai bayan wucewar abin. Idan kuma na faɗa daga baya, kar ki ga laifin kowa, ki ga laifin ki.”
Ta juya za ta fita da sauri. Nabila ta janyota cikin lallashi ta ce, “Yi haƙuri, ƙanwata ƙawallina. Faɗa min me ya faru, in har albishir ɗin mai daɗi ne, zan ba ki goro na musamman.”
Murmushi Rufaida ta yi kafin ta ce, “Kin yi alƙawari ko me na ce ina so za ki bani?”
Cikin gyaɗa kai ta ce, “Na yi. In dai abin da za ki faɗa ya kai na baki, duk abin da kike so ɗin zan baki.”
“Na ma san za ki bani ɗin don ya kai. Yaya Safwan ne ya zo tare da Yaya Hafiz.”
Zuciyarta ta bada dum! Ta kafe Rufaida da idanu, har ma ta rasa me za ta ce da Rufaida.
“Ya dai, Aunty Nabila?”
Cikin sanyin murya ta ce, “Da gaske kike, don Allah?”
“Wallahi da gaske nake. Yanzu haka suna babban falo.”
Ta fita ɗakin da sassarfa ta nufi falo. Fatima ta tashi da sauri tana hararar Rufaida, ta bi bayan Nabila. Gab da za ta shiga falon ta riƙo hannunta. Ta juyo da sauri ta ga Fatima.
“Me ye?”
“Aunty Nabila, tare suke da Yaya Safwan fa. Kin manta gargaɗin da Yaya Safwan ya miki kafin ya fita? Kuma ya kamata ki dinga tuna ke ɗin mace ce da Allah ya yi wa tarin daraja. Sannan mace ana so kunya ta zama ado a gare ta. Kar ki bari zuciya ta dinga rinjayar ki ko yaushe, tunani ya rinjaye zuciyarki, Aunty Nabila.”
Shiru Nabila ta yi tana kallon Fatima, yayinda zuciyarta da tunaninta suke kai da kawo. Ta rasa makamar ɗauka, yayinda zuciyarta ta zaƙu da son ganin abin da take so. Tunaninta yana tuna mata gargaɗin da Yaya Safwan ya mata. Komai zai iya faruwa idan har ta ƙi bin abin da zuciyarta take so ko kuma ta tsallake umurnin Yayanta.
Fulani