KUSKUREN WAYE?

Chapter 4

by @fulani2

Hawaye ne suka ciko a idanunta. Ta lumshe idanunta tana tuna maganar yayanta kafin ya fita. Ta fito cikin shiri, tana sanye da doguwar riga na les baƙi mai ratsin duwatsu. Ta sa ƙaramin mayafi ta yafa a kafaɗarta, tana riƙe da jaka. Ta shiga ɗakin Mama, ta samu Mama na kwance a kan gado. Zama ta yi gefen gado tana faɗin, “Mama, ba dai jikin ba?”

Tashi Mama ta yi ta zura ƙafafunta ƙasa ta ce, “Jiki kam Alhamdulillah ya yi sauƙi, sai ɗan abin da ba a rasa ba. Na dai kwanta ne, numfashina har yanzu bana jin shi daidai.”

Cikin damuwa ta ce, “Ubangiji Allah ya ƙara lafiya, Mama.”

“Amin ya Rabb. Ina zuwa naga kin shirya?”

“Mama, kin manta da safe na faɗa miki zan je gidan su Yaya Hafiz wajen Khadija?”

“Eh, na manta sam. Allah ya tsare ki. Gaida Momyn ta su.”

Ta miƙe tsaye tana faɗin, “Za ta ji, Mama.”

Ta juya za ta fita, suka yi ido biyu da Yaya Anwar da yake a tsaye bakin ƙofa. Ya watsa mata wani kallo da sai da ta ji hanjin cikinta sun murɗa. Ƙasa da idanunta ta yi ta ce, “Ina wuni, Yaya?”

“Lafiya,” ya amsa mata a gajerance.

Sumai-sumai ta yi ta bi ta gefensa za ta fita. Ya ce, “Ki jirani a falo.”

Rintse idanunta ta yi. A ranta tana faɗin, ‘Shi kenan, sarkin takura, yanzu sai ya hana ni fitar nan.’

Zuwa ta yi ta zauna a falo. Fatima tana zaune a kan kafet tana kallon TV. Bai jima ba ya fito. Zama ya yi a kan kujerar da take fuskantar ta. Ya kafeta da idanu, fuskarsa babu annuri, ya ce, “Yanzu Nabila, wuyanki har ya yi kaurin da za ki dinga zuwa wajen saurayi?”

Fito da idanunta ta yi cikin tsoro ta ce, “Ni Yaya, waye ya faɗa maka wajen saurayi zan tafi? Wallahi ko waye ya faɗa maka, sharri ya min.”

Yana harararta ya ce, “Sakaryar banza! Yanzu me na ji kina faɗawa Mama?”

Shiru ta yi tare da yin ƙasa da kanta.

“Ba tambayar ki nake ba!”

Fatima ta rage muryar TV ta mayar da hankalinta a kansu. Ta kasa kunne don jin abin da ake faɗa.

“Ka yi haƙuri, Yaya. Gidan su Yaya Hafiz na ce zan je, amma ni ba wajen shi zan je ba, wajen Khadija zan je.”

Gyara zaman shi ya yi kafin ya ce, “Nabila, ke mace ce ki riƙi mutuncinki na ‘ya mace. Ballagazar mace ce marar ta ido, ita ce take bibiyar namiji a duk inda yake, ko da yana sonta, bare ke da ba kya ma gabansa.”

Ya numfasa kafin ya ci gaba da magana, “Hafiz abokina ne, mutumin kirki ne, tabbas nagartaccen mutum ne da zan so a ce aurenki da shi ya yi. Amma fa idan shi ne ya ce yana sonki, ba wai ke ki dinga zubar da darajarki kina bin shi ba. Don haka daga yanzu na hana ki bibiyar shi, ciki kuwa har da kiran waya. Idan da rana ɗaya na ji kin neme shi ko kin je gidan su, ke ko ta ina ne, wallahi ranki in ya yi dubu sai ya ɓaci!”

Ya miƙe tsaye ya je gabanta ya murɗa kunnenta. Ta rintse idanunta da ƙarfi saboda azabar zafin da ta ji.

“Kin dai ji me na faɗa miki ko?”

Cikin muryar kuka-kuka ta ce, “Eh, na ji. Zan kiyaye.”

“Yawwa, kin taimaki kanki.”

Ya wuce ɗakinsa. Ta tashi ta bar wajen da gudu, ta bar falon. Fatima ta bita da kallo tana girgiza kanta. A ranta ta ce, ‘Iska na wahalar da mai kayan ƙara. Allah, kar ka jarabce mu da abin da ba za mu iya ba.’

Ta ɗauki remote ta ƙara muryar TV ta ci gaba da kallonta.

Tana zuwa ɗaki ta faɗa kan gado ta kwanta rigingine. Sai da ta yi kukan ta mai isarta. Ji take kamar zuciyarta za ta fashe. Wani irin so take wa Hafiz, tana ji a ranta idan har ta rasa shi za ta iya rasa ranta.

Tashi ta yi ta sauya tufafin jikinta ta dawo ta kwanta. Ta ɗauki wayarta tana duba hotunan. Fatima ta shigo ɗakin ta zauna a kan kujera tana dannar waya. Rufaida ta shigo ta faɗa mata zuwan Yaya Hafiz.

Ta ja numfashi ta furzar. Juyawa ta yi ta koma ɗaki, zuciyarta na mata wani irin zafi. Suka bi bayanta, zuciyar Fatima cike da tausayin ‘yar’uwarta.

“Ya Allah, ka rabamu da son ma son wani.”

“Amin dai. Ai kam Aunty Nabila tana fama da aiki, son cusa kai babu ƙwarjini,” Rufaida ta yi maganar ƙasa-ƙasa.

Fatima ta harareta ta ce, “Ai komai ya faru laifinki ne. Tana zaman zamanta kika zo kika faɗa mata. Da ba ki faɗa ba, da har ya tafi ba ta ma san ya zo ba. Yanzu kin zo kin ƙara mata damuwa.”

Tana yatsina fuska ta ce, “To, kanwa uwar haɗi, ni me ye nawa? Don naga abin da take so ta gani na zo na faɗa mata, shi ne kike so ki yi munafunci?”

Cikin masifa Fatima ta ce, “Ni kike kira da kanwa uwar haɗi, munafuka?”

“Eh ɗin, ko ƙarya na faɗa?”

Ta yi maganar cikin gatsini.

“Wallahi ni kin san ko wa ya ci tuwo da ni, tabbas miya ya sha. Kin sani, da ni da ke kar ta san kar ne. Wallahi yanzu sai na naɗa miki na jaki!”

“Hihihi!! Wallahi sai dai mu naɗawa juna na jaki. Ki daina ganin wannan jikin naki ki ɗauka za ki ɗibi wani abu a jikina. Ƙarfi ba daga jiki ba ne, abu a zuciya yake.”

“Dalla can! Ku fitar min a ɗaki, banzaye! Koyaushe ba ku da aiki sai faɗa kamar wasu kaji!”

Rufaida ta kai wa Fatima duka ta arce na kare, ta fita ɗakin a guje.

“Bala’i! Ni kika daka? Wallahi za ki sani. Bari su Yaya su bar gidan nan sai jikin ki ya faɗa miki!”

Ta yi maganar ranta a ɓace ta koma ta zauna a kan kujera. Ko ta kansu Nabila bata saki bi ba, ta koma ta kwanta a kan gado. A ƙuntace take jin zuciyarta.


Shiga office ɗinsa ya yi a gajiye. Ya zauna a kan kujera ya yi miƙa. Ya ɗauki wayarsa, ya ga kira sosai, ciki har da wata number da har ta fara zama a kansa saboda yawan kiran da ake masa da ita. Tun yana ɗauka ana masa shiru har ya gaji ya daina ɗauka.

Ya buɗe WhatsApp ɗinsa. Kai tsaye saƙon number ɗin da aka kira shi da ita ya fara buɗewa. Ciki da zaƙuwa ya rasa me ya sa yake matuƙar zaƙuwa da ta turo masa saƙo. Abin da kawai ya sani, saƙonninta suna matuƙar saka shi farin ciki, duk da bai santa ba, bai taɓa jin muryarta ba, bai taɓa ganinta a zahiri ba, sai dai a hotunanta da take turo masa.

Kyakyawa ce. Tana da diri irin kalar macen da yake da burin aure. Kenan, cikin shauƙi ya fara karanta saƙon.

“Ina son ka, My Noor. Zan kuma ci gaba da sonka har abada. Ina ciki da shauƙin kasancewa a tare da kai a matsayin miji da mata. Ina addu’a Allah ya sa ka zama mijina, uban ‘ya’yana. Haƙiƙa da na fi kowace mace sa’a da samun nagartaccen miji kamar ka, wanda yake matuƙar wahala a wannan zamanin. Ina SON KA da dukan raina, My Noor.”

Lumshe idanunsa ya yi ya kwantar da kansa jikin kujera, yana jin wani irin bugun zuciya da bai taɓa jinsa a ransa ba a kan mace. Ya buɗe su a hankali. Ya buɗe hotunan da ta turo masa, da video tana bin waƙa cikin natsuwa da shauƙi. Ba rawa take ba, a zaune take a kan kujera tana juya idanunta, haɗi da lumshe su tana buɗewa a hankali da murmushinta mai ɗaukar hankali sosai.

Ta tafi da imaninsa. Wannan ita ce sahihiyar macen da yake siffantawa da kuma mafarkinsa.

Wani saƙo ne ya shigo. Da sauri ya fara karantawa:

“Amincin Allah ya tabbata a gare ka, My Noor. Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya? Gaskiya na ji damuwa sosai, har sai da idanuna suka zubar da hawaye saboda gaba ɗaya yau ban ga ka online ba. Kuma na kira wayarka ba ka ɗaga ba. Har na fara jin tsoron ko lafiya? Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya. Ka kula min da kanka, Annurin Zuciyata.”

Yana so ya tura mata amsa, sai dai tuna baikon ‘yar’uwarsa Zhara ya kan katse masa hanzari. Hakan ya sa duk saƙon da take turo masa, iya ya karanta, amma daidai da rana ɗaya bai taɓa bata amsa ba.

Ci gaba ya yi da kallon videon, yana jin wani irin abu na fizgar zuciyarsa game da ita. Shigowar nurse ce ta dawo da shi daga duniyar da yake cikin. Mutuntawa ta ce, “Doctor, akwai marasa lafiya da yawa da suke jiran fitowarka ɗakin tiyata tun ɗazun fa.”

“Uhm! Ba na ce ki tura su wajen su Doctor Mujahid ba?”

“Na tura na safe. Waɗannan daga baya suka zo.”

Ya duba agogon da yake maƙale a hannunsa kafin ya dawo da dubansa a kanta ya ce, “Sister Rabi, lokacin sallah ya gabata. Amma bari na duba ko mutum biyu ne, sai na je na yi sallar azahar. Idan na dawo sai na ƙara sa duba sauran.”

“Ok, Doctor.”

Ta fita. Ya ajiye wayar yana mai yin ajiyar zuciya.


“In ka ga ruƙumi, ka ga akala, daga ina haka?”

Zhara da Halima suka yi dariya. Halima ta ce, “Aunty Laila, daga gida zuwa nan.”

Hankaɗa labulen ɗakin ta yi tana faɗin, “Lallai, yau kuma aljannun yawon gidana suka cilloku?”

Karasa shiga suka yi suka zauna. Bayan sun gaisa, ta je ta kawo musu ruwa da ɗan wake, yaji manja da yaji da kayan haɗi. Bajewa suka yi suna ci suna santi.

Zhara ta ce, “Shi ya sa muke son zuwa gidan nan, Aunty Laila. Ba kya rabu da abin daɗi.”

Dariya tayi, “Allah ya shirye ku, kamar kun san ina neman ku.”

Har haɗa baki suka yi wajen faɗin, “Ta samu kenan, Aunty?”

“Shaƙiyancin ku sai ku.”

Suna gama cin abinci Halima ta ce, “Aunty, faɗa mana wani labari ne?”

“Sarkin son jin labari kamar ‘yar jarida. Wai Halima, ba za ki fasa karantar lauya ba ki dawo jarida?”

“Banda abinki, Aunty Laila. Ai dai kusan duk abu ɗaya ne, tunda Lauya ma ai sai ya nemi labari ta yadda zai fahimci shari’ar gabansa. Yanzu dai faɗa mana mene ne?”

Cikin dariya Zhara ta ce, “Oh, Halima, son jin gulma”

“Ni fa makirci ne ba na so. Idan aka tuna zuciyarki, na tabbatar kin ma fini zaƙuwa ki ji.”

“To, sarakan musu, ya isa hakan. Dama tun ranar da kuka zo gidan nan, a kan hanyarku ta fita, idan za ku tuna kun haɗu da Abban Yasmeen tare da abokinsa?”

“Tab, mun manta wallahi. Jeki kan maganar ki kawai, Aunty Laila,” Halima ta faɗa tana gyara zamanta.

Murmushi Aunty Laila ta yi kafin ta ce, “To, abokinsa ya mun maganar. Yana son ɗaya daga cikin ku. Ya taɓa min bayani, na kasa ganewa tunda kaya iri ɗaya kuka sa. Sai da ya ce min mai hijab na gane Zhara yake nufi, tunda a cikin ku biyun dama ita kaɗai take yawo da hijab. Da farko dai na ƙyaleshi, sanin halinku na rashin kula samari, tunda ga su nan suna bibiyar ku kuna yaƙince su ta ƙarfi. To, sai matsin number yake min. Hakan ya sa na ce ya bari, zan neme ku.”

Dukansu suka ƙyalƙyace da dariya. Tana hararsu ta ce, “Au, dariya ma na baku ko?”

Halima ta ce, “Ba hakan ba ne, Aunty Laila. Aradu ki faɗa masa ya makaro, don Zhara kam an yi baiko.”

Kallon Zhara ta yi tana faɗin, “Wai haka, Zhara? Da gaske an yi miki baiko?”

Cikin murmushi Zhara ta ce, “Da gaske, Aunty Laila. Saura wata ɗaya biki.”

“Ikon Allah! Shi ne ban ji ga kowa ba.”

“Kin san kin kwana biyu ba ki je gida ba, mu ma ba mu zo ba. Zuwan da muka yi, mu faɗa miki kenan,” Halima ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa don yin alwala.

“Allah ya sanya alkhairi. Waye wannan da ya ciri tutar Zhara mai tsoron maza?”

Cikin dariya Halima ta ce, “Yayanta ne. Auren zumunci ne.”

“Ma Sha Allah. Allah ya sanya alkhairi. Bari na ce ya dawo wajanki ku daidaita.”

Har ta sa ƙafarta waje ta dawo da sauri ta ce, “To, da farko dai Amin. Sai zancen ya dawo wajena Allah Aunty kar ki suma. Ni karatu na sa a gaba, ba aure ko soyayya ba.”

“Sannu Mango Pak! Bari na je wajen Yaya, na ji idan ita ce ta ɗaure miki gindin rashin auren, sai na ji ta da toshe.”

Ta ɓata rai “Aunty Laila, kar ki sa na yi dana-sanin zuwa gidan nan, na kuma ɗauki ƙafata da gidan nan fa.”

“Allah ya baki sa’a. Idan kin sake dawowa ma ban gode ba, marar kunya kawai.”

Za ta yi magana, Zhara ta je da sauri ta turata waje tana faɗin, “Ji ki yi alwala mu yi sallah mu tafi. Kin dai san an ce kar mu daɗe.”

Bayan fitar Halima, Zhara ta dawo kusa da Aunty Laila ta ce, “Don Allah, Aunty Laila, ki yi haƙuri.”

Tsaki ta yi kafin ta ce, “Halima na da matsala. Rigimarta ta yi yawa ba dama a zauna da ita ba ta ɓata wa mutum rai ba. Ai da sai ta bari, idan ta gan shi bai mata ba sai ta ce bai mata ba.”

Haƙuri kawai Zhara ta bata. Suna yin sallah suka mata sallama.

A hanya sai mita Halima take tana faɗin, “Kaji rigima irin ta Aunty Laila. Kawai ta kwasu wani gara da ƙilama, yana fama da kayan tumbi kamar an dasa masa ‘ya’ya goma, kamar tulilin mijinta. Ta ce wai na so shi.”

Dariya Zhara ta yi tana faɗin, “Allah ya shirye ki, Halima.”

“Allah ta ban haushi ne. Idan na koma, za ta yi abin da ma ya fi wannan.”

“Oh! Halima mita, Halima rigima. Don Allah ya isa haka. Magana ta wuce, tunda dai kin faɗa mata ba kya yi ɗin.”

Ba ta dai daina mita ba. Tafiya kaɗan sai ta yi maganar. Sanin halinta ya sa Zhara ba ta sake cewa da ita komai ba.


Da dare bayan ta gama tilawa, ta ɗauki wayarta ta kunna data. Tana shiga WhatsApp saƙonsa ta fara dubawa. Gaisuwa ce da tambayar ya ta wuni. Fuskarta da murmushi ta ba shi amsa.

Yana online, suna magana sama-sama, don firar ba ta masa wani armashi, tunda ta kasa sakin jikinta da shi. A nan ya nemi da ta turo masa hotunanta. Ba musu ta turo masa masu yawa, ko wanne tana sanye da hijab, wani kuma da mayafi.

“Ke, ba kya hoto ne ba mayafi?”

Shiru ta yi tana nanata karanta saƙon. Tabbas tana da hoto marar mayafi, amma kuma ba za ta iya tura masa ba. Gaskiya ta rubuta masa:

“Eh, Yaya, duk haka nake hoto.”

Jim kaɗan ya dawo da amsa:

“Ok, ki ɗauka yanzu ki turo min. Kuma a yadda kike da kayan da suke jikinki nake so ki ɗauka ki turo min.”

Tana karantawa tana fito da idanu. Ta duba jikinta. Kayan bacci ne jikinta, rigar iya gwiwarta take, ga rigar ana ganin jikinta. Kasancewar ana zafi, shi ya sa ta sa ta. Kuma ita kaɗai take kwana a ɗakin ‘yan biyu, ɗakin Mama su ke kwana.

Kiranta ya yi ta WhatsApp. Cikin sanyin jiki kamar marar laka ta ɗaga kiran.

“Yaya.”

“Na’am. Me ya sa kika yi shiru?”

“Ba komai, Yaya.”

“To, ina jiranki. Ki turo min.”

Ɗora hannunta ta yi a kan goshinta, ta ma rasa me za ta ce masa.

“Kinyi shiru.”

“Yanzu zan ɗauka,” ta ba shi amsa tana miƙewa tsaye.

A ranta tana tunanin kawai ta yi sauri ta sauya kaya sai ta yi hoto. Kamar ya san tunanin da take yi ya ce, “A yadda kike na ce ki ɗauka. Idan har kika sauya kayan jikinki ko kika turo wanda kika jima da yi, zan gane.”

Turus ta yi ta tsaya da tafiyar da take. A ranta tana faɗin, ‘Wayyo Allah! Shi kenan ya gane. Mutum kamar aljani!’

Tsinke kiran ta ji ya yi. Ta janye wayar daga kunninta tana kallon wayar kamar za ta samu amsar yadda za ta yi daga cikin wayar ne.

Fulani