Chapter-04 (Her Dignity, Her Sacrifice)🥀
by @eshamuhd
A cikin ɗakin taron kwamitin gudanarwa (Boardroom), kowa ya fara watsewa bayan Bin Ali ya fita daga ɗakin da takunsa na ƙasaita da izza, yana mai nuna irin kwarin gwiwar da ke tattare da shi.
Mutane da dama suka riƙa magana cikin raɗe-raɗi, yayin da suke tattara takardunsu suna ficewa ɗaya bayan ɗaya. Kalaman kasuwancin da Bin Ali ya gabatar sun bar wani irin tasiri mai ƙarfi a zukatansu, har kowa ke ci gaba da nazarin abin da ya faɗa.
Hajiya Halima tana zaune cikin nutsuwa a kan kujerarta, amma fuskarta na ɗauke da alamun damuwa. Yatsun hannunta guda biyu suna dan dukan teburin gilashin a hankali, yayin da take ciza leɓenta na ƙasa, kamar wadda wani abu ke ci wa zuciya.
Idanunta sun sauya, suka cika da tsantsar takaici da baƙin ciki. Duk wani shiri da makirci da ta ƙulla domin raunana ikon Bin Ali a taron na yau, ya rushe shi nan take bayan ƴan gajerun kalamansa da suka sa kowa shiru, kafin ya miƙe ya fice daga ɗakin taron.
Hannunta ta matse a hankali, tana ƙoƙarin danne fushin da ke tasowa a zuciyarta.
“Mummy…” muryar sa fito a hankali daga bakin shi.
Jafar saurayin yarta, wanda ita ce ta shigo da shi cikin kamfanin domin ya riƙa yi mata leƙen asiri—ya katse mata tunanin da yake ta yawo a ranta.
Jafar ya ɗan matso kusa da ita, yana mai kallon ƙofar da Bin Ali ya bi ya fita. Fuskarsa cike take da takaici, kafin ya furta cikin sanyin murya:
“Yanzu ya za mu yi? Mutumin nan ya sake bata mana komai a gaban kowa.” Hajiya Halima ta juyo da sauri, idanunta cike da tsananin ƙiyayya da ɗacin zuciya. Fushin da ya cika ranta ya bayyana a fuskarta, yayin da muryarta ta fito a ƙasa-ƙasa, amma mai kaifi da ban tsoro.
“Kada ka sake kiran sunansa da ‘mutum’ a gabana, Jafar!” ta faɗa cikin tsananin ɓacin rai, tana murtuke fuska. Ta ɗan yi shiru na ƴan daƙiƙu, sannan ta ƙara da murya mai cike da ƙudurin ɗaukar fansa:
“Wannan karon, ba zan ƙyale shi ya sake cin galaba a kaina ba.”
“Tunda Alhaji Ali ya rasu ya bar wannan dukiyar a hannun wanan yaron, ban taɓa samun cikakken kwanciyar hankali ba. Wannan yaron ya zama babban cikas a rayuwata da makomar ‘yata!”
Ta miƙe tsaye da sauri, tana gyara gyalenta da lace din jikin ta mai tsadar gaske. Fuskarta cike take da fushi, yayin da take sauke numfashi mai nauyi.
“Yana tunanin ya san komai a fannin kasuwanci!?. Yana ganin babu wanda zai iya taɓa shi, saboda yana riƙe da kaso mafi girma na hannun jarin kamfanin—controlling shares.”
Hajiya Halima ta ɗan yi shiru, sannan ta saki wani murmushi mai sanyi, murmushin da ya ƙunshi mugunta da makirci.
“Amma ya manta da abu ɗaya…” ta faɗa a hankali, tana kallon Jafar da idanuwan ta da ke ɗauke da wani irin ƙuduri.
“Abin da ya ke iya rusa mutum mai girman kai irinsa ba lallai ya kasance a cikin kasuwanci ba ne. Wani lokaci, sirrin rayuwarsa na kashin kansa ne ke zama makamin da ya fi komai ƙarfi.”
Murmushin dake fuskarta ta ƙara faɗaɗawa, kamar wadda ta riga ta hango hanyar da za ta bi domin ta kai ga abin da take so.
Jafar ya buɗe baki, yana kallonta cikin mamaki yayin da yake ƙoƙarin fahimtar irin makircin da take ƙulluwa a zuciyarta. “Mummy… me kike shirin yi ne?” ya tambaya a hankali, idanun shi akanta.
“Bin Ali ba ya harka da mata, kuma ba aure bane a gaban shi, ba ya yarda kowa ya shiga harkar rayuwarsa ta kashin kansa. Wannan nisanta kansa da mata da yake ba a banza yake ba,” ta faɗa, tana matsowa daf da Jafar.
Ta ɗan rage murya, idanunta suka ƙara tsuke wa cikin wani irin ƙuduri.
“Akwai wani babban sirri da yake ɓoye wa duniya. Sirrin da ya shafi rayuwarsa ta kashin kansa. Idan kuwa muka gano sirrin nan…” Ta yi murmushin mugunta na ɗan lokaci. “To, a lokacin ne zai yi bankwana har abada da mulkin Bin Ali Holdings!”
Ta ciro wayarta daga cikin handbag ɗinta, ta danna wata lamba sannan ta sanya wayar a kunnenta. Idanunta suka yi wani irin sheƙi, cike da sabon makirci da mugun ƙuduri a zuciyarta.
“Bello… Ina buƙatar mutanenka mafi ƙwarewa wajen leƙen asiri. Daga yau, ina son a riƙa bin diddigin kowane motsi na Bin Ali, da lauyansa Taufeeq. Ina son sanin duk inda suke zuwa, waɗanda suke haɗuwa da su, har ma da inda yake samun ruwan da yake sha.”
Ta ɗan yi shiru, kafin ta saki wani murmushi mai sanyi.
“Wannan daular tasa kuwa… zan ga ko shi ne zai ci gaba da mulkarta, ko kuwa rushewa za ta yi a hannuna!”
A gefe guda kuma, a cikin ofishin Dr. Farooq na asibitin City Care...
Shiru ne mai nauyi ya mamaye office din bayan kalaman Taufeeq. Kowa ya yi gum, kamar babu wanda ya san abin da zai faɗa. Afeefa kuwa tana tsaye a tsakiyar office din, idanunta a waje saboda tsantsar mamaki da firgici. Wani irin ruɗani ya dabaibaye ta, har ta kasa tantance abin da ya kamata tayi.
A gabanta, alƙalamin da Taufeeq ya tura mata domin ta sanya hannu kan yarjejeniyar daya karanto mata ne. Duban alkalamin take tamkar wani takobi mai kaifi da ke barazanar datse mutuncinta ko kuwa rayuwar ƙanwarta Rahma.
"Sa'o'i arba'in da takwas kaɗai suka rage miki, Afeefa..." Muryar Taufeeq ta sake ratsa offince din cikin sanyi da jan hankali. "₦750,000 na aikin fiɗar Rahma za su shiga account ɗin asibitin nan a yanzu. Abin da ake buƙata kawai shine sa hannunki a kan wannan yarjejeniyar ta surrogacy saboda bin tsarin doka."
Afeefa ta lumshe idanunta da ƙarfi, tana ƙoƙarin danne kukan da ke tasowa daga kasan zuciyarta. Amma hakan ya gagare ta, sai hawaye masu zafi suka gangaro a hankali kan kumatunta.
A cikin zuciyarta, take hango fuskar mahaifiyarta wadda tun tana ƙarama ta koya mata sanin darajar mutuncinta na ‘ya mace, haƙuri da wadatar zuci. Sai kuma hoton ƙanwarta Rahma ya sake bayyana a idonta.
Ta yi tunanin abin da zai iya faruwa idan Litinin ta zo, aka kasa yin aikin fiɗar.
Wani irin ciwo ya tsaga mata zuciya. A gefe guda akwai mutuncinta, a ɗaya ɓangaren kuma rayuwar ƙanwarta da ke rataye a kan kafadunta.
A hankali, hannunta mai rawa ya miƙa zuwa kan teburin. Yatsunta suka kama alƙalamin, amma ta kasa ɗaga shi. Wani irin tsoro da ruɗani suka sake mamaye zuciyarta, yayin da numfashinta ya ƙara nauyi.
Dr. Farooq da Taufeeq suka riƙe numfashinsu, idanunsu a kafe kan Afeefa, suna bin duk wani motsi da take yi da kallo. Kamar dai wannan ɗan ƙaramin takun da hannunta ke yi ne kaɗai ya rage cikar burin BIN ALI.
Afeefa ta ɗaga alƙalamin dake dauke a hannunta ta saka hannu a kan takardar yarjejeniyar. Ta share hawayen fuskarta, muryarta ta fito a kassan makoshin ta cike da da raɗaɗin zuciya:"
“Na sa hannu ne saboda rayuwar ƙanwata… Amma Yallabai, ka sanar da mai gidan ka cewa shi yana da kuɗi da iko, ni kuma ina da mutuncina da Allah. Kada ya taɓa tunanin cewa kuɗinsa za su iya siya mutuncin Afeefa!”
Taufeeq ya yi murmushi kaɗan, sannan ya miƙe tsaye. Ya tattara takardun yarjejeniyar, ya shirya su a hankali, kafin ya sanya su cikin file ɗinsa. “Duk abin da kika faɗa zai isa gare shi. Yanzu Dr. Farooq zai gudanar da duk gwaje-gwajen da ake buƙata. Sannan gobe da dare za ki haɗu da shi ido-da-ido domin a kammala sa hannun ƙarshe.”