BOOK ONE CHAPTER 3
*ZAINAB*
Tun kafin a kira sallahn athuba tamiƙe, dama batai bacciba tsawon daren gabaɗaya.
Bayi ta shiga taɗauro alwallah tazo ta shimfida sallah ya tai raka'a tanil fijr, bayan ta idar ne aka soma kiraye-kirayen sallah.
Miƙewa tayi daga kan sallah yan ta bude kofar falon ta shiga dakin Anis da Khalid dake tsakar gida.
Tadasu tayi.
Khalid dake da shekaru goma sha uku yamiƙe yana cewa
"Mami kece..."
"Eh nine Khalid, katashi kaje kai alwallah gayican antada sallahn ma."
"Mami ina Abba yake?"
"Yarigada ya makarane shiyasa nazo da kaina"
Tana gama fadin haka tajuya abinta tasan shize tada Anis idan yafito.
Ɗakinta ta koma, ta shiga bedroom din su Ramlat ta tadasu suma sui sallah.
Irin tambayar da Khalid yemata shi Khadija tai mata, a wannan karon shiru tai mata bata amsataba.
Ita dama batasa ran yau Ahmed ze shigoba, hausawa sukace jumma'ar da zatai kyau tun daga laraba ake ganeta, ita din ma tun adaren jiya tai noticing haka kuma segashi yatabbata.
Bedroom din ta ta koma tai sallahn athuba, bayan ta idar takama karatun alqur'ani kamar yanda tasaba, tana cikin yin azkar segashi suduka yarannata guda hudu sun shigo.
Duƙawa sukayi suka gaidata suna karema dakin kallo cikin rashin sabo, tun tasowar su tare suke ganin Mami da Abba amma ayau babu Abba se Mami kaɗai.
Kamar yanda suka saba fitowa sukayi daga dakinnata.
Khadijah tadauko tsin tsiya da parker tai kaye kayen abinda ba za'a rasaba tasoma shara.
Khalid ya kunna karamar gas yasa ruwan wanka.
Zainab ta fito da dankalin da zasu karya dashi Ramlat ta zauna tasoma ferewa.
Anis yadauki tsin tsiyar kwa kwa yatafi tsakar gida yakama shara.
Kan kace me sun kammala komai,
Bakajin komai se ƙamshin tiraren wuta dana jikinsu.
A dining suka zauna bisa ƙaramar carpet suna karyawa.
Anis yakalli inda Ahmed yake zama a kodayaushe seyaji kewa da rashin sabo sun lullubeshi kamar dai sauran yan uwanshi.
Yakalli Zainab da idon tambaya yaname cewa
"Mami Abba baya nanne?..."
Kafin tasamo abin cewa taji muryan Khadijah ta amsa shi
"Abba na dakin amaryan shi....bazai zo wurin muba dama haka kawata da muke islamiyya tace indai Abban mu yaƙara aure to baze ƙara kula muba saboda suma haka Babansu yai..."
"Khadijah...."
Zainab takira sunan cikin kakkau sar murya tana watsa mata harara.
Dasauri Khadijah ta sun kunyar da kanta tana bata haƙuri.
"Kiya hakuri Mami...."
"don Allah Mami Kiya hakuri bazan karaba...."
Tasake fadi batareda taɗago kai takalli Mamin nasuba.
"Kada ki ƙara"
Zainab tafaɗi a takaice.
Dakin ye wani irin shiru naban mamaki yayinda hayaniya yakaure tsakanin zuciyar Zainab da ƙwaƙwalwarta.
Kalaman da suka fito daga bakin Khadijah ne suka janyo wannan hayaniyar.
Zuciyarta tayi imanida Ahmed baze taba juya mata baya kamar yanda sauran maza sukema matayensu ba.
Ƙwaƙwalwarta tace ba haka ba, tunda ya muna fun ceta ya auri aminiyarta to ba abinda baze iya aikata mataba arayuwa.
Tun yaran basu fahimci Zainab bata tareda suba har suka fahimta saboda juya spoon kawai take yi a plate batareda takai soyayyen dankalin bakin taba.
Ayan zuma magana suke ta mata amma batajiba.
Khalid yahaɗe tafukan hannayen shi awuri guda yatafasu asaitin fuskar Zainab.
Tai firgi git kamar wacce aka radama faskare a tsakiyar gadon baya, tasauke wani nan nauyar ajiyar zuciya mai sauti.
"Mami are you okay"
Kai taɗaga ma Khalid alamar Eh
Yaɗan kura mata oily eyes din shi kalan na Ahmed yana sake tambayar ta kamar mai niman tabbaci akan amsar da tabashi.
"Kin tabbata?"
"Na tabbata .....kutafi kar ku makara"
Ramlat ce taɗan ran kwafo ta rungume ta tana murmushi.
Sauran sukai mata sallama suka fice, har sun kai bakin kofa Khalid yajuyo ya kalleta.
Zainab tai mai murmushi kalanna uwa mai son birne gaskiyar zuciyarta saboda farin cikin ƴaƴanta.
*USTAZ RAYYAN*
Ustaz Rayyan ya buɗe idanunsa a hankali yana ƙoƙarin ɗaga kansa daga kan matashin kai, amma jikinsa ya ƙi amincewa da shi. Gajiyar jiya ta mamaye kowane sashe na jikinsa. Idanunsa sun yi nauyi, kansa yana juyawa kaɗan, kamar har yanzu hankalinsa yana can cikin hayaniyar bikin da bai daɗe da ƙarewa ba.
Ya lumshe idanunsa na ɗan lokaci.
Sai ya ji...
“Allahu Akbar... Allahu Akbar...”
Kiran sallah.
Nan take ya tuna. Ya yi aure. Ba mafarki ba ne.
Rayyan ya sauke ajiyar zuciya a hankali.
Sai ya miƙe, duk da yadda jikinsa yake nuna masa cewa yana buƙatar ƙarin hutu. Ya nufi bathroom domin ɗauro alwala cikin gaggawa.
Bai yi jinkiri ba. ya fito, yana gyara rigarsa, idanunsa suka sauka kan ƙofar ɗakin Aliya.
Ya tsaya.
Kamar yadda ƙafafunsa suka ƙi ci gaba da tafiya, duk da zuciyar sa na ce masa
“Ka tafi masallaci kawai...”
“Ba sai ka tashe ta ba...”
“Wataƙila tana barci sosai. Jiya ta gaji...”
Ya ɗan juya kamar zai wuce.
Amma wani abu a cikin zuciyarsa ya hana shi.
Hakkin Aliya ya hau kansa yanzu. Adaa tana iya zama wata mace a gare shi.
Yanzu kuma...Matarsa ce.
Ba shi ya nema ta zama matarsa ba a wannan lokacin. Rayuwa ce ta zo da shi a haka. Amma yanzu da aka ɗaura musu aure, ba zai iya guje wa nauyin da Allah Ya ɗora masa ba.
Rayyan ya kalli ƙofar na ƴan daƙiƙu. Sai ya taka zuwa bakin kofar.
A hankali ya ɗaga hannunsa ya yi knocking sau ɗaya. Ya ɗan ja baya yana jiran amsa.
A cikin ɗakin. Aliya dake kwance ta buɗe idanunta da ƙyar. Kanta ya yi nauyi. Jikinta ya yi mata nauyi.
Gajiyar bikin jiya ta haɗu da gajiyar tunani da ruɗanin shiga sabon gida, har barci ya kasance tamkar magani da take buƙata fiye da komai.
Da ta sake jin knocking ɗin, ta lumshe idanunta na ɗan lokaci tana shirin cewa
“Waye?”
Wani sashi acikin kanta yatina mata wanda keda alhakin zuwa wurin ta ayanzu.
Ta miƙe da sauri, duk da yadda jikinta ya yi rauni. Ta gyara doguwar riganta cikin gaggawa, sannan ta nufi ƙofar.
Ta buɗe.
Rayyan yana tsaye a waje. Amma ko kallonta bai yi ba.
Kamar yana tsoron idanunsa su faɗa kan wani abu da zuciyarsa ba ta shirya karɓa ba.
Sai ya ce cikin murya mai nutsuwa:
“Ki je ki yi sallah.”
Kalma guda. Bai ƙara komai ba. Bai jira amsarta ba ya juya ya tafi.
Aliya ta tsaya a bakin ƙofa tana kallonsa har sai da ya ɓace daga gabanta.
Ba ta san me ya kamata ta ji ba. Ta ji kunya..Ta ji wani irin sabon yanayi?! Ta ji kuma kamar wannan gidan ya riga ya fara koya mata cewa rayuwar aure ba ta kama da yadda take gani a mafarkinta ba.
Sai ta rufe ƙofar a hankali. Ta koma ciki. Ta ɗauro alwala.
Ta shimfiɗa sallaya. Ta tsaya agaban Allah.
A lokacin da ta ɗaga hannuwanta domin takbira, hawaye guda ya gangaro a gefen idonta.
Ba don tana baƙin ciki ba. Amma saboda rayuwarta ta canza.
A wasu lokuta can baya da suka shige yarinya ce a gidan yayarta.
Yau mata ce a gidan mijinta.
Bayan ta idar da sallah, Aliya ta zauna na ɗan lokaci tana kallon hannayenta.
Lallin hannun ta na haskawa ta cikin hasken glops ɗin solar dake dakin. Ta taɓa shi da yatsanta. Sai ta yi murmushi mara ƙarfi.
Wani sabon gida. Wani sabon suna. Wani sabon matsayi. Sabuwar rayuwa.
Ta miƙe.
Ba ta san abin da ya kamata mace ta yi a ranar farko da ta kwana gidan mijinta ba, amma abu ɗaya ta sani...
Ba ta son ta zama baƙuwa a gidan da Allah Ya ƙaddara ya zama nata.
Sai ta fita falo. Gidan ya yi shiru.
Haske kaɗan ne yake ratsawa ta tagogin, yana nuna mata abubuwan da ba ta samu damar lura da su jiya ba.
Ta kalli falon.
Ta kalli kayan gidan.
Ta kalli ɗakin da yake kusa da nata.
Sai ta fara gyara. Ta ɗauki tsintsiya. Ta fara sharewa a hankali.
Ba don akwai datti mai yawa ba. Sai don tana son ta ji cewa tana da amfani a wannan gidan.
Ta goge tebur, ta shirya wasu abubuwa, Daga nan sai ta nufi ɗakin Rayyan.
Ta shiga. Ta gyara gadon. Ta tattara wasu kayan da suke gefe. Ta goge inda ya kamata.
Ta gyara littattafan da ke kan tebur ɗinsa.
Duk abin da ta taɓa, tana yi ne cikin tsananin kulawa.
A ranta tana cewa:
“Duk da ban san yadda wannan aure zai kasance ba... zan yi ƙoƙarina na zama matar da ba za ta zama nauyi ga mijinta ba.”
Ta gama ta fito asannan gari ya fara haske.
A ranta taji ya kamata ta shiga ta gaida Ummu da sauran mutanen dake gidan tunda har yanzu akwai raguwar mutane ƴan biki.
Ta gyara hijabinta sosai sannan ta nufi sashin su
A can kuwa, Ummu tana zaune tare da sauran mutane daniginta dana Abba waɗan da basu tafi jiyaba sai yau.
Tun daga bakin kofa take gaida mutane suna amsa wa cike da fara'a, wasu sudan jata da wasa musamman waɗanda suke matsayin kakanni agareta sedai tana bada baya za'a soma magana akan yayarta Jamila tareda aibata ta.
“Assalamu alaikum.”
Ummu ta ɗago kai daga inda take zaune acikin falon ganin Aliya ya sanya murmushi bayyana a fuskarta.
“Wa alaikumussalam, Aliya. Ki shigo.”
Aliya ta shiga cikin ladabi, Ta zauna kusa da ita.
Ummu ta kalle ta ɗan lokaci kamar ba wadda take kallon suruka ba.
Sai kamar uwa take kallon sabuwar ɗiyarta.
Gaisawa sukayi inda Aliya keta sun kuyar da kai a kunyace.
Ummu ta yi murmushi kawai tana kara kallon ta akaro na ba adadi zuciyar ta nakara na tsuwa tare da jin gamsuwar sai ayanzu Rayyan zai san menene aure.
Kamar yadda mutanen dakin keta sanya musu albarka tare da fatan alkhairi agaresu da auren nasu gabadaya.
“Allah ya miki albarka, Safeena. Kin samu suruka mai mutunci.”
“Wallahi Ustaz Rayyan mutum ne mai kunya da nutsuwa. Allah ya ba ku zaman lafiya.”
“Allah ya sa ya zama alheri a gare ki, ya kuma sa ki zama alheri a gare shi.”
Aliya ta yi murmushi kawai, tana sunkuyar da kai.
Duk lokacin da aka ambaci Rayyan, sai zuciyarta ta buga da wani irin sauti da ita kaɗai take ji.
Ta kasance ɗalibarsa.
Ƙanwarsa a idon mutane.
Yanzu kuma… matarsa.
Har yanzu kalmar matarsa tana mata nauyi idan ta faɗo a cikin zuciyarta.
Ta ɗan ɗago kai, murmushi mai kunya ya bayyana a fuskarta.
“Amin,” kawai ta iya cewa.
Sai wata daga cikin matan dake matsayin kaka awurin Rayyan ta taɓa kafadarta cikin wasa.
“Ke dai kin yi sa’a. Ki kula da shi, ke ce yanzu amaryarsa tunda kin ƙwace min Shi"
Aliya ta sake sunkuyar da kanta.
Amma a cikin zuciyarta ta yi wata addu’a mai sauƙi:
Ya Allah, ka sa ni in zama abin da zai ƙara masa farin ciki, ba abin da zai ƙara masa nauyi ba.
Bayan wasu lokuta, Aliya ta koma sashinsu.
Tana nan zaune ita kaɗai, sai aka kawo mata ruwan wanka da abincin karyawa daga gidan su kamar yadda al'adan su take.
Ba tare da wani ɓata lokaci ba ta shiga tai wanka, ta fito ta kimtsa cikin wata abaya honey color dama tun asali batason kaya masu nauyi, daga kayan sallah kuwa har ankon biki takance ma Baba Abaya ko material tun Ummi na mata fada akan ajiye kaya kullum kala daya ba sauyi har ta daina, daga baya da tazama tailor sai yazama din kunan nata simple gown ne masu designs kala kala mara hayaniya da ɗaukan hankalin jama'a.
As usual ta sanya tirare tai simple make-up tafito falo ta zauna kewa na dabai bayeta hakan yasa ko abin cin da aka kawo bata kallaba.
Muryarsa mai zurfi tasoma jii yana sallama tukuna yashigo.
Fuskarsa babu yabo, babu fallasa. Babu murmushin da ta saba gani, babu kallon da zai nuna cewa akwai wata sabuwar mace a cikin gidansa.
Ta amsa sallamarsa cikin ladabi.
“Wa’alaikumussalam.”
Bai ko kalle taba yawuce dakinsa.
Aliya ta bi shi da ido har ya ɓace a bayan kofar dakinsa da yashiga, Jikinta ya yi sanyi.
Ta ji kamar an zuba mata ruwan sanyi a cikin zuciya.
Ko yana jin nauyin kasancewar ni a nan ne?
Ta sauke numfashi a hankali Sai kuma wani tunani ya kutso mata.
Amma ai ba Ni nakawo kai na ba, Ta girgiza kai “Aliya, ki yi haƙuri,” ta faɗa cikin zuciyarta.
Wani abune ya haska acikin kanta, akwai wani abu guda da ta sani game da Rayyan.
Ba ya jure yunwa.
Daga cikin abubuwan da suka fi hargitsa shi a duniya, yunwa tana daga cikin na farko.
Yana girmama abinci.
Idan ya ji yunwa, ko da yana cikin damuwa, sai yanayinsa ya sauya.
Kuma yanzu… Ta san bai ci komai ba.
Ta kalli abincin da aka kawo mata. Sai ta kalli ƙofar ɗakinsa.
Zuciyarta ta ƙara nauyi, bata san lokacin da ta miƙe ba seda taji ƙafafuwanta sun fara takawa suna tafiya dan kansu batareda sun tsaya niman zaɓin zuciyar taba.
Ta bi hanyar ɗakin Rayyan a hankali, kamar wadda take tsoron ko ƙarar takunta za ta bayyana sirrin zuciyarta.
Sai ga ta a bakin ƙofarsa.
Ta tsaya. Ta yi shiru. Ta ɗaga hannu da niyyar ƙwanƙwasa wa tasauke.
Ta sake ɗagawa.
Sai ta ƙwanƙwasa a hankali.
“Assalamu alaikum…”
Muryarta ta fito da rauni har ita kanta ta kasa gane ko ita ce ta yi maganar.
Taji shiru ba'a amsaba har wasu daƙiƙu suka ja, atinanin ta ko baiji bane takara bude baki da niyyar kuma yin sallama sai aka buɗe ƙofar.
Rayyan ya bayyana.
Idanunsa a lumshe, fuskarsa babu annuri.
Ya kalle ta.
A karo na farko tun bayan daurin aurensu, idanunsa suka haɗu da nata kai tsaye.