ƘYAURE KARIYAR GIDA

BOOK ONE CHAPTER FOUR

by @hindatuauwal

Aliya ta hadiye yawu mai kauri. Kallo ɗaya kacal ta yi masa amma takasa dauke idanunta akanshi wani abu da batasan ko meyeba na karyewa acikin zuciyar ta.


Bata son ganin wannan ciwon dake kwance akan fuskarsa, bata son heart broking ɗin dake kwance a ƙasar idanuwansa, hatta wannan numfashin nasa dake fita ahankali ƙirjinsa na ɗagawa da nauyin rashi bata son gani, lastly matsayin ta da take hangowa asamada komai.

Ta ji zuciyarta ta matse.

Wannan ba shi ne Ustaz Rayyan ɗin da ta sani ba.

Ba wanda ta saba gani yana koyarwa cikin natsuwa ba.

Ba mutumin da kullum yake ɗaukar nauyin wasu ba.

A gabanta yanzu akwai wani mutum da yake ƙoƙarin ɗaukar nauyin kansa shi kaɗai.

Ta ɗan runtse ido, sannan ta ce a hankali

“Ka zo ka karya…”

Ta yi ɗan shiru.

“An kawo abinci.”

Rayyan bai motsa ba. Sai ya amsa da gajeriyar murya.

“Ban ci.”

Kalmar ta sauka a zuciyarta kamar dutse.

Ta ɗago ido. A wannan karon ta kalle shi sosai, ba wai don tana son yin hakan ba.

Sai dai saboda zuciyarta ta ƙi barin ta kau da kai.

Ta nazarce shi. Sai ta ga abin da ba ta taɓa ganin sa a fuskar Rayyan ba.

Rauni!

A lokacin ne ta fahimci wani abu.

Wataƙila shi ma bai san yadda zai yi da wannan sabon matsayi ba.

Wataƙila shi ma yana jin tsoron wannan sabuwar rayuwar.

Wataƙila shi ma yana fama da abin da itama take fama da shi.

Sai zuciyarta ta yi wani irin ƙarfi.

Ni ba zan zama baƙuwa a cikin gidana ba.

Ba zan bari kunya ta hana ni zama matarsa ba.

Ba zan bari al'ada ta sa na tsaya ina kallonsa yana wahala ba.

Zuciyarta ta numfasa da alƙawarin sai ta sauya duk wannan, Shi da Ita sai sun saba, sai sun gina kyakkyawan alaƙa mai cike da tarihi, se sun sanya abinda ake ganin bazai yiwuba ya yiwu da yardan Allah.

Ta gyara tsayuwarta.

Idanunta suka cika da wani irin ƙarfin hali da ba ta san tana da shi ba.

Sai ta ce cikin murya mai laushi, amma babu sassauci a cikinta:

“Idan ba ka ci ba… Ni ma ba zan ci ba.”

Ustaz Rayyan ya ɗago kai.

A karo na farko, mamaki ya bayyana a idanunsa.

Ya kalleta na wasu daƙiƙu.

Aliya kuwa ba ta kau da kanta ba. Zuciyarta tana bugawa da ƙarfi, Ƙafafuwanta suna ɗan rawa, Amma ba ta ja da baya ba.

Ustaz Rayyan ya ɗan buɗe baki kamar zai yi magana sai ya yi shiru, magan ganun abokin sa Khalid ɗazu da suka hadu na dawo mai.



"Yanzu saboda an ɗaura maka aure da Aliya ne kake wannan damuwar?"


Sanin Rayyan ba zai bashi amsa ba yasan yashi cigaba da magana 


"Ita wacce ka ke niman kashe kanka akanta tana can gidanta cikin farin ciki, kasani sedai nakara tina maka idan ka cutar da zuciyar Aliya saboda wata banzar zuciyar ka to Allah ba zai bar kaba"


Jikin shine yai sanyi, zuciyar shi na karyewa da tsoron Ubangiji dan duk abinda Khalid yafadi mai gaskiyane saboda Aliya ta tashi aduk wani matsayi dayake kallon ta dashi ada, itadin matarsa ce, tanada haƙƙi akan komai nasa.

Ya sauke idanun sa akanta yana kiranta da muryarsa mai zurfi.

“Aliya…”

Ta amsa da sauri:

“Na’am?”


“Dagaske Ki keyi?”

Ta yi shiru na ɗan lokaci.

Sai ta gyada kai.


Sai ya matsa gefe kaɗan, yana nuna mata hanyar wuce wa.

“Mu je.”

Aliya ta ɗan tsaya. 

“Zamu ci?”

Ya gyada kai.

“Zamu ci.”

Sai ta yi murmushi aranta tana furta"wannan shine zai zama farkon tafiyar mu ahanya guda!".

Rayyan ya rufe ƙofar ɗakin su biyun suka nufi wajen abincin…dake falo, ba tare da sanin cewa wannan ƙaramin cin abinci tare ba, zai zama farkon wani abu da zai sauya yadda kowannensu yake kallon ɗayan ba.

Domin wani lokaci…

ba manyan kalamai ne ke gina gida ba.
Wani lokaci, gida yana farawa ne da abokin zama yanuna ma abokin zaman sa kulawa.



Shiru ya mamaye ɗakin.

Aliya ta zauna ne a gefen Rayyan tana kallon yadda yake cin abincin da ta zuba musu da hannunta. Ba ta ce komai ba, sai dai a duk lokacin da ta ɗaga idanunta ta kalleshi, wani irin kunya da fargaba sukan mamaye fuskarta.
Sabuwar rayuwa ce a gareta.
Sabon gida.
Sabon miji.
Sabuwar duniya wadda har yanzu zuciyarta take ƙoƙarin fahimta.

Ta ɗan motsa cokalin da ke hannunta, tana jiran ko zai ce mata wani abu.

Sai kawai Rayyan ya ɗaga hannunsa a hankali, ya ture farantin da ke gabansa kaɗan. Alamar ya koshi.

Aliya ta tsaya kallonsa na ƴan daƙiƙu. A zahiri, kamar za ta yi magana.

Lebenta ya motsa kaɗan...Sai ta yi shiru.
Ta sauke idanunta kan abincin da ke gabanta.

“Ko bai ji daɗin abincin ba ne?”

Tambayar ta taso a zuciyarta, amma ta kasa furta ta.

Ba ta so ta tilasta masa.

Ba ta so ya ji kamar tana matsa masa akan yayi abinda baiyi niyya ba.

Sai ta yi wa kanta murmushin da ba kowa ya gani ba.

“With time komai zai daidaita... Ai ba yau zaman mu zai zo ƙarke ba. Zai saba da ni... ni ma zan saba da shi.”

Ustaz Rayyan ya miƙe daga wajen cin abincin ba tare da ya ce komai ba.

Aliya ta ɗaga kai ta kalleshi.

Ya ɗauki wasu ƴan matakai zuwa ɗakinsa, sannan ya shige.

Ta bi bayansa da kallo har ƙofar ɗakin ta rufe.

Sai numfashinta ya sauka a hankali. Ta dawo da hankalinta kan abincin da ke gabanta, ta ci gaba da ci.

Amma duk da tana cin abincin, zuciyarta ba ta nan.

Tana can... A bayan ƙofar ɗakin Rayyan.
Tana tunanin mijinta.

Tana ƙoƙarin fahimtar mutumin da Allah Ya haɗa rayuwarta da shi.

Bayan ta gama cin abincin, ta tattara kayan wajen cin abincin sannan ta shiga cikin gidan.

Sashin su Ummu ta shiga, bata damu da kallon da mutane suke mataba ko magan ganunsu akanta sedai takan gaida duk wanda ta hadu dashi.


Kai tsaye wurin Baba Nafisa yayar baban su tanufa bayan ta tambaya inda take an gaya mata tana kitchen.



Ai kam acan ta ganta suna girki, sanin batada hayaniya yasan yata gaya mata ruwan wanka take so zata bama Ustaz Rayyan, nan take tabata dai dai wanka tai mata godiya ta ɗauko ruwan.


Kai tsaye ta nufi ɗakin Rayyan. A duk matakin da take ɗauka, zuciyarta na bugawa da sauri.


Ta isa bakin ƙofar. Ta tsaya. Ta ja numfashi a hankali.

Sai ta yi sallama.

“Assalamu alaikum.”

Daga cikin ɗakin aka amsa mata da murya mai sanyi.

“Wa alaikumus salam.”

Aliya ta tura ƙofar a hankali ta shiga.

Ustaz Rayyan na kwance. Da ya ji motsinta, ya ɗan juyo kansa ya kalleta.

Aliya ta shiga da ruwan wankan. Ta ajiye shi a inda ya dace.

Sai ta juyo ta fito daga bathroom din ta tsaya agaban sa kadan wurin dressing mirror, ta kalli Rayyan fuskarta cike da kunya.

Amma a cikin idanunta akwai wani irin kulawa da ba ta iya ɓoyewa.

Sai ta ce cikin sanyin murya:

“Ga ruwan nan na kawo maka... ka tashi ka yi wanka.”

Ta faɗi hakan ne ba tare da ta ɗaga idanunta sosai ba.

A zuciyarta kuwa ta riga ta shirya cewa watakila ba zai amsa ba.

Watakila zai yi shiru kamar yadda ya yi lokacin cin abinci.

Don haka ta juya da niyyar fita har ta kai bakin ƙofa hannunta ya riga ya kai kan handle ɗin ƙofan zata fita sai muryar Rayyan ta dakatar da ita.

“Na gode.”

Aliya ta tsaya cak.

Kamar ba ta yi tsammanin za ta ji wannan kalmar ba.
A hankali ta juya, idanunta suka haɗu da nasa.

Sai wani ɗan ƙaramin murmushi ya bayyana a fuskarta.

Murmushin da bai da hayaniya. Murmushin da ya fito daga zuciyar da ta samu ɗan haske bayan dogon tunanin da take yi.

Ta ɗan sunkuyar da kanta.

“Babu komai.”

Ta fita ta rufe ƙofar.

A wannan karon kuwa, murmushin da ke fuskarta bai ɓoye ba.

Ta zauna akan kujerar zuciyarta na cewa:

“Ya ce na gode...”

Ƙaramar kalma ce, Amma a gareta...ta kasance kamar babbar ƙofa da aka fara buɗewa.

Domin a farkon zaman aure, ba kowace magana ce ke gina gida ba.

Wani lokaci...ƙaramar kulawa ce. Wani lokaci...ƙaramar godiya ce..Wani lokaci kuma...murmushi guda ne kawai.

Amma idan zuciya tana da haƙuri, ƙananan abubuwa kan zama manyan ginshiƙan soyayya.

Aliya ta ci gaba da zama, tana murmushi a hankali.

Ba ta san abin da gobe za ta kawo ba.

Ba ta san ko Rayyan zai fara saba wa da ita ba.

Ba ta san ko wannan sanyin da ke tsakaninsu zai narke nan da nan ba.

Amma abu ɗaya ta sani...ba za ta gaji da ƙoƙarin gina gidanta ba.

Domin ta fahimci cewa gida ba bango ba ne.

Gida zuciyoyi ne.

Idan zuciya ta yi haƙuri...tausayawa da kulawa, kuma ta san lokacin da za ta yi magana da lokacin da za ta yi shiru...to ko gida ya fara da sanyi, wata rana zai iya ɗaukar zafi na soyayya.

Aliya ta zame ta kwanta ta sake yin murmushi.

“Ya ce na gode...”

Ta maimaita a zuciyarta.




*JAMILA*

      6:30am

Jamila ta buɗe idanunta, sai ta ji kamar idanunta ma sun gaji da ita.

Ta yi ƙoƙarin ɗaga murfin idanuwanta, amma sai ta sake rufe su a hankali.

Kuka!

Shi ne abin da ya mamaye daren da ya gabata.

Kukan da ta yi har ta ji kanta ya yi nauyi, idanunta suka kumbura, jikinta kuma ya yi mata wani irin raɗaɗi mai wahalar fassara.

Ta sauke numfashi a hankali.

Hannunta ya kai ga gefen gadon, ta yi ƙoƙarin tashi.

“Ahh…”

Ta furta sautin tana dafe kanta.

Jikinta har yanzu yana ciwo.

Ba wai ciwon rashin lafiya ba ne kawai. A’a. Akwai wani irin raɗaɗi da ya mamaye jikinta saboda tsananin buƙatar kusancin mijinta da take ji, ba ta taɓa sanin cewa sha’awar miji za ta iya kai zuciya da jiki irin wannan hali ba.
Sai dai a daren jiya…

Ta ji kamar zuciyarta tana son wani abu da ba ta iya samu.

Ta juya ta kalli gefen gadon, babu kowa, fuskar Samir ta dawo mata a zuciya.

Ta haɗiye yawu. Sai ta kawar da tunanin.

Da ƙyar ta sauka daga gadon, ta shiga bathroom.

Bathroom ɗin kuwa, kamar wani a ƙasashen ƙetare, duk yawace yawacen ta bata taɓa ganin irin saba, a tv kawai take gani cikin fina-finan ketare.

Duk inda idanunta ya sauka, akwai abubuwan alatu da kansa zuciyar ta nitsewa a ƙirjinta.

Madubai masu girman gaske, fitilu masu laushi, tawul masu laushi da aka jera cikin tsari, turaren wanka daban-daban, da kayan gyaran jiki da suka cika wani gefe na bayin.

Jamila ta tsaya gaban madubi na ɗan lokaci.

Fuskarta ta nuna gajiyar daren jiya wanda ke kwance akasan zuciyar ta.

Ta taɓa kumatunta.

“Jamila…!”

Ta furta sunanta a hankali kamar tana magana da kanta.

Sai ta shiga wanka.

Ta yi wankan tsarki cikin nutsuwa, tana ƙoƙarin share duk wani nauyin da ya rataya a zuciyarta.

Lokacin da ta fito, sai ta tsaya gaban madubi.

Duk yawace-yawacen da ta yi a rayuwarta, duk manyan gidaje da ta gani, duk matan da suka yi mata kwalliya a wurare daban-daban…
Ba ta taɓa ganin kanta cikin wannan irin yanayi ba.

Ta shafa man jiki mai tsada wanda ƙamshinsa ya cika ɗakin da wani ɗanɗano mai daɗi.

Ta shafa wani cream mai laushi a fuskarta, sannan ta ɗauki wani ƙaramin kwalban turare.

Ta feshe kaɗan a wuyanta, Fsss…Kamshin ya tashi a hankali.

Sai ta murmusa.

Tana son kwalliya mai kayatarwa, kullum tana son komai ya kasance cikin nutsuwa, amma a bayyane yake cewa duk abin da ta sa ba ƙaramin kuɗi aka kashe wajen samunsa ba.

Ta gyara gira cikin salo mai sauƙi. Ta shafa foundation mai laushi wanda ya yi daidai da fatarta, ta ƙara ɗan haske a kumatunta, sannan ta shafa lipstick mai launin da bai yi hayaniya ba.

Ta gyara gashin kanta cikin tsari mai kyau.

Daga nan ta buɗe wardrobe.

Tufafin da ke ciki suka yi mata caa kamar suna jiran zaɓinta.

Ta tsaya tana kallonsu.

Daga ƙarshe ta zaɓi wata doguwar riga mai tsada, wadda aka yi mata ado da ƙananan duwatsu masu sheƙi. Launinta ya yi mata matuƙar kyau, ya ƙara bayyana hasken fatarta dake shining yana wani irin glowing mai fizgar zuciya.


Ta saka agogon hannu. Ta ƙara wani ɗan turaren oil ajikinta.

Sai ta tsaya gaban madubi.

Wata kyakkyawar mace ce ta bayyana a gabanta, mai cikar kyau, zati da haiba, uwa uba kuma gayu.

Amma…

Idan mutum ya kalli idanunta sosai, zai ga abin da kwalliyar ba za ta iya ɓoyewa ba.

Damuwa!

Da wani abu mai zurfi da ita kanta ba ta san sunansa ba.

Ta fito daga ɗakinta, ta nufi dining. Da ta isa, sai ta tsaya na ɗan lokaci.

An shirya mata abinci kala-kala, Kusan nau'i biyar ne.

Akwai abubuwan karin kumallo daban-daban, kayan marmari, abin sha, da wasu kayan abinci da aka shirya cikin tsari mai kyau.

Ta kalli komai, sai ta zaɓi guda ɗaya mai akinta ta zuba mata a plate.

Ta zauna, ta fara ci a hankali da wani irin nisantaccen yanayi atare da ita.

Lokaci-lokaci tana ɗaga wayarta, Ta duba saƙonni, Ta sake ajiye ta. Ta ɗauka. Ta sake dubawa. Zuciyar ta danƙare da tsammanin ganin kira ko sako daga Samir.



Bawai dan taƙoshi ba ta ture abincin, ta mike tadawo falo tazauna idanunta suka koma kan talabijin da ke gefen ɗakin.

Amma babu abin da ke shiga zuciyarta.
Jikinta har yanzu yana amace saboda wani wutan sha'awa dake cii aduk wani sassa na jikinta.